Ticker

6/recent/ticker-posts

Shehu Jaha Da Abokinsa

 🤣🤣🤣

Wata rana Shehu ya dawo da rana ya gaji, da kyar ya bi matakalan gidan sama na gidansa ya hau, ya bude tagogi ya kwanta.

Bacci ya fara kwashe shi sai ya ke ji a na bugun kofar gidansa bugawa na gayya, ya tashi da kyar ya leko ta taga, sai ya ga wani mutum mai kiba, Shehu ya ce: Malan wurin wa ka zo?

Mutumin ya ce: wurinka na zo, Shehu ya ce: to ina jinka, mutumin ya ce: magana ce zan fada maka, Shehu ya ce: ba za ka fada mun daga nan ba? Ya ce: yallabai a yi hakuri a dan sakko.

Shehu ya tattaka ya sauka, sai mutumin ya ce: Yallabai dama na zo ka taimaka mun ne Ina da wata matsala ce, Shehu ya ji wani haushi ya kama shi, ya yi kokari ya danne, ya ce: mu hau sama.

Su ka hau sama, katon mutumin nan da kyar ya ke hawa, bayan sun kure sama, sai Shehu ya CE: Malan Allah ya ba mu Sa'a, mutumin nan ranshi ya baci, ya ce wa Shehu: MAI YASA KA HAWO DANI BAKA FADAMIN TUN A KASA BA?

Shehu ya ce: KAI MA MAI YA SA KA SAKKO DA NI BA KA FADA MUN TUN INA SAMA BA? Haka mutumin nan ya sauka da kyar ya fece 🤣🏃‍♂️

Shin ko shehu ya kyauta kuwa?

Shehu Jaha

Post a Comment

0 Comments