Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin Daukewar Jinin Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya kara ma Mallam Basira. Malam tambaya ta a kan jinin haila ne. Malam an ce alaman da ake gane karshen haila shi ne idan jinin ya canza kala zuwa ruwan kasa. Na ga alaman hakan Se na yi wankan tsarki Bayan haka Se kuma ya cigaba da zuba na kwana biyu Malam tsarkin nawa yayi? Yaya matsayin sallah da azumi? Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To 'yar'uwa abin da na sani daga malaman fiƙhu shi ne: Ana gane daukewar jinin haila ne ta hanyoyi guda biyu:

1- Kekasar kasanki- Ta yadda mace za ta ga gabanta ya bushe ko kuma tsumma ko always ɗin da ta tare jinin da shi.

2- Fitowar farin ruwa bayan ɗaukar lokaci ana haila.

Idan jininki ya koma ruwan kasa kafin ki ga ɗaya daga cikin waɗannan alamomi guda biyu, to ba ki gama haila ba, kuma ba za ki ɗauki hukuncin masu tsarki ba, don haka azuminki da sallarki ba su yi ba.

Idan kika ga ruwa mai kama da kasa bayan ɗaukewar jinin haila, to ba zai cutar da tsarkin da kika samu ba, kamar yadda hadisin Bukhari daga Ummu Addiya ya tabbatar da hakan.

Don neman karin bayani duba: Addma'uddabi'iyya shafi na: 14

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments