Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Zan Sha Sha'awata Ta Dawo?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Slm dan Allah malam inasan a taimakamin da magani kwata kwata bana sha'awar mijina ko taɓani ya yi sai na ji wani iri kuma da ba haka nakeba dan Allah a taimaka.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

To 'yar uwa dalililai dayawa da ke haifar da wannan. Sai dai zan ta kai ta a kan abubuwa uku kaɗai.

1. Sha'awa takan gushe daga jikin Mace ta dalilin wata chuta da ke tare da ita. Misali kamar ciwon sanyi da sauran nau'o'in chutukan da ke shafar Mata a al'aurarsu.

2. Wani lokacin idan mace tana shan wasu Kwayoyi masu karfi na asibiti sukan gusar mata da sha'awa. Misali kamar magungunan hawan jini, ciwon Sugar, Sickler, Arthritis, Asthma, da sauransu.

3. SHAFAR ALJANU: Idan mace tana da matsalar shafar Aljanu (Musamman aljanun Soyayya) sukan ɗauke duk wata ni'ima daga jikinta kuma su haifar mata da daukewar sha'awa, ko jin zafi ya yin saduwa.

Wata ma da zarar ta kammala Jima'i da maigidanta za ta rika ganin Maniyyin yana zubewa.

Shawara a nan ita ce idan kina fama da wasu daga dalilan nan dana Lissafa, to lallai sai kin magance abun kafin kisha kowanne maganin don samun dawowar sha'awa ɗin.

Amma ga wata fa'idah nan ki jarraba :

1. Ki nemi ruwan kwakwa, madara peak, da kuma ruwan Inabi ki rika sha. Domin waɗannan duk sukan haddasa dawowar ni'ima ko sha'awa ajikin Mace ko namiji.

 

2. Ki samu shammar ki nika shi ki rika haɗawa da zuma kina sha. In Sha Allah za ki samu lafiya.

3. namiji wanda be cika damuwa da mace ba ko kuma wanda bashida kuzari kuma yana so ya ga yana gamsarda matarsa yana da kyau ya jarraba wannan wanda nasan wasu suna sayan garin amma ba su gane yanda ake haɗawa ba dabino za a ɓare a jefar da kwallon asamu yayan zogale da furensa dukkansu wadanda suka bushe a inuwa sannan sai garin habbatussauda a haɗasu waje ɗaya adakasu sannan ana diban garin ana sha da madara peak ko nono wannan mace ko namiji kowa yana sha sai dai ban da me ciki.

Allah ta'ala ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CFp8AF5lYJt7v6HZ3i6mjf

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments