Amfani da Ka'idojin Rubutun Hausa a Rubutattun Kagaggun Labarai

    Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).

    Name: Sani Adamu

    Phone Number: 07065411971

    Gmail: adamufsk3501@gmail.com

    Tsakure

    Wannan aiki ya mayar da hankali ne a kan ƙa'idojin rubutun Hausa. Haka kuma ya bayar da muhimmanci ƙwarai a kan irin katoɓarar da wasu marubuta ke yi a fagen amfani da ƙa'idojin rubutu musamman a cikin litattafan ƙagaggun labarai. A yayin gudanar da wannan aiki, an yi amfani da gogaggun hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da: Bitar ayyukan da suka gabata, karance-karancen litattafan ƙagaggun labarai da kuma taƙaitaccen nazari a kan ƙa'idojin rubutun Hausa. wannan binciken ya gano cewa ba ma a fagen amfani da ƙa'idojin rubutu ba kaɗai, Marubutan sukan samu matsala ƙwarai musamman a wajen ginin Jimla. Wannan aiki ya tabbatar da cewa duka waɗannan kurakuren ana samun su ne sakamakon mafi yawancin Marubutan suna da ƙarancin ilimi a kan lamarin da ya shafi ƙa'idojin rubutu. A bisa haka ne wannan muƙalar ke ba da shawarar cewa, marubuta su yi ƙoƙari wajen inganta iliminsu musamman a fagen amfani da ƙa'idojin rubutu domin hakan zai taimaka wa masu karatu wajen samun sauƙin fahimtar saƙonnin dake cikin litattafansu.

     

    1.0 Gabatarwa

     

    Alamomin rubutu na nufin ‘yan ɗigagga da zane-zane da ake amfani da su yayin da ake rubutu. Ƙa'idojin rubutu kuwa waɗansu dokoki ne ko ladubba da aka gindaya da ya kamata mai rubutu ya kiyaye wajen rubutunsa (Bunza, 2002:16).

     

    Masana da dama, na gida da na waje sun yi aiki tuƙuru wajen daidaita rubutun Hausa ta hanyar amfani da ƙa'idojin da suka dace. Masana kamar su: (Lepsius, 1862) da (J.F. Schon da Prietzer, 1902) da (Mischlich, 1906) da (Westerman, 1911) duk sun gudanar da ayyuka daban-daban dangane da ƙa'idojin rubutun Hausa. Haka kuma an gudanar

    da taruka daban-daban domin gyara ƙa'idojin rubutun Hausa tun daga shekarar (1912) har zuwa (1980).

     

    Duk da irin wannan ƙoƙarin da masana suka yi bai hana samuwar kurakurai a cikin rubutu ba musamman a cikin litattafan ƙagaggun labarai.

     

    Wannan muƙalar za ta dubi irin kurakuren da masu rubutu cikin harshen Hausa ke tafkawa a yayin da suke rubutu musamman a cikin litattafan ƙagaggun labarai. Haka kuma za ta mayar da hankali wajen fito da wasu daga cikin ƙa'idojin rubutun Hausa tare da bayar da ƙananan misalai a kan yanda ya dace a yi amfani da su a cikin litattafan.

     

    1.1 Ra'in Bincike

     

    An ɗora wannan binciken ne a kan ra'in ƙwƙƙwafi (Close reading). An ɗora wannan aikin bisa wannan ra'i ne sakamakon bin diddigin da aka yi wa wasu litattafan ƙagaggun labarai na Hausa domin fito da kura-kuran marubuta a cikin litattafan. Ra'in ƙwaƙƙwafi, ra'i ne da ke nazarin rubutu ta ɓangaren amfani da kalmomi da jimloli da kuma ma'ana a cikin rubutu. Ra'in yana nazarin abinda aka rubuta da kuma yadda aka rubuta shi kamar yadda Snow, da Connor, (2016) suka ruwaito.

     

    1.2 Dabarun Bincike

     

    Domin samar wa wannan bincike ingantaccen muhalli, an yi amfani da gogaggun hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da:

    a. Bitar ayyukan da suka gabata

    b. Karance-karancen litattafan ƙagaggun labarai

    c.Taƙaitaccen nazari a kan ƙa'idojin rubutun Hausa

    d. Bincike ta hanyar yanar gizo

     

     

    2.0 Waiwaye A Kan Ma'anar Rubutu Da ƙa'idojinsa

     

    Rubutu wata hanya ce ta isar da saƙo a tsakanin al'umma. Wannan kuwa ya samo asali ne tun lokacin da al'ummar Hausawa ta buɗe idanuwanta dangane da harkar rubutu a faɗin duniya. Rubutu na ɗaya daga cikin hanyoyin da al'ummar Hausawa ke isar da saƙonninta musamman ta hanyar wallafa litattafai, jaridu da mujallu, da dai sauransu.

     

    Dangane da ma'anar rubutu kuwa, masana da dama sun ba da gudummuwa sosai. A bayanin Pavert (1993:8) cewa ya yi "Rubutu wata dabara ce ta yin wasu alamomi da za su wakilci magana". Shi kuwa Yahya (1988:1) ya bayyana cewa "Rubutu na nufin yin amfani da zayyana wasu alamomi a kan takarda ko a kan wani abu mai bagire don sadar da magana".

                   

    2.1 Ƙa'idojin Rubutu

     

    Ƙa'idojin rubutu na nufin dokoki ko ladubba da ya kamata mai rubutu ya kiyaye wajen rubutunsa. Waɗannan ƙa'idoji su ne ke gyara rubutu da sanya masa tsarin da zai ba da damar karantuwa (Sa'id, B. 2004). Wasu daga cikin waɗannan ƙa'idoji sun haɗa da:

    1. Ƙa'idojin raba kalma

    2.Ƙa'idojin haɗe kalma

    3.Nuna mallaka

    4. Alamomin rubutu

    Waɗannan rukunnai da aka lissafa a sama su ne ke ƙunshe da dokokin rabawa da haɗe kalmomi a yayin rubutu. Misali, kalmomin korau, dirka, tsayayyen wakilin suna, da dai sauransu. Haka kuma suna ɗauke da kalmomin mallaka doguwa da gajera. Sannan kuma suna ɗauke da dokokin dake bayani a kan yadda ake amfani da manya da ƙananan baƙaƙe a yayin rubutu. Bugu-da-ƙari suna ɗauke da alamomin rubutu. Wasu daga cikin waɗannan alamomi sun haɗa da:

     

    A. Aya (.)

    B. Kwama (,)

    C. Alamar tambaya (?)

    D. Alamar motsin rai (!)

    E. Ruwa biyu (;)

    F. Alamar zancen wani ("  ")

    G. Alamar zarce (.....)

    H. Alamar karan ɗori (-)

    I. Alamar baka biyu ( (  ) ) da sauransu.

     

    3.0 Waiwaye A Kan Ma'anar Ƙagaggen Labari

     

    Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar ƙagaggen labari. Misali: (Yahaya 2016:2) Cewa ya yi " Ƙagaggen labari, labari ne dake cike da zantukan hira da nishaɗantarwa wanda ba da gaske ya taɓa faruwa ba. Yahaya (1988:7) Ya bayyana tarihin rubuce-rubuce na ƙagaggun litattafai bai daɗe sosai ba, domin kuwa an same su ne bayan shigowar Turawa masu yaɗa addinin kirista. Turawa kamar irin su J.F Schon (1957) da sauransu.

     

    3.1 Kura-kurai A Cikin rubutun Hausa

     

    Ko shakka babu akan sami kura-kurai da dama a cikin rubutu wanda hakan ba ƙaramin cikas yake haifarwa a wajen fito da ma'anar saƙo ba. Irin waɗanann kura-kuran akan same su a wajen ƙirar kalmomi, ginin jimla da kuma sauran wuraren dake da alaƙa da dokokin rubutu. Yanzu ga waɗansu misalai na jimloli da za a iya dubawa kamar haka:

    1. Aminu bai je makaranta ba.

    2. Wanda bai ji bari ba, ya ji hoho!

    3. Wane ne ya zo?

    4. Matarsa malama ce.

    5. Waccan Akuyar tawa ce.

    6. A bar shi ya je karatu.

    7. Wannan al'ummar (Hausawa) Suna da karamci.

    8. An yi man wasa da hankali.

    9. Alhaji ya wuce buguzum-buguzum.

    10. Kayan da aka sarrafa ga su kamar haka:

     

    Idan aka yi la'akari da waɗannan misalan da aka lissafa a sama za a ga cewar, ƙa'idojin rubutu sun taka muhimmiyar rawa wajen fito da ma'anar waɗannan jimloli. Idan da kuwa za a cire waɗannan ƙa'idojin to da rubutun na iya hargitsewa ta yanda ma'anar ma za ta iya canzawa.

     

    Ta wani ɓangare kuma za a iya kawo misalai na wasu jimloli da rashin amfani da ƙa'ida kan iya haifar da canzawar ma'ana ko kuma ya sanya jimlolin su zama masu harshen damo. Misali:

    1a. Ba shi ya ci  (Let him eat)

    1b. Bashi ya ci  (He was credited)

    2a. Yaƙi ya je   (He went for a war)

    2b. Ya ƙi ya je  (He refuse to go)

    3a. Kin tafi kin bar ni ? (Quetion)

    3b. Kin tafi kin bar ni.

     

    A nan ma idan aka duba za a ga ƙa'idojin rubutu sun yi aiki sosai wanda idan da za a cire su mai karatu ba zai samu damar fahimtar abin da ake nufi sosai ba.

     

    3.2 Nazarin Kura-kurai A Wasu Litattafan Ƙagaggun Labarai Na Hausa

     

    Ko shakka babu litattafan ƙagaggun labarai na Hausa na cike da ɗumbin kura-kurai wanda har ya sa ake ganin wannan a matsayin gazawar marubuta litattafan ƙagaggun labaran. Samuwar irin waɗannan kura-kuran kan juya akalar saƙon da marubuci ke ƙoƙarin isarwa zuwa wata ƙusurwa ta daban. Ga dai misali a cikin wasu litattafai:

     

    a. Fateema ta ce kusan kullum abinda ke faruwa a gidanmu ke nan kullum sai ya daketa yace sai ta auri ɗan 'yar uwarsa , ita kuma ta dage bazata aure sa ba (Ribar biyayya, 2021:1)

    A cikin wannan zancen za mu ga cewa ba a yi amfani da alamomin kyautata rubutu ba. Ya kamata a yi amfani da alamar zancen wani. Haka kuma akwai wurare da yawa da ya kamata a sanya alamar aya, amma ba'a sanya ba. Sannan rubutun sam ba a yi amfani da dokokin rabawa ko haɗewa ba a cikinsa. Ga wasu misalan kamar haka:

     

    b. Tace yauwa gogo saisa nake sonki mema zakiyi dashi bani ina miki komi ba barima nai miki shara sai kiban kudin iloka (Matar soja, 2022: 2)

     

    A wannan misalin da ya gabata za a ga cewar, marubucin wannan littafin ya tafka ta'asa mai girma a cikin rubutunsa, domin kuwa rashin amfani da ƙa'ida ta janyo sauyawar ma'anar wasu kalmomi kamar: "Saisa", Bani" da kuma "Barima" waɗanda duka kalmomi ne da ke zaman kansu kuma suna ɗauke da ma'ana ta daban a cikin rubutun Hausa. Ga wasu misalan kamar haka:

     

    c. In ma ta yi mezanyi da ita tacigaba da masifa inbaka santa meyasa baka saketaba yace baze yihuba yarinyar kanen daddy ce fa (Rainon ta zan yi, 2014: 23)

     

    A wannan misalin ma za a ga cewar, baya ga cakuɗe rubutun da aka yi ta hanyar rashin yin amfani da dokokin raba kalma, an kuma haifar da sauyin ma'ana wajen rubuta jimalar "Yiwu ba" wadda marubucin ya rubuta kamar haka: "Yihuba". Ga wasu misalan kamar haka:

     

    d. Wayarta dake gefene yafara ringing dasauri tasa hannu tadau wayar hade dasawa a kunne tana fadin my one and only umma kin wune lafiya? daka dayan bangaren umma tace muneera kizu gida muna da bukatar ganinki akwai magana mai muhimmanci dazamuyi tana karasa fadan haka ta kashe wayar (Zaman Hostel, 2022: 1-2)

     

     

    e. Yayan mahaifinta wanda ake kira da baba bello shiya kalle muneera yace, muneera inaso kibude kunnowanki da kyau sanan kuma ki saurareni da kunnen basira, inason kisan ciwa abunda muka zaba miki a rayuwa har abada bazai taba zama cutarwa a garekiba saidai yazama alheri, kallonshi takeyi cikin rudo domin bata fahimce inda ya dosa ba (Zaman Hostel, 2022:3)

     

     

    A waɗannan misalan da suka gabata na 'e' da 'f' sai dai a ce Allah ya kyauta! domin kure da gazawar da aka samu a cikin rubutun har ya wuce misali. Idan aka lura da kyau za a fahimci cewa mafi yawan kalmomi da jimlolin da aka yi amfani da su a cikin rubutun an saɓa ƙa'ida sosai. Waɗannan kura-kurai duk suna faruwa ne sakamakon gazawar marubutan wajen tashi tsaye domin neman ilimin da zai ba su damar inganta rubutunsu. Ga wasu ƙarin misalai kamar haka:

     

    f. "Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowanne ɗan'Adam da irin tasa ƙaddarar, na wani yafi na wani amma sam kai baka ɗauki kaddara ba" (A Gidanmu Take, 2020:1). A cikin wannan misali da ya gabata za a ga samuwar kura-kurai da dama wanda inda za a yi amfani da dokoki to da ana sa ran rubutun ya kasance kamar haka:

     

    Haba Ahmad! Mi ya sa ba za ka ɗauki ƙaddara ba? Ka sani fa kowane ɗa'Adam da irin tasa ƙaddarar. Sai dai ta wani ta fi ta wani, amma kai sam ba ka ɗauki kaddara ba.

     

    g. Aiko zaki amayar da kayan cikin kine (Babban gida, 2015: 2)

    i. ashraf yabiya tare da sa hannu cikin aljihu ya ciro 'yan dari biyar guda shida sababbi (Shu'umin namiji, 2019: 2)

     

    A wajen rubutun Hausa, kuskure ne a yi amfani da ƙaramin baƙi wajen rubuta sunan yanka kamar yadda waɗannan marubuta suka yi. A doka ana fara rubuta sunan yanka da babban baƙi ne. Haka kuma a misalin da ya gabata na "h" an samu kuskure a wajen rubuta kalamar "Aiko" da "Zaki" waɗanda kalmomi ne masu cin gashin kansu a Hausa.

     

    Sanannen abu ne cewa a rubutun Hausa ba a liƙa wa kalmomin dirka  kowacce irin kalma walau a gaba ko a baya. Duk inda kalmomin dirka suke suna fitowa ne su kaɗai. A waɗansu lokutan akan sami masu rubutu su rinƙa rubuta su a cikin litattafansu kamar haka:

     

    h. Alhaji ya ce " Ba ita bace waccance "

    i. Menene haka Alhaji ? (Maraicin Nawara, 2020: 17)

     

    Idan aka lura za a ga cewar duk an haɗe kalmomin na dirka wato "Ne" da "Ce" wanda kuma hakan kuskure ne.

     

    A wasu jimlolin kuwa akan sami wasu marubuta masu amfani da kalmomin na dirka a nuhallin da bai dace ba. Wato sai su rinƙa sanya dirka jinsin namiji a muhallin da ya kamata a sanya ta mace. Misali:

     

    j. Ga ta fara, ga idanu, idan ka gan ta sai ka ce Balarabiya ne (Shu'umin namiji, 2019: 8)

    m. Nan take sai Amina ta tuna cewa wannan ai irin motar Usman ne (Shu'umin namiji, 2019:8)

    k. A bayan ɗakinsa ce ta ɓuya, wannan ne ya sa har Kadija ta fita ba ta gan ta ba (Shu'umin namiji, 2019: 19)

     

    Idan aka lura da waɗannan misalan za a ga cewa an samu kura-kurai na sanya kalmomin dirka a muhallin da bai dace ba. Kuma hakan kuskure ne a cikin rubutu.

     

    Alamar hamza waƙafi ne da ake sanyawa a saman gaɓar kalma (Ba a ƙasa ba) domin rabawa a tsakanin gaɓar da ta ƙare da wasali da kuma maƙwaɓciyarta da ta fara da wasali (Ba a amfani da wannan alamar a farkon kalmar da ta fara da wasali) Ana amfani da wannan alama ne saboda dalili biyu: Na farko domin nuna cewa ba ɗaurin wasali ko tsawon wasali ake nunawa ba. Na biyu kuwa, sauƙaƙa furuci, ( Bunza, 2001:184-186 ). Misali: Mu'amala, sa'a, ,ɗabi'a, fara'a, sa'adiyya, da dai sauransu.

     

    Marubuta ba su cika amfani da wannan alamar ta hamza ba, hakan ya sanya suke sanya ta a inda bai dace ba. Misali:

    l. Da Magajiya da Ummi Aisha suka dinga had'ata a dole ta hak'ura Ihsan ta karb'a (Ummi Aisha, 2019: 35).

     

    A cikin wannan misalin za a ga marubucin bai yi amfani da alamar hamza a kan yadda ya dace ba domin kuwa bai sanya ta a muhallinta ba.

     

    m. Daria sukai dukkansu suka nufa wajen mai adaidaitasahun akai ciniki (Ummi Aisha, 2019: 35). Bayan kwamacalar da wannan marubucin ya tafka, kuma za a ga cewar a rubutun nasa ya yi amfani da kalamar "Daria" wadda sam ba kalmar Hausa ba ce.

     

     

    4.0 Sakamakon Bincike

     

    Sakamakon wannan binciken ya yi daidai da hasashen binciken. Tun daga taken wannan aikin za a fahimci cewa an ɗauri aniyar bayyana gazawar marubuta litattafan ƙagaggun labarai na Hausa ta fuskar amfani da ƙa'idojin rubutu a kan yadda ya dace. A nan za a iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin kuwa ko da aka duba wasu daga cikin litattafan ƙagaggun labaran, sai ga shi an samu kura-kurai masu tarin yawa wanda har aka kawo misalan kaɗan daga cikinsu. Waɗannan kura-kurai da ake samu a cikin rubutu  suna da tasiri ƙwarai wajen dakushe daraja da ƙimar marubuta. Baya ga wannan matsala kuma, har ila yau suna janyo sauyawar rubutu ta fuskoki da dama kamar haka:

    1- Ta fuskar ma'ana

    2- Ta fannin ginin jimla

    3- Ta fannin ƙirar kalma

    4- Amfani da wasu haruffa da babu su a harshen Hausa. Misali, "x".

        Waɗannan matsaloli da aka lissafa a sama suna da tasiri sosai wajen janyo wa marubuta litattafan ƙagaggun labarai na Hausa wasu abubuwa kamar haka:

    1- Durƙushewar kasuwa.

    2- Gazawa wajen cimma manufa.

    3- Gundurar da masu karatu.

    4- Rikitar da masu karatu wajen ƙoƙarin fahimtar saƙo.

    5- Cin amanar ilimi.

    6- Lalata darajar harshen Hausa da kuma sauran abubuwa makamantan waɗannan.

    7- Amfani da kalmomin da ba na Hausa ba a matsayin Hausa.

     

    Wannan ba abin mamaki ba ne, domin kuwa bincike ya nuna cewa mafi yawa daga cikin marubuta litattafan ba su da ƙwarewa sosai ta fannin ilimin da ya shafi ƙa'idojin rubutun Hausa da ma Hausar ita kanta. Haka kuma ba sa tuntuɓar masana a yayin da suke gudanar da rubutunsu.

     

    4.1 Kammalawa

     

    A cikin bayanan da suka gabata na wannan muƙalar, an yi ƙoƙarin fito da ma'anar rubutu da ƙa'idojinsa. Haka kuma an yi gajeran sharhi dangane da kura-kurai a cikin rubutun Hausa inda har aka bayar da wasu ‘yan misalai. Bayan wannan kuma, an yi ƙoƙarin fito da wata ma'ana daga cikin ma'anonin ƙagaggen labari. Sannan kuma an bayar da misalai da dama dangane da kura-kurai waɗanda aka zaƙulo a cikin wasu daga cikin litattafan ƙagaggun labarai na Hausa. A cikin wannan aiki da ya gabata za a ga cewar, kura-kurai a cikin litattafan ƙagaggun labarai na Hausa abu ne wanda ya kamata marubuta su kiyaye, domin ta hanyar kiyayewar ne za su samu damar isar da saƙonninsu cikin sauƙi kamar yadda wannan muƙalar ta yi bayani.

     

    Manazarta

     

    Adamu, A. (2017). Maraicin Nawara. First Class Writters Assocition Com.L.T.D. Kano

    Abdullahi, A. (2022). Nana Fatima. Interligent Writters Association Com.L.T.D. Kano

    Aliyu, S.R (2020). Ummi Aisha. Writters Forum Company Press Limited Kaduna Zariya

    Abdulmajid, R. (2014). Rainonta zan yi. Khairat-up Company press limited Kaduna Zariya.

    Bunza, A.M (2002). Rubutun Hausa (Yadda yake da yadda ake yinsa) Don Masu Koyo Da Koyarwa. Lagos State, Nigeria.

    http://www.nazarinkura-kurai.amsoshi.com-google search

    Inuwa, Y.F. (2021). Ƙa'idojin rubutun Hausa. Gwammaja printing press, Nigeria Limited, Kano state.

    Junaid, A. (2020). Ribar biyayya. Interligent writters Association com.L.T.D.

    Muhammad, A. (2022). Matar Soja. Writters Association Company, press Kano.

    Tukur, S.(2022). Farar Wuta. Writters association Company Press Limited Kano.

    Yahaya, I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M Da 'Yar'aduwa T.M. (2007). Darussan Hausa, Domin

    Yahaya, S. (2019). Shu'umin Namiji. Hajara Love Company Press Limited Kano

    1 comment:

    1. Masha Allah! Da fatan Allah ya ba mu ikon amfani da abin da muka karanta.

      ReplyDelete

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.