Waƙa hanya ce ta ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa. Amma kash! Idan aka yi la'akari da waƙoƙin Hausa na zamani a yau musamman waɗanda matasa suke ribibin karkata gare su, sai a tarar babu wani ilimantarwa ko faɗakarwa da suke yi. Kai, sam ma "Ba Su Da Direction!"
Da fari na sako Rab Sarkin creation
Wanda ke
halitta ya sanya mata motion
A zuciya ya sa
feelings ya ƙaro
da emotion,
Ya sanyo sense
organs domin sensation,
Ga reflex
action, jiki ya yo reaction.
Don ya nuna mun
gaza muke excretion,
Su kam ga 'yan
uwanmu har da menstruation,
Ya wanzar da
rayuwa ya ƙaddara
extinction,
Ko ban mun
gushe akwai ran resurrection.
Yi salati gun
Rasulu ƙaro
salvation,
Sa da iyalansa
har sahabu in addition,
Da wanda kan
tafarkinsa ne mu kai retention.
'Yar magana zan
faÉ—a ina son
attention,
Sai an bar
motion ko duk locomotion,
An ba ni
hankali da full concentration.
Mawaƙan
zamani ku biyo ni cikin caution,
Allah ya yo mu daban-daban
da faction,
WaÉ—ansu na invention ko su
tsara fiction,
Waɗansu ba ƙwaƙwalar
yin imagination.
Baiwa ce an ka ba ku mai kuma
limitation,
A kan ku bi
turbar ƙwarai
sai ku kai divination,
To ku san ko waƙar an
fi ku ideation,
An fi ku tsara
baituka da kai
information,
An fi ku a
hangen nesa miƙaƙƙen perception,
An fi ku ko
style balle a fagen diction,
Kalamanku kaÉ—an
ne kamar an sa ration.
Ba ku da tsarin ƙwarai,
ba organization,
Ba hikimar zance da za
ku yi oration,
Duk batunku maimaici
babu variation,
Kun ƙware
ne kawai a shiga da ke seduction,
Shigar haram ta
batsa wai don
attraction,
Mata su tsuke ƙugu su sasshafo
lotion,
Su zo suna fitsara wai
sun iya action,
Su rinƙa gantsaro
ƙirji don ku san ovation,
Sai kiÉ—a da bin sa ne zuci ke corruption.
Ba kwa research
balle investigation,
Batunku babu illimi ko sabon notion,
Ba kwa sanar da mu tarihin nation,
Ba kwa taimako a fannin education,
Ba ku gane kun gaza sai a competition.
Kai Hausa hip-hop, ku zo ku amsa
question,
“Da so samu ne” bara in yo
quotation,
Wane saƙo ya
isar, mene intention?
To a
cikin “Chass”, me za ai emulation?
Ko “a Æ™ame Æ™am”? Mata ke imitation.
Matsalar
constitution ba wani regulation,
Sai ku ɓata
tarbiyya gare ku ba conviction,
In baicin
haka da yanzu ba ku function,
Kun cancanci kora total expulsion,
Kowane nation gare ku ai ejection,
A bi ku ma da eho bayan eviction.
Ko ba komai cikinku da exception,
Kai Aku Mai Magana congratulation,
Kana batu na hankali kana kawo
motion,
Kana so a yi gyara kana orientation,
Kakan nuno issues sannan ka yo
suggestion,
Kakan taɓa
har leaders domin su yo correction,
Da
kamarka duk ake ba wani contention.
Gare
ku ‘yar nasiha ku kau da opposition,
Ai
muna da deen da ya zo da regulation,
Mu
tittina ayoyi da akka yi revelation,
Ga
ko nan hadisai an yo narration,
Akwai
wuta da janna, an bar mana option,
Mu
daina biye duniya akwai implication,
Kamar
yau za mu gushe kan realization,
A
É—ebe mu sai kabari end of discussion,
Za
mu amsa tambaya tough examination,
In
mun ci mun haye, mu samu ventilation.
In
kuwa mun gaza highest frustration.
In za ku yo
waƙa to ku samu vision,
A ce akwai
intention a ce kuna da mission,
Baitukan ku
bayar domin observation,
Akwai massana,
ku yo consultation,
Duk baitukan
sai su sam purification,
Har mutan
ƙwarai za su yo appreciation.
Allah
taimaka mu yi preparation,
Guzzuri
na taqwa aya ta yi mention,
Mu kauce ruÉ—in
sheÉ—an ko manipulation,
Ka sa mu a
aljanna mu samu relaxation.
0 Comments
Rubuta tsokaci.