𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam ni ne aka ba ni yin istigfari da hailala ina yi kullum kuma aka ce na yi alkawari tsakanina da Allah ba zan dena yi ba har mutuwa, kullum zan dinga yi idan ban samu na yi ba sai na rama, to malam lokacin da na karba ɗin ban san yaya girman alkawari yake ba, to malam ya matsayin alkawarin da na yi yake? Kuma a yanzu sha'anin rayuwa ya sa ba kullum nake samu na yi ba saboda yau da gobe sai Allah.
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa'alaikumus salam, yar'uwa ba wani matsala don
kin saɓa wannan alƙawari, saboda ai shi
istigfari da hailala idan kin yi su kan ki kika yi mawa, ba wani ne zai sami
ladar da ake samu ba idan kin yi, don haka mene ne na wani sa masa sharaɗin da babu shi a Alƙur'ani da Sunnar Annabi ﷺ, kuma babu shi a ijmá'in
malaman Musulunci? Lallai yana da matuƙar muhimmanci kowane musulmi
ya dage wajen yin istigfári da hailala a da sauran zikirori a kowane lokaci,
saboda an ruwaito cewa Manzon Allah ﷺ ya kasance yana ambaton
Allah a dukkan halin da yake ciki.
Duba Sahihu Muslim 373.
Saboda haka, ke nan babu buƙatar sai an sa wa bawa wani sharaɗi ko alƙawari a kan zai riƙa yin istigfári a kullum, kuma har ma wai idan bai yi ba sai ya rama, lallai ba a ruwaito wannan daga Annabi ﷺ ba, wanda kuma shi ne mai shar'antawa ba waninsa ba. Saboda haka wannan alƙawarin dama ɓatacce ne, ba a gina shi a bisa ingantaccen dalili na shari'a ba. Jama'a lallai mu riƙi istigfári kamar yadda shari'a ta koyar, lallai yawan istigfári yana fitar da bawa daga ƙuncin rayuwa na duniya da lahira.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.