Ticker

6/recent/ticker-posts

Ana Bi Na Ramakon Azumi, Amma Ina Kokonton Yawansu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Mal Mace ce Tasha Rabin azumi kuma bayan Azumin Ya wuce ta ranka Sai dai ba duka ba yanzuxu Tana so ta ida Amma ta manta Azumi Nawa ta yi baya Tana ganin ba ta yi Rabi ba kuma Tana ganin kamar ta yi rabi Amma ita ta manta Dan Allah Mal Ya za ta yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam, za ta yi gini ne a kan tabbas wajan ramako, misali idan kına zaton ashirin suka rage miki ko kuma ashirin da biyar, to sai ki rama ashirin da biyar (25), saboda in kin yi haka za ki fita daga kokwanto, kuma zai zama tabbas kin rama abin da ake binki.

Allah ne mafi sani.

Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

 ************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments