Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba na sha'awar mace sai namiji, mene ne mafita?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum, Mallam ina da tambaya kuma zan ji dadi idan za a iya amsa mun. Mallam mutun ne balagagge namiji, tun lokacin da ya malliki hankalin shi yasan cewa yana cikin matsala, amma ya rasa inda zai danganta matsalan saboda ya daure masa kai. Bai taɓa kawo son mace a zuciyan shi ba ko sau ɗaya, baya taɓa sha'awar mace illa namiji kamar shi...wannan ba saboda yana kallon batsa ba ne ko kuma yana tare da marasa imanin mutane ba.a'a tun yana karami ake fada masa, cewa yakan daukan dankwali ya ɗaura, yanayin sa ma kamar mace yake yi. muryan shi ma idan ba kasan shi sosai ba sai ka dauka mace ce magana, abun yana damun sa sosai, ya kai ga idan ya yi barci ya yi mafarki da maza yake yi wato saduwa har maniyyi ya fita. Toh mallam yanzu ya rasa yadda zai sa kanshi. wannan wace irin matsala ce? Kuma wani hanya za a bi wajen samun shifa'a?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

To Ɗan'uwa tabbas ka haɗu da babbar musiba, sai dai akwai shawarwari da nasihu kamar haka:

1. Ka rinka yawaita istigfari, saboda yana warware matsaloli, sannan sha'awar maza tana kaiwa zuwa ga LUWAƊI, Allah ya hallakar da al'uma kacokan saboda suna aikata LUWAƊI.

2. Ka dinga yawaita addu'a a lokutan da ake amsar roko, kamar cikin sujjada da ƙarshen dare, saboda Allah zai iya karɓar kukanka, ya kare ka daga wannan fitinar.

3. Duk lokacin da tunanin namiji ya zo maka a zuciya ka yi ƙoƙari wajan kautar da tunanin zuwa wani abu daban mai amfani.

4. Shagaltuwa da ayyukan alkairi na taimakawa wajan kaucewa Alfasha.

5. Tuna azabar Allah da girmansa, suna taimakawa wajan barin saɓo.

6. Kada ka dinga kwanciya bacci, sai lokacin da ka tabbatar kana jin bacci, saboda tunane-tunane suna yawan zuwa a wannan lokacin.

7. Nisantar abokan banza yana gyara halaye.

8. Nisantar cakuduwa da maza zai taimaka maka wajan rashin sanya su a rai.

9. Yawaita karatun Alƙur'ani na nisanta mutum daga Shaiɗanu, waɗanda suke juya dabi'ar mutum.

Tare da cewa akwai mutanen da Allah yake halitta suna da siffofin mata sai dai ya wajaba ka yi iya bakin ƙoƙarinka wajan nisantar kamanceceniya da mata, saboda Annabi S.A.W ya la'anci namijin da yake kamanceceniya da mata, a hadisi mai lamba ta:5546 a Sahihul Bukhari, sifar da ka yi iya bakin ƙoƙarinka ta ki canzuwa, to Allah ba ya dorawa rai sama da abin da za ta iya, kamar yadda aya ta ƙarshe a suratu Bakara take nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments