Ticker

6/recent/ticker-posts

"Ɗan Takarar Zama Gwamna" - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

            Magatakarda Wamakko,

            Aliyu kar ka ɗau reni,

            Kuma kar ka ɗau wulaƙanci

 

Jagora: Waƙar ga tamu mun suma ta,

            Mun fara ta da roƙon Allah,

            In Allah ya so ya yarda,

Yara: Gwamnanmu mun yi mun ƙare

(Amshi)

 

Jagora: Waƙar ga tamu mun suma ta,

            Mun fara ta da roƙon Allah,

            In Allah ya so ya yarda,

Yara: Gwamnanmu mun yi mun ƙare

(Amshi)

 

Jagora:  Baba in dai kana shirin yaƙi ka fito,

            In ka ga ba ka yi ka gayin,

            Siyar jahar ga in bar ta,

            Yaƙi sai da uwa ɗan Barade,

            Yaƙi babu uwa banza ne,

Yara: Har ƙarama zaman karta.

(Amshi).

 

Jagora:  Baba in dai kana shirin yaƙi ka fito,

            In ka ga ba ka yi ka gayi man,

            Siyar jahar ga in bar ta,

            Yaƙi sai da uwa ɗan Barade,

            Yaƙi babu uwa banza ne,

Yara: Har ƙarama zaman karta.

(Amshi).

 

Jagora: Ni na tabbata kana da basira,

            Na ani kana da tunani,

            To amma fa ka ƙara kulawa,

            Angulu munahukin Allah ne,

Yara: In ka ga nai wurin yaƙi,

            Shi ba da gaske ya zo ba.

 

Jagora: Ni na tabbata kana da basira,

            Na ani kana da tunani,

            To amma fa ka ƙara kulawa,

            Angulu munahukin Allah ne,

Yara: In ka ga nai wurin yaƙi,

            Shi ba da gaske ya zo ba.

 

Jagora: Mun san masu takara gwamna,

            ‘Yan takara zama mun san su,

            ‘Yan shaye-shaye mun san su,

            Mun bar wane ɗan wiwi ne,

Yara: Can nig ganai cikin lungu,

            Ya laɓe ana yi mai moli.

 

Jagora: Mun san masu takara gwamna,

            ‘Yan takara zama mun san su,

            ‘Yan shaye-shaye mun san su,

            Mun bar wane ɗan daga ne,

Yara: Can nig ganai cikin lungu,

            Ya laɓe ana yi mai moli.

 

Jagora: Tun sadda wane yay gwamna,

            Martabar jaharmu ta hwaɗi,

            Mai ilmi da marar ilmi,

            Dole ne a samu bambanci,

            Ku Sakkwatawa albishirinku,

            Ga ɗan uwanku nan ɗanku,

            Shi za ya takara gwabna,

            Ku daure ku ba shi goyon baya,

Yara: In Aliyu ya zamu gwamna,

            Martabar jaharmu ta tashi.

 

Jagora: Yanzu kowa ka cin amana jama’a,

            A kwan a tashi Ɗanbau,

            Sai ka ga nai cikin tarko,

            Tarkon da ba ya hishshe shi,

            Ji wanda a cikin jama’a tai 

            Sai ga shi yanzu ya bar su,

            Waɗanga nan da ya samu,

            Ya biɗo abarba don ya raba musu,

Yara: Sai ga abarba tay tsutsa.

 

Jagora: Da ya biɗo abarba don ya raba musu,

Yara: Sai ga abarba tay tsutsa.

 

Jagora: Sakkwato mun canza masu suna,

            Ba ‘yan abarba a sunansu ba,

Yara: ‘Yan tukuwa ɗiyan ɗiɗi.

 

Jagora: Tsaya abin ga na da mamaki,

            Birni da ƙauye na duba,

            Kuma manya da yara na duba,

Yara: Duk inda ka ishe ɗan abarba,

            Ya iya shirin munahucci.

 

Jagora: Tsaya abin ga na da mamaki,

            Birni da ƙauye na duba,

            Kuma manya da yara na duba,

Yara: Duk inda ka ishe ɗan abarba,

            Ya iya shirin munahucci.

 

Jagora: Wannan,

Yara: Ya iya shirin azuzanci.

 

Jagora: Ni Ɗanbau hamdullahi,

            Na yi godiya wajen Allah

            Siyasa su wane ta watce,

            Yau shekara takwas suna mulki,

            Girman sarakuna su ka sai,

            Ga ɗan talaka ya sha ƙwaya,

            Wai za ya kori sarkinmu,

            Kahin ya kori sarkinmu,

            Allah ya biya bukatunmu,

Yara: Sai ga sakamako ya yi shi,

            Rigaye hisshe shi.

 

Jagora: A yanke mutum a yanke dabba,

            Don tattalin baƙin tsahi,

            Don ɗai a hau kujerar mulki,

Yara: In lokacinka ya ƙare,

            Tsahi duk na banza ne.

 

Jagora: A yanke mutum a yanke dabba,

            Don tattalin baƙin tsahi,

            Don ɗai a hau kujerar mulki,

Yara: In lokacinka ya ƙare,

            Tsahinka duk na banza ne.

 

Jagora: Wawa,

Yara: In lokacinka ya ƙare,

            Tsahinka duk na banza ne.

 

Jagora: Saga,

Yara: In lokacinka ya ƙare,

            Tsahinka duk na banza ne.

 

Jagora: Ga magatarda ga Muntari,

            To amma fa ku ƙara kulawa,

            In dai abin rabo ya samu,

            A ɗanƙa ma masu imani,

            Dun kada a bai wa kuraye shiya,

Yara: In su haɗe shi an huta.

 

Jagora: Ga Magatakarda ga Muntari,

            Ga wani zance za ni gaya muku,

            In dai abin rabo ya samu,

            A damƙa ma masu imani,

            Dun kada a bai wa kuraye shiya,

Yara: In sun haɗe shi an huta.

 

Jagora: Mu Sakkwatawa sannu dai aiki,

            A gaishe ku Sakkwatawan Shehu,

            Na gaishe ku Sakkwatawan Shehu,

            Na tabbata kuna da ɗiyauci,

            Domin abarba kun ƙi ta,

            Sai yawo su kai suna ƙarya,

Yara: Sun rikirkice musu,

            Sai hwaɗa su kai da junansu,

            Harka su ta yi dameji.

 

Jagora: Gaishe ku Sakkwatawan Shehu,

            Na tabbata kuna da ɗiyanci,

            Domin abarba kun ƙi ta,

            Sai yawo su kai sun ƙarya,

Yara: Sun rikirkice musu,

            Sai hwaɗa suke da junansu,

            Harka su ta yi dameji.

 

Jagora: An tsaida wane takara gwamna,

            Kare mai baƙin jini da yawa,

Yara: Du inda ya biya hurce,

            ‘Yan yara na yi mai yiho,

Jagora: Yiho kar.

 

Jagora: Ina ɗan buga-buga wane,

            Ya leƙa gabas ya leƙa Yamma,

            Ya leƙa Kudu ya Leƙa Arewa,

            Kullum wurin muhahucci,

            Ba Sakkwato noz ba da Sakkwato sawuz,

            Ko Isa mun hi ƙarhinka,

            Wawa!

Yara: Ko Isamun fi ƙarfinka.

 

Jagora: Kowa tasu tare da manya,

            Ka san yana da tarihi,

            Don haka manya sun ka gaya mini,

Yara: Danginsu Maguzawa ne.

 

Jagora: Na iske wane na ta jawabi,

            Ya ce Sakkwato duk kaji muke,

            Shi bai biɗar mu sai ran zaɓe,

            Nan take za ya jawo mu.

Yara: Yanzu talakawa sun gane,

            Nera kia ba ta jawo su.

 

Jagora: Na iske wane na ta jawabi,

            Ya ce Sakkwato duk kaji muke,

            Shi bai biɗar mu sai ran zaɓe,

            Nan take za ya jawo mu.

Yara: Yanzu talakawa sun gane,

            Nera kia ba ta jawo su.

 

Jagora: Ko ƙara shiri in za ku shirawa,

            An ce mahaukaci ya rantce,

            Ya shedi ba ya kafara,

            Sai ya yi gwamna Sakkwato binni,

Yara: Irinta dauri ta dawo,

            Ha yau muna cikin ƙangi.

 

Jagora: Ko ƙara shiri in za ku shirawa,

            Ko ja ɗamara in za ku shirawa,

            An ce mahaukaci ya rantce,

            Ya shedi ba ya kaffara,

            Sai ya yi gwamna Sakkwato binni,

            In kunka yarda yay gwamna,

Yara: Irinta dauri ta dawo,

            Har yau muna cikin ƙangi.

 

Jagora: Idan ka gane ni da manyan kuɗɗi,

            Aljihuna ya cika damfam,

Yara: To ka tambaya malam,

            Tambari Tahida ya ba mu.

 

Jagora: Idan ka gane ni da manyan kuɗɗi,

            Aljihuna ya cika damfam,

Yara: To ka tambaya malam,

            Tambari Tahida ya ba mu.

 

Jagora: Idan ka ga babura sababbi,

            An lodo an kai Illela,

            Har ana biɗar gidan Ɗanbau,

Yara: To kar ka tambaya malan,

            Yahaya Buhari ya ba mu.

 

Jagora: Idan ka ga babura sababbi,

            An lodo an kai Illela,

            Har ana biɗar gidan Ɗanbau,

Yara: To kar ka tambaya malan,

            Yahaya Buhari ya ba mu.

 

Jagora: Idan ka ga riguna sababbi,

            Aska biyu cunkin Zazzau,

Yara: To kar ka tambaya malan,

            Ladan na Shuni ya ba mu.

 

Jagora: Idan ka ga riguna sababbi,

            Aska biyu cunkin Zazzau,

Yara: To kar ka tambaya malan,

            Ladan na Shuni ya ba mu.

 

Jagora: Na gaishe ka ciyaman fati,

            Arzika Tureta ɗan girma,

            Ka taimaka ma ‘ya’yan bunni,

            Ka taimaka ma ‘ya’yan ƙauye,

            Gulbi babu jira sai kwalhwa,

Yara: Kowa ishe ka ya samu.

 

Jagora: Na gaishe ka ciyaman fati,

            Arzika Tureta ɗan girma,

            Ka taimaka ma ‘ya’yan bunni,

            Ka taimaka ma ‘ya’yan ƙauye,

            Gulbi babu jira sai kwalhwa,

Yara: Kowa ishe ka ya samu.

 

Jagora: Baba,

Yara: Kowa ishe ka ya samu.

 

Jagora: Idan ka ga ne ni da babba mota,

            Kuma mota nan tsadadda ce,

            Kuma mota nan mai tsada ce,

            To Muntari ka ai mini mota,

Yara: To kar ka tambaya malan,

            Na ishe mataimakin gwamna.

 

Jagora: A idan ka a ne ni da mota babba,

            Kuma mota nan tsadadda ce,

            Alhaji Muntari ke ba ni,

Yara: To kar ka tambaya malan,

            Na ishe mataimakin gwamna.

 

Jagora: A gaishe ka mataimakin gwamna,

            Ga jikan Mahmudu Gummi,

            Ga ɗan Abubaka Gummi nan,

Ɗan malan kake jikan malan,

Yara: Yaƙinka ya yi rinjaye,

 

Jagora: Mataimaki gwamna,

            Muntari ɗan Shehu dattijo,

            Ga ɗan Abubakar Gummi,

            Ɗan Malam kake jikan malan,

Yaƙinka ya yi rinjaye.

 

Jagora: Na gode wa haji Muntari ɗan Bello,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta,

 

Jagora: A Muntari mai gona ɗan Bello,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Ɗalha Sidi uban Ɗanbau,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Turakun yaƙi ne na Sakkwato,

            Tsalha Sidi muna gaishe ka,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Alu A.A.  Alu Ɗan boko,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Alu A.A.  Alu Ɗan boko,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gaishe ka mai matasan bunni,

            A gaishe ka mai matasan ƙauye,

            Nasiru Itali na gode ma,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya ga Muntari ɗan Bello,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Muntari maigona ɗan Bello,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Na gaishe ka Usama Giyawa,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Em sai godiya Usama Giyawa,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Mai ban mota da ɗanbau,

            Don magatakarda Wamakko,

            Umar Tambuwal a gaishe ka,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Mai ban mota don in hau,

            Don Magatakarda Wamakko,

            Umar Tambuwal a gaishe ka,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Haji Aliyu ku gai sai,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Kabiru ɗan haya ina gaishe ka,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Kabiru ɗan haya ina gaishe ka,

Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ina ubandawaki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ina ubandawaki,

            Na gode ma,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Mai farin gida uban Ɗanbau,

            Ɗanɗa mana na gode ma,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gai da Ɗanɗa mana babban baƙo,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Kabiru Marafa na cida kai ɗa,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Tsoho Ata Alhaji na gode mai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Da kai aka zuwa a dawo da kaiya,

            Ni tsoho Ata sannu da aiki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ɗan takara majalisa ta Habuja,

            Ummaru Bature na gode mai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina kwamared na Aliyu Gamji,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Ibrahim Kwamared yay ɗa,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gaishe ka Nazi’a na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gaishe ka Nazi’a ɗan kirki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Isuhu Suleman na gode mai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Isuhu Suleman na gode ma,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Sarkin noma na jahar Sakkwato,

            Sa Jibrin Haji Mamman Bello,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Haji Bello Jibrin na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina sanata Abubakar Umar na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Mani Sardaunan Illela,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ina Haji Abu baƙi ɗan Liman,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Haji Abu baƙi ɗan Liman,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Na Alhaji Hasdi Haji Ɗanmalam,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ciaman Sanusi Ɗanwali,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ciyaman Sanusi Ɗanwali,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Jikan Liman Shehu Waliyin Allah,

            Hantsi Ɗanmaliki na gode mai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Hantsi Ɗanmaliki sannu da aiki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Zama da masoyi mai daɗi,

            Zama da masoyi mai daɗi ne,

            Ina Ibrahim Loto na Ɗangaskiya?

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Ibrahim Loto na Ɗangaskiya,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina haji Mai’akwa Yabo,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Ɗangaskiya ina Ibrahim?

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Em Abdurraziƙu na gode mai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Sarkin yaƙi na minista yay ɗa,

            Yahaya Buhari sannu da aiki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Yahaya Buhari sannu a himma,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In Arzika ɗan asali mai fata,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In koma Gada don in huta,

            Ciyaman masuki na gode mai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In Ahmadu Masuki sannu da aiki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ko ana batun maza Ɗanbau,

            Sai na tuna mata na ƙwarai,

            Alhajiya Rabi Giyawa,

            Ina ‘yar Amadu jikanyar Gatau?

Yara: A nagode miki Rabi Giyawa,

            ‘Yar Amadu,

 Du yanda ta yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina muka sauka garin Illela,

            Ina kula rungumi na gode,

 Yara: Du yanda ta yi ta kyauta.

 

Jagora: Ina ‘ya taniniyo ta kyauta,

Yara: Du yanda ta yi ta kyauta.

 

Jagora: A ina Kulu rungumi ban rena ba,

Yara: Du yanda ta yi ta kyauta.

 

Jagora: Ina ‘ya Taniniyo na gode,

Yara: Du yanda ta yi ta kyauta.

 

Jagora: A ina Balarabe Hassan na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Alhaji Baba Uwar yaƙi,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Haji Isuhu jinfa yay ɗa,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ciyaman can birni Wamakko,

            Ina Abu bakanike na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ciyaman Kware ina gode ma,

            Jafaru Ɗan sarki na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ni Jafaru Ɗansarki na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Waƙa ga ta mu mun suma ta,

            Mun fara ta da roƙon Allah,

            In Allah ya so ya yarda,

Yara: Gwamnan mu mun yi mun ƙare.

 

Jagora: Miloniya Alu A.A.

            Shi ne za ya ba ni 406,

 

Jagora: Miloniya Alu A.A.

            Shi ne za ya ba ni 406,

 

Jagora: Muntari Mafiya mai motoci,

            Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Muntari Mafiya na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Ahmed Muhammed Gudau,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Ahmed Muhammed Gusau Ɗanwaziri?

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: ‘yan yara na yi mamaki,

            ‘Yan yara na yi mamaki,

            An ce kwa ga raƙumi shi ga Buzu,

            Ga raƙumi cikin daji,

Yara: Sai ga ya ban ga Buzu ba.

 

Jagora: Ɗantakara zama gwamna Magatakarda,

            Wamakko Aliyu kar ka ɗau reni,

            Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.

 

Yara: Ɗantakara zama gwamna Magatakarda,

            Wamakko Aliyu kar ka ɗau reni,

            Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.

 

Jagora: In dai kana shirin yaƙi ka fito,

            In ka ga ba ka yi ka gaya min,

            Siyasar jahar ga in bar ta.

            Yaƙi sai da uwa ɗan Barade,

            Yaƙi babu uwa banza ne,

Yara: Har ƙarama zaman karta.

 

Jagora: Tsaya abin ga na da mamaki,

            Birni da ƙauye na duba,

            Kuma manya da yara na duba,

Yara: Duk inda ka ishe Ɗanabarba,

            Yi iya shirin munahunci.

 

Jagora: Tsaya abin ga na da mamaki,

            Birni da ƙauye na duba,

            Kuma manya da yara na duba,

Yara: Duk inda ka ishe Ɗanabarba,

            Yi iya shirin munahunci.

 

Jagora: Wawan,

Yara: Ya iya shirin azuzanci.

 

Jagora: A gaishe ku Sakkwatawan Shehu,

            Na tabbata kuna da ɗiyauci,

            Don ‘yan’abarba kun bar su,

            Sai yawo su kai suna ƙarya,

Yara: Duk sun rikirkice musu,

            Sai hwaɗa su kai da junansu,

            Harka su ta yi dameji.

 

Jagora: Ina Ɗanfakauniya wane,

            Ya leƙa Gabas, ya leƙa Yamma,

            Ya leƙa Kusum ya leƙa Arewa,

            Kullum wurin munahucci,

Yara: Ba Sakkwato noz ba har da Sakkwato sawuz,

            Ko Isa mun hi ƙarhinka.

 

Jagora: Kowa tasu tare da manya,

            Ka san yana da tarihi,

            Don haka manya sun ka gaya mini,

Yara: Danginsu Maguzawa ne.

 

Jagora: Idan kun shira ku ƙara shirawa,

            An ce mahaukaci ya rantce,

            Ya shedi ba ya kaffarci,

            Shi za shi gwamna Sakkwato birni

            In kunka yarda ya yi gwamna,

Yara: Irin ta dauri ta dawo,

            Har yau muna cikin ƙangi.

 

Jagora: Na iske wane na ta jawabi,

            Ya ce Sakkwato duk kaji muke,

            Shi bai biɗar mu sai ran zaɓe,

            Nan take za ya jawo mu,

Yara: Yanzu talakawa sun gane,

            Nera ka ba ta jawo su.

 

Jagora: Na gaishe ka Bello birnin Gwiwa,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Im Bello na Gwiwa ina gaishe ka,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora:  Im Nasiru mai mai birnin Wurno,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Im Nasiru mai mai birnin Wurno,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A dai gaishe ka ciyaman fati,

            Sharifu Isa na gode ma,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Sharifu Isa Baba na gode ma,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ciyaman Gwaranyo na gode mai,

            Mai hantci mai biredi sannu da aiki,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In Hantsi mai biredi sannu da aiki,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Na gode ma ciyaman Raɓah,

            Gaskiya Mu’azu na Rara,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gaishe ka dai Mu’azu na Rara,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ciyaman birnin Wamakko,

            Alu bakanike ina gaishe ka,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ciyaman Gudu Abu na gode,

Yara: Da yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ina Abuabakar Gudu na gode,

Da yanda ya yi ya kyauta.

Yara: (Amshi)

 

Jagora: Ciyaman Binji Ɗandattijo,

            Ina Nabunkari ina gaishe ka,

Da yanda ya yi ya kyauta.

Yara: (Amshi)

 

Jagora: Ina haji Sahabi Isa Gada,

Da yanda ya yi ya kyauta.

Yara: (Amshi)

 

Jagora: Ina haji Sahabi Isa Gada?

Da yanda ya yi ya kyauta.

Yara: (Amshi)

 

Jagora: Ciyaman na Yabo na gode ma,

            Saboda madawaki Ɗandattijo,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ina Sabo madawaki a gaishe ka,

Da yanda ya yi ya kyauta.

Yara: (Amshi)

 

Jagora: Na gode ma ciyaman Wurno,

            Sani Dinawa na gode.

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Sani Dinawa na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ɗantakarar zama gwamna

Magatakarda Wamakko,

            Aliyu kar ka ɗau reni,

            Kuma kar ka ɗau walƙanci.

 

Yara: Ɗantakarar zama gwamna,

            Magatakarda Wamakko,

            Aliyu kar ka ɗau reni,

            Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.

 

Jagora: Sai godiya ni kai Isuhu,

            A gaishe ka Ɗan Suleman yay ɗa,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Im Bello Yahaya birnin Wurno,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ciyaman fati Arzika kai ɗa,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Tsalha Sidi Mamman yay ɗa,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Sai na sauka garin Boɗinga,

            Ciyaman Abubakar ɗan tsara,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ciyaman Abubakar dan tsara,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Sardaunan shagari ku gai sai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Im ciyaman Shagari na gode,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In ciyaman Shagari Shehu,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Sardaunan Shagari ya yi ɗa,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ɗantakara zama gwamna,

            Magatakarda Wamakko,

            Aliyu kar ka ɗau reni,

            Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.

 

Yara: Ɗantakarar zama gwamna,

            Magatakarda Wamakko,

            Aliyu kar ka ɗau reni,

            Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.

 

Jagora: Na gaishe ka Tukur Laɓɓo,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In na gaishe ka Tukur Laɓɓo,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Alhaji Altine sannu da aiki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ni Alhaji Altine na gode ma,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gaishe ka Madugu Idi,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Alhaji Ɗahiru sarki ku gaisai,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ba ka kuɗi ba a ƙirga ba,

            Ɗan Damana na gode ma.

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A mai sai min mota sabuwa,

            Honda hala mai sanyi,

            Abba Aleru sannu da aiki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Im Abba Aleru sannu da cuki,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In dai kana shirin yaƙi ka fito,

            In ka ga ba ka yi ka gaya man,

            Siyasar jahar ga in bar ta,

            Yaƙi sai da uwa Ɗan Barade,

            Yaƙi babu uwa banza na.

Yara: Har ƙarama zaman karta.

 

Jagora: Ina Ibrahim Ɗangaskiya?

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A mai akwai na Yabo,

            Na gode ma.

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gaishe ka mai akwai Jareɗi,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Dole mu gaishe ka mai akwai Jareɗi,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Ciyaman bugun ciyamomi,

            Rai ya daɗe Haji Sani Aka,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: In jikan Magaji ɗan Iliyasu,

            Sani Aka uban Ɗanbau,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Sani na Sani mai dabi,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A ina baba Audu ɗan nakasara,

Yara: Du yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: Jagora: Mutanen Sakkwato ga ɗaya,

            Har yau yana cikin ƙangi.

Yara: (Amshi)

 

Jagora: Mutane Sakkwato kaf baki ɗai.

            Du wanda,

Yara: Ba ya PDP har yau yana cikin ƙangi.

 

Jagora: Sai dodiya ga Sardauna,

            Mijin ‘ya sarki Alhaji Mani.

Yara: (Amshi)

 

Jagora: A yanke mutum,

            A yanke dabba,

            Du tattalin baƙin tsafi,

            Don dai a hau kujera mulki,

Yara: In lokacinka ya ƙar,

            Tsahinka du na banza ne.

 

Jagora: Malam,

Yara: In lokacinka ya ƙare,

            Tsahinka duk na banza ne.

Post a Comment

0 Comments