Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwaɗayi Mabuɗin Wahala

 Ta ce masa, "wani ɗan aiki za ka yi mini in biya ka dubu biyar." Duk da Danliti bai san matar ba, bai kuma taɓa ganin ta ba, ya ce ya yarda. Wanda ko naira ɗari ka ce za ka ba shi, zai iya share maka ƙunci ka sharara masa mari. Ga shi da rufin asiri amma son banza ya yi masa yawa. 


"Gaban Alkali za mu tafi," in ji matar, "ka ce masa kai mijina ne da ka yi tafiya, shekara uku ba ka gida, yanzu ka dawo ba ka ra'ayina, ka sake ni saki uku. Idan ka yi mini wannan zan ba ka dubu biyar cur!" 


Da suka tafi gaban Alkali, Danliti ya maimata magana kamar yadda matar nan ta tsara masa. Alkali ya ce, "Na kuwa shaida, matarka ta saku, saki uku." Danliti ya washe baki, wai har ya gama aikin dubu biyar. Ya yunƙura zai tashi, sai matar nan ta ce wa Alkali, "Allah ya kyauta aikin Malam, ashe ya kyautu miji ya yi tafiya tsawon shekara uku, bai san ci da shan matarsa ba, kuma ya dawo ya yi mata wannan irin yankan ƙauna! To, lalle ina ƙarar tsohon mijina da ya biya ni kuɗin abinci na shekaru uku."


Da aka buga lissafi, kuɗi suka tashi naira dubu ɗari uku da ashirin. Sai ta ce ya ba ta dubu dari uku, ta rage masa ashirin saboda tsohuwar soyayyar da ke tsakaninsu. Danliti ya haɗi yawu kut, idanu suka raina fata, sai zufa, kamar wanda ya haɗiye kunama. Ba dama ya ce ƙarya ya yi, Alkali ya sa a daure shi, ko ma a haɗa masa da bulala. Ya tarkato kuɗi ya ba matar. Ta zare dubu biyar ta ba Alkali ta ce, "Allah gafarta Malam, akwai bashi na dubu biyar tsakanina da tsohon mijina, ga shi na biya a gabanka."

Kwaɗayi Mabuɗin Wahala

Post a Comment

0 Comments