Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Da Olcer, Kuma Ana Bi Na Azumi Na Shekara Uku Saboda Haihuwa Da Shayarwa, Ya Zan Yi?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, ya zan yi ramuwar azimin shekara uku da ban yi ba a dalilin haihuwa kuma ina da olsa kuma mai sa ni yinwa da wuri ce?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumus Salamu, a lokacin da Allah S.W.T. ya wajabta yin azumin Ramadana a kan Muminai, sai ya kawo sauƙi ga marasa lafiya da matafiya a kan shan azumin, su kuma rama a wasu ranakun na daban, da kuma ya matsa gaba sai ya ce: "Abin da ke kan waɗanda ba sa iya azumin shi ne fidiya, ciyar da miskinai..."

Suratul Baƙara, aya ta 183 - 184.

Malamai sun yi ma wannan aya fassarori mabambanta, amma ba za mu tsawaita bayaninsu a nan ba, kawai abin da ke kan ki shi ne kowane azumi ɗaya ki ciyar masa da miskini ɗaya a madadinsa. Kuma wannan shi ne hukuncin waɗanda suka gaza yin azumi saboda tsananin tsufa, ko rashin lafiyar da ba ta da alamar warkewa, kuma ba za ta barsu su iya yin azumi ba, kamar yadda waccan ayar ta tabbtar.

Don neman ƙarin bayani sai a duba Aljámi'u Li'ahkamil Ƙur'an 1/668-67.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments