Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Ɗaga Hannu Lokacin Addu'a 🤲

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam ina da tambaya mallam ya halarta kana addu'a kana ronkon Allah ka daga hannunka sama? 🤲

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam. Eh lallai ya halatta mutum ya daga hannunshi lokacin addu'a, hadisai da yawa sun nuna hakan kamar hadisin da Annabi ke cewa " lallai Ubangijinku mai kunya ne mai karamci ne yana kunyar bawa ya daga hanunshi ya roƙeshi amma ya mayar dasu batare da komai ba" haka manzon Allah ya lissafa daga hannu ya yin addu'a cikin sabbuban amsa addu'a, dan haka ya halatta, sai dai inda manzon Allah bai daga hanu ba ba za mu daga ba, kamar lokacin da liman ke hudubar juma'a, ko tsakanin sujjada biyu, ke nan in da Annabi ya daga za mu daga, in da bai daga ba ba za mu daga ba, a addu'oinmu na yau da gobe za mu daga matuƙar shari'a ba ta hanamu ba.

Allah ne mafi sani

Amsawa:🏻

ABDULLAHI ISMAIL AHMAD.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments