Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Addu'a Da Yaren Da Ba Larabci Ba A Sujjada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Akramakallahu mutum zai iya yin addu'ar neman wani abu a sujudar sallar farilla da wani yare koma bayan larabci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ɗan'uwa Annabi S.A.W yana cewa: "Amma sujjada to ku dage da addu'a saboda ya kusa a amsa muku" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 479.

Malamai sun yi saɓani akan yin addu'a a sujjada da yaran da ba larabci ba, amma zance mafi inganci shi ne halaccin yin addu'ar da take ta neman wani abu a wajan Allah da yaran da ba larabci ba ga wanda bai iya larabci ba, saboda Allah ba ya kallafawa rai sai abin da za ta iya, sannan kuma Allah yana gane duk yaren da mutum ya yi addu'a da shi, amma wasu malaman sun karhanta yin zikirorin da suka zo a hadisi da yaran da ba larabci, saboda Annabi S.A.W ya fade su ne don su zama ibada, wannan yasa ba za a canza su da wasu lafuzan ba.

Duba :Muhallah na Ibnu hazm 4\159 da Majmu'ul fataawa na Ibnu-taimiyya 22\488.

Allah ne mafi Sani

Amsawa:- Dr. Jamilu

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwaa Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments