This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.
Ibrahim
Baba
Department of
Nigerian Languages and Linguistic, Bauchi State University, Gaɗau, Bauchi State, Nigeria
Musa Isah Abubakar
Departmant of Hausa,
School of Languages, Jigawa State College of Education,
Gumel, Jigawa State, Nigeria
Fatima
Umar Sanda
Department of
Linguistics and Foreingn Lanuages, Bayero University Kano, Nigeria
Tsakure
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni daban-daban cikin salo mabambanta. Wannan ya sanya waƙa ta zama sha-kundum, har ake yi mata kallon magani ga dukkanin abin da
ake da cutarsa. A wannan maƙala, an yi ƙoƙarin bibiyar wasu waƙoƙin situdiyo domin a fito da misalan turakun da suke ƙunshe cikin waƙoƙin baka na situdiyo, wanda hakan ya nuna cewa lalle waƙoƙin baka na situdiyo sun zama magani ga kowace irin damuwa a cikin
al’umma. Wannan nazari ya yi ƙwai da ƙyanƙyasa a farfajiyar waƙoƙin na situdiyo, inda aka taɓo turke kaɗai domin fito da A’i daga rogo, sannan aka yi ƙoƙarin bayyana wasu waƙoƙi a kowane ɓangaren da suka shafi
rukunin da aka ajiye su. Yayin gudanar da binciken, an bi hanyoyi da dama da
kuma yin amfani da dabaru, inda aka yi ƙoƙarin nemo waƙoƙin da kuma sauraronsu
sauraronsu, da zaƙulo irin abin da ake buƙata a waƙar, domin ishara zuwa ga gaɓar da ake magana a kai. Wannan bincike, an yi ƙoƙarin ɗora shi a kan Ra’in Mazahabar Nason Adabi a Aladu (Folk-Cultural
Theory) wanda Williams Bossom ya ƙirƙire ta, sannan aka sami mabiya daga ƙasar Amurka waɗanda suka bi ta. Wannan bincike ya ƙarƙare da zayyano sakamakon da aka samu yayin gudanar da shi.
1.0 Gabatarwa
Fito da saƙonni daga waƙoƙin baka
muhimmin abu ne da yake ƙara fito da fasahar makaɗan baka tun a jiya, har zuwa yau da aka sami sauyi cikin waƙoƙin Hausa,
sauyi ta fuskar kayan kiɗa, tsarin rerawa,
masu rerawa da sauransu. Wannan bincike, ya yi ƙoƙarin zaƙulo wasu
turaku daga waƙoƙin baka na situdiyo, inda aka sami warwara daga ƙishirwar da ake
fama da ita daga kowane ɓangare na ilimi da rayuwar al’ummar Hausawa har ma da maƙwabta.
1.1
Ma’anar Waƙar Baka da Waƙar
Situdiyo
Wajen bayyana ma’anar waƙar baka, masana sun yi maganganu da dama,
Sa’id (1981: 235), da Umar (1987: 28) da Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007: 131) da Ɗangambo (2007: 6) amma idan aka bibiyi ma’anonin za a ga kusan bori ɗaya suke wa tsafi. Bisa haka, za mu taƙaita ga ma’anar Gusau (2003: ƊIII) yana ganin
“Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin
hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa, a rere
cikin sautin murya da amsa-amo na kari da kiɗa, sau da yawa kuma a tare da amshi”.
Ita kuwa waƙar situdiyo, ita ce waƙar da ake rerawa a ɗan ƙaramin ɗakin situdiyo wanda ke ɗauke da abin kiɗa na
zamani. Tana iya kasancewa an rubuta ta ko kuma da ka ake rera ta. Mafi yawa wannan waƙar matasa maza da mata ne ke aiwatar da ita, kuma a sanya musu a fefen
sidi (CD) ko a memori.
1.2
Taƙaitaccen Tarihin Waƙar Baka
Masana
sun yi ƙoƙarin
bayyana asalin samuwar waƙar baka a ƙasar
Hausa, daga ciki akwai ra’ayin Gusau (2003: 5-6) inda ya kawo hasashe guda uku
waɗanda yake ganin su ne
asalin waƙar baka, waɗannan hasashe kuwa su ne: Ra’ayi na farko,
suna ganin ana jin ɗan’Adam
ya ƙagi waƙa ne tun
lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta, daga nan ya gano noma sai waƙa
ta ƙara haɓaka. Ra’ayi na biyu kuwa, an nuna cewa, ana
ganin waƙa ta samo asali ne daga wani maroƙi
‘Sasana[1]’
domin haka a wannan ra’ayi ana jin makaɗan Hausa jikokin wannan mutum ne. A ra’ayi na
uku kuwa, ana ganin waƙa ta samo
asali ne daga bautar iskokai.
A
nasa ra’ayin, Satatima (1999: 30) ya bayyana cewa, “Al'ummar ƙasar
Hausa sun sami basirar kiɗa da waƙa
daga tsofaffin daulolin Ghana da Mali da Songhai wanda wasu sassa na ƙasar
Hausa suka kasance ƙarƙashin
mulkinsu kafin ƙarni na sha tara.
Masu wannan ra'ayi har sun kai ga cewa daga waɗannan tsofaffin dauloli Hausawa suka samu
kayan kiɗa irinsu
kakaki wanda aka samu daga Songhai cikin ƙarni na
sha shida. Algaita kuwa an samo ta ne daga Songhai da Mali”.
1.3
Samuwar Waƙoƙin Baka na
Situdiyo
Su kuwa waƙoƙin
baka na zamani su ne waƙoƙin
da aka sami sauyin rerawa aka sami sauyin kayan kiɗa daga waƙoƙin
baka na gargajiya suka sauya zuwa sabuwar hanya ta zamani kamar mandiri da
fiyano da kayan kiɗan disko.
Irin waɗannan waƙoƙi
su ne waɗanda Gusau
(2016) ya ambace su da waƙoƙin
situdiyo[2],
wato a ciki ne ake haihuwarsu tare da sanya musu tufafi. A yanayin rera waɗannan waƙoƙi
da kuma muhallan rerawar akwai bambanci da waƙoƙin
baka na gargajiya. Ire-iren waɗannan waƙoƙi
sun samu ne ta hanyar tasirin da baƙin al’ummu
suka yi wa Hausawa. Gusau (2014: 9) ya ba da ma'anar waƙoƙin
baka na zamani da "Waƙoƙi
ne da suka wanzu a sakamakon iya rubutu da karatu na ajami da na boko da
Hausawa suka yi. sannan bisa yawanci ake shirya su a rubuce, a samar da rauji
da kiɗa, a kuma fitar da
rerawa a sitidiyo. Daga nan ne za a iya sadar da su ta bin ƙaramar
murya daga kwamfuta. Ana ajiye waƙoƙin
baka na zamani kai tsaye ta naɗar su a sidi-sidi
ko a albom-albom.
2.0 Magani a
Falsafar Bahaushe da Tasirinsa
Magani a wurin kowace al’umma abu ne mai matuƙar
muhimmanci, wannan ya sanya da zarar mutum ya gamu da wata cuta ake ta ƙoƙarin nemar
masa magani ba tare da ƙaƙƙautawa ba. Ƙamusun Hausa (2006: 316) ya bayyana magani da
ma’anoni da dama amma ga biyu daga ciki: “Magani na nufin abin da samuwar sa
kan kore wani daban”. Haka kuma ta ce, “Magani na nufin harhaɗa ko yin wasu abubuwa na musamman don shawo kan wani abu, ko samun galaba
a kan wani abu”.
Ko ba mu faɗa ba, mun
san waɗannan ma’anoni za su hau kan waƙoƙin baka na
situdiyo, domin akan yi amfani da waƙoƙi wajen ribatar zuciyar wanda ake so, ko domin neman
ƙuri’u ga ‘yan siyasa, ko domin neman magance wata matsala da ta addabi
al’umma, ko domin wayar da kan jama’a a kan su aiwatar da wani aiki da dai sauransu. Ke nan waƙa ta sami
tasiri irin na magani kamar yadda za a sha da nufin kore wata cuta da ta addabi
gangar jiki, haka ake sauraron waƙa domin kore wata damuwa ko samun wani abu.
2.1 Turke a Waƙoƙin Hausa
Turaku jam’i ne na turke. Gusau (2008: 369-371)
bayan ya kawo ma’anoni biyu, ma’ana ta lugga da ta ƙa’ida, sai ya taƙaita ma’anar
ga fagen nazarin waƙar baka kamar haka: “Na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi.
Idan an ce saƙo kuma ana magana ne kan manufar da ta ratsa waƙa tun daga farkonta
har zuwa ƙarshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa
ba”. Amma a yayin fahimtar saƙon waƙa, akwai muhallin da ake samun turken a dunƙule, wato
cikin ɗa ɗaya ko biyu, inda a
nan aka taƙaita turken, sauran ɗiya ɗin za su iya kasancewa bayani ne ga turken. A taƙaice dai,
kowace waƙa tana ɗauke da irin turkenta imma dai an taɓa yin waƙa kan wannan turken ko kuma ba a taɓa yi ba.
2.2 Ra’in Bincike
Ra’in Mazahabar Nason Adabi a Aladu (Folk-Cultural Theory) wadda cikin
William Bascom (1912 – 1981) ya qirqire ta, shi ne Ra’in da ya cancanci karɓar wannan nazari. Wannan Mazahaba tana kallon yadda hikima da sauran
dabarun fasahar baka suka danganci abubuwan da al’umma suke gudanarwa. Har wa
yau, Mazahabar ta faɗaɗa zuwa ga abubuwan
da suka danganci fasahar zamani ta amfani da na’urorin kwamfuyuta wajen alaƙanta
maganganun adabi da al’adu. Ana amfani da wannan ra’i wajen nazarin al’adu na
Hip-Hop da rawar disco da rawa ta masu nuna tsiraici da al’adun da ake amfani
da su wajen shirya finafinai a Amurka.
Wannan Mazahaba ta sami mabiya waɗanda suka haɗa da: Robert Gorges, da Micheal Owen Jones, da
Daniel Crowley, da Alan Dundes, da Kenneth, da Propp L.V, da Blank Trever J. da Robebstcin James, da Kaplan Merrill da sauransu (Gusau, 2015: 49
– 50).
2.2
Hanyoyin Gudanar da Bincike
Yayin gudanar da wannan bincike, an bi hanyoyi da dama domin sauqaqa
aikin da kuma samun bayanan da za su gida wannan bincike domin ya zama
ingantacce. Daga cikin hanyoyin da aka bi akwai nemo waqoqin situdiyo inda aka
same su ta hanyar sauqewa a Youtube da samun wasu daga wurin makaxan kai tsaye,
da kuma wuraren masu turawa a wayoyi.
Bayan wannan, an yi amfani da wayar salula wajen sauraron waqoqin, sannan
aka bibiyi saqonnin da suke cikin su domin samun abin da ake nema.
Har wa yau, an bibiyi wasu ayyukan masana waxanda suka danganci wannan
nazari, inda su suka taimaka wajen ciro wasu muhimman abubuwa.
3.0
Wasu Turaku Daga Waƙoƙin Baka na Situdiyo
A wannan ɓangare, za a
zaƙulo muhallan da aka taƙaita turaku ne a cikin wasu waƙoƙin Hausa na
situdiyo, inda za a kawo misali guda ɗaya daga
kowace waƙa domin nuna yadda waƙoƙin suka zama sha-kundum a kowanne ɓangare.
3.1
Waƙa a Matsayin Hanyar Bayyana Soyayya
Makaɗa da dama sukan yi amfani da salon waƙoƙin
soyayya; wanda hakan kan sanya mabiya su so su. A gefe guda kuwa, da yawa masoyi kan
bayyana soyayyarsa ga wadda yake so a cikin waƙa,
ta hakan ne yakan yi ƙoƙarin
ribatar zuciyarta,
ko kuma ya janyo hankali kan su so wani abu, ko a kwantar musu da hankali a fagen soyayya
da waƙoƙi.
Idan muka kalli waɗannan
ɗiya daga na 4 zuwa
na 6 kallo na garai daga cikin waƙar
“Jarumar Mata” ta Makaɗi Hamisu Breaker, za mu ga lalle hakan na iya faruwa.
Jagora:
Tilas ganin mu tilas barinmu,
: Ƙaunarki
tun da nai nisa,
: Sam ba batun na fasa ko za a
ce mun in ba da rai fansa.
Jagora:
Tsarin zubin ki daidai ne,
: Ya kama zuciyata ne,
: Ina ji kamar mafarki ne,
: Ina son ki so mataki ne.
Jagora:
Ni ban da damuwa in har zan buɗe
‘yan idanuna,
: In kalle ki ga ki dab da ni,
: To me za ya dami ƙalbina.
(Breaker,
Waƙar Jarumar Mata).
A nan,
za a ga yadda makaɗin yake
bayyana tsananin ƙaunarsa ga wadda yake so, to duk
wadda kuma aka yi wa waɗannan ɗiya a matsayin masoyiya, babu shakka zuciyarta za ta yi
sanyi, sannan ta sami gamsuwa da nutsuwa cikakkiya kan wanda yake sonta la’akari da
yadda ɗiyan suka zo da tsananin nuna shauƙi da bege ga abin da ake so.
Makaɗi Yakubu Mohammed ya bayyana
irin wannan turken soyayya tsantsa a cikin waƙar fim ɗin Larura (2003), inda jarumin ke
rera waƙar soyayya ga budurwarsa ta hanyar bayyana
tsantsar son sa gare ta. Ga abin da ya bayyana a wannan ɗa:
Jagora: Abar yabo na a ruhina,
: Farin ciki ke kike guna,
: Batunki kullum yake ci na,
: Al’amarina yau da gobe, ke nai
zaɓe, ke nai zaɓe.
Jagora: A yau fa ni dai na tantance,
: Ƙaunarki ni kar ki ban rance,
: Ki mallaka min in sangarce,
: In kika bar ni zan susuce, zan
kwarkwance, zan susuce.
Jagora: Zaman fahimta muke sosai,
: Hakan ya sa har na ce ni sai,
: Na ɗan yi bege na so sosai,
: Na yi bayani ki ji sosai amshi
batun amshi batuna (ɗa 2-4).
A waɗannan ɗiya, an ga yadda makaɗin ya bayyana tsantsar
soyayyarsa ga wadda yake so; ta yadda rashin ta zai iya kai wa ga ya haukace.
Ba ya ga
soyayyar da ke gudana tsakanin mace da namiji wadda waƙa ke zama silar bayyanawa, ko ƙara ƙarfafawa. Haka zalika waƙa kan nuna tsananin son da wani ke yi
wa wani a fagen ubangida ko shugaba. A nan, zan buga misali da yadda makaɗan addini ke amfani da waƙa wajen nuna tsantsar soyayyarsu ga
Annabi S.A.W ko wani malami. Ga misalign bayyana tsantsar soyayya ga Annabi
S.A.W daga waƙar ‘Habibi Sayyadil Wara’ ta
Kabiru Yahaya (Classic):
Jagora: Sirrin ƙaunar Ma’aiki a yau sai ci gaba na ta
samu na,
: Da ma da yawa daina suna ta
aza ni a kan biɗar
sunna,
: Son Annabi son iyalansa girmama makusantansa ja izna,
: Waƙa in ba ta Manzo ba ce ni kam ban sanya
bakina.
A wannan ɗa, Makaɗin ya
bayyana tsantsar soyayyarsa ga wanda yake so, ta yadda muddin ba waƙarsa ba ce,
to fa shi ba shi da lokacin da zai yi. Wannan kam ya kai maƙura wajen ƙauna.
3.2 Waƙa a Matsayin Hanyar Mayar da Martani
Waƙa hanya ce ta mayar da martani ga wanda ya ƙalubalanci wani ko
wasu, wannan abu kuwa ba ɓoyayyen abu ba ne a
tarihin waƙoƙin Hausa. Makaɗan baka tun na gargajiya sun shahara da wannan salon
a mayar da martani. Idan muka dawo ga waƙoƙin situdiyo,
akwai misalai da dama daga wurin makaɗan situdiyo.
Ga misali daga waƙar ‘Almajiri’ ta Haruna Aliyu Ningi.
Jagora: Ni Almajiri ne,
: Kai ma Almajiri ne,
: Ku ma almajirai ne,
: Ai waƙar almajiri ce,
: Gwamnoni kun ji kunya,
: Kuna sukar almajiranci,
: Amma kuma ga jiharku,
: Ana buga harkar karuwanci. (ɗa na 1).
A nan, Makaɗi Haruna Ningi yana mayar da martini ga gwamnonin
jihohin arewa a game da kyarar almajiranci.
Makaɗa Ali Jita ma, ya yi wani martani kan waɗanda suke kiransu da ‘yan nanaye. Ga abin da ya ce, bayan ya jero sunayen
wasu makaɗan situdiyo:
Jagora: Ga zancen mai waƙa,
:
Ga lafazin mai waƙa,
:
Na faɗa na ƙara,
:
Wanda ya so ka ka so shi,
:
Wanda ya ƙi ka ka ƙyale shi,
:
Hassada babban ciwo,
:
A zuciyar mai ƙulla ta,
:
Na gaba tuni ya yi gaba,
:
Haka Allah ya hukunta,
:
Ga zuma rumbun daɗi,
:
Maɗaciya ba mu kula ta
:
Tsuntsu daga Allah ne,
:
Ɗaukakar sa a duba ne,
:
Jirgin sama ya yi sama,
:
Hanya an nuna ta,
:
Kun ji azancin mai waƙa,
:
Da farin zare za mui saƙa.
Jagora: Dukkanmu kun ga mawaƙa ne,
:
Kowa yana da masoyansa,
:
Wasu burinsu su ɓace mu,
:
Wai mu ‘yan nanaye ne,
:
In mu ‘yan nanaye ne,
:
To kai ɗin ɗan wane ne?
Jagora: Hassada babbar cuta,
: Annabi ma ya yi haninta,
: Kowa na harkarsa,
: Tamu wasu na damunta.
A wannan ɗiya, za a ga yadda Makaɗin yake mayar da martani ga wasu da suke ƙyamatarsu wanda
yake ganin hakan hassada ce tsantsa. A nan, ya yi ƙoƙarin yi musu
martani tare da bayyana su a matsayin mahassada. Akwai waƙoƙi masu yawa
waɗanda ke ɗauke da irin wannan turke.
3.3 Waƙa a Matsayin Hanyar Nishaɗantarwa
Gusau[3] (2021), ya bayyana cewa ba lalle waƙa ta zama nishaɗi ga kowa ba, wani takan zama nishaɗi, yayin da wani take zame masa akasin haka, inda ya buga misali da waƙar “Jarumar
Mata” ta Hamisu Breaker.
Bisa wannan bayani, kusan dukkanin waƙoƙi tushensu
nishaɗantarwa ne, sai dai a yayin da take zama nishaɗi ga wani, wani kuma duk daɗinta da ma’anarta
ba za ta zama nishaɗi gare shi ba, musamman ga wanda ke mata kallon
haramci a addinance.
Baya ga gama-garin waƙoƙi da ake yi musamman na soyayya waɗanda su ne ke nishaɗantar da masoya.
Akwai waƙoƙi da dama da ake yi domin nishaɗantar da
al’umma, ire-iren waɗannan waƙoƙi su ne waƙoƙin da ake samu daga makaɗan ban-dariya irin su Sani Liya-liya, da Kamal Aboki, da Adamu Nadanko da
sauransu.
A taƙaice dai, waƙoƙin nishaɗantarwa sun danganta ga mai sauraro, domin kowa akwai
irin waƙar da take sanya shi nishaɗi. Ga misalign wani
ɗa a waƙar ‘Matar Sarki’ ta Makaɗi Sani Liya-liya.
‘Y/amshi: Liya-liya kai ne ka zagi matar Sarki?
Jagora: Lalalala ba ni na zagi matar Sarki.
Jagora: Ni ca na ce mata wannan ciki uban tulaƙi,
: Kamar ƙabilun nan masu sai da garin kwaki,
: Da a Yankari ne ta yi kyau da matar Gwanki,
: Amma ban ce mata ƙugunta yai zubin kura ba.
A wannan ɗa, Makaɗi ya kawo
muhallin turkensa, inda asali matar Sarki ta yi ƙarar Liya-liya ga mijinta
kan zaginta da ya yi, ga shi kuma a gaban Sarki ya maimaita. Don haka ire-iren
waɗannan waƙoƙi ne na ban-dariya, duk da kasancewar suna ɗauke da wasu saƙwanni.
3.4 Waƙa a Matsayin Hanyar Wayar da Kai
Daga cikin manufofin waƙoƙi akwai wayar da kan jama’a, wannan ta sanya hukumomi
ko gwamnati kan yi amfani da makaɗan situdiyo yayin
da suke son isar da wani saƙo ga jama’a. Ga misalin wani ɗa nan game da wayar da kan al’umma a kan cutar Korona daga cikin waƙar ‘Korona’
ta Zainab A. Baba.
Jagora: Ga kira ga mutane bai-ɗaya,
:
Korona Bairos cutar da ta addabi duniya,
:
Mu kiyaye tsafta lafiya ce jarin rayuwa.
A wannan ɗiya, zabiyar
tana ƙoƙarin wayar
da kan al’umma kan taka-tsantsan da wata cuta mai suna Korona wadda ta addabi
al’umma, sannan sai take kiran su da su riƙi yin tsafta
domin ita ce babbar hanyar magani daga wannan cuta.
3.5 Waƙar Situdiyo a Matsayin Hanyar Faɗakarwa
Faɗakarwa na daga cikin abubuwan da ake nazarta a cikin
waƙoƙin situdiyo, sannan su kansu makaɗan sun shahara wajen aiwatar da waƙoƙin faɗakarwa. Ga wasu misalai nan daga wasu waƙoƙi:
Jagora: Duniya ba madauwamar ɗorewa ba,
: Ba bigire na miƙe sawaye ne ba,
: Mai barci ka wattsake tun ba ta zo ba,
: Mai raba gardama da yayyanke ƙauna.
(Waƙar Ɗamarar ko ta kwana, ɗa na 8, ta Makaɗi Alan Waƙa).
A wannan ɗiya, an ga yadda Makaɗin ya yi faɗakarwa kan mutuwa, inda yake nuni da cewa duniya fa
ba gidan zama ba ne, za ta zo kowane irin lokaci ta yi gaba da mutum.
Jagora: Ya ‘yan’uwa ku tashi mu mata mu kama sana’a,
: Rayuwa in babu sana’a an yi zama na kare a Karofi,
: Rashin sana’a ni na hanga shi ne ke sa aikata laifi,
: ‘Yar’uwa in ba ki sana’a za ki ɓige da aro na mayafi,
: Haka komai in ya tashi dangi kan ki sa riƙa haufi,
: In ko kina sana’a ba ki aro sai dai ranta.
(Waƙar Mata mu kama sana’a ta Makaɗiya Murja
Baba).
A wannan ɗiya, Makaɗiyar ta yi
wa mata faɗakarwa ne a kan su tashi su kama sana’a, inda har
take ƙoƙarin nuna cewa idan fa mutum ya zama ba shi da wata sana’a to zai kasance
cikin ayyukan laifuka, da roƙo.
Haka zalika, Makaɗi Yakubu Muhammad cikin wata waƙarsa yana
cewa:
Jagora: Wasanni na kwamfuta,
: Mu lura yana
illa,
: Yakan sa a bar
sallah,
: Hakan ko ta zam
illa.
(Waƙar fim ɗin Hawaye 2006, ɗa na biyu).
A nan, an ga yadda Makaɗin ya bi salon faɗakarwa ga al’ummar musulmi kan wani muhimmin al’amari da ya shafe su,
wato ibada, inda ya bayyana shagaltuwa ga wasan kwamfuta zai sanya mutum ya bar
sallah ta wuce shi.
Ga wani turke cikin waƙoƙin faɗakarwa daga cikin
waƙar Aminu Ladan Abubakar:
Jagora: Auwalu Garba Ɗanbarno,
: Ka bi a hankali yanzu,
: Sha’anin mutum yanzu ba sha’anin amana ba.
Jagora: Yau in ana biɗar ranka,
: Da naka za a ɗau ranka,
: Shaƙiƙi ko amininka,
: Da ina amana ba. (ɗa na 1 da na 3).
A waɗannan ɗiya da suka gabata,
Makaɗin ya yi ƙoƙarin faɗakar da wanda ya yi wa waƙa game da
taka-tsantsan ga mutane, ta yadda kada ya bayar da yarda ɗari bisa ɗari ga kowa, domin za a iya haɗa baki da wanda aka bai wa yarda a cutar da wanda ya bayar da yarda.
Makaɗi Yakubu Muhammad ma, a cikin fim ɗin Khushu’i (2005), na kamfanin Kajol Production, ya sake faɗakarwa a inda ya ce:
Jagora: Allah ya yi ƙira mu iyo taƙawa,
‘Y/amshi: Ka tambalili,
Jagora: Ƙima ta ka gani har kai sha’awa,
‘Y/amshi: Ka tambalili,
Jagora: Kifi ba shi adawa shi da ruwa,
‘Y/amshi: Ka tambalili,
Jagora: Ka ji zance na tamgalili riƙi zance na tambalili,
‘Y/amshi: Tangalili ayyara iye ka tambalili,
: Sanga dalili ayyara iye ka tambalili.
Idan aka lura da wannan ɗa, za a ga Makaɗin ya yi faɗakarwa kan jin tsoron Allah kamar yadda Allah ɗin Ya yi kira ga muminai a kan jin tsoronSa a wurare da dama cikin Alƙur’ani.
Haka zalika a yayin faɗakarwa, akan duba
wasu matsaloli na al’umma domin a yi musu hannunka-mai-sanda ko nuni cikin
ishara kan wata matsala da ta addabe su, sannan a iya kawo musu mafita ma daga
wannan matsala. Makaɗan Hausa na situdiyo sun shahara da bin wannan
hanya. Ga misali daga Zabiya Lawisa cikin waƙarta ta Mace-macen
aure:
Jagora: Da farko
sallamata gare; ku ya jama’a ku amsa mini,
: Ku saurara
ku ban hankalin; kun gunku nake biɗar izzini,
: Jawabi zan
yi amma a kan; batun auren cikin zamani,
: Domin faɗakar da ku har da ni,
: Mu gyara
halinmu mui tunani,
: Ku bar ruɗin cikin zamani; hakan shi ne kaɗai magani.
‘Y/amshi: A yau dai
zan yi ɗan tsokaci; a kan auren cikin
zamani,
: Sakin aure
a yau yai yawa; ina mafita ina magani?
A nan, Zabiyar ta yi ƙoƙarin fito da abin da take son yin magana a kai, wato
tana son ta yi faɗakarwa ne kan yawaitar mace-macen aure. A wannan
matashiya ta nuna haka, yayin da a cikin waƙar ta zo da bayanan
da suke nuna su ne dalilan mace-macen aure a wannan zamani a matsayin faɗakarwa.
3.6 Waƙa a Matsayin Hanyar Bayyana Tarihi
Tarihi ɗaya ne abin da makaɗa ke ambata a cikin waƙoƙinsu na baka, shi ya sa idan aka duba waƙoƙin baka na
gargajiya cike suke da ambaton tarihin al’ummomi ko daulolin da suka shuɗe, musamman makaɗan da suke yi wa
sarakuna waƙa. Sukan yi wannan ƙoƙarin ambaton waɗannan tarihin ne domin alaƙanta shi da daular sarkin da suke yi wa kiɗa da waƙa.
Makaɗan baka na situdiyo, su ma ba a bar su a baya wajen
ambato tarihin dauloli ko wasu sarakuna ko mashahuran mutanen da suka shuɗe ba. Ga wani misali daga waƙar Alfanda ta Makaɗi Aminu Alan Waƙa inda ya tabbatar da waƙa matattarar tarihi
ce.
Jagora: Za ni in waiga talifi,
: Kan Ahmadu Sardauna,
: Gamji maza abin koyi,
: Amadu Bello Sarduna,
: Yarda akai wa Sardauna,
: Yarda ya manna bankwana,
: In na tuna a
koyaushe,
: Sai ya saka nake kuka.
‘Y/amshi: Gamji maza abin koyi,
: Amadu Bello Sardauna,
: In na tuno
wafatinsa,
: Sai ya saka ni in kuka.
Jagora: Nai nazari a hankalce,
: Gun magabata ‘yan
baya,
: Nai nazari da
bincikke,
: Littattafan tulin
ƙarya,
: Na biɗi son tulin hujja,
: Ta kashe ‘yan mazan
baya,
: Na kula dai nifaƙa ce,
: Sai fa ƙabilancin hauka.
A waɗannan ɗiya da suka gabata, an ga yadda Makaɗin ya bayyana tarihin wani abu da ya faru a wani lokaci. Wannan ya sanya
waƙar sai ta tuno baya, ta bayyana tarihin wanzuwar rayuwar wani da kuma
yadda aka hallaka shi.
Akwai waƙoƙi da dama masu wannan turke, daga ciki akwai: Waƙar “Ku zo mu je mu
gai da gida” ta Mr. Affan, Waƙar “Mashigan Kano” ta Makaɗi Aminu Alan Waƙa, Waƙar “Alfanda” ta Makaɗi Aminu Alan Waƙa, Waƙar “Buwayar Harshen Hausa” ta Sarfilu Umar Zarewa da
sauransu.
3.7 Waƙa a Matsayin Hanyar Bayyana Mutum
Waƙa kan zama sababin da za ta sa a san mutum, shin mutumin da aka yi wa waƙar ne ko
kuma shi kansa makaɗin ne. Wannan abu kuwa ba baƙo ba ne ga dukkanin
masu sauraron waƙoƙi ko kuma masu nazari.
Game da waɗanda waƙa ke fito da su daga cikin makaɗan, a kalli yadda a yau makaɗan suka zama
ababen kallo da sowa a sakamakon jin waƙoƙinsu, wannan
ya sanya ke nan an san su, kuma waƙa ta fito da su. Makaɗi Aminuddeen Alan Waƙa ya bayyana shuhurarsa a waƙa, wadda ita ce
silar sanayyarsa a cikin waƙarsa ta Shahara. Ga abin da ya ce:
Jagora: Zan matsa kan maudu’in,
: Da ya jaddada in bayana,
: Kan shuhura masu bi na,
: Da na ce tsanin sanina.
: Shahara sanadin sani na,
: Sanadi na sani fununa.
: Shuhura sanadin ƙwarewa,
: Sababin na fahimci kaina.
A wannan ɗiya, an ga yadda Makaɗin ya shaida cewa dalilin sanayyarsa da shahararsa, ita ce waƙa.
Alhaji Kabiru Yahaya (Classic), shi ya ya bayyana haka a cikin waƙarsa mai
sunan “Habibi Sayyadil Wara’. Ga abin da ya ce:
Jagora: Shukuran lil Laahi na goda Allah ban faharin faɗin kaina,
: Ba yunwa ba ƙishirwa da tsumma ba mai cin mutuncina,
: Allah kai arziki gun mawaƙa sha’irai masoyana,
: Waƙa Allah ya ce in yi to kuma na yi ta yi min rana. (ɗa na 7).
A wannan ɗa, an ga yadda Makaɗin ya bayyana cewa waƙa ita ce ta fito da shi aka san shi, sannan ita ce
sanadin dukkanin wani arzikinsa da ɗaukakarsa.
Ta fuskar waɗanda ake yi wa waƙar kuwa, idan a
kalli yadda waƙar da aka yi wa wani, za a ga idan a baya ba a san shi ba, ko ba a san ƙwarewarsa
ba, to yayin da aka saurari wata waƙa wadda wani makaɗi ya masa, wannan zai sanya sunansa ya shiga bakunan mutane, masu sauraro
da masu nazari su san shi. Misali mafi kusa, a duba yadda waƙoƙin
faya-fayen “Farfeshiya” na Aminu Alan Waƙa, wanda a ciki ya ƙara fito da
ilimin farfesoshin Hausa kafataninsu. Idan aka koma ga sarakuna ma, za a iske
makaɗa sun fito da su sakamakon waƙoƙinsu. Haka ‘yan siyasa, sau da dama waƙa kan fito
da ɗan takara a san shi, kuma a so shi a dalilin waƙar da wani makaɗi ya masa. Ga misalan wasu waƙoƙi da suke zama sababin fito da mutum: Waƙar “Abba
gida-gida”, Waƙoƙin fim ɗin “Sarmadan”, na Sadi Sidi Sharifai, Waƙoƙin finafinan
“Mujadala” da “Furuci” da “Gidauniya” da “Jarumai” da “Jarida” da “So” da
“Tawakkali” na Yakubu Mohammad, Waƙar “Jega munafukin zaɓe”, Waƙoƙin fim ɗin “Guɗa” na Abubakar
Sani, Waƙoƙin finafinan “Ƙauna” da “Rana” da “Nagari” na Mudassir Ƙasim, Waƙoƙin fim ɗin “Madubi” na Sani Musa Danja da sauransu.
Mafi yawa ‘yan finafinan Hausa da makaɗansu sun fi
faɗawa wannan kaso, domin daga cikin abin da yake fito da fim fili, ya yi
tashe da suna, akwai waƙa.
3.8 Waƙa a Matsayin Hanyar Tallata Haja
Kamfanunuwa
da dama da ‘yan kasuwa manya da ƙanana kan
yi amfani da waƙoƙin
situdiyo wajen tallata hajojinsu; ta yadda za su sami masaya da dama. Wannan
al’amari ba ɓoyayyen
abu ba ne a wannan zamani, domin kusan dukkanin nau’o’in kasuwanci sukan nemi a
yi musu waƙoƙin da za a
waƙe kamfani ko kuma wannan sana’ar tasu.
Misalai a kan wannan akwai: Waƙar
“Alhikima Maganin Musulunci” da sauransu.
3.9 Waƙa a Matsayin Magani
Magani
shi ne dukkanin abin da za a sanya a jiki, ko wani abu da za a karanta, ko a
sha, ko a fesa domin waraka daga wata cuta da ta kama ɗan’adam. Amma ga waƙa, maganin
kan ɗauki ma’anar wasu ɗiya da za a saurara domin samu waraka
ta zuciya ga wanda ya kamu da son jin wata waƙa ko kuma
ya shiga wata damuwar da nishaɗin waƙa
ce kaɗai zai samar masa da
waraka da hucin zuci. Tun lokacin da aka fara shirya finafinai na Hausa, ake
kuma tsarma waƙoƙi a ciki,
an sami ire-iren waɗannan
misalai da dama.
Aminuddeen
Ladan Abubakar, ya bayyana haka cikin waƙarsa ta
‘Shahara’, inda ya kawo misalan wasu mata da waƙoƙinsa
ne kaɗai ke raba
su daga cutar da take damunsu. Mai wani ɗa da hakan ya zo a waƙar
‘Shahara’ ta Makaɗi Aminu
Alan Waƙa.
Har wa yau, a wani ɗa ya kawo
yadda waƙoƙinsa suka
zama sababin zamantakewar aure. Ga abin da ya ce:
Jagora: Ko da tan nutsu ko ta huta,
:
Sai ta hau yi mana bayana.
:
‘Yar ɗiyata ce na wanke,
:
Sanadin aure na sunna.
:
Mun yi mun yi ta zauna,
: Sai ta ce sharaɗin ta zauna.
: Sai an kai matta
kaset,
: Wanda nai Ummi
Momina.
A nan, mun ga yadda wannan mata ta bayyana ɗiyarta ta kasa zaman aure sakamakon rashin
samun waƙar Alan Waƙa, wannan
kuwa cuta ce babba.
A wata ɗiya, Makaɗin ya bayyana yadda wata jikar Sarki
ta kamu da sonsa, waraka daga wannan cutar shi ne sauraron murya ko waƙar
Alan Waƙa. Ga abin da ya ce:
Jagora: Sai labarin Sa’ade,
:
Shekarunta bakwai na rana.
:
Wata Jikanya ta Sarki,
:
Wayonta wuce sanina.
:
In ana so tai karatu,
:
Sai a sai mata faifayena.
:
Waƙa
ta hardace su,
:
Bitar su dare da rana.
Da waɗannan ɗiyoyi za mu fahimci waƙa
magani ce wadda ke kawo waraka daga cutar da ta addabi mutum.
4.0 Sakamakon
Bincike
Babban
abin lura a wannan nazari, shi ne yadda aka buɗe ƙirji da faɗaɗa tunani wajen zaƙulo turaku
mabambanta daga cikin waƙoƙin
baka na situdiyo daban-daban domin nuna yadda waƙoƙin
suka zama tamkar ruwan dare game
duniya. Baya ga wannan, an fahimci yadda makaɗan baka na situdiyo ba su taƙaita
wajen yin waƙa kan turken soyayya kaɗai ba kamar yadda ake zargi, a’a sun
yi ƙoƙarin baza
tunaninsu wajen lalubo matsaloli daban-daban na al’umma da kuma yin waƙa
a kai. Har wa yau, binciken ya fito da fasahar makaɗan da kuma kyakkyawan tunaninsu da baiwarsu
ta yadda suke ɗauko
abubuwan da suka shafi al’umma su yi a waƙe, ko su
mayar da martani ko kuma su isar da saƙo ga
al’umma a cikin waƙoƙinsu.
Binciken dai, ya gano yadda irin rawar da makaɗan baka na situdiyo suke takawa wajen yaɗa manufofi kyawawa a c ikin a cikin
al’umma cikin fasaha da raha.
4.1 Kammalawa
Bahaushe
ya ce, “Kowa ya ci zomo; ya ci gudu”. Ba makawa haka wannan al’amari yake,
domin kamar yadda kafin cin zomo aka yi
gudu; haka a gudanar da wannan binciken aka sha wahala, amma dai ƙarshen
tika-tika-tik, domin an kammala shi
bisa yadda aka tsaro. A binciken, an yi gabatarwa sannan aka zo da ma’anar waƙa
da waƙar situdiyo da kuma tarihin samuwarsu a ƙasar
Hausa. Baya ga wannan, an yi bayanin magani da tasirinsa da kuma bayanin turke,
da ra’in bincike. Nazarin, ya yi ƙoƙarin
fito da wasu turaku mabambanta har guda goma da ake samu a cikin waƙoƙin
baka na situdiyo. Binciken ya fito da su da ɗan taƙaitaccen
bayani a kai, sannan aka bayyana sakamakon binciken.
Manazarta
1. C.N.H.N.
(2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: ABU
Press.
2.
Ɗangambo, A. (2007) Xaurayar Gadon Fexe Waqa (Sabon Tsari) Zaria: Amana
Publishers Limited.
3.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers.
4. Gusau,
S.M. (2014). Makaxan Hausa Jiya da Yau. In Garkuwan
Adabin Hausa: A Festschrift in Tribute to Abdulqadir
Xangambo.
Zaria: A.B.U Press.
5. Gusau,
S.M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarke a
Adabin da Al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.
6. Gusau, S.M.
(2016a). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa (1 – 2).
Kano: Century Research and Publishing.
7. Gusau, S.M.
(2016b). Ƙamusun
Kayan Kiɗan Hausa. Kano: Century
Research and Publishing Limited.
8. Junaidu,
I. da ‘Yar’aduwa, T.M. (2007) Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandare.
Ibadan: Nazareth Press Limited.
9. Sa’id, B.
(1981). ‘Bambancin Waqar Baka da Rubutacciya’ in Yahaya, I.Y.; Rufa’i, A. &
Abu-Manga, A. (ed) Studies in Hausa
Language, Literature and Culture: The Second Hausa International Conference. Kano: Centre for
the Study of Nigerian Languages, Bayero University.
10. Satatima, I.G. (1999). Tarsashin Adabin Baka a Cikin Rubutattun Waqoqin Hausa. Kundin digiri na biyu. Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeirya, Jami’ar Bayero.
11. Umar, M.B. (1987). Dangantakar adabin baka da al’adun gargajiya. Kano:
Triumph Publishing Company Limited.
[1]Tarihi bai bayyana
takamaiman garin da Sasana ya fito ba, sai dai ana da'awar cewa ya fito daga
nahiyar Asiya ne. Masu wannan da'awa
suna ambata Sasana shi ne makaɗi wanda
ya fara kiɗa da waƙa
a duniya" (Gusau (2008: III).
[2]Wani ɗan ƙaramin ɗaki
ne mai ɗauke da
kayan kiɗa na
zamani; musamman Fiyano, da jita da sauransu.
[3] a wata
ziyara da muka kai masa a yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu, a gidansa da
ke Rijiyar Zaki, kan kwanar Masallacin Imamul Bukhari.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.