Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora: Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Yara: Gwamnan Sakkwato ya
zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Yara: Gwamnan Sakkwato ya
zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Yara: Gwamnan Sakkwato ya zauna
daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Yara: Gwamnan Sakkwato ya
zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Alu Magatakadda
sadauki ne,
Yara: Gwamnan Sakkwato
gamji sha sara.
Jagora: Alu Magatakadda
sadauki ne,
Yara: Gwamnan Sakkwato gamji
sha sara.
Jagora: Alu Magatakadda
sadauki ne,
Yara: Gwamnan Sakkwato
gamji sha sara.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda gamji sha sara.
Jagora: Abi ka kai Allah yab
ba,
Yara: Ƙasag ga babu gwarzo
yau sai kai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Abi ka kai Allah yab
ba,
Yara: Ƙasag ga babu gwarzo
yau sai kai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Masu ja da kai duka
sun damu,
Yara: Sun ce karo da giwa
ba daɗi,
Kaura da Ali sai manyan hwarko.
Jagora: Masu ja da kai duka
sun damu,
Yara: Sun ce karo da giwa
ba daɗi.
Kaura da Ali sai manyan hwarko,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Kwaz zo gare ka,
In ya zo tuba,
Yara: Amsai Alu ka ce mai
ba komai.
Jagora: Kwaz zo gare ka,
In ya zo tuba,
Yara: Amsai Alu ka ce mai
ba komai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Wane bana siyasa ta
basai,
Na ganai cikin guntun layi.
Yara: Kahin a lisaha ya ce
ya bi,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Jagora: Wane bana siyasa ta
basai,
Na ganai cikin guntun layi.
Yara: Kahin a lisaha ya ce
ya bi,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Jagora: Masi cewa Gud Lok
yat turo shi,
Mun tabbatar da ƙarya ta yay yi.
Yara: Ko ga get na farko
bai kai ba,
Balle ya kai ga ADC giwa,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Yara: Gwamnan Sakkwato ya
zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Sannu da famab
Badar,
Alu jikan Umar.
Yara: Yaƙin Alu akwai sa’a kullum,
Saboda Rabbana ya ce sai kai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Sannu da famab
Badar,
Alu jikan Umar.
Yara: Yaƙin Alu akwai sa’a
kullum,
Saboda Rabbana ya ce sai kai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Kwamishinan kuɗi Faruƙu,
Faruƙu Yabo namijin
duniya,
Mai gaskiya kamal littafi.
Yara: Faruƙu jarumi yaƙi an,
Maga takarda bai rena ma ba,
Yadda kay yi mai Allah shi ma,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Kwamishinan kuɗi Faruƙu,
Kwamishinan
kuɗi Faruƙu,
Mai gaskiya kamal littafi.
Yara: Faruƙu jarumi yaƙi an,
Maga takarda bai rena ma ba,
Yadda kay yi mai Allah shi ma,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Kwamishinan kuɗi Faruƙu,
Faruƙu Yabo namijin
duniya,
Mai gaskiya kamal littafi.
Yara: Faruƙu jarumi yaƙi an,
Maga takarda bai rena ma ba,
Yadda kay yi mai Allah shi ma,
Jagora: Kai ne Alu ba su ne
ba,
Yara: Mahassadanka sun
koma baya,
Suna biɗat su sheƙo sui tuba.
Jagora: Kai ne Alu ba su ne
ba,
Yara: Mahassadanka sun
koma baya,
Suna biɗat su sheƙo sui tuba.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Duniya sai …………..
7:12
Yara: Kwaj ja da kai gwada
mai bai kai ba,
Jahas Sakkwato kai ɗai ke cara.
Jagora: Duniya sai …………..
Yara: Kwaj ja da kai gwada
mai bai kai ba,
Jahas Sakkwato kai ɗai ke cara
Jagora: Gwada musu kai ab
babbansu,
Yara: Ko mutum ya so ko
bai so ba.
Jagora: Aliyu gwada musu kai
ab babbansu,
Yara: Ko mutum ya so ko
bai so ba.
Jagora: Gwada musu kai ab
babbansu,
Yara: Ko mutum ya so ko
bai so ba,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Faɗa wa masu taron
dangin can,
Sui a hankali Alu bai son wargi,
Yara: In ya sako igwa ba
mai tsira,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Faɗa wa masu taron
dangin can,
Sui a hankali Alu bai son wargi,
Yara: In ya sako igwa ba
mai tsira,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Sultan ya ce ya gode
ma,
Ka riƙe talakkawa zak kyau,
Shagari Shehu ma ya gode ma,
Ma’aikatanka duk sun ruwaita,
Ma’aikatanka dun sun ruwaita,
Gud Lok Jonatan ya gode ma,
Don kana da kyakkywan niya.
Yara: Birni da ƙauye kowa na hwata,
Sun ce Alu ka dawo kai maimai,
Magatakadda yau ba mai ji ma
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Sultan ya ce ya gode
ma,
Ka riƙe talakkawa zak kyau,
Shagari Shehu ma ya gode ma,
Ma’aikatanka dun sun ruwaita,
Gud Lok Jonatan ya gode ma,
Don kana da kyakkywan niya.
Yara: Birni da ƙauye kowa na hwata,
Sun ce Alu ka dawo kai maimai,
Magatakadda yau ba mai ji ma
Jagora: To tsaya Gud Lok
Jonatan ya gode ma,
Don kana da kyakkyawan niya,
Yara: Birni da ƙauye kowa na hwata,
Sun ce Alu ka dawo kai maimai,
Magatakadda yau ba mai ji ma
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Alhaji Abubakar Ɗanladi Kuce,
Yara: Ya ce wurinsu ko yaƙƙi yaz zo,
Sabo da kai Alu bai jin sauna.
Jagora: Alhaji Abubakar Ɗanladi Kuce,
Yara: Ya ce wurinsu ko yaƙƙi yaz zo,
Sabo da kai Alu bai jin sauna.
Jagora: Alhaji Abubakar Ɗanladi Kuce,
Yara: Ya ce wurinsu ko yaƙƙi yaz zo,
Sabo da kai Alu bai jin sauna.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Ummm Muktari mai
gona sadauki ne,
Muktari mai gona sadauki ne,
Ƙashin bugun ƙashi na Alu zaki,
Yara: Na gwamna wanda sara
ke sauna,
Kwaz zo gidanshi bai raina mai ba.
Jagora: Muktari mai gona
sadauki ne,
Ƙashin bugun ƙashi na Alu zaki,
Yara: Na gwamna wanda sara
ke sauna,
Kwaz zo gidanshi bai raina mai ba.
Magatakadda yau ba mai ji ma
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Fam sek sikuriti na
gode mai,
Muhammadu Tukur Namijin duniya,
Yara: Na gauga gwamna mai halin girma,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Fam sek sikuriti na
gode mai,
Muhammadu Tukur Namijin duniya,
Yara: Na gauga gwamna mai halin girma,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Fam sek sikuriti na
gode mai,
Muhammadu Tukur Namijin duniya,
Yara: Na gauga gwamna mai halin girma,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Fam sek sikuriti na
gode mai,
Muhammadu Tukur Namijin duniya,
Yara: Na gauga gwamna mai halin girma,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Fam sek sikuriti na
gode mai,
Muhammadu Tukun namijin duniya,
Yara: Na gauga
gwamna mai halin girma.
Jagora: Matar shi Amina ta
kyauta,
Saboda kai Alu ta kyauta min.
Yara: Saboda kai Alu ta
kyauta min.
Jagora: Matar shi Amina ta
kyauta,
Yara: Saboda kai Alu ta
kyauta mim.
Jagora: Matan shi Amina ta
kyauta,
Yara: Saboda kai Alu ta
kyauta mim,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Ina Ɗan Mahiya na Alu A.A.?
Yara: Na gwamna ko da kai
bai ji sauna.
Jagora: Ina Ɗan Mahiya na Alu A.A.?
Yara: Na gwamna ko da kai
bai ji sauna.
Jagora: Ina Ɗan Mahiya na Alu A.A.?
Yara: Na gwamna ko da kai
bai ji sauna.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Ina Ɗan Mahiya na Alu A.A.?
Yara: Na gwamna ko da kai
bai ji sauna.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Jagora: Haji Ibrahim Ɗan Cadi,
Da shi da Sardaunan Ɗan Gobir,
Yara: Yankin gabas Alu kak
kai sauna,
Waɗan ga na taro ma kan kowa,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Ciyaman Ibrahim Ɗan Cadi,
Da shi da Sardaunan Ɗan Gobir,
Yara: Yankin gabas Alu kak
kai sauna,
Waɗan ga na taro ma kan kowa,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Ciyaman Ibrahim Ɗan Cadi,
Da shi da Sardaunan Ɗan Gobir,
Yara: Yankin gabas Alu kak
kai sauna,
Waɗan ga na taro ma kan kowa,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Difiti Muktari Shagari,
Yara: Na
shugaban ƙasa mai yin hau,
Ya bi ka babu jayayyar komi,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Difiti Muktari Shagari,
Yara: Na
shugaban ƙasa mai yin hau,
Ya bi ka babu jayayyar komi,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Alu
ka ja mutum ya ja shi aƙ ƙarya,
Yara: Ga
wanga lokaci kowa ne su,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Alu
ka ja mutum ya ja shi aƙ ƙarya,
Yara: Ga
wanga lokaci kowa ne su,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Madawakin sarkin Yamma,
Ɗan
Ama maroƙin mai girma.
Yara:
Fadar gidan Alu ba mai ja ma.
Jagora:
Madawakin sarkin Yamma,
Ɗan
Ama maroƙin mai girma.
Yara:
Fadar gidan Alu ba mai ja ma.
Jagora:
Madawakin sarkin Yamma,
Ɗan
Ama maroƙin mai girma.
Yara:
Fadar gidan Alu ba mai ja ma.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Tsaya Hamza Isah Sani ya gode,
Ya gwada mini ɗan
milki ne shi.
Yara: Ya
gwada mini ɗan milki ne shi.
Jagora:
Tsaya Hamza Isah Sani ya gode,
Ya gwada mini ɗan
milki ne shi.
Yara: Ya
gwada mini ɗan milki ne shi.
Magatakadda ba mai ja
ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Hamza Sani ya gode,
Yara: Ya
gwada mini ɗan milki ne shi.
Magatakadda ba mai ja
ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja
ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Kwamishinan kuɗi Faruƙu,
Da gaskiya yake aiki kullum.
Yara:
Kullum Aliyu na kan hanyar daidai,
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Kwamishinan kuɗi Faruƙu,
Da gaskiya yake aiki kullum.
Yara:
Kullum Aliyu na kan hanyar daidai,
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Ciyaman fati Waziri Boɗinga,
Yara:
Wanda yai ma jam’iya gata,
Ko’ina sananne ne Hausa.
Jagora:
Ciyaman fati Waziri Boɗinga,
Yara:
Wanda yai ma jam’iya gata,
Ko’ina sananne ne Hausa.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Tureta jagoran yaƙi,
Ko’odinetan mai girma gwamna,
Yara:
Kwamishina sadauki mai aiki,
Wurin Alu ga yau kai ne gwarzo,
Magatakadda yau a mai ja ma.
Jagora:
Tureta jagoran yaƙi,
Ko’odinetan mai girma gwamna,
Yara:
Kwamishina sadauki mai aiki,
Wurin Alu ga yau kai ne gwarzo,
Magatakadda yau a mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Jagora:
Tureta jagoran yaƙi,
Yara:
Ko’odinetan mai girma gwamna,
Kwamishina sadauki mai aiki,
Wurin Alu ga yau kai ne gwarzo,
Magatakadda yau a mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Jagora:
Fam-sek Bello Abubakar Wamako,
Yara: Ƙanin Aliyu mai halin girma.
Jagora:
Fam-sek Bello Abubakar Wamako,
Yara: Ƙanin Aliyu mai halin girma.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Fam-sek Bello Abubakar Wamako,
Yara: Ƙanin Aliyu mai halin girma.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Jagora: Han
na tuna da mai girma sarki,
Salihu Baraden Wamako,
Sarkin da ba shi wargi ba ai mai.
Yara:
Allah shi tabbatam ma alheri,
Fata ake ƙasa
duk baki ɗai,
Kana riƙon ƙasa haggun Madi.
Jagora: Han
na tuna da mai girma sarki,
Salihu Baraden Wamako,
Sarkin da ba shi wargi ba ai mai.
Yara:
Allah shi tabbatam ma alheri,
Fata ake ƙasa
duk baki ɗai,
Kana riƙon ƙasa haggun Madi.
Magatakadda yau ba mai ja
ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Jagora: Han
na tuna da zakin Wammako,
Salihu zakin Wamako,
Salihu zakin Wamako,
Sarkin da ba shi wargi ba ai mai.
Yara:
Allah shi tabbatar ma alheri.
Jagora:
Salihu Baraden Wamako,
Sarkin da ba si wargi ba ai mai.
Yara:
Allah shi tabbatam ma alheri,
Fata a kai ƙasar
dub baki ɗai,
Kana riƙon ƙasa har gun Madi,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Jagora:
Darecto Bello da af fainas,
Yara:
Fata shi kai da ai alheri kullum,
Burin ka kada kowa,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Jagora:
Bello fam-sek darecto fainas,
Yara:
Fata shi kaiai ta alheri kullum,
Gwamna ka kada kowa naj ja ma,
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Bello fam-sek darecto fainas,
Yara:
Fata shi kaiai ta alheri kullum,
Gwamna ka kada kowa naj ja ma,
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Bello fam-sek darecto fainas,
Yara:
Fata shi kaiai ta alheri kullum,
Gwamna ka kada kowa naj ja ma,
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Fata shi kai ai ta alheri kullum,
Yara:
Gwamna ka ka da kowa ke ja ma,
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda ba mai ja ma.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja am.
Jagora:
Bello Fam-sek darecto finas,
Yara:
Fata shi kai ai ta alheri kullum,
Gwamna ka kada kowa ke ja ma,
Ƙwarai
ya daɗe
shina wannan fata,
Gwamna ka ka da kowa ke ja ma,
Jagora: Ƙwarai ya daɗe
shi wannan fata,
Yara:
Gwamna ka ka da kowa ke ja ma
Jagora:
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Yara:
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Sakkwato ta Yamma ka bam ma Faruku,
Ga shi ga Alu A.A. naka,
Sannan kuma ga sanata Tambuwal,
Suna da rundunar yaƙi na
gani.
Yara: Su
ukun ga na kawo mata,
Kowa yai karo da su bai jin daɗi
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Umm! Sakkwato ta Yamma ka bam ba Faruƙu,
Ga shi ga Alu A.A naka,
Sannan kuma ga sanata Tambuwal,
Suna da rundunar yaƙi na
gani.
Yara: Su
uku ɗin
ga na kawo mata,
Kowa yai karo da su bai jin daɗi,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Sakkwato ta Yamma ka bam ma Faruku,
Ga shi ga Alu A.A. naka,
Sannan kuma ga sanata Tambuwal,
Suna da rundunar yaƙi na
gani.
Yara: Su
ukun ga na kawo mata,
Kowa yai karo da su bai jin daɗi
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: To!
Bello Halliru Guiwa sadauki ne,
Babban sakataren fensho bod,
Yara:
Kayan shi Bello kullum na ka,
Allah shi ƙara
girma maigirma,
Magatakadda ya zauna daidai.
Jagora:
Ummm!
Yara:
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: To!
Bello Halliru Guiwa sadauki ne,
Babban sakataren fensho bod,
Yara:
Kayan shi Bello kullum na ka,
Allah shi ƙara girma
mai hidima,
Magatakadda ya zauna daidai.
Jaora: To kai!
Yara:
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Bello Halliru Guiwa sadauki ne,
Babban sakataren bensho bod.
Yara:
Kayan Bello kullum na ka,
Allah shi ƙara girman
girma,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Haji Aminu Ɗan Iya Nasarawa,
Yara:
Basakkwacen da bai ɗaukan wargi,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Ai
Haji Aminu Ɗan Iya Nasarawa,
Yara:
Basakkwaɗen
da bai ɗaukan
wargi,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: To,
umm!
Magatakadda yau ba mai ja
ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Jagora: Kai
ne Alu ba su ne ba,
Yara:
Mahassadanka sun koma baya,
Suna biɗar su sheƙo sui tuba,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Kai
ne Alu ba su ne ba,
Yara:
Mahassadanka sun koma baya,
Suna biɗar su sheƙo sui tuba,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Godiya ga Buba Galadima,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda
yau ba mai ja ma.
Jagora:
Buba Galadima Wamakko,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Haji Isa Sidi mu gode mai,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min.
Jagora: Isa
Sidi mu gode mai,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Garba Sarki Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Usaini Tukur Faro Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Alhaji Mu’azu Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Alhaji Mu’azu Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Mai-Lato Gumbi ban raina mai,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Eee!
Mai-Lato Gumbi ban raina mai,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Ɗan Maya Kalambaina ya kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Haji Ɗan Mayya na Kalambaina,
Ni Alhaji Sani na gode.
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Aminu Dodo Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Ciyaman Fati Kangiwa,
Alhaji Sani ya gode.
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Maga,
Jaora: Fatima Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ta kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
.
Jagora:
Ummi Gada kuma ta kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ta kyauta min,
Jagora:
Ummi Gada kuma ta kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ta kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
‘Yar Shehu Guiwa ta kyauta min,
Yara:
Saboda kai Alu ta kyauta min.
Jagora:
‘Yar Shehu Guiwa Sani ya gode.
Yara:
Saboda kai Alu tai kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Garba bakanike kuma ya kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min.
Jagora:
Garba makanike kuma ya kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Audu maji-daɗi ban raina mai ba.
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Jagora:
Ahamed Makanike kuma ya kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Jagora:
Ahamed Barade Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Jagora: Ado
mai mai kumka ya kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Jagora:
Sani dalla-dalla ya kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Jagora:
Ibrahim Ango Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Shugaban majalisa na gode mai,
Aminu Tambuwal namijin duniya.
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Jagora: To!
Yara:
Gwamnan Sakkwto ya zauna daidai.
Jagora:
Sugaban majalisa na gode mai,
Aminu Tambuwal na gode mai,
Aminu Tambuwal namijin duniya.
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Ummaru Ɗahiru Tambuwa kuma ya kyauta,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Sanata Gobir kuma ya kyauta.
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Jagora:
Yara sai mu gode Sardaunan Gobir,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Jagora:
Yara sai mu gode Sardaunan Gobir,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Alhaji Mutta Arkilla,
Alhaji Sani ya gode.
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Audu sifika Sani ya gode,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja ma,.
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau bamai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Sakkwato sawuz lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Sakkwato sawuz lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Sakkwato noz lokal gommen,
Yara:
magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Sakkwato noz lokal gommen,
Yara:
magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Wamakko nan lokal gommen,
Yara: magatakadda
duk sun ce sai kai.
Jaogra: Wamkko duk lokal
gommen,
Yara:
magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Sannan Binji lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magaakarda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Sannan Tangaza lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Mutan Tangaza lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Sanan Gudu duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:Kware
lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Kware lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Su
yilami lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Boɗinga
lokal gommen,
Yara: Magatakadda
duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: Boɗinga
lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Boso Boɗinga
namijin duniya,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Jagora:
Goso Boɗinga
namijin duniya,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Jagora:
Gojo Boɗinga
namijin duniya,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta mi.
Jagora:
Gojo Boɗinga
mai ɗauka
yaƙi,
Yara:
Saboda kai Alu ya kyauta min,
Magatakadda yau ba mai ja,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Jagora: A
Dange-Shuni duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadd yau ba mai ja ma.
Jagora: A
Dange-Shuni duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora: A
Dange-Shuni duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Basulluɓen
mutum bai jin shakka,
Dange-Shuni duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Han
na tuna da nau harɗen Shun,
Allah shi ƙara
girma babana.
Yara:
Allah shi ƙara girman Babana.
Jagora: Ai
han na tuna ɗan fadan Shuni,
To!
Yara:
Allah shi ƙara girman babana,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Han
na tuna nau harɗen Shuni,
Yara:
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Tureta can lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Tureta kowa ya yadda,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakardda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba maija ma.
Jagora: To!
Yara:
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Mutan Yabo duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Mutan Yabo duk lokal gommen,
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Yabo jikokin Fodiyyo,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Yabo jikokin fodiyo,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Shagari lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Shagari lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Shagari lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Na
ji Tambuwal lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Na
ji tambuwal lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora:
Sannan Keɓɓi duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: A
sannan Keɓɓi duk lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Mutanen Wurno lokal gommen,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: A
mutanen Wurno garin Shehu,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Mutanen Wurno garin Shehu,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai.
Jagora:
Mutanen Gwadabawa sun yarda,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Duk
‘yan Gwadabawa sun yarda,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Sannan mutanen Illela,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora:
Sannan mutanen Illela,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Duk
elda da son kowa ya bi,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Duk
elda da son kowa ya bi,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Duk
elder da son kowa ya bi,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: Raɓa
garin Sardauna Amadu,
Na yanzu Raɓa to
sun bi,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: A
Raɓa maza
da mata sun bi,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Jagora: Raɓa
maza da mata sun bi,
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai.
Magatakadda yau ba mai ja
ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Jagora:
Umm!
Yara: Yau
ba mai ja.
Jagora: Ka
gode ma mutanen Isa,
Dum maza da mata yau sun bi.
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai,
Jagora: Ka
gode ma mutanen Isa,
Dum maza da mata yau sun bi.
Yara:
Magatakadda duk sun ce sai kai,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Jagora:
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Yara:
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Jagora: To!
Yara:
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma,
Jagora: Alu
Magatakadda sadauki ne,
Yara:
Gwamnan Sakkwato gamji sha sara.
Jagora: Alu
Magatakadda sadauki ne,
Yara:
Gwamnan Sakkwato gamji sha sara.
Jagora: Alu
Magatakadda sadauki ne,
Yara:
Gwamnan Sakkwato gamji sha sara.
Magatakdda yau ba mai ja ma,
Gwamnan Sakkwato ya zauna daidai,
Magatakadda yau ba mai ja ma.
Jagora: A
bi ka kai Allah yab bai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.