Jigo na nufin babbar manufa ko muhimmin saƙon da mai aikin adabi ke da shi ga jama’ar da aka shirya aikin adabin domin su.
Dangantakar Jigogin Wasu Labaran Magana Jari Ce Da Na Tatsuniyoyin Hausa
Abdulbasir
Ahmad Atuwo1
Abdurrahman Faruk2
1Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sakkwato
2Department of Nigerian Languages, Umaru Musa
Yar’adua University, Katsina
Tsakure
Idan dai mutum ma’abocin
karatun rubutattun labaran Hausa ne, ko mai sha’awar sauraro ko karatun
tatsuniyoyin Hausa ne, babu shakka zai riƙa ganin wasu kamannu tsakanin wasu rubutatttun labaran
Hausa da kuma tsatsuniyoyi na Hausa. Wannan dalili ne ya sa wannan takarda ta
yi tsokaci a kan kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin rubutattun labaran Hausa
da tatsuniyoyin Hausa. Taken wannan takarda shi ne, “Dangantakar Jigogin Wasu
Labaran Magana Jari Ce da Na Tatsuniyoyin Hausa.” Manufar takardar ita ce,
kwatanta dangantakar da ke akwai tsakanin wasu labaran da ke cikin Magana Jari
Ce I - III da tatsuniyoyin Hausa ta fuskar jigogi, wato saƙonnin da suke ɗauke da su. An karanta wasu
ayyukan masana da suka yi a kan fagagen tatsuniyoyi da rubutattun labaran Hausa.
An kuma karanta littafin Magana Jari Ce I-III a matsayin dabaru da hanyoyin
gudanar da bincike. An ɗora wannan bincike a kan Ra’in
Tsarin Adabi (Structural Theory) na Propp (1928). Bayan an ƙare binciken, sai aka gano
cewa, akwai kyakkyawar alaƙa
ta fuskar jigogi tsakanin wasu labaran Magana Jari Ce I-III da tatsuniyoyin
Hausa. Wannan alaƙa
kamar yadda aka gano ta samu ne saboda rubutattun labaran Hausa sun tusgo
gyauronsu ne daga tatsuniyoyin Hausa. Haka kuma, mawallafin littafin Magana
Jari Ce I-III wato Abubakar Imam ya daɗe
yana sauraron tsatsunoyin Hausa daga bakin kakanninsa tun yana yaro ƙarami kamar yadda kowane
yaro ke tashi da sauraron su a ƙasar
Hausa. Wannan babu shakka ya tasiranci tunanin Abubakar Imam wajen gina
littafin Magana Jari Ce I-III.
Fitilun
Kalmomi: Jigo;
Tatsuniya; Labari; Magana Jari Ce
1.0 Gabatarwa
Babu
wata nahiya ta duniya da al’ummarta ba ta da labaran kunne-ya-girmi-kaka. Da
ire-iren waɗannan labarai ne kowace
al’umma ke tashi, kuma a cikinsu ne suke samun tarihin asali da samuwar
al’ummar tasu. Nahiyar Afirika ma ba a bar ta a baya ba dangane da tattalin
ire-iren waɗannan labarai. Shi ya
sa ma al’ummomin nahiyar suka yi tarayya a kan tsari iri ɗaya
na aiwatarwa da bayar da waɗannan
labarai (Usman, 2013: 8). A ƙasar
Hausa, labaran nan na kunne-ya-girmi-kaka da aka fi sani da tatsuniyoyi. Ita
tatsuniya labari ne ƙagagge
da aka ƙirƙira aka yi amfani da gizo da
ƙoƙi da dabbobi da ƙwari da tsirrai da tsunuka
da aljannu na tudu da na ruwa da ma wasu abubuwa da babu su a zahiri waɗanda
tunani ke kintatowa. Ana ƙaga
tatsuniya da nufin a ba al’ummar da ke tasowa wato yara tarbiyya a kan hani da
horo domin su tashi masu amfani ga kansu da iyayensu da al’ummominsu da ma
duniya baki ɗaya (Zarruƙ, 1987: 5).
Kafin zuwan Larabawa da Turawa a ƙasar Hausa, wato kafin Bahaushe
ya yi mu’amala da baƙin
al’ummomin da suka kawo masa tsarin karatu da rubutu, waɗannan
labarai na tatsuniya da ka ake ƙirƙirar su, a bayar da su da
baka ga yara, kuma da ka yaran suke adana su, su tashi da su, su yi amfani da su
wajen daidaita rayuwarsu, sannan idan sun girma su ma, su bayar da su ga ƙannensu ko ‘ya’yansu da ke
tasowa. Ke nan dangane da tatsuniya, ana rama wa kura aniyarta ne, ko ma a ce
inda akuyar gaba ta sha ruwa, a nan ta baya ita ma za ta sha (Furniss, 1996: 57).
Kamar yadda aka nuna a sama, Bahushe
ya sami ilmin karatu da rubutu ne daga baƙin al’ummomi da suka yi ta
karakaina ƙasar
Hausa da burace-burace iri-iri (Yahaya, 1988: 8). Larabawa ne suka fara zuwa ƙasar Hausa suka koya wa
Hausawa karatu da rubutu a cikin haruffan Larabci. Da Hausawa suka ƙware, sai suka fara tunanin
rubuta nasu harshen na Hausa da haruffan Larabci, ganin cewa sun fahimci muryar
kowane baƙi
da wasali na Larabci. Wannan fasaha ta rubuta harshen Hausa da haruffan Larabci
ce ake kira Rubutun Ajami (Yahaya, 1988: 31).
Bayan shuɗewar
Larabawa, al’ummomin da suka ratso ƙasar
Hausa su ne Turawa a ƙarshen
ƙarni
na sha tara (Ƙ19)
zuwa farkon ƙarni
na ashirin (Ƙ20).
Turawa sun zo wa Hausawa da ilmin boko, wato karatu da rubutu cikin haruffan
Turanci. Hausawa sun dage sun iya, daga nan sai suka fara tunanin rubuta
harshen nasu na Hausa cikin baƙaƙe da wasula na boko. Wannan
lamari ne ya kawo Hausar Boko (Yahaya, 1988: 72).
Tun da rubutu da karatu cikin Hausar
boko ya samu a ƙasar
Hausa, sai Hausawan suka fara tunanin mayar da rubutattun labaran Hausa cikin
tsarin Hausar Boko. Kodayake, kafin Hausawa su fara wannan namijin ƙoƙari na rubuta ƙagaggun labaran Hausa cikin
Hausar boko, Turawan suka fara yin wannan shiga hanci da ƙudundune. Sun kutsa sosai
sun koyi magana da harshen Hausa, saboda haka, sai suka fara tunanin rubuta
tatsuniyoyin Hausa da Hausar boko. Da haka ne littafin Edgar (1911) da na
Skinner (1969) suka samu (Furniss, 1996: 56). Tun bayan bayyanar waɗannan
rubutattun tatsuniyoyi na Hausa, aka ci gaba da samun rubutattun labaran Hausa
a ƙasar
Hausa. Ken an akwai kyakkyawar alaƙa
tsakanin ƙagaggun
labaran tastuniyoyi da kuma rubutattaun labaran Hausa.
Manufar wannan takarda ita ce yin
sharhi game da labaran tatsuniya da kuma wasu labaran da ke cikin littafin
Magana Jari Ce I-III. Takardar ta nazarci dangantakar da tsakanin tatsuniyoyin
Hausa da wasu labaran Magana Jari Ce
I-III ta fuskar jigogin da labaran suka ƙunsa. Takardar ta lura duk
rubuce-rubucen da suka gabata na masana da manazarta, babu wanda ya yi tsokaci
dangane da wannan dangantaka, duk da kuwa cewa fage mai muhimmanci. Rubuce-rubucen
da aka yi tayi a kan tasuniyoyi da kuma littafin Magana jari Ce I-III, sun
ta’allaƙa
ne kawai ga nazarce-nazarce a kan gundarin tatsuniya (Edgar (1911) da (Ruth,
1970) da (Poul, 1970) da (Yahaya, 1971) da (Thomson 1977) da (Umar 1982) da (Zarruƙ, 1986) da (Yahaya 1992) da
(Koko, 2009) da Usman (2012) da Usman (2013) da sauransu. Wasu kuma
nazarce-nazarcen kuma, sun karkata akalarsu su ne a kan littafin Magana Jari Ce
I-III, inda suka yi tsokaci a kan fagage daban-daban da littafin ya ƙunsa. Misali ayyuka ire-iren
su Ibrahim (1990) da Musa (1993) da Geza (2004) da Guga (2010) da Hassan (2013)
da Guga (2015). Duka waɗannan
rubuce-rubuce dam asana da manazarta suka yi, sun shafi labaran Hausa da kuma littafin
Magana Jari Ce. Kodayake masana sun
bar giɓi, wato babu ɗaya
daga cikinsu da ya danganta wasu labaran da ke cikin littafin Magana Jari Ce I-III da kuma tatsuniyoyin
Hausa, saboda haka wannan takarda ta yi yunƙurin cike wannan giɓi
domin ganin an sami daidaito a ɓangaren
nazari.
1.1
Ra’in Bincike
An ɗora
wannan bincike a kan Ra’in Tsarin Adabi (Structural Theory) wanda Ɓladimir
Propp ya ƙirƙiro a shekarar (1928).
Wannan ra’i yana ƙarfafa
nazarin tsarin adabi ne wanda ya fara ɓulla
a doron ƙasa
tun kafin shekarar (1960). Kamar yadda maƙirƙirin ra’in ya bayyana, ra’in
ya ƙunshi
nazarin bayanin sigar labari ne dangane da ginshiƙansa da kuma haɗuwarsu
da juna. Ke nan ana maganar wasu rassa na adabi da suke haɗuwa
da juna su amfanar da waɗanda
aka ƙirƙiri adabin domin su (Gusau,
2001: 37).
Akwai dangantaka tsakanin wannan ra’i da kuma wannan bincike
da aka gudanar. Dalili kuwa yadda Ra’in Tsarin Adabi yake bayanin sigogin adabi
da yadda suke haɗuwa
da juna, wato jigogin aikin adabi da yadda ake samun alaƙa tsakanin wani aikin adabi
da wani, haka wannan bincike yake fayyace haɗuwar
wasu labaran Magana Jari Ce I-III da tatsuniyoyin Hausa ta fuskar jigogi. Ganin
cewa Ra’in Tsarin Adabi da wannan maƙala
alƙiblarsu
ɗaya ce shi ya sa aka ɗora
binciken a kansa.
1.2 Labari
Idan aka ce labari, ana nufin labarai ko wasu bayanai ko ƙagaggen labari ko almara.
(Bargery1934: 706). Bayyanawar wani abu da ba a sani ba ma labara ne (CNHN,
2006: 296). Ma’anar da Bargery tare da Ƙamusun Hausa na Jami’ar
Bayero suka bayar, ba ta gamsar da wannan takarda ba, saboda ma’anar ta taƙaita a kan bayanai ko ƙagaggen labari ko almara. Haka
kuma an taƙaita
ma’anar ga faɗar abin da ba a sani
ba. A wannan lokaci, ma’anar labari ta wuce nan. Saboda haka, aka lalubi
ma’anar labari ta ilmi. Dangane da haka, aka dubi ma’anar labari wadda
Malumfashi, (2019) ya bayar. Ga abin da Malumfashi ya bayyana a kan labari cewa:
Ayyanannen lamari ne
da ke ƙunshe
da gaskiya da kuma ƙarya
domin a nishaɗantarwa da sa walwala
da kuma isar da saƙo.
Shi wannan ayyanannen lamari ba ƙagawa
ba ce, ba zayyanawa ba ce ba ƙirƙira ko firtsa ba ce, ba kuma
wani sanabe ba ne. Haka kuma samuwa da tabbatuwar wannan ayyanannen lamari yana
bisa matakan halittar Ɗan’adam
da yananyin wanzuwar Ɗan’adam
a doron ƙasa
musamman abin da ya danganci rayuwar yau da kullum da abin da ƙwaƙwalwa ke rayawa da kitsawa
na daga abin da ta ci karo da shi na ji ko gani ko na cikin gado ko kuma
zamantakewa ta kusa ko ta nesa ta al’umma (Malumfashi, 2019: 35).
Kamar
yadda aka gani a sama, ma’anar da Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero ya kawo game da labari taƙaitacciya ce ƙwarai. Dalilil kuwa an sake
maimaita kalmar labari ne kawai a cikin wasu kalmomi na daban kamar bayani da
almara. Ma’anar da Malumfashi (2009) ya kawo ta fi fito da ma’anar labara a
fili. Shi a ra’ayinsa duk bayanin da aka sake ambatowa ga mai sauraro ko karatu
wanda dama can ba baƙon
abu ba ne ga mai gabatarwa ko mai karɓa.
Imma dai ya taɓa ji an faɗa
ko ya taɓa gani ko ya taɓa
karantawa daga wani littafi. Wannan bayani yana iya kasancewa gaskiya ne ko
kuma ƙirƙira ce ta mai gabatarwa. Ke
nan ga yadda Malumfashi ya nuna, duk abin da mai gabatar da labara zai faɗa,
to, ba shi ne mafarinsa ba, yana da tasirinsa a cikin ƙwaƙawalwarsa da kuma zuciyarsa.
1.3 Ma’anar Jigo
Idan aka yi maganar jigo, ana magana ne a kan saƙo na musamman da marubuci
yake ƙoƙarin bayyana wa ga jama’a a ƙagaggen labari ko wasan
kwaikwayo ko waƙa
(CNHN, 2006: 217). Masana sun bayar da ma’anar jigo daidai gwargwado. A cewar ɗaya
daga cikinsu, “Jigo dai kodayaushe yana nufin saƙo ko manufar da abu ke ɗauke
da ita zuwa ga waɗanda
ake nufi” (Koko, 2009: 18). Kodayake, wani masani ya nuna cewa, “Jigo na nufin
manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara da ita, saboda haka ana iya
cewa, jigo shi ne saƙon
da marubuci ke son sadarwa ga jama’a. Duk wani salo da tsari ko wata dabara da
marubuci zai yi amfani da su, zai yi haka ne da nufin isar da saƙon nasa ga jama’a” (Sarɓi,
2007: 71).
Duk idan aka tattara waɗannan
ma’anoni da Ƙamusun
Hausa da masana suka bayar dangane da jigo, za a iya bayyana jigo da cewa
babbar manufa ko muhimmin saƙon
da mai aikin adabi ke da shi ga jama’ar da aka shirya aikin adabin domin su. Ke
nan jigo shi ne ƙudurin
da mawallafi ke da shi ga jama’a. Babu wani aikin adabi da ba ya da jigo ko
manufar da aka yi shi dominta. Kowane aikin adabi kamar waƙa da zube da wasan kwaikwayo
suna ɗauke da saƙon da aka tsara, wanda ake
son a isar ga jama’a. Kowane aikin adabi da irin jigon da yakan zo da shi. Daga
cikin ire-iren jigogin da ayyukan adabi kan zo da su sun haɗa
da faɗakarwa da ilmantarwa
da nishaɗantarwa da
hannunka-mai-sanda da tsoratarwa da gargaɗi
da sauransu. Akwai kuma ƙananan
jigogi ire-iren su jarunta da kishi da ladabi da biyayya da ƙeta da tausayi da sauran
illolin wasu miyagun ayyukan da al’adun da zamantakewar al’ummar Hausawa take ƙyama da dai sauransu.
2.0 Samuwar Littafin Magana Jari Ce
A wajen shekarar 1932-1933, ‘yan ƙasa sun sami ilmin boko
bakin gwargawado. Da yawansu sun iya karatu da rubutu. Sai dai kash!, Ga dai
ilimi ya samu, amma kuma ga ƙishirwar
litattafan karantawa. La’akari da cewa litattafan da ake karantawa a makarantu
sun yi ƙaranci,
ga rashin dacewa ga ɗalibai.
ɗaliban makarantar Elemantare
sun gaji da karanata su, saboda babu sauyi. Ga litattafan da saurin gundurar
mai karatu, saboda babu ɗaya
daga cikinsu da ya shafi tantagaryar adabi. Duka-duka ma litattafan da ake koya
wa yara karatu da su guda biyu ne: Daga Aljaman
Yara, sai Littafin Koyarwa na Karatu
da Rubutu (Malumfashi, 2009: 52).
Ko da Gwamnatin Arewa ƙarƙashin Hukumar Ilmi ta
fahimci wannan matsala ta rashin littattafan karantawa a makarantun Elemantare,
sai ta sa wani Jami’inta wato Dr. R.M. East a ƙarƙashin Hukumar Fassara, ya
kewaya cikin ƙasa
ya yi yekuwar cewa, Hukumar Ilmi za ta sa gasar rubuta ƙagaggun labarai na Hausa.
Kamar yadda sunan litattafan ya nuna, an sanya dokokin gasar waɗanda
su ne R.M. East ya kewaya ya shaida wa ‘yan ƙasa da suka ilmanta, cewa ba
fa fasssara ake so ba, a wannan karon ana buƙatar ƙagawar mawallafi ne. Duk
wanda ya yi nasara, za a ba shi kyauta mai tsoka, kuma a buga masa littafinsa
kyauta, littattafan su kuma kewaya cikin ƙasa (Malumfashi, 2019: 52).
Bayan an yi wannan gasa a shekarar
1932-1933, sai aka fitar da sakamakon gasar, inda littattafai biyar suka fice
kuma suka lashe gasar. Ga litaffan:
1.
Ruwan
Bagaja na Abubakar Kagara
2.
Ganɗoki
na Bello Kagara
3.
Shaihu
Umar na Abubakar Bauchi
4.
Idon
Matambayi na Sani Gwarzo
5.
Jiki
Magayi na R.M. East da John Umaru Tafida Zariya
(Malumfashi, 2009: 25).
Wannan
nasara da Abubakar Imam ya samu ta sa an buga littafinsa na Ruwan Bagaja a shekarar 1933, kuma sai
aka aro Abubakar Imam daga Lardin Katsina inda yake aikin koyarwa ya zo ofishin
Hukumar Fassara da ke Zariya don ya rubuta littaffan da za a raba a makarantun
da ke Arewacin Nijeriya. Kafin ya fara rubuta komai, sai da ya ba da shawarar
sauya wa Hukumar fassara suna, wadda aikinta a da fassara ne daga Turanci da
Larabci zuwa Hausa. Daga nan sai aka mai da ita Hukumar Talifi, saboda yadda
aikin wallafe-wallafen littattafai ya ƙaru
ga hukumar (Adamu, 2019: 17).
Aikin
da Abubakar Imam ya fara yi ƙarƙashin Hukumar Talifi shi ne
rubuta litattafan Magana Jari Ce na
I-III. Kafin ya fara wannan aiki, sai da uban gidansa wato Dr. R. M. Esat ya
tattara masa littattafan labaran Turawa da Larabawa da Mutanen Sin da na
Al’ummar Rasha, ya yi ta karantawa. Da yake Abubakar Imam yana jin harsuna da
dama. Da ya naƙalci
yadda rubuce-rubucen labaran wasu al’ummomi suke, sai ya yi azama ya fara
rubuta Magana Jari Ce (Pweddon, 1977:
151).
Kodayake,
Pweddon ya tabbatar da ba Abubakar Imam ne ya rarraba littafin Magana Jari Ce littafi-littafi ba. Abubakar Imam ya faɗa
masa haka a hirar da ya yi da shi, sai Abubakar Imam ya tabbatar masa da cewa
sam, shi bai karkasa littafin Magana Jari
Ce littafi na farko zuwa na uku ba. Shi ya ci gaba da rubuta labaransa kara
zube. Duk labarin da ya faɗo
masa a rai, sai ya rubuta abinsa. A cewar Imam editan littafin ne wato Dr. R.
M. East ya kasarkasa shi zuwa littafi na farko da na biyu da na uku don ya yi
daɗin karantawa ga ɗalibai
(Pweddon, 1977: 151). A cikin wannan liitafi na Magana Jari Ce wannan maƙaka
ta yi nazarin dangantakar jigogin wasu labarin cikinsa da tatsuniyoyin Hausa.
3.0 Tatsuniyar Hausa
Tatsuniya labari ne da ake ba wa yara na hikima domin
hira (CNHN, 2006: 433). Tatsuniyar Hausa ƙagaggen labari ne da ake
shiryawa game da gizo ko waninsa da ya ƙunshi wani darasi ko ya cim
ma wata manufa ta musamman cikin hikima (Zarruƙ, 1987: 11). A ganin wani
masani, tatsuniya wani ƙagaggen
labari ne da al’adar Hausawa ta tanada domin nishaɗantarwa
da kuma cusa tarbiyya ga ‘ya’yan Hausawa (Yahaya, 1971: 5). Wata manazarciya ta
bayar da ra’yinta game da tatsuniya inda ta nuna tatsuniya a matsayin wasu
labarai da mutane ke ƙirƙirowa cikin azanci don su
tarbiyyantar da ‘ya’yansu da kuma cim ma wasu buƙatoci dangane da al’umma
(Koko, 2006: 4).
Duk idan aka tattara waɗannan
ma’anoni na tatsuniya da Ƙamusun
Hausa da kuma masana wannan fage suka bayar, za a iya daddagewa da cewa, tatsuniya
labari ne ƙagagge
da ake shiryawa domin ba yara da nufin yi musu tarbiyya musamman abin da ya
shafi hani a kan abubuwan da al’umma ta ɗauka
su ne gurɓatattu da horo a kan
lamurran da al’umma ta aminta su ne kyawawa. Tastuniya tsohon labarin Hausawa
ne da suke amfani da shi suna bayar da tarbiyya ga yaransu da nufin yaran su
girma a cikin al’umma masu amfani ga kansu da iyayensu da ma al’ummar da suke
rayuwa a cikinta. Tatsuniya tana da lokacin da al’adar Bahaushe ta ware na yin
ta, wato da dare bayan yara sun ci abincin dare, musamman idan akwai farin
wata. Muhallan tatsuniya ba su wuce gidajen tsofaffi mata ba. Ana yi wa yara a
cikin gida inda kakanninsu ke yi musu. Ana kuma yin tatsuniya a dandali wurin
wasa ko kuma ma a gidan sabuwar amaryar da takan gayyaci yara a gidanta don su ɗebe
mata kewar iyaye da ƙawayenta
da ta baro.
Mabuɗin
tatsuniyar Hausa shi ne, “Ga ta nan, ga ta nan ku.” Marufinta kuma shi ne, “Ƙungurus kan kusu ko Ƙurunƙus kan kusu, ba don gizo ba,
da na yi ƙarya,
ko yanzu ƙarya
ce na giggilla muku.” Akan ɗaure
gizo kafin a yi tatsuniya da rana, ta hanyar ajiye tsakuwa ko sakaina a hanyar
da mai tastuniya ya biyo ko zana da’ira a ƙasa. Idan ba a ɗaure
shi ba, mai gabatarwa zai yi ciwon dundumi (Makantar dare) kokuma ɗemuwa
ta kama shi. An raba tatsuniya gida biyu: Tatsuniyar Labari wadda ake zubo
labari mai ɗauke da darussan
zaman duniya da na rayuwa. Akwai kuma Tatsuniyar Almara wadda ake kawo wasu
matsaloli guda biyu ko abin da ya fi biyu a buƙaci mai sauraro ya warware
su cikin hikima. Akan kuma kawo wata sarƙaƙƙiya daga ƙarshe a buƙaci mai sauraro ya nuna idan
shi ne lamarin ya shafa, yaya za ya yi?
4.0 Dangantakar Jigogin Wasu
Labaran Magana Jari Ce Da Na Tatsuniyoyin
Hausa
Dangantaka na
nufin ‘yan’uwantaka (CNHN, 2006: 95). Idan aka ce dangantakar wasu labaran Magana Jari Ce da tatsuniyoyin Hausa ke
nan ana nufin ‘yan’uwantakar wasu labaran Magana
Jari Ce da tatsuniyoyin Hausa. Ke nan a wannan fasali, an bayyana
kyakkyawar dangantaka da ‘yan’uwantaka da alaƙar da ke tsakanin labaran
guda biyu. Kamar yadda aka bayyana a baya, ana ƙoƙarin a kawo wuraren da wasu
labaran da ke cikin Magana Jari Ce I-III
suka yi kama ainun da labaran tatsuniyoyin Hausa musammam ta fuskar saƙoƙnnin da duka labaran ke ɗauke
da su. Akwai dangantaka tsakanin wasu labaran Magana Jari Ce da tatsuniyoyin Hausa ta fuskar saƙoƙnnin da duka labaran ke ɗauke
da su. Akwai jigogi da dama da aka yi tarayya tsakanin Magana Jari Ce da tatsuniyoyin Hausa. Daga cikinsu akwai ladabi da
biyayya da illar cin amana da kishi da jarunta da soyayya da adalcin
shuwagabanni da wayon zaman duniya da illar bijire wa iyaye da raha da illar ruwan
ido da dai sauransu.
4.1 Dangantaka ta Fuskar
Jigon Ladabi da Biyayya
Ladabi na nufin biyayya ko ƙasƙantar da kai (CNHN, 2006: 297).
Yayin da biyayya ke nufin ladabi da bin na gaba (CNHN, 2006: 49). Shi ya sa
kodayaushe kalmomin suke jingine da juna ake kuma amfani da su tare saboda
kusancin ma’anoninsu a harshen Hausa. Ke nan ladabi da biyayya na nufin ƙasƙantar da kai ga wani mutum
da yi masa biyayya ga kyawawan shawarwarinsa. Daga cikin jigogin da wasu
labaran Magana Jari Ce da
tatsuniyoyin Hausa suka yi tarayya a kansu akwai jigon ladabi da biyayya. A
kwai labaran da suka zo da wannan jigo na ladabi da biyayya a cikin labaran Magana Jari Ce I-III da kuma
tatsuniyoyin Hausa. A cikin Magana Jari
Ce littafi na uku a labarin, “Mai Arziƙi Ko a Kwara Ya Sai Da Ruwa”
an fito da wannan jigo inda aka nuna yadda Bawa yake yi wa mahaifiyarsa ladabi
da biyayya. Saboda ladabinsa ne ya sa da mahaifiyarsa ta umurce shi ya tafi ya raka
tsohuwa Inna don ya ɗaukar
mata tafasarta ya kai mata har gidanta, bai yi musu ba, duk da kuwa cewa sun
rigaya sun fara samun saɓani
da aljana Inna saboda raina musu sana’a da ta yi da ta sunsuna musu tafasa:
“Ɗebo mini ta sisin kwabo in
tafi, amma don Allah ki sa ɗan-ɗan
nawa ya ɗaukar mini ya raka ni
da ita. Kin san ni yanzu ba na iya ɗaukar
kome, ni ma kaina sai in da sanda nake iya tafiya.” Ko da jin haka, sai Bawa ya
yi farat ya ce, “Wallahi Inna, in ba ta ɗauka
sai ta bari, ba dominta kaɗai
muka kawo ba. Ni dai ba na ɗaukar
mata. Duk faɗin kan nan nata ta ce
ba ta iya ɗaukar tafasar sisin
kwabo, to, ina amfaninsa?” Uwar ta dubi tsohuwa, ta ga ranta ya ɓaci
bisa ga wamnan magana, sai ta tsananta wa ɗanta
dai ya tafi. Don ba ya son ya yi wani abin da zai ɓata
wa iyayensa rai, sai ya tashi ya shige gaba, tsohuwa na bin sa, suka kama hanya
tinƙis,
tinƙis sai
ka ce masu shiga ɗaki
(Imam, 1940: 123).
Dubi
yadda tsohuwar aljanar nan ta fusata Bawa, da yadda Bawa ya yi rantsuwa da
Wallahi ba zai kai mata tafasa gida ba, amma saboda ladabi da biyayya ga
mahaifiyarsa, sai dai ya haƙura
ya tafi. A dalilin wannan rakiya da Bawa ya yi wa aljanna Inna da ta fito musu
a matsayin tsohuwa, ya sa ta cuce shi ta sauya masa siffofinsa ta mai da shi
tsoho mai doro da ƙusumbi.
Da Irin wannan jigo ne aka yi amfani aka gina tatsuniyar Gizo da Sarki. Kamar yadda
aka nuna a tatsuniyar, tsohuwa ba ta yi wa sarki gardama ba da Sarki ya buƙaci ta ba shi santa da ta
turka. Duk da cewa ita ta turka abinta, amma da Gizo ya zo bara ya gan shi, sai
ya tafi ya tsegunta wa Sarki, shi kuma sarki ya aika mata kawai ta kawo san
nata, an ƙawace
mata:
Sarki ya tura dogarai
don a kamo kuma a kawo masa san. Da dogarai suka kama hanya ba su tsaya ko’ina
ba sai gidan tsohuwa. Suka same ta, suka isar da saƙon Sarki. Da ta ji bayanin
dogaran sai ta ce, “To yaya zan yi yanzu?” (Usman, 2012: 94).
Dalilin
rashin yi masa gardama ya ta’allaƙa
ne da ladabi da biyayyar da tsohuwa take nuna wa Sarki. Tabbas, da ba sarki ba
ne ya nemi ya ƙwace
mata sa ba, da ta yi mursisi kuma sai inda ƙarfinta ya ƙare. Ke nan an yi kunnen doki
a labarin, “Mai Arziƙi
Ko A Kwara Ya sai Da Ruwa” na cikin Magana
Jari Ce III da kuma tatsuniyar Hausa ta “Gizo da Sarki” ta cikin Taskar tatsuniyoyi.
4.2 Dangantaka ta Fuskar
Jigon Illar Cin Amana
Akwai alaƙa
ƙwarai
tsakanin Magana Jari Ce I-III da tatsuniyoyin Hausa ta fuskar jigon illar cin
amana. A cikin wasu labaran Magana Jari
Ce, an nuna cewa cin amana ba shi da wani amafani. Idan aka ce cin amana,
ana nufin yaudadar wanda ya aminta da mutum. Idan aka aminta da wani, kuma ya
yi yaudara, sai a ce ya yi zamba cikin aminci, wato dai ya ci amana ke nan. A
cikin Magana Jari Ce littafi na uku.
A cikin labarin, “Munafunci Dodo Yakan Ci Mai Shi,” an nuna yadda Sarki Sabitu
ya amince da Maisango ƙwarai
har ya saka shi cikin ‘ya’yansa kamar Sarki ya haife shi. Da yake Maisango
maciyin amana ne, sai da ya yi ƙulle-ƙulle ya tura ‘ya’yan Sarki Sabitu
suka haɗa kai suka kashe shi
har lahira:
Ba a daɗe
ba da yin wannan taɗi,
sai aka ga kawai ran nan daga Sarki ya gama cin abinci sai ya yi ta murɗe-murɗe,
cikinsa na ciwo. Kasuwa ta buɗe ga
‘yan bori, amma duk a banza, ciwo sai gaba-gaba yake yi (Imam, 1940: 67).
Kamar
yadda aka nuna a labarin nan na sama, Maisangon da Sarki Sabitu ya tsinto ne ya
haɗa baki da mai kai wa sarki
abinci, aka zuba masa guba ya ci ya mutu. Ya yi haka ne saboda ya yi ƙulle-ƙullen da aka naɗa
wanda yake so daga cikin ‘ya’yan Sarki don ya yi wa Maisango wata sarauta mai
tsoka. Wannan ba ƙaramin
cin amana ba ne, Sarki Sabitu ya taimaki Maisango ya ɗaukaka
shi, amma shi Maisango ya yi dalilin halaka Sarki Sabitu. Maisango bai tsaya nan ba, Bayan Sarki Sabitu
ya rasu kuma, sai ya riƙa
bi yana raba kawunan ‘ya’yansa, suka yi ta faɗa
a tsakaninsu. A cikin tatsuniyar, “Talipaku da Kurciya” ma irin wannan saƙon ne aka aika da shi ga mai
sauraro. An nuna yadda yadda Talipaku ta ci amanar Kurciya inda a matsayinsu na
ƙawayen
juna ta sace mata ‘ya ta gudu. Ita ‘yar Talipaku bakinta dogo ne ba ya barin ta
ko ta ci abinci. Ita kuwa kurciya bakinta ɗan
ƙarami
ne madaidaici, shi ya sa take da kyau.
Shi ke nan, sai
Talipaku ta yanke shawarar sace ‘yar Kurciya ta gudu da ita. Wata rana suna
wurin neman abinci, sai Talipaku ta sulale ta je ta sace ‘yar Kurciya ta gudu
da ita. Da Kurciya ta ɗaga
kai ba ta ga Talipaku ba, kuma suna daf da tafiya gida, kuma ta nemi ƙawarta har ta gaji, sai ta
dawo gida ita kaɗai.
Da ta shiga sheƙa,
sai ta ga ba ‘yarta, sa ɗiyar
Talipaku. Sai ta fita ta kama cigiya. Sai aka ce mata an ga Talipaku ta ɗauki
‘yar Kurciya sun yi Yamma (Usman, 2012: 120).
Satar
‘yar ƙawarta
da Talipaku ta yi cin amana ne, wanda daga ƙarshe sai da lamarin ya kai ta
ga da-na-sani. Dalili kuwa, an nuna a tatsuniyar cewa, bayan da Kurciya ta gaji
da neman Talipaku, sai ta tafi gidan Sarkin Tsuntsaye ta kai ƙara. Shi kuma ya sa dogarawa
su tafi duk inda Talipaku ta shiga a kawo ta. Haka aka yi, suka gano ta suka zo
da ita gaban Sarki. Shi kuma ya karɓi
‘yar Kurciya da Talipaku ta sace, ya mayar mata da abinta. Ya kuma miƙa wa talipaku ‘yarta da ta
bari, ya kuma sa aka hukunta Talipaku hukunci mai tsanani a kan wannan cin amana
da ta yi wa ƙawarta
Kurciya. Ke nan da labarin, “Munafunci Dodo Ne Yakan Ci Mai Shi” na Magana Jari Ce III da tatsuniyar, “Talipaku
da Kurciya” duka da jigo iri ɗaya
aka saƙa
su wato jigon illar cin amana.
4.3
Dangantaka ta Fuskar Jigon Kishi
Kishi na nufin rashin jituwa da nuna ƙyashi irin wanda matan da ke
auren mutum ɗaya ke yi wa juna
(CNHN, 2006: 247). Tsananin son da mace ke yi wa mijinta ko neman keɓancewa
zuwa ga mijunta ko wanda take son ta aura da take nuna ƙauna da kyakkyawar fata gare
shi tare kuma da nuna ƙiyayyarta
ga duk wata da ke son sa da aure ko kuma shi yake son ta da aure, shi ne kishi
(Bakura, 2014: 8-9).
Kishi yana cikin zuciyar kowace mata sai in akwai kawaici.
A tsarin zamantakewar al’ummar Hausawa, kishi wani furen kallo ne a tsakanin
mata. Da yake al’adar Hausawa da addinin Musulunci da aka san Hausawa da shi,
sun aminta da auren mace fiye da ɗaya.
Wannan dalili ne ya sa kishi ya zama wani lamari da ke ci wa matan Hausawa tuwo
a ƙwarya.
Su kuwa mazaje, rikice-rikicen kishi ba ya hana su auren mace fiye da ɗaya.
Kishi jigo ne da ya haɗa
wasu labaran Magana Jari Ce da
tatsuniyoyin Hausa ya sarƙe.
Misali a cikin labarin, “Yadda Muka Yi da Ubangijina Ojo” da ke cikin Magana Jari Ce littafi na farko, an fito
da wannan jigo ƙarara.
Mawallafin littafin Abubakar Imam ya nuna yadda wani tauraron labarin ya auro
mata uku suna zaune gida ɗaya,
sai kuma ya ƙaro
wata matar suka zama huɗu:
Amma duk da haka,
abin ya ba ka mamaki in ka ji na ce matarsa ɗaya
ce tal. Da yana da uku, sai ya auro wata hatsabibiyar karuwa suka yi huɗu.
Ko da karuwan nan ta shiga gidansa, sai ta tasar ma shiga bokaye da ‘yan bori
don ta sami maganin da za ta kori sauran matan. Kwanci tashi ta ko samu (Imam,
1939: 53).
A nan, an nuna yadda Ojo ke da matansa uku. Duk da yake
dai Ojo ba Bahaushe ba ne, kamar yadda aka nuna a labarin, shi Bayarabe ne,
amma yana rayuwa a ƙasar
Hausa. Al’adu da ɗabi’u
da tsarin rayuwar Hausawa sun haɗiye
nasa na Yarbawa, saboda haka, ya auri mata uku a lokaci ɗaya.
An kuma nuna cewa ya ƙara
auren wata hatsabibiyar karuwa a matsayin mata ta huɗu,
wato dai ya kai maƙurar
abin da addinin Musulunci ya tsara wa kowane namiji. Karuwa Ojo ya aura a
matsayin mata ta huɗu
kuma ya haɗa da ukun da yake da su.
A ƙasar
Hausa, an san yadda karuwa take da ƙulle-ƙullen makirci har ma dai
idan ta sami nasarar shiga gidan kishiyoyi. Karuwa tana da tsananin kishi, kuma
takan haɗa kishinta da bin
malaman tsibbu da bokaye da ‘yan bori don ta kori sauran matan gida ta mallaki
miji ita kaɗai.
A cikin tatsuniyar, “Kaza da Gishiri”
ma irin wannan jigo na kishi ne aka warware zaren labarin da shi. Gishiri ne
dai ya auri Kaza suna zamansu. To, amma saboda gishiri ba ya son ruwa, narkewa
yake yi, sai Kaza ta ce idan ta ga hadari ya taso alhali shi kuma yana gona,
sai ta hau danga ta yi cara ta kira shi. Haka suka yi ta yi, har ya riƙa samun amfanin gona mai
yawa. Suna cikin wadata da yalwa. Da ya ga sun fi ƙarfin kome, sai ya yi mata
kishiya, inda ya auro tunkiya. Ita ma da ta zo gidan:
Ana nan sai damina ta
kama. Gishiri ya kira matansa ya ce musu damina ta kama, don haka za a yi yadda
aka saba. Sai Kaza ta ce za ta yi, amma sai ranar kwananta kawai za ta kira
shi, ran kwanan Tunkiya ita za ta kira shi (Koko, 2009: 56).
Kaza
ta nuna cewa, ba ta ji daɗin ƙara aure ko kishiyar nan da
mijinta Gishiri ya yi mata ba. Duk macen da ta ji martanin da Kaza ta mayar ga
mijinta da kishiyarta Tunkiya, ta san cewa akwai ɓacin
rai da zafin kishi a zuciyar Kaza, saboda haka ta nuna ba za ta kira mijinsu
ba, idan ba ranar girkinta ba ne. Akwai haɗari
tattare da rashin kiran Gishiri da Kaza ta yi ranar girkin kishiyarta, domin ruwan
sama zai bugi Gishiri ya narke ya mutu su duka su huta. Saboda zafin kishi ne
ya sa ta ƙi
kiran sa, kuma daga ƙarshe
ya rasa ransa.
4.4 Dangantaka ta Fuskar
Jigon Jarunta
Wani jigo da wasu labaran Magana Jari Ce da Tatsuniyoyin Hausa suka yi tarayya a kansa shi ne
jigon jarunta. Juriyar wahala da ƙalubale
wajen cim ma wani buri ita ce jarunta (CNHN, 2006: 214). A cikin labarin “Jimrau
Ɗan
Sarkin Noma na Biyu” da ke cikin Magana
Jari Ce littafi na biyu, an nuna yadda Jumrau ya yi amfani da jarunta ya
kashe dodanniyar da ke tare fatake tana kashe su ta ƙwace musu kaya. Jimrau ya
cire fargaba ya tunkari gidan Dodanniya. Da ya yi sallama, Dodanniya ta fito
sai ya yi ta-maza ya riƙa
yi mata shaguɓe yana kambama ta. Ta
nuna wa Jimrai tana iya rikiɗa ta
koma dabbobi manya da ƙanana.
Ta yi ta rikiɗa tana komawa dabbobi
iri-iri, sai kawai ya ce mata:
“Ai wani abu sai mai
shi. Yanzu kina iya rikiɗa ƙananan dabbobi kamar su ɓera
ko? Dodanniya ta ce, “Af, ɓeran
me kuma? An rikiɗa
giwa balle ɓera?” Sai ta girgiza
jikinta, ta zama ɓera.
Da ganin ta zama ɓera,
sai Jimrau ya yi farat ya saki kyanwarsa yadda yaron nan ya gaya masa. Ko da
kyanwa ta ga ɓera, sai ta yi tsalle
ta kama shi ta kashe ta cinye. Ko da ta cinye Dodanniya, sai ya ji gidan ya ɗauka,
“Haa! Jimrau ka yi nasara, babu kuskure, ka yi nasara (Imam, 1940: 43).
Jaruntar
da Jimrau ya nuna a wannan gaɓa
ita ce yadda Jimrau ya tunkari gidan Dodanniya ya yi ido-da-ido har suka yi
zance na raha a tsakaninsu. Haka kuma, bai ji tsoron cewa Dodanniya ta gane
cewa akwai mage tare da shi ba, ganin cewa za ta iya gane haka, saboda ita ba
mutum ba ce. Yin farat da Jimrau ya yi ya saki kyanwar da ke cikin jikinsa ma
wani nau’i ne na jarunta. Domin da ya yi fargabar sakin kyanwa, to da Dodanniya
ta gama rikiɗe-rikiɗenta,
sai ta yi kansa ta kuma halaka shi har lahira. A cikin Tatsuniyar, “Sarkin Maƙera da Dodo” ma irin wannan
jigo ne na jarunta aka gina ta da shi. A cikin tatsuniyar an nuna yadda babban
tauraron tatsuniyar wato Fugo Sarkin Maƙera ya nuna jarunta wajen
kisan Dodon da ya tare ƙanwarsa
za ya cinye ta a cikin daji. Abin da ya faru shi ne, ƙanwar Sarkin Maƙera Fugo ne mahaifiyarsu ta
rasu. Ta yi nufin ta tafi wajen zaman makoki. A kan hanyarta, sai Dodo ya tare
ta zai cinye. Da ta ga lamarin ba girma, sai ta haye kan wata bishiya. Tana nan
zaune Dodo na ƙasan
bishiyar yana jira ta sauko ya cinye ta, sai ga Kurciya, sai ta ruga garin su
Fugo Sarkin Maƙera
ta shaida masa abin da ke faruwa. Ko da Fugo ya zo sai:
Ya zaro kibiya ya ɗirka
wa Dodon nan. Kafin ya farka ya farka, sai da Fugo ya yi masa ruwan kibau kamar
ashirin. Da ya farka kafin ya wartsake, Fugo ya jefa masa masu kamar guda tara.
Amma duk da haka, da ya wartsake sai aka ji yana cewa: “Kai wane cinnaka ne
yake damuna?” Shi kuwa Fugo sai ya zaro wasu kibau masu dafi ya dinga ɗana
su yana sakar wa Dodo ɗaya
bayan ɗaya a idonsa na dama,
nan take idonsa ya tsiyaye. Kafin ya san abin da ake ciki, Fugo ya sake auna ɗaya
idon, kuma ba kuskure ya same shi. Shi ma nan take ya tsiyaye. Dodo ya zama ba ya
iya gani. Tuni dafin kibiyar ya bi jikin Dodo, har ya zamanto ba zai iya tashi
ba. Sai Fugo ya ce da Awa ta sauko (Usman, 2012: 194).
Abin
da mai karatu zai gamu da shi a cikin wannan bayani na samu shi ne, tsananin
jaruntar da Fugo Sarkin Maƙera
ya nuna wajen ceto ƙanwarsa
daga hannun Dodo. Dodo ya yi niyyar ya halaka Awa, amma da yake Awa na da
Jarumin ɗan’uwa wato Gugo, sai
ga shi ya tseratar da ita daga zaluncin Dodo. Kamar yadda aka gani a cikin
bayanin, Fugo ya yi amfani da ƙarfi
da salon harbi da juriya da rashin fargaba da jajircewa da ƙarfin hali ya kashe Dodo.
Wannan namijin ƙoƙari d Fugo ya yi, ba ƙaramar jarunta ba ce. Don
haka, yadda ake samun wasu labaran Magana
Jari Ce I-III na zuwa da jigon jarunta, haka ake samun tatsuniyoyin Hausa
su ma suke zuwa da jigon jarunta.
4.5 Dangantaka Ta Fuskar
Jigon Soyayya
Soyayya gamon jinni. Soyayya
ruwan zuma, in an sha a ba masoyi. Waɗannan
duk kirare-kiraren da Hausawa ke yi wa soyayya ne. Bayan haka, Nuna ƙauna daga ɓangarori
biyu na masu ƙaunar
juna, musamman mace da namiji shi ne soyayya (CNHN, 2006: 398). Soyayya babban
jigo ne na wasu labaran Magana Jari Ce
I-III da Tatsuniyoyin Hausa suka
yi tarayya a kansa. Da jigon soyayya ne aka bayar da labarin, “Sauri Ya Haifi
Nawa” na cikin Magana Jari Ce littafi
na farko. An fito da soyayyar da ta ƙullu
tsakanin Nana Yauƙi
da ɗan Sarki. Sarki ya tafi
rangadi tare da ɗansa,
har Allah Ya kai su garin su Nana. Lokacin da ya ga Nana, sai soyayyarta ta
kama shi:
...Ya taƙale ta da maganar aure, ya
ga alamar lalle tana son sa. Wancan mijin da za a ba ta, wai dattijo ne mai
gemu. Ita kuwa ta ce ba ta auren mai gemu. Bayan sun shirya da ita a nan sai ta
tafi. Ya ɗauki buta a masallaci
ya yi alwala, ya shiga ya yi salla. Da yai sallama, ya yi addu’a ga Fiyayyen
Taliki ya nufa Allah Ya sa ya auri wannan yarinya. Don ɗokin
buƙatar
auren yarinyar nan har ya yi suɓul
da baka ya ce wai in Allah Ya nufa ya aure ta ya kashe kansa don murna (Imam,
1939: 117).
Haka nan ma a cikin tatsuniyar, “Marainiya” ma, babban
jigonta shi ne soyayya. An fito da soyayyar da ta ƙullu tsakanin Aminu ɗan
sarki, da wata yarinya marainiya wadda iyayenta suka rasu. Bayan iyayenta sun
mutu, sai kishiyar uwarta ta riƙa
ƙuntata
mata, saboda haka, sai ta tafi daji ƙarƙashin wata bishiyar kurna ta
zauna tana kuka tana tunani. Akwai wani ɗan
sarki mai suna Aminu da yakan zo kullum ya hau kan bishiyar kurnan nan ya sha
iska da yamma. Kullum yana ganin ta bai taɓa
yi mata magana ba, sai ran nan dai Aminu ya gan ta a wurin:
Aminu ya ce, “Me ke
damun ki ne? Kullum sai in zo in gan ki a gindin wannan bishiya, har ma domin
tunanin da kike yi ba ki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni
sai da la’asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gan ni b a. “To yaya kake
zama a kan bishiyar Kurna mai ƙaya?”
Ta tambaye shi. Sai ya ce: “Ni na san dabarar da nake yi.” Haka dai suka ci
gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure. Sai ta ce, “Ni marainiya ce, ban
da uwa, ba ni da uba.” Sai ɗan
sarki ya Aminu ya ce: “Yau na zama uba da uwa a wurinki.” (Usman, 20126-7).
Idan
aka lura da waɗannan bayanai na
sama, za a iya ganin kyakkyawar dangantaka ta fuskar jigon soyayya tsakanin
labarin, “Sauri Ya Haifi Nawa” na cikin littafin Magana Jari Ce II, da kuma tatsuniyar Marainiya. An nuna yadda
soyayya ta yi ƙarfi
tsakanin Nana Yauƙi
da ɗan sarki na cikin Magana Jari Ce II da kuma soyayya mai
danƙo
tsakanin Marainiya da Aminu ɗan
sarki. Tabbas akwai alaƙa
tsakaninsu. Aalaƙar
ta farko ta jigon soyayya da aka gina duka labaran da ita, sai kuma yadda
samarin suka zama ‘ya’yan sarki su kuma ‘yanmatan suka zama ‘ya’yan talakawa.
Haka kuma, duka masoyan sun sami damar cim ma gurinsu na auren juna.
4.6 Dangantaka ta Fuskar
Jigon Adalcin Shuwagabanni
Adalci yana nufin tausayawa ko yin hukunci bisa gaskiya
ko rangwantawa (CNHN, 2006: 2). Yayin da shugaba a ɗaya
ɓangaren, yake nufin jagora
ko jagaba wanda ya ɗauki
nauyin jan ragamar jama’a ko wata ƙungiya
ta mutane (CNHN, 2006: 415). Shugaba guda ɗaya
ke nan ko mace ko namiji, yayin da jam’in kalmar akan ce, “Shuwagabanni.” Akwai
kyakkyawar dangantaka tsakanin wasu labaran Magana
Jari Ce I-III da tatsuniyoyin Hausa dangane da jigon adalcin shuwagabanni. A
“Labarin Annabi Sualaimanu” na cikin Magana
Jari Ce littafi na farko, an nuna yadda wasu mata suka zo wajen Annabi
Sulaimanu domin ya yi musu hukunci da adalci a kan matsalar da ta shiga
tsakaninsu.
Waɗannan
mata gida ɗaya ɗaya
suke kuma sun haihu, kowace tana goyon jariri. Sai ɗaya
ta kwanta a kan ɗanta
ba ta sani ba, tana cikin barci. Da ta farka ta ga abin da ke faruwa, sai ta
tashi ta yi wa ‘yar’uwarta musayar ɗa,
ta ajiye mata gawa, ita kuma ta ɗauki
mai rai, sai gardama ta sarƙe
tsakaninsu, kowace na cewa, mai ran ce tata:
Da Annabi Sualaimanu
ya ji maganar matan nan, sai ya sa aka ɗauko
takobi aka zare, ya ce, “Tun da yake abin ya rikice haka, abu ɗaya
kaɗai za a yi a raba gardamar
nan. Zan raba ɗan nan biyu,
kowacenku ta ɗauki rabi kowa ya
huta, ku dangana har Allah Ya sake ba ku waɗansu.
Da mace ɗaya ta ji haka, sai
ta ce, “Don Allah kada a kashe shi. A ba ta na yarda mata.” Amma waccan ta ce,
“A’a daidai ne, ya Annabi. A dai raba shi kowa ya huta.” Da Annabi Sulaimanu ya
ji haka, sai ya ce, “Ku miƙa
ɗan nan mai rai ga waccan da
ta ce kada a kashe shi. Ɗanta
ne ita ta haife shi.” (Imam, 1939: 94).
Tatsuniyoyin
Hausa ma kan zo da irin wannan jigo na Adalcin Shuwagabanni. Dubi abin da ya
faru a cikin tatsuniyar, “Talipaku da Kur4rciya.” Sheƙa ɗaya
Talipaku da Kurciya suka yi ƙwayayensu
suka ƙyanƙyashe. Zuriyar su Talipaku
da dogon baki suke haihuwar ‘ya’yansu. Su kuma zuriyar su Kurciya da ɗan
ƙaramin
baki mai kyau ake ƙyanƙyashe su. Ashe wannan lamari
ya dami Talipaku ganin ba mai son ɗaukar
‘yarta ya taya ta raino, saboda dogon bakin da ‘yarta ke da shi. Ita kuwa
kurciya kowa sai son ɗaukar
‘yarta yake yi, saboda bakinta ɗan ƙarami mai kyawu. Hassada ta
turnuƙe
Talipaku, saboda haka, sai da ta bari sun fita neman abinci da ita da Kurciya,
sai Talipaku ta yi waiwai-da-baya ta dawo gida ta sace ‘yar Talipaku ta fice da
ita ta bar wa Talipaku ‘yarta mai babban baki. Da Kurciya ta dawo ta ga abin da
ya faru, sai ta fita neman Talipaku don ta karɓi
‘yarta, ita kuma ta ba ta tata. Tana ta cigiya, sai aka ce mata an ga Talipaku
da ‘yarta sun yi Yamma. Ko da Kurciya ta tabbatar da zargin da take yi, sai ta
garzaya gidan Sarkin Tsuntsaye ta shigar da ƙara:
Sai Sarkin ya sa aka ƙwace ‘yar Kurciya aka ba ta
‘yarta. Ita ma Talipaku aka ba ta ‘yarta. Sarkin Tsuntsaye ya ja kunnen
Talipaku da kada ta kuskura ta sake satar ‘yar wani tsuntsu. Idan kuwa aka sake
kawo ta ƙarar
ta, to, za a kashe ta. Sai aka sallame su. Kurciya ta ɗauki
‘yarta. Ta yi godiya ta tafi. Ita kuma Talipaku ta tafi da ‘yarta (Usman, 2012:
121).
Akwai
dangantaka sosai dangane da saƙon
adalcin shuwagabanni da aka isar a cikin labaran nan guda biyu: “Labarin Annabi
Sulaimanu” da kuma tatsuniyar “Talipaku da Kurciya.” Duka shuwagabannin cikin
labaran biyu: Annabi Sulaimanu da Sarkin Tsuntsaye sun yi hukunci da gaskiya.
Hukunci da gaskiya ga masu jayayya ko mai laifi shi ne adalci. Akan nusar da
shuwagabanni a kan yin adalci cikin hukunci ta hanyar rubuta ƙagaggen labarin Hausa kamar Magana Jari Ce da kuma tatsuniyar Hausa
kamar tatsuniyar Talipaku da Kurciya.
4.7
Dangantaka ta Fuskar Jigon Wayon Zaman Duniya
Wayo na nufin dabara ko cuta (CNHN, 2006: 472). Tun da
wayo dabara ce, ke nan idan aka ce “Wayon zaman duniya,” ana nufin dabarar
zaman dauniya. Babban jigo ne da masu bayar da labari ke amfani da shi. An kuma
samu dangantaka mai danƙo
tsakanin wasu labaran Magana Jari Ce da
tatsuniyoyin Hausa. A cikin “Labarin Kyanwa da Ɓera” da ke cikin Magana Jari Ce littafi na farko, an
warware irin wannan jigo. A cikin labarin an nuna yadda ɓera
yake da wayon zaman duniya, inda ya nuna dabara daban-daban wajen cinye igiyar
ragar tarkon da ta kama muzuru. Tarkon mai gona ne ya kama muzuru. A ɗaya
ɓangare kuma, ɓera
ya ga maciji da shirwa a wurin. Ɓera
ya san ba su jituwa da shi. Ɓera
ya yi amfani da wayon zaman duniya inda ya yi shawarar cinye igiyar ragar da ta
kama muzuru:
Ɓera
kuwa da ya waiga ya ga tarko ya kame muzuru, sai ya yi rawa yana murna. Yana
nan yana murna, ya duba haka cikin kara kusa da raminsa, sai ga wani maciji nan
yana jira ya rabo da muzuru ya haɗiye
shi. Ya duba sama don ya hau, sai ya ga shirwa na kewaya tana jira ya motsa ta
fyauce shi. Abu ya zama masa gaba siyaki baya damisa. Yana nan sai ya tuna da
wata dabara, ya ce, “Na san dai da maciji da shirwa ba mai iya zuwa kusa da
muzuru. Yanzu ba abin da ya fi sai in je wajen muzuru in ce ya rantse ba zai
sake cuta ta ba, ni ko in cinye igiyar ragar nan in sake shi” (Imam, 1939: 44).
Wannan
tunani na neman kuɓutar
da rayuwa da ɓera ya yi, wayo ne na
zaman duniya. Da bai yi wannan tunani ba, da ya rasa ransa, domin maciji ko
shirwa za su halaka shi. Dubi yadda ɓera
ya yi nazarin mummunar dangantakar da ke akwai tsakanin maciji da shirwa da
muzuru, wadda a kanta ne ya shirya yadda zai haɗa
su wuri guda, shi kuma ya kuɓuta.
Wayo wani lokaci yana nufin cuta ko yaudara kamar yadda (CNHN, 2006) ya nuna.
Ta wannan fuska, muzuru ya cuci ɓera,
ya kuma yaudare shi Domin bayan sun ƙulla
abota, sai suka shirya haɗa
kayan abincinsu wuri ɗaya,
da yarjejeniyar cewa, ba za su fara amfani da su ba, sai lokacin hunturu. Ko da
aka kwana biyu, sai Muzuru ya yi wa ɓera
ƙaryar
an gayyace shi taron suna, sai ɓera
ya ce da shi kada ya manta da shi ga kayan suna:
Muzuru ya ce, “Haba,
in na manta da kai, in tuna da wa?” Ya nufi gari. Da ma ƙarya yake yi, ba wanda ya
gayyace shi suna, wajen ajiyarsu yake so ya je ya ci. Da ya ci ya ƙoshi, sai ya sami wuri ya
kwanta yana lasar gashi, yana gurnani. Can da rana ta yi sai ya komo (Imam,
1949: 47).
Wannan
jigo na wayon yaudara da cuta shi ne aka warware a cikin wannan bayani na sama.
Kamar yadda ake gani, muzuru ya cuci ɓera
ta hanyar yaudararsa yana sulalawa yana cinye musu kayan abincinsu da ba shi kaɗai
ya tara su ba. Duk lokacin da ya je ya ci, sai ya dawo ya yi wa Ɓera ƙarya, har ya faɗa
masa sunan jariri wanda sunan ke aika saƙon shaguɓe
da habaicin cutar da ya yi wa masa. Ta fuskar wannan jigo ne kuma aka samu
kamanceceniya da tatsuniyar Hausa ta, “Ƙawancen Kyanwa da Ɓera.” A cikin wannan
tatsuniya ma Ɓera
ne ya yaudari kyanwa, yana zuwa yana cinye kayan abincin da suka yi tanaji sai
lokacin hunturu su yi amfani da shi. Ya riƙa yi wa Kyanwa ƙaryar an gayyace shi ne
wajen bikin ƙanwarsa:
Suna nan, ran nan Ɓera ya ce da Kyanwa zai je
bikin ƙanwarsa.
Da ya fita sai ya nufi rumbun abincin da suka tara, ya ci har sai ya da ya ƙoshi. Da ya dawo gida sai
Kyanwa ta yi masa maraba, ta tambaye shi, “Me aka samu ne?” Ɓera ya dubi Kyanwa ya ce,
“Abin da aka samu shi ne Wuyar Aikin Ba a Fara Ba.” (Usman, 2012: 69).
Idan
aka lura, za a ga cewa akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin “Labarin Kyanwa
da Ɓera”
da ke cikin Magana Jari Ce littafi na
farko da kuma tatsuniyar, “Ƙawancen
Kyanwa da Ɓera.”
Labarin iri ɗaya ne, sai dai wajen
ruwayar labaran ne aka samu bambanci. A cikin Magana Jari Ce, an nuna cewa Muzuru ne ya cuci Ɓera, yayin da cikin
tatsuniyar “Ƙawancen
Kyanwa da Ɓera”
kuma sai aka sauya lamarin aka nuna Ɓera
ne ya yi wa Kyanwa Wayon cuta da yaudara, amma dai jigon na wayon cuta da
yaudara, iri ɗaya ne bai sauya ba.
4.8
Dangantaka ta Fuskar Jigon Illar Bijire wa Iyaye
Bijirewa na nufin kangarewa (CNHN, 2006: 46). Yayin da
Kalmar “Iyaye” ke nufin uwa da uba (CNHN, 2006: 209). Bijire wa iyaye wato
kangare wa koyarwarsu a al’adar Bahaushe da addininsa illa ace babba. Masu ba da
labari kan ɗauki wannan lamari a
matsayin jigo na musamman da suke isarwa ga jama’a a cikin labaransu. A cikin
labarin, “Babban Mugun Abu Ɗa
Ya Yi Hushi da Iyayensa” na cikin Magana
Jari Ce littafi na farko, an nuna yadda wani yaro ɗan
makarantar boko wai shi Ilu ya bijire wa iyayensa kawai don sun yi masa faɗa
a kan ya ƙara
mai da hankali a kan karatunsa, saboda sakamakon jarabawarsa bai yi kyau ba.
Kawai sai:
Yaro ya tashi yana ta
hushi, wai uban ya ce in bai yi ƙoƙari ba, zai ba da shi ga
mahauta ya je ya yi tallar tsire. Ya koma ƙaramin zauren gidan ya
zauna. Yana nan yana ciccika, lokacin cin abinci ya yi, ƙanensa Ibrahim ya zo ya kira
shi su je su ci. Sai Ilu ya dube shi da hushi ya ce, “Je ka ci, ni ban ci!”
Ibrahim ya bushe da dariya, ya ce, “Kana tsammani wani ya kula don ba ka ci
abinci ba. Je ka huta.” (Imam, 1939: 75).
Fushin
da Ilu yake yi da iyayensa wani ɓangare
ne na bijire musu. Ba sa son ɗabi’ar
da yake yi ta fushi da yajin cin abinci kwana da kwanaki. Sun yi, sun yi ya
daina fushin amma ya kangare musu. Ya riƙa ɗaukar
kayansa na sawa yana kai wa kasuwa yana sayarwa yana cin abinci ba su sani ba.
Da Allah Ya tsahi kama Ilu, sai da ya sayar da kayan, ya nufi tukubar mai nama,
ya saya ya ci, ya sha ruwa ya dawo gida. Ya kwanta ke nan yana ta fushi, sai
cikinsa ya kama ciwo, ya yi ta amai yana fitar da naman nan, ya galabaita matuƙa. Iyayen nasa da yake fushi
da su, su dai ne suka tarairaye shi, suka nema masa magani ya warke. Daga baya
ya yi nadama. Irin wannan jigo ne aka yi amfani da shi aka gina “Tatsuniyar
Wani Yaro Mai Taurin Kai” da shi. Wani yaro ne da ba a ambaci sunansa ba, ya
zama mai taurin kai da bijire wa iyayensa:
Wata rana wannan yaro
ya je gona da iyayensa. Bayan sun yini suna aiki sai suka koma gida da rana ta
faɗi. Da tsakar dare sai yaron
nan ya tuna da cewa ya manta mabusarsa a gona. Ya ta da iyayensa daga barci ya
gaya musu cewa zai je gona ya ɗauko
mabusarsa da ya manta a can. Iyayensa suka roƙe shi da kada ya je, ya bari
har safiya ta waye, amma ina! Kafin ma su ƙare magana, har yaron nan ya
yi nisa da tafiya cikin duhun dare ya nufi gona (Koko, 2009: 44).
Dubi
yadda yaron nan ya kangare wa iyayensa ya nufi gona ɗaukar
mabusarsa da ya manto. Ga shi kuma dare ya yi sosai. Wannan bijirewa da kangarewa
da ma taurin kan da ya yi wa iyayen ne suka sa ya haɗu
da aljannu a gonar inda suka azabtar da shi ta hanyar tursasa masa ya riƙa yi musu busa suna rawa. Da
ƙyar
wannan yaro ya kuɓuta.
Wannan wahala da ya sha a hannun aljannu ce ta sa ya zama yaron kirki, ya yi
nadamar laifukan da ya yi wa iyayensa. Ke nan an sami kyakkyawar dangantaka
tsakanin labarin, “Babban Mugun Abu ga Ɗa Ya Yi Fushi da Iyayensa”
na cikin Magana Jari Ce littafi na
farko da “Tatsuniyar Wani Yaro Mai Taurin Kai” ta fuskar jigon illar bijire wa
iyaye.
4.9
Dangantaka ta Fuskar Jigon Raha
Akwai
dangantaka mai ƙarfi
tsakanin wasu labaran Magan Jari Ce
da tatsuniyoyin Hausa ta fuskar raha. Walwala ko fara’a ita ce raha (CNHN, 2006:
364). Babban jigo ne da masu bayar da labari ke laɓewa
bayansa wajen isar da saƙonnin
labaransu ga jama’a. Raha a cikin labari, ta ƙunshi kawo wata gaɓa
mai sa nishaɗi da ban dariya ga
mai sauraro ko karatun labari. A cikin labarin, “Sahoro da Sahorama” na cikin Magana Jari Ce littafi na farko,
mawallafin ya kawo wata kokawa da ta kaure tsakanin miji (Sahoro) da mata
(Sahorama) mai ban dariya. Sahorama dai ce take tsaye a tsakiyar ɗakinta
inda mijinta Sahoro ke kwance yana hutawa. Labari ya kawo inda Sahorama take
nuna yadda za ta yi wa almajirin da za su ɗauko
ya riƙa
yi musu kiwon awaki da tata da ta mijin. Lamarin ƙaddara, sai ta buge goron
zumar da ta rage musu da sanda. Gora ya fashe ya malale ƙasa. Sahorama ta duƙa tana kwasa da hannu tana
zuwa rabi cikin gora, rabi kuma tana shanyewa. Wannan hali na Sahorama ya
kufula mijinta Sahorami, saboda haka sai ya tsawata mata. Ai sai Sahorama ta
ce, “Ina wuta ta jefa shi?” Kai! Har da dai su zagi. To, a wannan gaɓar
ne Sahorami ya ce, “Ni kika zaga?: ”
Sahorama ta ce, “An
je an zage ka, kai dai ne Kafiri ba ni ba. In kai ɗa
ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!” Sai zuciya ta turniƙe Sahoro, ya tashi daga
kwance ya sauko ya tarar da matar, sai kokowa kicici-kicici, kica-kica. Can
Sahoro ya gaji ya ga bai kada matar ba, sai ita ke neman tandara shi da ƙasa, sai ya ce mata, “To
sakar ni kin kayar. Na ce ko iyakarta ke nan?” Sahorama ta ce, “Af! in sake ka
ni in faɗi?” (Imam, 1939: 31).
Akwai
lamurran da ke sa raha a cikin wannan kokawa da ta kaure tsakanin Sahoro da
Sahorama. A matsayinsa na namiji, Sahoro ya kamata a ce ya ci galabar Sahorama
ya ka da ita. Sai ga shi ana zaton wuta a maƙera, an same ta masaƙa. Sahorama ta ɗaga
Sahorami sama za ta kayar. Ga shi Sahorami ya saduda har ya yi raki, yana cewa
Sahorama ta sauke shi ƙasa
ya saduda. Abin ban dariya, ashe ita kuma ba ta kama ƙasa ba, ta dogara da ƙafar Sahorami guda ɗaya
da ta rage a kan ƙasa,
da ya faɗi, ita ma za ta faɗi.
Ba ta yi nauyin baki ba, sai ta sanar da abokin kokawar halin da take ciki.
Banza ta kori wofi. Irin wannan jigo na raha ne aka yi amfani da shi aka gina
tatsuniyar, “Lolloda.” A tatsuniyar, an bayyana yadda tsohuwa ta tsinci wani ƙashi mai magana. Da ta
tambaye shi sunansa, sai ya ce mata Lolloda. Ta yi tunani mai kyau ta sake
tambayar sa me yake yi? Ƙashi
ya ce mata shi “Zuzzuba” ne aikinsa. Tsohuwa kuwa ta ce ya zuzzuba. Da ya dinga
zuzzuba mata kuɗi,
sai da ta kasa ɗauka.
Abin
ƙaddara,
sai Sarki ya ji labarin yadda tsohuwa ta yi arziƙi. Ya kuma ji labarin arziƙin tsohuwa sanadiyyar wani ƙashi ne mai Magana, saboda
haka ya aika wa tsohuwa ta yi gaugawar kawo ƙashin nan. Ba ta yi gardama
ba ta kawo masa, don haɗama
irin ta Saraki:
Sai ya ce a rufe shi
tare da ƙashin
kuma ko me aka ji, a ƙyale
shi kada a buɗe. Aka rufe sarki,
sarki ya ci gaba da kiran Lolloda, ƙashi
na ta loda masa bugu ga kai yana ta kuwa. Kowa ya ƙyale shi. Sai da ya sha kashi
sosai sannan aka buɗe
shi duk kansa ya kumbura (Koko, 2009: 79).
Kamar
yadda aka sha dariya a cikin labarin “Sahoro da Sahorama” na cikin Magana Jari Ce littafi na farko, haka
ita wannan tatsuniya take ba mai sauraro ko karatu dariya. Abin dariya a wannan
bayani da aka ciro daga tatsuniyar Lolloda da ke sama shi ne, yadda Sarki ya ƙwace wa tsohuwa ƙashi don zalunci. Saboda
garajen ya sami kuɗi
bai tambayi tsohuwa kalmar da ake faɗa
wa ƙashi
ya yi aman kuɗi ba. Domin wauta
irin ta Sarki ma, sai ya ce a rufe shi cikin ɗaki
tare da ƙashi
domin ba ya son wani ya sami ko ɗari
daga kuɗin da ƙashi zai amayar masa. Yadda
Lolloda ya riƙa
loda wa Sarki bugu cikin ɗaki
yana raki, shi ma abin dariya ne kuma zai sa mai sauraro ko karatu raha. Wani
abin da zai ƙara
ba da dariya cikin tatsuniyar shi ne yadda aka fito da sarki daga ɗakin
nan, duk ƙashi
ya saɓa masa kamannu.
Saboda haka, dangane da jigon raha, tabbas akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin
wasu labaran Magana Jari Ce da
tatsuniyoyin Hausa.
4.10
Dangantaka ta Fuskar Jigon Illar Ruwan Ido
Idan
aka ce, “Ruwan ido” ana nufin rashin tsai da rai a wajen zaɓen
abu (CNHN, 2006: 377). Ruwan ido ɗabi’a
ce mai illa a tsarin zamantakewar Bahaushe. Mutum mai ruwan ido ma, Hausawa na
kallonsa a matsayin mutum marar nagarta da son abin duniya. Illar ruwan ido
babbar jigo ne ga masu ba da labarin Hausa. Ana kuma samun dangantaka tsakanin
wasu labaran Magana Jari Ce I-III da
kuma tatsuniyoyin Hausa ta fuskar jigon illar ruwan ido. A cikin labarin, “Wanda
Ke Wulaƙanta
Jama’a Duk ya Ga Iyakarsa” na cikin Magana
Jari Ce littafi na Uku. Labarin wata ‘yar sarki ce mai suna Mama aka bayar.
Mama ta kasa zaɓen
wanda za ta aura, duk da cewa ta girma sosai ta isa a yi mata aure. Ga yadda
aka nuna a labarin duk tsararrakinta ma sun haihu. Lamarin ya dami mahaifinta
Sarki, saboda
kowa
ya je nemanta sai kushe shi, sai wani aljani daga zuriyar Ƙurungu Sarkin Kawuna, waɗanda
halittarsu kai ne kawai babu gangar jiki ya ji labari. Ya kuwa aiko wata
tsohuwa da ta tambaya masa izni. Amsa kuwa ta yi daidai, Sarki ya yi murna ya
buƙaci
tsohuwa ta kawo ango fada a gan shi. Ko da tsohuwa ta shaida wa Ƙurungu buƙatar Sarki:
Kai ya ce, “Ba kome,
sa ni cikin tasa ki kai ni.” Tsohuwa ta sa shi cikin tasa, ta ɗauka
ta kai gaban Sarki duk jikinta na rawa. Ta ajiye, ta ce, “Allah Ya baka nasara,
ga ɗan nawa.” Sarki ya ja kujera
baya, fadawa kowa ya ja da baya. Sarki ya ce, “Me zan gani haka? Har abada ba na
aurar da Mama ga wannan dodo. Ku kira Mama ta ga abin da ruwan idonta ya jawo
mana.” (Imam, 1940: 40).
Illar
ruwan ido ce ta sa Mama, babbar tauraruwar labarin, “Wanda Ke Wulaƙanta jama’a Duk Ya Ga
Iyakarsa” ta auri dodo. Domin a nuna a ƙarshen labarin cewa Mama ta
tare gidan Kai babu yadda ta iya. Domin zuriyar Ƙurungu sun yi alƙawarin cewa idan ba a ba su
matarsu ba, za su saka al’ummar gari cikin bala’i. da Mama ba ta yi ruwan ido
wajen zaɓen ɗaya
daga cikin ‘ya’yan sarakunan da Sarki ya tara mata ba, da ba ta shiga wannan
matsala ba. Da irin wannan jigo na illar ruwan ido aka warware tatsuniyar,
“Budurwa Marar Tabo.” A cikin tatsuniyar, an nuna yadda wata budurwa marar tabo
ta sha alwashin auren saurayi marar tabo. Wannan alwashi nata ne ya kai ta ga ruwan
ido wajen zaɓen mijin da za ta
aura. Duk saurayin da ya zo neman aurenta, sai budurwar nan ta sa ya cire
kayansa ta dudduba jikinsa, ko ga yatsa ta ga tabo, kome ƙanƙantarsa, sai ta hau kujerar
na-ƙi,
ta ce ta fasa auren.
Ana nan, ana nan, sai wasu aljannun macizai suka ji
labarin wannan cin mutunci da budurwar nan take yi wa maza, sai suka yi alƙawarin yi wa tufƙar hanci. Macizan suka rikiɗa
suka zama samari santala-santala, jikin nan nasu sumul, suka tafi domin budurwar
nan ta yi musu jarabawa. Da ta dudduba jikinsu, sai ta ga babu tabo ko ɗaya
a jikinsu, saboda haka ta aminta za ta auri ɗaya
daga cikinsu. Aka kuwa ɗaura
aure:
Shi ken an, ta
tattara kayanta suka tafi da amaryarsu. Da suka je jeji sai suka ce, “Yawwa mun
iso gida.” Ita ko ta ce, “Ina gidan a nan?” Sai suka ce da ita, “Ai nan ne
gidan.” Amarya ta yi zuru-zuru babu yadda za ta yi domin ta riga ta auri ɗayansu,
kuma ga shi sun kai ta dokar daji inda ba za ta iya komawa gari ba. Daga nan
sai suka saka ta a kogon bishiya, suka rikiɗe
macizai suna lasar jikinta har ta zama fara fat, babu kyan gani kuma abin ƙyama (Usman, 2012: 20).
Kamar
yadda yadda Mama ta cikin labarin, “Wanda Ke Wulaƙanta Jama’a Duk Ya Ga
Iyakarsa” ta tsaya ruwan ido wajen zaɓar
miji, daga ƙarshe
ta auri Aljani kuma kai babu gangar jiki, haka ita ma wannan budurwa, babbar
tauraruwar tatsuniyar “Budurwa Marar Tabo” ta yi ruwan ido wajen zaɓen
nata mijin aure, daga ƙarshe
ita ma ta auri macijin aljani. Ke nan, an sami dangantakar jigon ruwan ido
tsakanin labarin cikin Magana Jari Ce da
tatsuniyar Hausa.
4.11
Sakamakon Bincike
Bayan
an ƙare
wannan bincike, sai aka gane cewa, wasu daga cikin labaran da aka gina Magana Jari Ce I-III da su, tushensu
daga tatsuniyoyin Hausa ne musamman ta fuskar jigo. Da yake jigogin rubutattun
labaran Hausa da na tatsuniyoyin Hausa suna da alaƙa ƙwarai, sai ma aka gane cewa
Abubakar Imam, mawallafin Magana Jari Ce
I-III, ya tasirantu matuƙa
da tatsuniyoyin Hausa, wato ya ji su daga bakin magabata, shi ya sa ya yi wa
wasu kwaskwarima ya sake mayar da su cikin rubutaccen labarinsa na Magana Jari Ce. Dubi “Labarin Kyanwa da Ɓera” na Magana Jari Ce I, da kuma “Ƙawancen Kyanwa da Bera” na tatsuniyar
Hausa, a gaskiya tatsuniyar ce Abubakar Imam ya yi wa baddala ta hikima. Taken
labaran iri ɗaya ne, taurarin
labaran iri ɗaya ne kuma jigon
labaran ma iri ɗaya
ne.
Haka
kuma, irin wannan baddalawa ce ta faru ga labarin, “Babban Mugun Abu Ɗa Ya Yi Fushi da Iyayensa”
na Magana Jari Ce I” da kuma
tatsuniyar, “Wani Yaro Mai Taurin Kai” duka jigon iri ɗaya
ne, wato suna aikawa da saƙon
illar bijire wa iyaye. An kuma gano cewa, dangantakar jigogi tsakanin Magana Jari Ce da Tatsuniyoyin Hausa ta
fi shafar Magana Jari Ce littafi na
farko, saboda an fi samun labarai masu kama da tatsuniya waɗanda
aka gauraya rayuwar mutane da dabbobi da ƙwari da tsirrai da dai sauran
halittu kuma a nuna suna magana da aiwatar da wasu ɗabi’u
da halaye irin na ɗan’adam.
5.0
Kammalawa
Saƙonnin
da ke cikin wasu labaran littafin Magana
Jari Ce I-III na Abubakar Imam, su ne kuma ke cikin tatsuniyoyin Hausa,
kuma su ne masana da manazarta ke kira jigogi. Jigogin da littafin Magana Jari Ce da tatsuniyoyin Hausa suna
da ɗimbin yawa, d babu wanda domin
babu wanda zai bugi gaba ya ce ga yawansu. Jigogin nan sun fi karkata a kan
hani da wasu miyagun halaye na zamantakewar al’umma da kuma horo a kan aikata
wasu kyawawan ɗabi’u da al’umma ta ɗauka
su ne masu kyawu. Takardar ta kwatanta tare da alaƙanta jigogin wasu labaran Magana Jari Ce da tatsuniyoyin Hausa. An
yi bayanin gabatarwa a farkon takardar, daga nan sai da aka kawo ma’anonin
tubalan take, kamar labari da jigo da tatsuniya. Daga nan sai aka yi taƙaitaccen jawabi a kan
samuwar littafin Magana Jari Ce I-III.
An kawo dangantakar wasu jigogin labaran da ke cikin Magana Jari Ce da tatsuniyoyin Hausa. Duk dangantakar da aka kawo,
sai a shiga cikin matanin labarin da kuma tatsuniyar domin a samo misalai a
kafa hujja da su. Daga ƙarshe
sai aka kawo sakamakon bincike, sannan aka kawo jawabin kammalawa. An kawo
muhimman wuraren da aka sami bayanan da aka gina maƙalar da su a matsayin
manazarta.
Manazarta
Bakura, A.
R. (2014). Kishi a Ƙasar Hausa. Kaduna: Garkuwa Media
Publication.
Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, (2006). Ƙamusun Hausa na
Jami’ar Bayero. Zaria: Ahamadu
Bello University Press.
Furniss,
G. (1996). Poetry, Prose and Popular
Culture of Hausa. England: Edinburgh University.
Guga, S.
B. (2010). Yanayin Sarauta a Cikin Magana
Jari Ce I-III. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da
Afirika. Zaria: Jami’ar Ahamadu Bello.
Guga, S.
B. (2015). Gaskiya a Bahaushiyar Al’ada. Ƙalubalen Magana Jari Ce ga Sarakuna. A Cikin Kadaura, Journal of Multi-discipilinary
Studies. Department of Nigerian Languages, Kaduna State University. Kaduna: Winners Printers Limited. P46-58
Gusau,
S.M. (2015). Mazhabobin Ra’i Da Tarke A
Adabi da Al’adu Na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Ltd.
Geza, S.
M. (2004). Matsayin Karin Magana a Cikin Rubutaccen Adabin Hausa. Nazarin
Littafin Magana Jari Ce. Kundin
Digiri na Farko. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Hassan, S.
(2013). Nazari a Kan Mutuntaka da Adabi. Tasirin Abubakar Imam a Magana Jari Ce. Kundin Digiri na Uku.
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afirika. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Ibrahim,
I. S. (1990). Morality in Abubakar Imam’s Magana
Jari Ce. A Paper Presented at Departmental Seminar. Department of Nigerian
and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello University.
Imam, A.
(1939). Magana Jari Ce Littafi na Farko.
Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
Imam, A.
(1940). Magana Jari Ce Littafi na Biyu.
Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
Imam, A.
(1940). Magana Jari Ce Littafi na Uku.
Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
Koko, H.
S. (2009). Jagoran Nazarin Tatsuniya. (Babu
Wurin Ɗab’i).
Malumfashi,
I. (2009). Adabin Abubakar Imam.
Sokoto: Garkuwa Media Serɓices Limited.
Malumfashi, I. Ed. (2019). Labarin Hausa A Rubuce 1927-2018. Zaria: Ahamadu Bello University
Press.
Musa, S.
(1993). Juyar da Labarin Kalala da Kalalatu na Magana Jari Ce na Dr. Abubakar Imam Zuwa Wasan Kwaikwayo. Kundin
Digiri na Farko. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Poul. R.
(1970). African Folklore. New York: University Press.
Propp, Ɓ.
(1928). A Morphology of Folktale.
Lincoln: University of Nebreska.
Pweddon,
N. (1977). Thematic Conflict and Narratiɓe Techniques in Abubakar
Imam’s Ruwan Bagaja. Ph.D Thesis. Department of African Languages. Madison: University of Wisconsin.
Ruth, F.
(1970). Oral Literature in Africa. Ibadan: Oxford University Press.
Sarɓi, S.
(2005). Nazarin Waƙen Hausa. Kano: Samarib
Publishers.
Todorov, T. (1969). The Theories Du Symbole. Translated into
English by Fludernik, M, 2004. England: Routledge.
Thomson,
S. (1977). The Folktale. Lodon: University of Caliponia Press Barkley.
Umar, M.
B. (1982). Dangantakar Adabin Baka da
Al’adun Gargajiya. Kano: Benchmark Publishers.
Usman, B.
(2012). Taskar Tatsuniyoyi. Kano: Gidan
Dabino Publishers.
Usman, B.
(2013). Folklore and History. The Twin Riɓers of World Heritage. Abuja: Klamidas
Communications Limited.
Yahaya, I.
Y. (1988). Hausa a Rubuce: Tarihin
Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
Yahaya, I.Y.
(1971). Tatsuniyoyi da Wasanni na IV.
Ibadan: Oxford University Press.
Yahaya, I.Y. (1992). Darussan
Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan University Press Plc.
Zarruk, R. M. (1986). Sabuwar
Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun. Ibadan: University Press Plc.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.