Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda-Kai

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Don Allah tnbayata ita ce kamar hatsinda ake badawa ranar Sallah na fidda-kai duk mutun ɗaya mudu nawa garai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Sahabin Manzon Allah (SAW), Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.”

Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abun da za su ci a lokacin Karamar Sallah

 YADDA AKE FITARWA:

Mutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda yake ciyarwa kamar mata, ’ya’ya da ma’aikata da sauransu idan Musulmai ne.

Manzon Allah Ya wajabta fitar da zakkar kono ga babba da yaro, ’yantacce da bawa, daga cikin waɗanda kuke ciyarwa,” kamar yadda Abdullahi bn Umar ya ruwaito a Hadisi.

Mai fitar da zakkar zai fara ne da fitar wa kansa, sannan sauran mutanen gwargwadon wajibcin ciyar da su a kansa.

 ADADIN DA AKE FITARWA:

Kowanne mutum ɗaya za a fitar masa da Sa’i ɗaya, wato Mudun Nabi Huɗu. Idan babu Sa’i ko Mudun Nabin awo, ana iya aunawa da hannu. Malamai sun ce Mudun Nabi ɗaya daidai yake da cikin tafin hannu biyu na matsakaicin mutum.

 ABIN DA AKE FITARWA:

Ana fitar da zakkar kono ce daga nau’in danyen abincin mutanen garin.

 Ana fitarwa ne daga abin da ya karu a kan abincin rana da yinin mai fitarwa da iyalansa a lokacin.

 LOKACIN FITARWA:

Malamai sun bayyana cewa ya halalta a fitar da zakkar tun daga ranar 28 ga Ramadan.

Hadisi ya nuna, “Abauullahi bn Abbas kan ba da ita da kwana daya ko kwana biyu kafin ranar Sallah.” Amma tana wajaba ne daga safiyar ranar Karamar Sallah, a kuma gama kafin Sallar Idi. Wanda ya bayar kafin sallah to zakka ce karbabbiya, wanda ya bayar bayan sallah kuma to sadaka ya bayar kamar sauran sadakoki.”

Malamai sun ce haramun ne a jinkirta fitar da da ita ba tare da uzuri ba.

 WAƊANDA AKE BA WA:

Hadisi ya nuna miskinai ake bai wa. Wasu malamai na ganin ana iya ba da ita ga sauran mutanen da ake ba wa zakkar farilla (bayi, matafiya, masu bashi a kansu, masu aikin karbar zakka, masu aikin fisabilillahi, waɗanda ake kwadayin su musuluntar).

Wanda aka ba wa zakkar shi ma zai fitar, idan har an samu ragowa.

WALLAHU A'ALAM

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments