Ina Da Ulcer Zan Rama Azumi Ne Ko Ciyarwa Zan Yi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum malam

    Ina da ulcer kuma bana iya awa huɗu banci abinci ba kuma ina shayarwa zan, iya ciyarwa ko inna warke zan rama kuma ana bina huɗu nabara ban rama ba ina laulayi anabina uku danace zan in ALLAH yabiyamin wata bukatata

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Toh a nan abun da yake a kanki shi ne idan ulcer dince tasa ba za ki iya azumi ba toh ba za ki ciyar ba jira za ki yi idan kin warke seki rama. In kuma likitanki ya ce miki wannan irin ciwon naki bincike yanuna cewa ba a cika warkewaba da ciwon ake mutuwa toh a nan shi ne kawai seki ciyar kuma ko da daga baya Allah ya sa kin warke to ba za ki ramaba. Amma idan ba don ulcer ɗin ba ne kika kasa azumin A'a ciki ne da ke ko kuma kina shayarwa shi ne ya sa ba za ki yi azumiba toh wannan kawai ciyarwane a kanki ba za ki ramaba. Amma akwai saɓani domin wasu malamai suna ganin akasin abun da na faɗa, sedai kuma ni wannan shi ne na gamsu da shi kuma shi ne fahimtar me littafin Alwajiz fi fiƙhis sunnah. Amma wadancan guda ukun wadanda ake binki na bakance toh sukuma wadannan ba za ki ciyarba jira za ki yi inkin warke seki yisu. In kuma har kika mutu bakiyiba toh magadanki za su yi miki azumin ba ciyarwaba azumi za su yi.

    WALLAHU TA'AALA A'ALAM

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    ************************************** 

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.