Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayar Da Kuɗin Kashewa Ba Wajibi Ba Ne A Kan Miji

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam, Dan Allah ga wata tambaya ataimaka Mana da amsar ta, wata aminiyata ce take so a taimaka mata, ita dai ta kasance mijin ta yana da Hali sosai kuma kullum Yana Mata duk laluranta wadanda Allah ya daura mishi a kanshi, to Amma ba ya daukan kuɗi haka kawai ya ba ta, to shi ne ita kuma sai ta yi ma mijin karya cewa wasu masu neman taimako sun zo da lalura sun ce Dan Allah ya taimaka musu, to idan ya bayar se ta rike, ko kuma idan masu neman taimakon na gaskiya suka zo in ta fada mishi in ya ba ta se ta cire wani Abu a ciki ta ba su sauran, shi ne ta keso taji wannan kuɗin da ta ke ci, mene ne matsayinta?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa’alaikumus Salam, In ta yi haka ta ci haramun, ta kuma yi Algus, Annabi yana cewa “Wanda ya yi Algus ba ya cikinmu” kamar yadda Muslim ya rawaito.

Allah da Manzonsa ba su wajabtawa miji ya bawa matarsa kuɗin kashewa ba, abin da aka wajabta masa shi ne Ciyar da ita da Shayar da ita, yi mata Sutura, da yi mata duk abin da rayuwarta ba za ta tafi ba sai da shi gwargwadon halinsa, kamar yadda ayar suratu Addalak da hadisai ingantattu suka tabbatar.

Ba da extra kuɗi ba wajibi ba ne, tare da cewa kyautatawa iyali abu ne mai kyau, Annabi yana cewa “Mafi alkairinku shi ne wanda ya fi kyautatawa iyalansa”, wannan sai yake nuna cewa: Mijin da yake bada kuɗin kashewa ya fi wanda ba ya bayarwa.

Babu bukatar ta bi ta hanyar Algus, idan ta lallabi mijinta, ta yi masa biyayya, za ta same shi a hannunta.

Allah ne mafi sani.

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments