Ticker

6/recent/ticker-posts

Banbancin Tsakanin Zinar Ido, Da Ta Jiki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Dafatan An Wuni lfy Malam dama tambaya Nike a kan Hukuncin Zinar ido ta hayar kallon abin da yake na haramu, Kuma da Banbancin da ke tsakanin Zinar jiki data ido.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Zinar ido (wato kallon abin da Allah ya haramta) da kuma zinar jiki da jiki, dukkaninsu laifuka ne masu girma. Domin kuwa Allah ya haramtasu a cikin Alƙur'ani da kuma hadisai ta harshen Annabinsa .

1. Zinar ido tana daga manyan hanyoyin da Shaiɗan yake bi domin jan mutane zuwa ga aikata zinar jiki da jiki. Shi ya sa ma Allah ya ce wa Annabinsa "Ka gaya wa muminai maza su runtse idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, wannan shi ya fi tsarkakewa gareku. Hakika Allah masani ne game da abin da suke aikatawa".

Imam Ibnu Katheer ya ce: "Wannan umurni ne daga Allah (SWT) zuwa ga bayin sa Muminai cewa su runtse idanuwansu daga kallon duk abin da ya haramta musu. Kada su kalli komai sai abin da ya halatta musu kallonsa".

Manzon Allah ya faɗa a cikin wani hadisi cewa "Kallo, wani kibiya ne mai dafi (poison) daga kibiyoyin iblees. Duk wanda ya barshi (wato ya bar kallon) domin tsorona, zan chanza masa da wani imani, zai ji ɗanɗanonsa a cikin zuciyarsa".

(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).

2. Ita kuwa zinar jiki da jiki, ai Manzon Allah ya ce "Bayan yin shirka da Allah, babu wani zunubi mafi girma kamar maniyyin da wani mutum ya sanya a cikin mahaifar da ba ta halatta gareshi ba". Kuma ya ce "Mazinaci ba zai yi zina alhali yana mumini ba". (Wato sai bayan an cire masa imani).

Zinar ido babu haddi a kanta. Amma zinar jiki da jiki, in dai shaidu suka tabbata a kan masu laifin, ko aka samu Iƙirari tabbatacce daga masu laifin, ana yi musu haddin bulala ɗari (100) idan basu taɓa aure ba. Idan kuma sun taɓa yin aure hukuncin rajamu ake musu (wato jefesu da duwatsu har sai sun mutu).

Kuma Manzon Allah ya bada labarin da ke nuna cewar ko da a cikin wuta, mazinata wajen azabtar da su ya bambanta, ya fi muni fiye da na sauran 'yan wuta. (Allah shi kiyaye mu da aikata zina, kuma ya kiyaye mu daga shiga wuta).

Allah ta'ala ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DTrJJCF04ƘpACEtA7hyu4R

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments