Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Bai Ƙayyade Lokacin Rama Azumi Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Dr. Mace ce ta sha Azumin shekara uku ajere saboda ciwon ulcer, kuma abin da za su kai baki gagaransu yake ballatana ta ciyar. Mene ne mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam Ta jira har Allah ya ba ta lafiya sai ta rama.

Allah madaukakin sarki a cikin Suratul Bakara aya ta: (185) ya sanya ramuwar azumi ga mara lafiya a wasu kwanaki na daban don ya nuna abin a buɗe yake, zuwa lokacin da aka samu dama, ba tare da yin sakaci ba.

Allah ne mafi sani

Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments