Ticker

6/recent/ticker-posts

Assalamu alaikum. Shin Ya Halatta Na Ba Wa Iyaye Na Zakkar Fidda Kai?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Shin Ya Halatta Na Ba Wa Iyaye Na Zakkar Fidda Kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

وعليكم السلام ورحمة الله.

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Malamai sun yi ittifaaƙi a kan cewa bai halatta ba mutum ya ba da zakkatul mafrud (Kamar zakkar fidda kai) ga waɗanda nauyinsu ya rataya a wuyansa, kamar Iyaye da 'ya'ya.

An fada a cikin Al-Mudawwanah (1/344): Toh zakkar dukiya ta fa, su waye bai halatta Na bawa ba abisa ra'ayin imam malik??.

Yace; Malik ya ce: Karka bada ita ga duk wani ɗan'uwanka wanda nauyinsa yake akanka.

Al-Shaafa’i yace a cikin Al-Umm (2/87): Bazai bada (Zakkar dukiyarsa) ga Mahaifinsa ba ko Mahaifiyarsa ko Kakansa ko Kakarsa ba.

Ibn Ƙudaamah (rahimahullah) yace a cikin Al-Mughni (2/509): Babu daya daga cikin Zakkah ta farillah da za a bawa Iyaye komai nisan nasabarsu (ma'ana Kakanni maza da Kakanni mata) ko 'Ya'ya komai Nisan nasabarsu (ma'ana Jikoki).

Ibn Mundhir (rahimahullah) ya ce: Malamai sun yi ittifaaƙi a kan bai halatta ba abawa iyaye zakkah ba, a yanayi na kasancewar nauyinsu ya rataya a wuyansa. Saboda haka basu zakkah tamkar shi ne ya bawa kansa zakkah da kansa. Basu zakkah kamar Yana nufin su basa bukatar taimakon komai a wajensa ne, kuma babu nauyinsu na dawainiyarsu a wuyansa.

والله أعلم،

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments