Ticker

6/recent/ticker-posts

"Ka Yi Biyu Saura Biyu" - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.


Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza

            Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ka yi biyu yau saura biyu,

            Ga ka difiti gwamna ga ka sarkin Yamma Sakkwato,

            Sai in ka zama gwamna a Sakkwato.

Yara: Sannan a ba ka Barade cikin gida.

 

Jagora: Sai in ka zama gwamna a sakkwato,

Yara: Sannan a ba ka Barade cikin gida.

 

Jagora: Ka ga sarauta sarki Yamma,

            Ba fa sarautar yaro ce ba,

            Sai an zaɓi mutum mai kirki,

Yara: A ba shi sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ka ga sarauta sarkin Yamma,

            Ba fa sarautar yaro ce ba.

            Ba ko sarauta wargi ce ba,

            Sai an zaɓi mutum mai kirki,

Yara: A ba shi arkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Na yi mahwalki jiya mai daɗi,

            Amma hwa ban magana,

            Sai ya zao,

Yara: Allah ya sa ya zame ma gaskiya.

 

Jagora: Na yi mahwalki jiya mai daɗi,

            Amma hwa ban magana,

            Sai ya zao,

Yara: Allah ya sa ya zame ma gaskiya.

 

Jagora: In Allah ya so ya yarda,

            Tutawuza sabin in ta zo,

Yara: Kai za ka gwamna jaharmu ta Sakkwato.

 

Jagora: In Allah ya so ya yarda,

            Tutawuza sabin in ta zo,

Yara: Kai za ka gwamna jaharmu ta Sakkwato.

 

Jagora: Ko mu masu adawa mun saki,

Yara: Saboda mun ga alamun gaskiya.

 

Jagora: Ko mu masa adawa mun bari,

Yara: Saboda mun ga alamun gaskiya.

 

Jagora: Ran Juma’a na kwan mamaki,

            An yi sarautu Sakkwato bunni,

            Mai korin shi adda mutane,

            An yi naɗi kowa ya watce,

            Mai jama’a ya kwashi abi nai,

            Sai ni biya garka wani sarki,

            Ni ishe ‘yan banga sun taru,

Yara: Da haka ‘yan shuli ɗai ni gani.

 

Jagora: Ran Juma’a na kwan mamaki,

            An yi sarautu Sakkwato bunni,

            Mai korin shi adda mutane,

            An yi naɗi kowa ya watce,

            Mai jama’a ya kwashi abi nai,

            Sai ni biya garka wani sarki,

            Ni ishe ‘yan banga sun taru,

Yara: Da haka ‘yan shuli ɗai ni gani.

 

Jagora: Wanda duk aka ci da haki nai,

            Allah shi kai mai sakayya,

            Makircin da su kai ma Sakkwato,

            Aliyu kar ka ji tsoron komai,

Yara: Bar su akwai Allah,

            Shi ya gani.

 

Jagora: Wanda duk aka ci da haki nai,

            Allah shi kai mai sakayya,

            Makircin da su kai ma Sakkwato,

            Aliyu kar ka ji tsoron komai,

Yara: Bar su akwai Allah,

            Shi ya gani.

 

Jagora: Aliyu kar ka ji tsoron komai

Yara: Bar su akwai Allah shi ya gani.

 

Jagora: Aliyu kai ka gadi sarauta,

            Ka yi naɗi daidai da sarauta,

            Wana duk bai gadi sarauta ba,

            Yara ko ga naɗi sau mun ganai,

Yara: Wane naɗi nai ya cika girma,

            Wanga uban humi sai ‘yan dako.

Jagora: Aliyu kai ka gadi sarauta,

            Ka yi naɗi daidai da sarauta,

            Wana duk bai gadi sarauta ba,

            Yara ko ga naɗi sau mun ganai,

Yara: Wane naɗi nai ya cika girma,

            Wanga uban humi sai ‘yan dako.

 

Jagora: I taƙamarka Alu daidai kake,

            Taƙama sai dai ɗan sarki,

            Jan biri in dai ya yi taƙama.

Yara: Tabbata hwadaman nan ya gani,

            Yana nuhwa ya kare geron wani.

 

Jagora: I taƙamarka Alu daidai kake,

            Taƙama sai dai ɗan sarki,

            Jan biri in dai ya yi taƙama.

Yara: Tabbata hwadaman nan ya gani,

            Yana nuhwa ya kare geron wani.

 

Jagora: Na gaishe ka Italin Nasiru,

            Shugaba na matasan Sakkwato,

            Kai ne a ka sani duk Sakkwato,

            Duk wanda an ka naɗa shirme ne,

Yara: Nasiru naka naɗi a gaskiya.

 

Jagora: Mun gaishe ka Italin Nasiru,

            Shugaba na matasa Sakkwato,

            Kai ne an ka sani duk Sakkwato,

            Duk wanda an ka naɗa shirme ne,

Yara: Nasiru naka naɗi a gaskiya.

 

Jagora: Bello na giwa masoyin Ali,

            Ni na gane kana ƙauna tai.

Yara: Alhaji tun ga naɗi ni tabbatar.

 

Jagora: Bello na giwa masoyin Ali,

            Ni na gane kana ƙauna tai.

Yara: Alhaji tun ga naɗi ni tabbatar.

 

Jagora: Bello na giwa masoyin Ali,

            Ni na gane kana ƙauna tai.

Yara: Alhaji tun ga naɗi ni tabbatar.

 

Jagora: Ahmed Aliyu ku gai sai,

            Ahmad Ali ya ban mota,

            Saboda kai Itali ba ni sitalet,

Yara: Saboda sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ahmed Aliyu ku gai sai,

            Ahmad Ali ya ban mota,

            Saboda kai Itali ba ni sitalet,

Yara: Saboda sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Nasiru Itali ba mu sitalet,

Yara: Saboda sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Nasiru Itali ba mu sitalet,

Yara: Saboda sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ƙi sake bajini kwarzon maza,

            Ali sarkin Yamman Sakkwato,

Yara: Ƙi sake bajini kwarzon maza,

            Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Kai bari dai in ta da gwanina,

            Bari dai in wasa ubana,

            Ɗanbarade jikan Umar,

            Baba kizabo ba ka da sabo,

Yara: Masassaƙi ya tsare hannu ƙwarai.

 

Jagora: Kai bari dai in ta da gwanina,

            Bari dai in wasa ubana,

            Ɗanbarade jikan Umar,

            Baba kizabo ba ka da sabo,

Yara: Masassaƙi ya tsare hannu ƙwarai.

 

Jagora: A ƙi sake bajini gwarzon maza,

            Ali sarkin Yamman Sakkwato,

Yara: A ƙi sake bajini gwarzon maza,

            Ali sarkin yamman Sakkwato.

 

Jagora: Musa damo ya ban gero,

            Musa damo ya ban dawa,

            Musa damo ya ban kuɗi,

            Da riguna Musa ya ba ni,

            Kaf Illela lokal gamun,

            Duk wanda ke son sarkin Yamma,

Yara: Alhaji babu irin Musa damo.

 

Jagora: Musa damo ya ban kuɗi,

            Musa damo ya ban gero,

            Musa damo ya ban dawa,

            Da riguna tcadaddu ya yi man,

            Kaf Illela da ke son sarkin Yamma,

Yara: Alhaji babu irin Musa damo.

 

Jagora: Magatakarda difiti gwamna,

Yara: Maza su kara shiri sai ka zamo.

 

Jagora: Magatakarda difiti gwamna,

Yara: Maza su kara shiri sai ka zamo.

Jagora: Hankalinka ya kwanta Sakkwato,

            Tun mulkin gargajiya Aliyu don mulkin ga,

            Na zama in da duk Allah ya ce a yi,

            Babu wanda ka cewa ba a yi.

 

Jagora: Aliyu Hamza na gode mai,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bello Giwa sannu da aiki,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Muntari ɗan Bello,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Muntari mai gona Ɗan Bello,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Aliyu ku gai sai,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Aminu Dikko na gode mai,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Aminu Dikko ban rena ba,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: In Buba Ɗangaladima,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Wmakko zan je in baje koli,

            Don baba Ɗangaladima,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Audu Sifika, Audu,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Audu sifika Audu,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Sa’idu Wurno ban rena ka ba,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bello I.O. sannu da aiki,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bello I.O. ban manta ka ba,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Ni Ɗanmasani Boɗinga,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Ga Ɗanmasani Boɗinga,

            Sannan ma’ajin Boɗinga,

            Kai wanga Ɗanmasani gode masa,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Kai wanga Ɗanmasani ka motsa,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Tsaliawa,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Nasiru Itali ni tuna,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Nasiru Itali sannu da aiki,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Ahmad Abudullahi Kalambaina,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bayis ciyaman na gode ma,

Yara: Ahmad Abdullahi ku gai sai.

 

Jagora: Rai ya daɗe Ibrahim Ango,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Rai ya daɗe Ibrahim Ango,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Gai da Muhammadu ɗangwaggo,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bayis ciyaman na gode ma,

            Abubakar Alhaji Lamiɗo,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bayis ciyaman na gode ma,

            Alhaji Abuabakar Lamiɗo,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Habibu tsoho daraktan gona,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Daraktan gona Gwadabawa,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Daraktan soshiyal Illela,

            Garba Galadima,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Darakta soshiyal Illela,

            Garba Galadima himma ba aiki ba,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Aliyu harka mutumin kirki,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Aminu harka mutumin kirki,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Mu Abdullahi na Romo,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora:

 Abdu duniya sai Allah,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Abdu duniya sai Allah,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Macciɗo Abdullahi,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Macciɗo Abdullahi,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Abubakar Abba birnin Tambuwal,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Ran Juma’a na kwan mamaki,

            An yi sarautu Sakkwato birni,

            Mai kurin shi ad da mutane,

            An yi naɗi kowa ya watce,

            Mai jama’a ya kwashin abin nai,

            Sai ni biya garka wani sarki,

            Na ishe ‘yan banga sun taru.

Yara: Don haka ‘yan shuli dai ni gani.

 

Jagora: Na ishe ‘yan banga,

            An yi cinjim,

Yara: Don haka ‘yan shuli dai ni na gani.

 

Jagora: Wanda du aka ci da hakki nai,

            Allah shi ka yi mai sakayya,

            Allah shi ka yi mai sakayya,

            Makircin da su kai ma sakkwato,

            Aliyu ka ji tsoron komai,

Yara: Bar su akwai Allah shi ya gani.

 

Jagora: Haji Hali Aliyu na gode ma,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Malami Gulma sannu da aiki,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Rai ya daɗe Bellon Sifawa,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Rai ya daɗe Bello Sifawa.

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Dole in yi yabon gogana,

            Tun da garinmu guda da shi,

            Shehu Adamu birni rara,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Shehu na Sani ɗan Adamu,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Shehu na Sani ɗan Adamu,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Gwamna jahar birni Yobe,

            Gwamna jahar birni Yobe,

            Abba Bukar ɗan Ibrahim,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Gwanna jahar birni Yobe,

            Abba Bukar ka yi da,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Mataimaki sifika Sakkwato,

            Rai ya daɗe Alhaji mai Gwandu,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Mataimaki sifika Sakkwato,

            Rai ya daɗe Alhaji mai gwandu,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bello Haliru birni Guiwa,

            A gai da ciyaman birnin Wamakko,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Bello Haliru birni gwiwa,

            A gai da ciyaman birnin Wamakko,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: A malami Shehu ku gai sai,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Godiya gun Malami Shehu,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Abubakar Shehu babban kansila,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Abubakar Shehu babban kansila,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora:DPM birni shagari,

            A gai da Alhaji uban Ɗanbau,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora:DPM birni shagari,

            A gai da Alhaji uban Ɗanbau,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Nasiru mai mai birni Wurno,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Yara: Haji Mu’azu Zabira ka yi ɗa,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Mustapha Alhaji maigandi,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Ni Mustapha Alhaji Maigandi,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Malami Buhari Hubbare,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Ahmed wakili,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Alhaji Ahmed wakili,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Ni ma’aji Illela ku gai sai,

            Abubakar ɗan Adamu ka yi ɗa,

Yara: Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

Post a Comment

0 Comments