Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Fama Da Ciwon Qoda, Zan Iya Ciyarwa A Maimakon Azumi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malamina ina da tambaya, mace ce ba ta da lafiya, ciwon ko da ya fara tsananta gare ta, sai satinnan likitoci suka ba ta shawara duk bayan minti talatin ta ci wani abu daga Abinci amma kar ta ƙoshi, to malam yaya za a billowa maganar Azumin da ta sha, ciyarwa za a cigaba da yi ko jira za a yi sai ta warke ta rama?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

 Wa alaikum assalam, in har tana tunanin samun sauƙi kafin wani azumin ya zo, ba za ta ciyar ba, za ta bari ta rama bayan ta samu dama, saboda aya ta: 184 a suratul Baƙara ta nuna cewa: wajibin mara lafiya shi ne rama azumin da bai yi ba na Ramadan bayan ya samu dama a wasu kwanakin.

Matukar likitoci sun tabbatar ba za ta samu sauƙin da za ta rama azumi daga baya ba, ya halatta ta ciyar a maimakon kowacce rana.

Allah ne mafi sani.

Wa alaikum assalam, in har tana tunanin samun sauqi kafin wani azumin ya zo, ba za ta ciyar ba, za ta bari ta rama bayan ta samu dama, saboda aya ta: 184 a suratul Baqara ta nuna cewa: wajibin mara lafiya shi ne rama azumin da bai yi ba na Ramadan bayan ya samu dama a wasu kwanakin.

أَيَّامًا مَّعْدُودَاتٍ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ وَأَن تَصُومُوا خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ

Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhri to, shi ne mafi alhri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhri a gare ku idan kun kasance kuna sani. (suratul Baqara aya ta 184)

Matukar likitoci sun tabbatar ba za ta samu sauqin da za ta rama azumi daga baya ba, ya halatta ta ciyar a maimakon kowacce rana.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments