Ticker

6/recent/ticker-posts

Sharuddan Amsar Addu'a

Sharuɗɗan Amsar Addu'a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alikum Malam ina da tambaya: Mene ne sharuɗdɗan yin addu, a?Maana wanne sharaɗi za ka cika kafin addu'arka ta karɓu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Allah s.w.t yana karɓar addu'ar bawansa idan bawan ya cika wasu sharuɗɗa kamar haka:

1- Tsantsnta addu'ar ga Allah kaɗai: Ma'ana: ya zama Allah kaɗai ya roƙa kuma gare shi kaɗai ya sallama wa lamurransa bai haɗa shi da kowa ba.

2- Dacewa da koyarwar Manzon Allah s.a.w cikin addu'ar: Saboda addu'a ibada ce kamar sauran ibadu, ibada kuwa ba ta karɓuwa sai ta dace da koyarwar Manzon Allah s.a.w.

3- Yardar zuciya da sakankancewa: Yayin da kake addu'ar da bayanta ka zama mai gamsuwa da yaƙini a zuciyarka cewa Allah zai karɓi addu'arka. Ko da ka ga jinkiri ka nutsu da cewa lallai sakamako yana nan tafe matuƙar ba an ci karo da wani dalili da zai hana a biya maka buƙatarka na daga wasu laifukanka ko rashin dacewar buƙatar da kai ba.

4- Halartowar zuciya da khushu'i da ƙasƙantar da kai ga Allah yayin addu'a.

5- Ƙarfin azama: kada ka roƙi Allah kana mai taraddudi abin zai yiwu ko ba zai yiwu ba, ka roƙi Allah roƙo na yankan shakku.

6- Nisantar cin haram: Ka tsarkake cikinsa da jikinsa daga haram.

7- Kada abin da za ka roƙa ya zama haram ne ko yanke zumunci.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwaa Sunnah.

SHARUƊƊAN AMSAR ADDU'A

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alikum Malam ina da tambaya: Mene ne sharuɗdɗan yin addu, a? Ma'ana wanne sharaɗi za ka cika kafin addu'arka ta karɓu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh.

Allah s.w.t yana karɓar addu'ar bawansa idan bawan ya cika wasu sharuɗɗa kamar haka

1. Tsantsanta addu'ar ga Allah kaɗai: Ma'ana: ya zama Allah kaɗai ya roƙa kuma gare shi kaɗai ya sallama wa lamurransa bai haɗa shi da kowa ba.

2. Dacewa da koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cikin addu'ar: Saboda addu'a ibada ce kamar sauran ibadu, ibada kuwa ba ta karɓuwa sai ta dace da koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

3. Yardar zuciya da sakankancewa: Yayin da kake addu'ar da bayanta ka zama mai gamsuwa da yaƙini a zuciyarka cewa Allah zai karɓi addu'arka. Ko da ka ga jinkiri ka nutsu da cewa lallai sakamako yana nan tafe matuƙar ba an ci karo da wani dalili da zai hana a biya maka buƙatarka na daga wasu laifukanka ko rashin dacewar buƙatar da kai ba.

4. Halartowar zuciya da khushu'i da ƙasƙantar da kai ga Allah yayin addu'a.

5. Ƙarfin azama: kada ka roƙi Allah kana mai taraddudi abin zai yiwu ko ba zai yiwu ba, ka roƙi Allah roƙo na yankan shakku.

6. Nisantar cin haram: Ka tsarkake cikinsa da jikinsa daga haram. Yana daga cikin sharaɗin addu'a musulmi ya kasance babu haram a cikinsa (baici abincin haram ko abin sha na haram ba),

7. Kada abin da za ka roƙa ya zama haram ne.

8. Musulmi ya kasance bai yanke zumunta ba.

9. Nisanci Neman gaggawar karɓawa. Ya tabbata a hadisi cewa; An Karɓo daga Abu Hurayrah (R.A) Ya ce; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Ya ce: (Allah) yana karɓawa ɗayanku (addu'arsa) matuqar baiyi gaggawa ba, (shi ne) ya ce nayi addu'a (amma har yanzu) ba a amsamin ba. (Bukhari, 5865. Muslim, 2735).

10. Akwai wasu lokuta idan bawa yayi addu'a Allah na karɓa masa kai tsaye. Misali kamar sulusin dare na karshe kamar yadda ya tabbata a hadisi.

11. An karbo hadisi daga Buraidata (r.a) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنِّي أَشْهَدُ أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ الأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ

MA'ANA: "Ya Allah hakika ina rokonka, na shaida kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai, makaɗaici, madawwami, wanda ba ya haifuwa kuma ba a haife shi ba, kuma babu wanda ya kai shi." sai manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: “Lallai ka yi roƙo da sunan da Idan aka yi roƙo da shi ana bayarwa, kuma idan aka yi addu'a da shi ana amsawa". mutane huɗu suka ruwaito shi, Ibn Hibban ya inganta shi.

Wannan hadisin na nuna mana ke nan ana saurin Amsa addu'ar Wanda ya yi amfani da waɗannan sunayen ke nan. Don haka Idan mutum zaiyi addu'a, sai ya fara ambaton waɗancan sunayen, sannan sai addu'ar ta biyo baya.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Ya ce : "hakika ubangijinku mai kunya ne, mai karamci ne. yana jin kunyar bawansa yayin da ya cira hannayensa ya rokeshi, ace ya mayar dasu ba tare da komai ba".

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa... 

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments