Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukunce-Hukuncen Jinin Haila Dana Haihuwa Darasi Na [03]

  JININ HAIHUWA (JININ BIKI)

Jinin Biki wani jini ne da yake fitowa a lokacin haihuwa, wasu daga cikin maluman musulunci su kace:

 Wani jini ne da mahaifa take turo shi a lokacin haihuwa, ko kafin haihuwa da kwana biyu ko uku, ko bayan ta tareda naƙuda.

ƘARANCIN KWANAKIN SA DA TSAWON KWANAKIN SA

Ƙarancinsa bashi da kwanaki takamammu, kawai duk lokacin da mace taga alamar tsarki wato bushewar gaba ko farin ruwa, ko da kafin kwana arba‘in ne,to za ta yi wanka taci gaba da yin sauran ibadu.

Tsahonsa kuwa baya wuce kwana arba‘in, domin kiwa duk wacce jinin haihuwarta ya cika kwana arba‘in bai tsaya ba, za ta yi wanka ta cigaba da yin sauran ibadun ta, saboda tsawon kwanakinsa shi ne kwana arba‘in, kamar yadda ya zo a nassin hadisin Manzon ALLAH {s.a.w}.

 HUKUNCE-HUKUNCEN SA

Hukunce-hukuncen jinin haihuwa kamar jinin haila ne, cikin abubuwan da yake halattawa ko

haramtawa ban da abubuwa masu zuwa:

Na farko: Idda:

Ba a lissafa shi a cikin idda idan an saki mace, amma ana irga na haila.

 Abin nufi idan aka saki mace ko mijinta ya rasu lokacin da take da ciki, iddar ta tana ƙarewa ne da haihuwa, bawai da jinin haihuwar ba.

 

 Amma idan aka sake ta bayan ta haihu, to za ta jira dawowar jinin haila ne sannan ta yi jini uku.

 

Na biyu: Balaga:

 

Jinin haila alama ne na mace ta balaga saɓanin jinin haihuwa.

Na uku: Saki:

Haramun ne mutum ya saki matarsa a lokacin da take yin jinin haila saɓanin jinin haihuwa.

 TAMBAYOYI DA AMSOSHIN SU

TAMBAYA:

Meye hukuncin wacce jinin haihuwarta ya ɗauke sannan ya dawo a cikin kwana arba‘in?

AMSA:

 Matuƙar a cikin kwanaki arbain ɗin data haihu ne jinin haihuwa ne, hukuncin ta ɗaya da mai jinin haihuwa.

TAMBAYA:

 Idan mace ta haihu shin za ta iya fita daga gidan ta kafin ta yi tsarki daga jinin haihuwa saboda wata buƙata?

AMSA:

 Babu laifi, matuƙar buƙatace za ta fitar da ita, amma idan ba haka ba zamanta a gidanta shi yafimata.

TAMBAYA:

 Idan mace mai ciki taga jini dafda haihuwar ta shin za ta bar yin sallah da azumi saboda wannan jinin?

AMSA:

 Idan taganshi tareda jin ciwon naƙuda, to jinin haihuwa ne, ba za ta yi sallah da azumi ba, amma idan jinin ne kawai babu ciwon naƙuda a tare dashi, to za ta yi sallar ta da sauran ibadu, saboda jinin cuta ne.

TAMBAYA:

 Meye hukuncin wacce ta haihu ta hanyar tiyata, shin za ta yi wankan tsarki?

AMSA:

 Idan taga jini ya fito daga mafitar sa, to hukuncin ta hukuncin mai jinin haihuwa ne, ba za ta yi sallah ba har sai ta yi tsarki, idan kuma ba ta ga jini ba, to za ta yi wanka ta cigaba da sauran ibadun ta.

TAMBAYA:

 Meye hukuncin wacce ta haihu ba tare da jinin haihuwa ya fito ba?

AMSA:

 Za ta yi wanka ta cigaba da dukkanin ibadun ta, basai ta jira ta yi har kwana arba'in ba.

TAMBAYA:

 Shin mace za ta iya aure a lokacin da take jinin haihuwa?

AMSA:

Za ta iya, amma baya halatta mijin ya sadu da ita, sai bayan ta yi tsarki.

ALLAH shi ne mafi sani.

Duk mai neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments