Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mace Da Takeyin Haila Sau Biyu A Wata?

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin meyene hukuncin mace da takeyin jini sau biyu a wata?

Sannan kuma idan lokacin da take cikin jini wallahi tana shan wahala sosai dan sai taji kamar za ta bar duniya gaba daya

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Toh asali a shara'a ya tabbata Mace za ta iya yin haila sama da sau ɗaya a cikin wata guda. Idan aka koma can cikin Sahihul Bukhari ya kawo hadisin Matar da tagama idda a cikin wata guda. Kuma haila uku ta yi a cikin wata ɗaya. Dan haka wannan abune sananne kamar yadda Sheikh Binbaz shi ma ya tabbatarda hakan a cikin Fatawarsa. Amma batun tanajin ciwo toh wannan kuma aikin likitocine setaje ta yi musu bayani ba fanninmu ba ne. Mu namu a nan kawai shi ne mu gaya mata tuntuni ansamu matanda suka yi haila sama da sau ɗaya a cikin wata guda. Sekuma mu tayata addu'a Allah yabata lafiya

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/ECƘsg2ycfS0FUI3fHfIdjƙ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments