Ticker

6/recent/ticker-posts

Na haɗu da yar maɗigo, ta tsunduma ni a cikin harkar, mene ne mafita?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

İna wuni Malam dan Allah ina da tambaya Malam na farayin facebook a dalilin haka wata ta turo mun friend reƙuest ashe yar Lesbian ce to Malam sai ta tura min hoton ta na batsa, watarana ma Ni nake tambaya to Malam yanzu har ya zame min ina shiga ina searching dakaina ina gani na yi na yi in hana kaina na kasa sai na bari watarana sai na kara komawa

Toh Malam shi ne nake neman Shawara kuma ina tsoron na dena mata magana taga kaman na yaudare ta Malam dan Allah mene ne mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Da Alama ta yi Miki Wasu Abubuwa guda Biyu da suke yi wa Waɗanda suke son suna Yin LESBIAN da su.

Na farko. Da Alama ta yi Miki Sihirin da ba za ki iya Rabuwa da ita ba. Domin wannan shi ne Mataki Na Farko da suke Bi Wajen Kulla Alaka da Waɗanda suke son Suna yin Wannan Musifar da su. Shi ya sa ma har ba kya son Rabuwa da ita. Har da kike jin Cewar Kar Tace kin yi Mata Wulakanci.

Na biyu Kuma. Da Alama Ta Nuna Miki Mu'amula Irin ta su ta yan Lesbians. Ma'ana ko ta Kashe Miki kuɗi. Irin yadda Suka Yi ke nan. Sai Suna yi wa Mace Dunkuna da Turaruka da Kayan Kwalliya da Sauransu. Allah ya Sawwake.

Indai ba Kin Tsunduma ne a cikin Wannan Harkar ba. Wanda ni a Tunani na kinyi Nisa a Cikin Harkar. Tinda kina cewa kar Abokiyar Wannan Harkar taki tana ganin Kinyi Mata Wulakanci. Sannan Kuma kina son ki dena amma kin kasa denawa. To tinda Har Kin Nemi Shawara ta, A shawara idan har kina son ki dena, kuma denawa na tsakani da Allah. To Ki Hakura da Babbar Wayar da kike Amfani da ita. Wadda ita ce Silar ta kaiki ga aikata wannan Masifar. Domin ta dalilin wannan Babbar wayar ne Ta Aiko Miki Friend Reƙuest Ke kuma Kika yi Accepting Ɗin ta.

 Abu na Biyu. Ki Cire wannan Layin da kike Amfani da shi. Wanda ta sanki da shi. kin ga ke nan ko da ta kira ki ba za ta same ki ba. A haka har ta Hakura da nemanki a waya. Kuma za ki cire ki dena Amfani da shi Ne na Har Abada. Domin Muddin kika Sanya Wannan Layin za ki Ji Kiranta ya Shigo. Sabida Yan Bala'i ne waɗannan Mutanen. Sai dai kuma Allah ya sa ba ta san Garinku ba. Domin Matukar ta san Garinku idan ta nemeki ba ta same ki ba. za ta zo har inda kike. Muddun Kuka Haɗu da ita sai ta yi Wannan Abin da ke. Domin haka Suke yi.

 Sun Taɓa Biyo Wani yaro daga ganin Hotonsa ya yi irin Askin Banza ya tura ta Facebook a page Nasa. Ashe irin Askin su ne. Shi bai sani ba. Suka Kulla Abota da shi. rana ɗaya suka zo har garinsu, Wai sai sun Tafi da Shi sun yi Homo da shi. Da kyar Mutane suka kwace Shi a Hannunsu.

 A ƙarshe Kuma ki ji Tsorin Allah. Domin Wallahi na tabbata idan kika Mutu Baki dena Aikata Wannan Masifar ba Wallahi Wuta zaki. Kuma tin daga kabari za ki fuskanci Bala'i Kala-kala. Kai tin daga karɓar Rayin ki ma Al'ummar da aka ɗauki Rayin ki a Gabansu. za su san cewar baki cika da Imani ba. Domin Mala'ikun da suka zo karɓar Rayinki. Sun dinga Fincikar sa ke nan. A haka kina Ihu za su Rabaki da shi. Sai kuma Bala'in Kabari, kafin Bala'in Lahira.

 Sabida Wallahi Masu Wannan Harkar. Maza ko Mata. Ba sa Mutuwa a cikin Rahamar Ubangiji.

Sabida haka Ki kama Istigfari da Kuka a gaban Ubangijinki da Kuma Nadamar Aikata Abin da Kika yi a baya. Ko kin samu ki Rabauta daga Fushin Ubangiji.

Allah shi ne Masani.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments