Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).
Nasiru Lawali
Tarho: 07065701663
Imel: nasirulawali10@gmail.com
Tsakure
Wannan muƙala mai taken “Tasirin Sana’ar Sayar Da Ruwa A
Garin Kwatarkwashi” muƙala ce wadda ta binciko
yadda wannan sana’a take da matuƙar tasiri wajen samar
da tsaftataccen ruwan sha a cikin
garin Kwatarkwashi musamman gida-gida da unguwanni sauran lunguna da saƙo ta
kuma bayyana yadda wannan sana’a take da tasiri ga mutanen garin Kwatarkwashi
wajen samar da ayyukan yi ga maza musamman matasa da yara da manyan maza. Idan
aka nutsa sosai da sosai a cikin wannan takardar, za a ga yadda muƙalar ta bayyana
irin rawar da yara ‘ƴan
mata ke takawa wajen gudanar da wannan sana’a.
1.0 Gabatarwa
Wannan
muƙala mai taken “
Tasirin Sana’ar Sayar da Ruwa A garin
Kwatarkashi” za a gudanar da bincike ne domin a gano tasirin da sana’ar sayar da ruwa ke yi ga masu yinta a cikin garin Kwatarkwashi. Haka kuma, za a binciko tare da taskace yadda sana’ar
take gudana tun tsowan zamanin da ya shuɗe mai tsawo har ya zuwa yau.
Hakazalika, za a yi tsokaci a kan alfanun da wannan sana’ar take samarwa ga masu
yinta da kuma sauran al’ummar garin Kwatarkwashi tare da bayyana irin rawar da
sana’ar take takawa wurin kawo cigaba da kuma raya ƙasar garin Kwatarkwashi da
al’ummarta.
1.1. Maƙasudin
Bincike
Manufar
yin wannan bincike ita ce a yi ƙoƙarin fito da abubuwa da dama domin a nuna wa
al'umma wani abu sabo wanda ba a sani ba, ko kuma an san shi amma ba a fito da
shi a fagen ilimi ba,
domin a ƙara samun haske da fahimtar
wannan sana’ar ta sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi.
Bugu
da ƙari, daga cikin manufar wannan bincike akwai fito da wannan sana’a
ta sayar da ruwa a sarari musamman a ɓangaren
ilimi domin a nazarci wannan sana’a a ilmance tare da taskace ta.
1.2 Ra’in
Bincike
A
yayin gudanar da wannan bincike,
an ɗora shi ne a bisa ra’in da ya shafi ayyukan gargajiya. Wato an ɗora ra’in
wannan bincike a bisa mazhabar gargajiya da kuma zahiranci kasancewar ana sa
ran su ne suka fi dacewa da wannan nazari.
1.3 Dabarun Bincike
A lokacin da aka zo nazarin wannan bincike, an bi wasu dabaru
na manazarta da magabata da dama waɗanda suka gabaci wannan muƙala domin samun
makamar wannan aiki. Kaɗan daga cikin dabarun wannan bincike akwai nazartar
maƙalun da suka gabaci wannan takarda, da ziyartar ɗakunan karatu, da tambayoyi
da kuma neman shawarwarin magabata waɗanta suka rigayemu a irin wannan aiki.
Domin tabbatar da ingancisa tare da samun nasarar kammaluwarsa.
2.0
Ma’anar Sana’a
Yahaya,
(1992) ya ce, " Sana'a hanya ce ta amfani da azanci da hikima da sarrafa
albarkatu da ni'imomin da ɗan'Adam ya mallaka domin buƙatunsa na
yau-da-kullum".
Zarruƙ, (1987) ya bayyana ma'anar sana'a da
cewa, " Wata aba ce da mutum ke yi domin samun abin masarufi wajen gudanar
da harkokin rayuwa na yau-da-kullum".
Zabarina, (1987) ya ce, " Sana'a wata
aba ce da mutum yake yi domin samun abin masarufi wajen gudanar da harkokin
rayuwa na yau-da-kullum".
Ɗangambo, (2004) ya bayyana cewa, "
Sana'a hanya ce ta sarrafa ɗimbin albarkatun ƙasa da dabbobi da abubuwan da ke
hannun ɗan'adam da nufin juya shi ya zama abin buƙata don samun abin rufa ma
kai asiri.
2.1
Rabe-Raben
Sana'a.
Masana
sun rarraba sana'o'in Hausawa zuwa manyan gidaje biyu kamar haka;
A.
Sana'o'in Hausawa na gargajiya
B.
Sana'o'in Hausawa na zamani.
Haka kuma, Ɗangambo, A. (1984). Junaidu da ‘Ƴar’aduwa (2002).
Zarruk, Alhassan (1987) sun ce: a gargajiyance dai, Bahaushe yana da sana’o’i
da dama waɗanda yawansu zai yi wahalar ƙididdigewa. Daga cikin irin waɗannan
sana’o’i akwai manya da kuma ƙanana. Bugu da ƙari, masana sun rarraba waɗannan
sana’o’in zuwa rukuni-rukuni har guda uku kamar haka:
1. Sana’o’in maza
2. Sana’o’in mata
3. Sana’o’in haɗaka ko gamayya ko kuma na tarayya.
Mafi
yawancin sana'o'in Hausawa na gargajiya jinsin maza ne suka kasa suka tsare a
wajen aiwarta da sana'o'in. Amma a wajen sana'o'in Hausawa na zamani, abin ba
haka yake ba domin kuwa akwai waɗanda kowa ke yi, wato na tarayya.
3.0 Sana’ar
Ruwa a Garin Kwatarkwashi
Sana’ar sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi sana’a ce
kamar kowace sana’a ce ta hannu wadda ake gudanar da ita ta hanyoyi da dama ko
kuma hanyoyi daban-daban kama daga daɗaɗɗiyar hanya zuwa hanyoyin zamani.
Sana’ar
sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi ta kasu kamar haka:
a. Sayar da ruwa ta daɗaɗɗiyar hanya ( gargajiya).
b. Sayar da ruwa ta sabuwar hanya (zamani).
3.1 Masu
Sana’ar Ruwa a Garin Kwatarkwashi
Masu sana’ar ruwa
a garin Kwatarkwashi sun haɗa da maza da mata. A ɓangaren maza, sana’ar ta
ƙunshi manya, matasa tsofaffi da kuma yara masu aure da marasa aure. A ɓangaren
mata kuwa, sana’ar ta haɗa da matasa da yara ne kawai. Domin kuwa ba kasafai
ake samun manyan mata suna yin wannan sana’ar ba musamman matan aure da
zawarawa. Bugu da ƙari, yara ‘yanmata su suka fi yin wannan sana’ar musamman waɗanda
ba su ida cimma munzali ba.
wannan hanyar ta ƙunshi sayar da ruwa hanyar amfani da
abubuwan da suka shafi tulu,kwalla, guga ko wasaki, ko kuma amfani da garewani
mai yagiya ko igiya tare da sanda a ɗauka
a kafaɗa a ɗauko ruwa domin sayarwa. Dukkan waɗannan hanyoyi ne da akan yi
amfani da su domin a sayar da ruwa a wancan lokacin da ya shuɗe duk da yake har
yanzu a kan yi amfani da wasu daga cikin hanyoyin a wannan zamanin kamar a
wajen sayar da ruwa ta hanyar ɗibar ruwan da guga ko wasaki a jawo daga cikin
rijiya domin sayarwa.
A
zamanance, ana sayar da ruwa ta hanyoyi a dama. Waɗannan hanyoyin kuwa sun ƙunshi sayar da ruwa ta yin amfani da
matallatan zamani da kuma yadda zamani ya bayar da dama domin aiwatar da
sana’ar a cikin garin Kwatarkwashi kamar ta yin amfani da rijiyar burtsatse ta
hannu tare da haɗa ta da injin domin a zuƙo ruwan a fitar da su zuwa ga mai
baro ya sayar wa al’umma kamar yadda za a gani a zahiri a nan;
3.2 Tasirin
Sana’ar Sayar Da Ruwa A Garin Kwatarkwashi.
Wannan
sana’ar ta sayar da ruwa a cikin garin Kwatarkwashi tana da ɗimbin tasiri mai yawa
domin ko babu komai dai mun san cewa babu wata halitta a doron ƙasa wadda za ta
iya rayuwa ba tare da ruwa ba. Domin ko Bature ya ce; “ water is life” haka
kuma a cikin alkur’ani Allah maɗaukakin sarki yana cewa; “ mun sanya rayuwar kowace
halitta a kan ruwa”. Kaɗan daga cikin
tasirin sana’ar sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi sun haɗa da:
1. Alfanu
ta hanyar addinin musulunci.
2. Alfanu
ta ɓangaren zamantakewa.
3. Ana
samun ɓangaren tattalin arziki.
4. Alfanu
ta sashen kiwon lafiyar al’umma.
5. Sana’ar tana hana mutane zaman banza da yawon banza a
gari.
6. Sana’ar
tana sa a samu abin rufawa kai asiri.
7. Sana’ar
tana hana
abinda ba naka ba
ya tsone maka ido.
8. Sana’ar
tana hana yawaitar ɓarayi.
9. Sana’ar
tana haifar da zumunci mai ƙarfi a tsakanin al’ummar Hausawa da
Waninsu.
10.
Sana’ar ana haifar da auratayya.
1.
Alfanu ta hanyar Addinin Musulunci:
Sanadiyyar wannan sana’a ta haifar da taimakawa zuwa ga
al’ummar da ke zaune a garin Kwatarkwashi ta samar da tsaftattun ruwan sha ,
ibada, abinci, wanka, wanki duk a kyauta ‘fisabilillahi’.
2.
Alfanu ta fuskar Zamantakewa:
Ta fuskar zamantakewa kuwa al’umma suna amfani da ruwa
daga wannan masana’anta domin zubawa itatuwan da aka shuka da dabbobi da
tsirrai musamman masu noman rani, da masu ɗiba domin aikin gina ko gini ko masu
gidajen biredi dake makwabtaka da wannan masana’antar da makarantu da dai
sauransu.
3.
Alfanu ta ɓangaren Tattalin Arziki:
Alfanun wannan sana’ar ta sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi
ga masu ɗauka da baro ko masu mota ya wuce tunanin mai ƙaramin tunani saboda
sana’a ce wadda take ɗauke da ɗimbin rufin asiri idan har aka jure. Ta
sanadiyyar wannan sana’a ta sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi ni ke ɗaukar
nauyin karatuna. Hakazalika, wannan sana’a ta ba ni damar saka yarana shida (6)
a makarantu daban-daban waɗanda nake biyawa kuɗin karatunsu a ƙarshen kowane
zangon karatu. Har ila yau, wannan masana’antar tana tallafawa wurin gudanar da
al’amurran gida na yau da kullum abin sai dai mu ce wuyar aiki ba a fara ba.
4.
Alfanu ta sashen kiwon Lafiya
Wannan masana’antar ta sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi
ta samar da cigaba wurin amfani da tsaftattaccen ruwan sha da sauran nau’in
lalurorin da ake amfani da ruwa domin su, wannan ya haifar da samun sauƙin
cututtuka irin su kwalara wato cutar amai da gudawa, da zazzaɓin cizon sauro da
masassarar taifod wato cuta mai rarake kayan cikin mutum da cutar fitsarin jini
da dai sauran cututtukan da ake iya ɗauka ta hanyar amfani da gurɓataccen ruwan
sha.
4.1 Sakamakon Bincike
A yayin da aka kawo ƙarshen wannan bincike, an samu
nasarar gano abubuwa da dama. Kaɗan daga cikinsu akwai:
1. An gano cewa sana’ar sayar da ruwa garin Kwatarkwashi
tana da tasiri sosai ga maza da mata manya da yara domin samun abin rufawa kai
asiri.
2. An lura da cewa sana’ar tana ƙara samar da tattalin
arziki ga al’ummar garin Kwatarkwashi dama waninsu domin samun saukin rayuwa.
3. An gano cewa sana’ar maza da mata kowa kan yi ta ba
kamar yadda aka sani ba a lokutan da suka gabata.
4. An lura da cewa sana’ar ta ƙara ɗaukar wani sabon zomon
salo, domin yanzu ta kai har an zamanantar da ita ta hanyar yin amfani injina
wurin yin sana’ar da kuma amfani da man fetur wanda a can da ba a san hakanan
ba.
4.2 Kammalawa
Wannan bincike ya yi bayanin abubawa da dama kama daga
tarihin garin Kwatarkwashi, da ma’anar sana’a da ire-iren sana’o’in Hausa. Hakazalika,
bincikn ya tattauna akan masu sana’ar sayar da ruwa a garin Kwatarkwashi ta
hanyoyi mabambata kama daga daɗaɗɗiyar hanyar gargajiya zuwa sabuwar hanyar
zamani.
Har ila
yau bincike ya samu bayyana tasirin sana’ar sayar da ruwa garin Kwatarkwashi. A ƙarshe kuma, an bayyana
sakamakon wannan bincike tare da taƙaitaccen bayanin kammalawa.
Manazarta:
Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancin sa
ga Rayuwa
Hausawa. Kano: Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’
Gidan
Sa’adu Zungur.
Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002).
Harshe da Adabin Hausa a
Kammale Don Manyan Makarantun
Sakandire. Ibadan-
Nigeria. Spectrum Books
Limited, Ring Road.
Madabo,
M.H. (1979. “ Ciniki da Sana’o’i a Ƙasar Hausa”. Lagos: thomasa
Nelson Nigeria Limited.
Tukur,
A. (2020. “Rukunin Hausar Masu Sana’ar Waya a Garin Gusau”.
Kudin Bincike na neman Digirin Farko
(BA)Hausa a Sashen Nazarin
Harsuna da Al’adu. Jami’ar Tarayya
Gusau.
Yahaya, I.Y, da
wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan
Makarantun Sakandare. Littafi na biyu. Ibadan: University press
Plc.Ibadan-Nigeria.
Zarruƙ da wasu, (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan
Makarantun Sakandire. Littafi na Biyu. Ibadan-Nigeria.
University Press P.L.C.
Zarruƙ da wasu, (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan
Makarantun Sakandire. Littafi
na Biyu. Ibadan-Nigeria.
University Press P.L.C.
Zurmi, Y.S (2010). Matakin Nazarin
Hausa Don Ƙananan Makarantun
Sakandare. ( Babu maɗaba’a).
0 Comments
Post your comment or ask a question.