𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam tanbayana shi ne ina da miji yanzu a haka 'ya'yanmu 3 amma baya sallah. Ba yadda banyi ba idan ya fara sai ya bari amma sallar Juma’a ba ya wuce shi yanzu a haka mahaifina ya ce zai yi karar sa ya sake ni tun da baya Sallah to malam in kashe auren ne ko yaya?
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Tabbas idan har an yi masa nasiha amma bai ji ba, to
bai halatta ki cigaba da zama amatsayin matarsa ba. Domin kuwa akwai sashen
Malaman Musulunci da ke ganin cewa ko da sallah guda ce mutum ya barta da
gangan to ya kafirta, balle kuma shi Mijin naki wanda ba ya yin dukkan sallolin
ma in ban da Juma'a.
Abin lura a nan shi ne tun ranar da aka ɗaura aurenku aka damƙa masa amanar ciyar da ke da tufatar dake, da kuma koyar da
ke addini. To Mutumin da shi kansa ba ya yin sallah, ta yaya zai koyar da ke addini?.
Ta yaya zai koya ma 'ya'yanku kulawa da muhimmancin sallah? Cigaba da zama da
shi awannan halin zai iya kaiwa zuwa ga lalacewar taki tarbiyyar ma. Kuma zai
wahala bai lalata tarbiyyar yaran naku ba.
Manzon Allah ﷺ ya ce: "SALLAH ITA CE
GINSHIKIN ADDINI. WANDA YA TSAYAR DA ITA, TO HAKIKA YA TSAYAR DA ADDINI. WANDA
KUMA YA RUSHETA TO HAKIKA YA RUSA ADDINI". Kuma ya fa'da a cikin wani
hadisin wanda Muslim ya ruwaito: "TSAKANIN MUTUM DA TSAKANIN SHIRKA DA
KAFIRCI shi ne BARIN YIN SALLAH".
WALLAHU A'ALAM.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.