Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarbiyyar Yara A Musulunci - Darasi Na 17

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

 Question and Answers in Islam

Iyaye maza da mata kune kike fara bawa 'ƴa'ƴanku gudun mawar lalacewa tun suna matakin shan nono har izuwa fara rarrafe har zuwa ga lokacin da suka fara mallakar hankalin kasanu.

Dalili kuwa bakwa iya tausasa harshenku a kan 'ƴa'ƴanku, ɗan laifi kaɗan yaro ko yarinya za ta yi ko da ɗan kuka jariri ya yi sai kaji mahaifiyarsa tana cewa ɗan iskan yaron nan, ko 'ƴar iskar yarinyar nan, bakusan cewa kalamanku suna tasiri akansu ba?

Ko kuma ku rinƙa kiransu da shegen yaro ko shegiyar yarinyarnan ta fiya yawan kuka, ko kuma a zageta a ce dan ubanta ko dan uwarta koma a danna mata ashar wanda hakan yana tasiri a kan yaran tun suna farkon haihuwarsu.

Bakin iyaye yana saurin kama 'ƴa'ƴansu da gaggawa na fatan alkhairi ko sharri, da zarar kuna aibantasu to sai wannan aibin ya kamasu, da zarar kuna zaginsu sai wannan zagin ya tabbatu akansu, shiyasa yara a wannan zamanin ba sa tausayawa iyayensu.

Abin mamaki sai kaji yara suna zage iyayensu a cikin wasa kuma zagi mai muni idan kaji irin kalmomin da suke amfani dasu sai abin sai ya baka tsoro, kamar ba 'ƴa'ƴan musulmi ba.

Lallai iyaye kuji tsoron ALLAH ku kiyaye harsunanku a kan yaranku mutuƙar kunaso su rinƙa yi muku addu'a bayan ranku, a ya yin da kuke cikin ƙabarinku, idan kuwa kuka cigaba da zaginsu da kuma yin zagi agabansu to kuna cikin ƙabarinku za ku rinƙa samun saƙon zagi yana shigo muku.

 

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce ALLAH ya tsinewa mai zagin iyayensa.

 

Wato mutum yana zagin iyayensa ne ta hanyar zagin iyayen wasu, idan ka zagi iyayen wani idan bai ramaba to naka ka zaga, idan kuwa ya rama dukkanku kun haɗu kun zagi iyayenku kuma kun zama tsinannu domin ALLAH ya tsine muku.

 

ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

 

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen ya ALLAH.

Post a Comment

0 Comments