This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.
A’ishatu Isma’il Adamu
Hausa Department, Sa'adatu Rimi College of Education Kumbotso, Kano, Nigeria
aishaismailadamu@gmail.com
Tsakure
Marubuta
waƙoƙin siyasa
na Hausa kan yi amfani da basirar da Allah ya yi musu wajen yin amfani da
sarrafa harshe cikin hikima domin su jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa. Aminu
Ibrahim Ɗandago shi ma na ɗaya daga
cikin irin waɗannann
marubuta da Allah ya horewa wannan. A wannan nazari an kalli yadda marubucin ya
yi amfani da dabarar sarrafa harshe a waƙar Ba Na Shakka ta ANPP. An ɗora wannan
nazari bisa Mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo
(2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.
Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun hada da tattaunawa
da marubucin an kuma samo matanin waƙar daga
hannun marubucin kai tsaye a kuma rubace. A binciken kuma an gano marubucin ya
yi mafani da dabarar sarrafa harshe ta hanyar aron kalmomin Ingilishi da
Larabci da Fulatanci da kalmomin Hausa masu sabuwar ma’ana karin harshen
Kananci da ƙari a cikin kalma da kuma maganganun hikima
irinsu: karin Magana da habaici da kuma zambo. Gudunmawa da binciken ya bayar ita
ce, ƙara bada haske ga manazarta da ɗalibai ta
yadda za su nazarci sarrafa harshe a rubutacciyar waƙa,
musamman a ɓangaren waƙoƙin
siyasa ta fannin adabin Hausa.
1.0 GABATARWA
Sarrafa
harshe dabara ce da marubuta da makaɗa waƙoƙin
Hausa kan yi amfani da su a cikin waƙa domin su
isar da saƙonsu cikin armashi ga jama’a. Marubutan sukan
yi amfani da wannan dabara ta hanyar sarrafa kalmomi da jimloli a harshe cikin hikima
a waƙa. A wannan nazari, an kawo yadda marubuci
Aminu Ibrahim Ɗandago ya yi amfani da wannan dabara ta
sarrafa harshe a waƙar jam’iyar ANPP
Ba Na Shakka. Ya
yi amfani da su irin su ararrun kalmomin Ingilishi da
Larabci da Fulatanci da kalmomin Hausa masu sabuwar ma’ana da karin harshe da
maganganun hikima irinsu, karin magana da habaici da kuma zambo. An
fito da misalansu tare da yin sharhi a kansu.
Aminu
Ibrahim Ɗandago shi ne mawallafin waƙar
Ba Na Shakka ta jam’iyyar ANPP, an haife shi a unguwar Marmara da ke ƙaramar Hukumar Birni da
Kewaye ta Jihar Kano a shekarar 1964. Ya fara karatun allo a gida daga bisani
ya shiga makarantar firamare ta Gwale daga shekarar 1972-1978, sannan ya wuce
zuwa ƙaramar makarantar sakandire ta maza da ke garin Ringim a shekarar
1979-1981, daga nan kuma ya dawo babbar sakandire ta Gwammaja II inda ya
kammala a shekarar 1984. Bayan nan kuma ya sami damar ci gaba da katatu a
Kwalejin Ilimin Horon Malamai ta (A.T.C.) Gumel daga shekarar 1986-1989, inda
ya sami shaidar takardar karatun malanta mai daraja ta ɗaya (NCE) a ɓangaren (P.H.E.) wato ilimin wasannin motsa jiki na kula da lafiya. Ya yi
koyarwa a wurare daban-daban, daga cikinsu akwai makarantar firamare ta Sheikh
Abdulwahab, ya kuma koyar a makarantar sakandire ta maza ta Gwarzo da sauransu.Tun yana ƙarami, mutum ne mai sha’awar yin waƙe-waƙe. Yakan rubuta waƙoƙi ga duk abin da yake so, musamman a kan waƙoƙin yabon Annabi da kuma siyasa.
Wannan shi ya haifar da ƙwarewarsa ta samun ci gaba da wallafe-wallafen waƙoƙi a wasu ɓangarori daban-daban, misali ya yi waƙoƙi a kan aure da sarauta da siyasa da
yabon Annabi (S.A.W.) da sauaransu. Adamu, (2012: 56)
Waƙar Ba Na Shakka ta Jam’iyyar ANPP,
an yi ta a shekarar 1999 lokacin da ake ƙoƙarin kafa mulkin dimukaraɗiyya a jamhuriya ta hudu. Mawallafin ya gina ta ne a kan manufa ta ra’ayin
jam’iyya da kuma yin tallan; ɗan takararta mai neman gwamnan Jihar Kano wato Magaji Abdullahi. Mawaƙin yana so ya isar da saƙonsa ga jama’a na
bayyana musu manufofin jam’iyyar da irin ayyukan da za ta yi da kuma irin ci
gaban da za a samu a ƙasa, domin kowa ya zaɓe ta. Haka kuma mawallafin yana so ya bayyana saƙonsa ga abokiyar hamayyar tasu,
jam’iyyar PDP da kuma wasu da suka zame musu bara-gurbi a cikin jam’iyyarsu ta
ANPP.
2.0 Sarrafa
Harshe
Masana da masu bincike sun bayyana ma’anar sarrafa harshe
da cewa; Ɗangambo, (2007: 54) ya bayyana ma'anar sarrafa harshe da cewa; sarrafa
harshe hanya ce ta amfani da harshe a cikin waƙa (nahawu) duk da cewa ba za a iya
raba shi da salo ba, domin kuwa wani lokacin a sarƙe suke. Wannan hanya ta ƙunshi yadda marubuci
yake zaɓar kalmomi da tsarin jimloli da kuma
irin yadda yake amfani da su wajen isar da saƙonsa ga jama'a.
A nan, abubuwan da mai nazari zai duba a wannan sashe sun
haɗa da baƙin kalmomi da tsofaffin kalmomi da
karin harshe da karin magana da maganar hikima da ƙari ko ragi a cikin kalma da ƙarangiya da habaici da
sauransu.
Sarrafa harshe hanya ce ta amfani da kalmomi da jimloli a
waƙa cikin hikima. Adamu, (2012: 54). Sarrafa
harshe hanya ce ta amfani da harshe a cikin waƙa. Don
haka ta ƙunshi yadda mawallafi yake zaɓen kalmomi
da jumloli ta yin la’akari da yadda yake amfani das u wajen isar da saƙonsa
ga al’umma Abubakar, (2017: 151)
A dunƙule dai sarrafa harshe dabaru ne da mawallafa ke amfani
da su wajen sarrafa kalmomi da jimloli a waƙa ta hanyar hikima.
3.0 Dabarar Bincike Da
Hanyoyin Tattara Bayanai
Duk wani
bincike na ilimi da za a gudanar ya na da dabaru da hanyoyi da mai yin nazarin
kan zaɓa domin ya bi wajen cimma nasarar
wannan bincike. An ɗora wannan bincike bisa ra’in Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Dabaru da hanyoyin da aka bi
wajen gudanar da wannan nazarí sun haɗa da samo matanin waƙar kai tsaye daga wurin marubucin, an kuma same ta a
rubuce da kuma a cikin kaset, sannan an sami cikakkiyar waƙar a cikin kundin binciken Adamu, (2012:
253-264) domin samun sauƙinm nazari. Haka kuma an tattauna da marubucin dangane da
tarihinsa da kuma ita kanta waƙar.
3.1 Ra’in Bincike
Ga
yadda Ɗangambo (2007) ya kawo Ra’in:
1. Bayanan
share fage
2. Jigo
3. Zubi da
tsari
4. Salo
5. Sarrafa
harshe
1. Bayanan Share Fage: Manufar
Marubuci/Mawallafi
a. Bayanin
Diddigi.Salsala
b. Shekarar
da aka Wallafa Waƙa
2. Jigo
a. Furucin Gundarin
Jigo/Ƙwayar Jigo
b. Jigo a
Gajarce
c.
Warwarar Jigo da shimfiɗarsa
3. Zubi da Tsari
a. Zubi da
tsarin waƙa na gaba ɗaya
b. Zubi da
tsari a cikin baitoci
c.
Yawan baitoci da ɗango a waƙar
d. Nazarin
karin waƙa (Aruli)
e. Amsa-amo (ƙafiya)
f.
Gangara da saɓi-zarce
4. Salo
a. Ma'anar
salo da Nau'o'insa
b. Sauran
dabarun Salon sarrafawa
c.
Kwatantawa
d. Siffantawa
e. Kamantawa
f.
Dabbantarwa
g. Abuntarwa
h. Abuntarwar
abuntarwa
i.
Alamtarwa
j.
Kambamar zulaƙe
(kambame)
k. Jaddadar Ƙarfafawa
l.
Jerin Sarƙen
Daidaito/Bambanto
m. Ƙarangiya
n. Kalmomin
Fannu/Dangantakar Kalmomi
o. Baubawan
Burmi/Gamin-Baurar Kalmomi
p. Zubi Mai
Jan-rai/Ɗaga Hankali
q. Gangara
r.
Saɓi-zarce
s.
Jinkirin Faɗar
Sakamakon Wani abu a Cikin Waƙa
t.
Tasirin Al'adu, Karin Magana, Tatsuniya
u. Samarwa da
Korewa ("I" + "A'a")
5. Sarrafa Harshe (Nahawu)
a. Amfani da
Kalmomi
b. Tsarin
Jimla
c.
Ginin Ƙirar Jumla
d. Giɓin Jimla
da Kwance Ƙullin Jimla
e. Sauran
Abubuwan da Suka Shafi Nahawu
An
ɗora wannan
bincike ne bisa wannan mazhaba ta Ɗamgambo,
2007, amma an fi mayar da hankali ne a kan abubuwa da suka shafi sarrafa
harshe.
4.0 Sarrafa Harshe a Waƙar Ba
Na Shakka
Mawallafin ya yi amfani da sarrafa harshe a cikin waƙar; inda ya yi amfani da sauƙaƙan kalmomi da ake jin su, yau da
gobe, misali: kyautatawa da alƙawari da tuta da hassada da moriya da juriya da adawa da ƙage da sauransu. Haka kuma ya yi amfani da kalmomin da suka
dace, a cikin waƙar, misali, ya yi amfani da sababbin kalmomi da tsofaffin kalmomi da
ararraun kalmomi. Ya kuma yi amfani da karin magana da habaici da sauransu.
Waƙar Ba Na Shakka tana ɗauke da baituka 69, kuma kowane baitin yana ɗauke da ɗangwaye biyar-biyar wato “muhammasa” ko mai ƙwar biyar. Haka kuma tana da
amsa-amo na ciki da na waje, wato babban amsa-amo da ƙaramin amsa-amo. Amsa-amon cikinta
yana canjawa, babban amsa-amonta kuma yana ƙarewa da ya. Mawallafin ya yi hikima wajen yin amfani da kalmomin Hausa sauƙaƙa.
Mawallafin ya yi amfani da salo mai armashi ko mai
karsashi a waƙar. Saboda waƙar ta ƙunshi abubuwa da suka haɗa da hanyoyin dabarun jawo hankali da zaɓaɓɓun kalmomin da suka dace. Ya yi amfani da tsofaffi da sababbin kalmomi da
karin magana da habaici da zambo. Haka kuma ya yi amfani da ararrun kalmomi da
karin harshen Kananci da dabarun salon sarrafawa da sauransu. Domin haka za a
iya cewa salon mawallafin na gaba ɗaya tsaka-tsaki ne.
4.1 Ararrun Kalmomi
Mawallafa suna
aro wasu kalmomi daga wani harshe domin yin amfani da su a cikin waƙoƙinsu, mafiya yawan mawallafan waƙoƙin Hausa sun fi aro kalma daga
harshen Larabci da kuma Ingilishi. Haka ma mawallafin wannan waƙar ya yi amfani da
ararrun kalmomi daga harsuna uku wato Larabci da kuma Ingilishi (Ingilishi) da
Fulatanci a cikin waƙar. Misali;
4.1.1 Kalmomin Larabci
A nan
marubucin ya yi amfani da kalmomin Larabci a baitika da yawa a cikin waƙar.
Ga misalin yadda ya kawo a baiti:
Bismillahi Hakimu Allah Mahaliccina,
Kai ne mai taimakon mutum safe da rana
Ban iko Jalla za na waƙe abar ƙauna
Ni a wajena da
dukkanin magujin ɓarna,
Zai so ta ta zam
uwa a yankin Najeriya.
A
wannan baitin mawallafin ya yi amfani da kalmomin Larabci irin su Bismillah da
Jalla da Hakimu kamar yadda ya kawo a baitin.
A
baiti na gaba ma ya ƙara faɗin:
6.Har ta zartar ana faɗi an ce za a yi,
Sauƙi ga biyan kuɗin Hajji bana
mai so ya yi,
Kuɗinka
ƙalilan idan ka so tafiya sai ka yi,
Ba wata matsala za fa ta zo ta hana don a yi,
Cinikayyar arziki ta ɗaukaka Najeriya.
Haka ma a wannan
baitin ya yi amfani da kalmar Hajj kamar yadda ya kawo a ɗango na
biyu a cikin baitin.
Haka dai mawallafin
ya cigaba da kawo ire-iren waɗannan kalmomin Larabci a wasu baitukan
kamar haka.
Baiti |
Ararriyar Kalma |
Harshe |
Asalin Kalma |
Ma’ana |
bt,
1 |
Bismillah
|
daga
Lar. |
Basmalah |
Da
sunan Allah |
bt,
1 |
Jalla |
daga
Lar. |
Jalla |
Allah
Maɗaukaki |
bt,
1 |
Hakimu |
daga
Lar. |
Hakimu |
Mai
hikima |
bt,
6 |
Hajj |
Daga
Lar. |
Hajj |
ɗaya daga cikin
shika-shikan Musulunci |
bt,51
|
nufin
ya sami mutum |
daga
Lar. |
Ƙadar |
Abin da Allah ya yi |
bt,
51 |
alkausara |
daga
Lar. |
alkausar |
Ruwan
aljanna |
bt,
53 |
da’awa |
daga
Lar. |
da’awa |
tinƙaho ko galaba da
wani abu |
bt,
54 |
kattabawa |
daga
Lar. |
kattabawa |
Kammalawa |
bt,
51 |
Sallallami |
daga
Lar. |
Sallallami |
Juyayi |
bt,
20 |
ni’ima |
daga
Lar. |
ni’ima |
Wadata |
bt,
26 |
Hassada |
daga
Lar. |
Hasdun |
Ƙyashi |
bt,39 |
Liman |
daga
Lar. |
liman |
jagora wajen salla da wasu ayyukan addini |
bt,39 |
raka’a |
daga
Lar. |
raka’atun |
Rukuni
a cikin salla |
bt,44 |
Imani |
daga
Lar. |
Iman |
Yarda |
bt,45 |
almajiri |
daga
Lar. |
Almuhsdir |
Ɗalibi komai neman
sani |
bt,
48 |
Bayani |
daga
Lar. |
bayan |
Jawabi |
bt,63 |
alhaki |
daga
Lar. |
Alhaƙƙi |
zunubi |
bt,67 |
Haram |
daga
Lar. |
haram |
hani ga barin abu marar kyau |
bt,69 |
nasara |
daga
Lar. |
Nasr |
sa’a,
galaba |
bt,50 |
Alfarma |
daga
Lar. |
alhurmah |
nuna
isa |
bt,50 |
ƙaddara |
daga
Lar. |
Alƙaddaru |
nufin
Allah |
bt,50 |
ɗahira |
daga
Lar. |
Ɗahiratu |
Tsarkakkiya |
bt,50 |
khairul
ambiya |
daga
Lar. |
khairul ambiya |
Mafificin
annabawa |
4.1.1
Ararrun
Kalmomin Ingilishi
A nan
mawallafin ya yi amfani da ararrun kalmomin Ingilishi a wasu baituka na waƙar.
Ga misalin yadda ya kawo a baitin:
14.
'Yan kudu
har arewa mun zaɓi farar
uwa,
Peoples Party kasarmu bana ta zamo
kokuwa,
Yau kaf Najeriya mu ta hada ba ta garkuwa,
Ita ce jirgin fitar shiga bana a haye ruwa,
APP is the best head
of Nigeria.
A wannan baitin
mawallafin ya yi amfani da ararrun kalmomin Ingilishi irinsu: Peoples Party da APP
da APP is the best head to Nigeria. Haka dai, ya cigaba da kawo ire-iren waɗannan
kalmomi na Ingilishi a wasu baituka a waƙar, kamar
haka:
Baiti |
Ararriyar Kalma |
Harshe |
Asalin Kalma |
Ma’ana |
bt, 14 |
Peoples
Party |
daga Tur |
Peoples
Party a |
Jam’iyyar al’umma |
bt, 14 |
APP |
daga Tur |
All
Peoples’ Party |
Jam’iyyar Kowa da
Kowa |
bt, 14 |
APP is the best
head of Nigeria |
daga Tur |
APP is the best to
head Nigeria |
Jam’iyyar kowa da
kowa ce wadda ta fi dacewa ta shugabancin Nijeriya |
bt, 19 |
Kwamanda |
daga Tur |
Commander |
Shugaba (na soja) mai ba da umarni |
bt, 24 |
Mitin |
daga Tur |
Meeting |
Taro |
bt, 24 |
Oda |
daga Tur |
Order |
Umarni |
bt, 24 |
Kamfani |
daga Tur |
Company |
Masana’anta |
bt, 25 |
Kwamiti |
daga Tur |
Committee |
taron jama’a da ake zaɓa ko naɗawa domin su yi nazari da tattauna wasu al’amura domin fito da wasu
bayanai da za a yi aiki da su, akwai shugaba da sakatare |
bt, 26 |
Lokal gwabmen |
daga Tur |
Local
government |
Ƙaramar hukuma |
bt, 50 |
Bankuna |
daga Tur |
Banks |
wuri na musamman da aa gina domin ajiye kuɗi da gudanar da harkokinsu |
bt, 56 |
Sanata |
daga Tur |
Senator |
Ɗan majalisar dattijai a ƙasa (wakili a majalisar ƙasa masu gudanar da dokoki |
bt, 58 |
Santa |
daga Tur |
Centre |
Tsakiya |
bt, 65 |
Biredi |
daga Tur |
Bread |
dunƙulallen abinci
da aka yi da fulawa ko alkama |
bt, 48 |
D.P.O. |
daga Tur |
Divisional Police Officer |
babban Jami’in ‘yan sanda mai kula da ƙaramar hukuma |
4.1.3 Kalmomin Fulatanci
A nan mawallafin ya yi amfani da ararrun kalmomin
Fulatanci ga misalin yadda ya kawo a wannan baitin.
16. Kun samu
rabautuwa Fulanin Najeriya,
Bana za ku yi dariya wajen kiwon saniya,
Ba mai duban ku bana ya ƙara yi
muku dariya,
Kaɗo da Jauro Iyamuri Yaruba gaba ɗaya,
Za ku ji daɗi idan ta
kame Najeriya
A wannan baitin
mawallafin ya yi amfani da kalmomin Fulatanci irinsu Kaɗo da Jauro
Baiti |
Kalma |
Ma’ana |
bt,
16 |
Kaɗo |
Bahaushe |
bt,
16 |
Jauro |
Maigari
ko dagaci |
4.1.4Kalmomin
Hausa Masu Sabuwar Ma’ana
Mawallafin a nan ya
yi amfani da kalmomin Hausa masu sabuwar ma’ana ga misalin yadda ya kawo a
wannan baitin.
41 Tsuntsun
da ya ja ruwa ku ƙarasa magana in ji,
Nai ɗamara
za ni kwankwatse kan madurguji,
In tai daɗi
gare ku wasu haushi za su ji,
Dangina sai ku karkaɗe kunne don ku ji,
Farin labarin da ya fi kyautar wazobiya.
A nan
mawallafin ya yi amafani da kalmar Hausa mai ɗauke da sabuwar ma’ana Wazobiya.
Wazobiya- tana nufin
Naira hamsin (kuɗi)
4.2Karin Harshe
Mawallafin ya yi amfani da karin daidaitacciyar Hausa.
Misali:
5APP rundunar ƙwararru ga ci gaba,
Babu kasala
cikinta ba a kuma fargaba,
Kai da gani ta mu
ita ta dace ta zame gaba,
Lallai
Najeriyarmu za ta zamo tai gaba,
APP in ta zam da mulkin Najeriya
4.3 Ragi da Ƙari a Cikin Kalma ko Jimla
Mawallafin ya yi amfani da damar da aka bai wa mawaƙa na yin amfani da
‘yancin waƙa wajen yin ragi ko ƙari a cikin kalma ko jumla. Suna iya gutsirewa ko su ƙara wani abu a farkon
kalma ko ƙarshenta ko su yi wasa da farkonta.
Misali
Ƙari – Juya Siffar Kalma
43.Karatu ne ga shi nan a je a riƙe
don gaba,
Da a wajen kishiyar uwa dole da fargaba,
Limanci bai yiwo ga shege marashin uba,
Ku duba baƙaƙenmu wanda duk yaji bai gan su ba,
Sai ya yi nazari ya ƙara
duba da idaniya.
A
wannan baitin mawallafin ya yi amfani da juya siffar kalma, inda ya kawo kamar
haka:
Marashin
uba maimakon marar uba
4.4Ma’anonin Wasu
Kalmomi
Mawallafin a nan ya
yi amfani da wasu kalmomi ya danganta su ga abokan hamayya, ga
yadda ya kawo a baitin
30.Mai taya kishi ga kishiya shashan gari,
Mai ba da
gudunmuwa ga 'yan iska shagiri,
An yi butulci a bara aka ɗau ɓatakalkari,
Shashashan babu wanda ya tsira da ko ɗari,
Bana a yi hattara a duba waina toyayya.
A wannan
baitin mawalalfin ya yi amfani da kalmomin shagiri
da ɓatakalkari wanda
ya jingina su ga abokan hamayya. Sai ya ci gaba da kawo ire-iren waɗannan kalmomi a cikin wasu baitoci a waƙar kamar haka:
bt,
30Shagiri – mutumin da gemu ba ya fitowa a haɓarsa
Ɓatakalkari-tana nufin
shashasha
57Zuga-tana nufin ayari
bt, 41Madurguji-kaɓaki ko ƙatuwar malmala
bt, 46Kube – gidan wuƙa ko takobi ko kibiya
Sassabe – sharar da ake yi wa gona domin shuka
bt, 49Bisa – dabbar gida da ake cin namanta
bt, 62Gurɓiya – dage-dagen miya
bt, 65Naɓuwa –
naman baki ko kaurin leɓen sama
bt, 68Karkiya
– igiya da ake ɗaurawa a tsakanin cinyoyin ɗan
kaciya
bt, 59 “barankaci”- ɗan itace da ake kaɗa shi
bt,65 “kadab-karan”- kirarin da ake yi wa
mutum mai
rowa
bt, 24 “madurguji”- kaɓaki ko ƙatuwar malmala
C.N.H.N, (2006)
4.5Karin Magana
Karin magana, dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kaɗan, cikin hikima Ɗangambo, (2008: 14).
A nan mawallafin ya yi amfani da karin magana a cikin waƙar domin ya daɗa inganta waƙar da isar da saƙonsa ga abokan adawa cikin hikima; misali:
31Hantar kura a gun kare ta fice lasuwa,
Ɓarin gari
ba a yi a kwashe tsab ɗan’uwa,
Ba a dukan uba a
ce an yi da mantuwa,
Dashen
Allah ba dashe mutum ba dashen kainuwa,
Hukuncin Allah a
bi shi shi ya fi da hayaniya.
A nan mawallafin
ya yi amfani da karin maganar nan da Bahaushe yake cewa;
Ba
a ɓarin gari, a kwashe duka
Wato, a nan ba a yin wani abu a ce lallai sai
ya zama daidai ko sai ka ga yadda kake so.
Haka kuma ya yi amfani da karin maganar da Bahaushe yake cewa “Ba a dukan
uba a ce an yi da mantuwa”.
Wato ka yi wani abu ka na sane, ko mutum ya yi wani abu da niyya.
Sannan kuma ya yi amfani da karin maganar nan ta Bahaushe da yake cewa, Kainuwa dashen Allah ba dashen mutum
ba.Wato idan Allah ya dasa mutum a waje babu wanda ya isa ya cire shi.
A baiti na gaba ma,
ya cigaba da faɗin:
41Tsuntsun da ya
ja ruwa ku ƙarasa magana in ji,
Nai ɗamara za ni kwankwatse kan madurguji,
In tai daɗi gare ku
wasu haushi za su ji,
Dangina sai ku karkaɗe kunne
don ku ji,
Farin labarin da
ya fi kyautar wazobiya.
A nan ma, mawallafin ya yi amfani da karin maganar nan da Bahaushe yake
cewa, “Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan doka”. Wato a nan duk wanda ya jawo
wa kansa wani abu to kansa zai koma. Wato, a nan yana mayar da martani ne zuwa
ga abokin hamayya.
Mawallafin kuma sai ya ci gaba da cewa:
62Tilas tsohon zuma da shi za ai magani,
Tsohon yankan rake daban da na ‘yan zamani,
Na ga taɓaɓɓan su o’o ya fara
guna-guni,
Da kai motsi ga uban gidanmu ka sha tsunkuni,
Dafaffen ɗawisu namu ku ko gurɓiya.
A nan mawaƙin yana zuga ɗan takarar jam’iyyar APP a kan
nagartarsa da ƙwarewarsa ta irin gudummawar da ya daɗe yana bai wa jam’iyyar. Don haka shi ne wanda ya cancanta. Sannan kuma
yana yi wa ɗan adawa habaici da nunawa shi
mahaukaci ne, da ɗaga darajar ɗan takararsu na APP.
4.6Habaici
Ma’anar habaici ita ce furta wata kalma ta suka ko zagin wani a fakaice,
kuma a gaban idonsa, ta yadda wani daban ba lalle ne ya gane da wanda ake ba.
Amma idan aka ambaci wani abu da yake da dangantaka da mutum, to ba makawa zai
fahimci da shi ake. Wani lokaci shaguɓe ko gugar zana suna iya ɗaukar ma’anar habaici. Galibi an fi yi wa abokan hamayya ko maƙiyi habaici domin a
tunzura shi ko a tsokane shi ko kuma a ɓata masa rai Sa’id, (2002: 231: 1)
Ga misalin yadda ya
ce:
42Baƙar mage abin tsiyarki yas sa na ya da ke,
Dirakun da mukai gini da su ke kika tunɓuke,
Sanda ta gane gininmu zai faɗi ta tsallake,
Babu mutunci a yau tsakaninmu da mu da ke,
Baƙar mage baƙar tsiyarki na gaji tsinanniya.
A nan mawallafin ya yi wa wata 'yar jam’iyyar adawa habaici, inda ya
kwatanta halayyar da ta yi musu da halayyar mage, magen ma kuma baƙa, wato yadda mutum zai
ji zafin abin. Wannan 'yar adawa da a cikin jam’iyyar take daga baya kuma da ta
ga tafiyar ba za ta yi nisa ba, sai ta koma take yin zagon ƙasa ga jam’iyyar.
A baiti na gaba
ma, ya ƙara da cewa:
45Abin mamaki kare
da talan tsire gari,
Ga wani attajiri da siffar almajiri,
Na lura da shi da kyau yana tara mare-mari,
Hannunsa da gatari yana faman yunƙuri,
Na fuskance shi maza ku nemo bulaliya.
A nan mawallafin yana yi wa wani uban jam’iyya habaici a kan wata halayya
da yake nunawa, shi kuma mawaƙin ya ƙasƙantar da shi inda ya danganta shi da mai kwaɗayi da kuma cutarwa.
Wato, ita ɗabi’ar kare kwaɗayi. Halayyar kuma da ya bayyana yana tanadar makaman
cutarwa ne, hannunsa kuma da gatari
yana faman yunƙuri. Wato uban jam’iyyar ne yake dakushe tallata wani ɗan takara, kan ya dakushe jam’iyyar APP.
A wani baiti kuma
wannan mawaƙi yana cewa:
46Ga makaho da wuƙar ƙashi a hannu yana lalube,
Yau ga kuturu da sungumi zai gwada sassabe,
Ku ji makara yau ake buƙata a yi wa kube,
In tafiya tai tsawo na kirki sa rarrabe,
Su zo ga da shirin gaskiya su kauce wa hayaniya.
A nan ma habaici aka yi wa ɗan takarar adawa, duk lokacin da aka yi zaɓe sai a ce shi ya ci, alhalin ba shi yake ci ba, kuma ba
zai iya yin mulkin ba. Sannan kuma yana kwarzanta ɗan takararsa ne sama da sauaran ‘yan takarkaru.
A waƙar dai ya cigaba da faɗin:
47Ƙaryar kashin kare
ya zama taki na gani,
Ba a sayarwa a kasuwa ku sani tun tuni,
Ba a jiƙawa a sha
shi don neman magani,
Ba wani mai tanadinsa don ajiya had da ni,
Ku zo zan fasa ƙwai ku ji ni in ba mu da gaskiya.
Idan aka kalli wannan baitin za a ga mawallafin ya ƙasƙantar da ɗan takarar adawa inda ya nuna rashin amfaninsa a cikin
al’umma, domin haka ba wani amfani da zai yi wa al’umma idan an zaɓe shi.
Ya sake kawo irin
wannan dabarar ta habaici, ga abin da yake faɗi:
49Har yau da bazarmu dai ake taka rawar isa,
Karon nan dai bana ba mu yi da rago sai mai bisa
In ka san kai ƙahon karo
ka matso kusa,
Zo ga bardanmu mu da kai mu ga mai cin ƙasa,
Mu tona asiri mu keta rigarka ta kwalliya.
Wannan baitin mawallafin yana yi wa ɗan hamayya gori. Sannan kuma baiti ne na kwarzantawa da kuma barazana da
ake yi wa ɗan adawa.
Sannan a baiti na
gaba ya ƙara da cewa:
61A ran bikin tsuntsaye a daina son a kira mujiya,
Jemage na karanci sam ba ka da tsuliya,
Rigar babban
cikinsu ta zama yagaggiya,
Babu tufafin ado bare bana a yi kwalliya,
Mu ke da wuƙa muke da nama a Najeriya.
A wannan baitin mawallafin ya ƙasƙantar da ɗan takarar jam’iyyar adawa, inda ya kwarzantar da ɗan takarar jam’iyyar APP da kuma fito da nagartarsa sama
da ta ɗan takarar adawa.
Sannan a baiti na
gaba ya ƙara da cewa:
62Tilas tsohon zuma da shi za ai magani,
Tsohon yankan rake daban da na ‘yan zamani,
Na ga taɓaɓɓen su o’o ya fara
guna-guni,
Da kai motsi ga uban gidanmu ka sha tsunkuni,
Dafaffen ɗawisu namu ku ko gurɓiya.
A nan mawallafin yana nuna muhimmancin Magaji Abdullahi ta yadda jam’iyyar
ba za ta kai ga nasara ba sai da shi, domin haka ya kira shi da “tsohon zuma”
da “tsohon yankan rake” wato ya daɗe a cikin tsarin ana cuɗawa da shi, domin kwarzonta shi. Sannan kuma ya ƙasƙantar da ɗan takarar adawa inda ya kwatanta shi da mahaukaci ya
kuma nuna ɗan takarar APP ya fi na jam’iyyar
adawa magoya baya.
Ya sake amfani da
habaicin inda yake cewa:
63,Ga wata ruɓaɓɓiyar kula babu ruwa
ciki,
‘Ya’yan mowar gidan su ‘o’o suna cin tsaki,
Kai da gani jami’insu na ɗaukar alhaki,
In sun magana ya yunƙura yai masu ɓaɓɓaki,
Kai ka ji wai baba ne ya ce kada a yi kwalliya.
A nan mawallafin
yana yi wa shugaban jam’iyyar PDP habaici inda yake nuna shugaba ne marar
adalci mai danniya da babakere a kan haƙƙin magoya bayansa.
4.7 Zambo
Shi zambo ba kamar habaici ba, zagi ne na kai tsaye, idan an kwatanta shi
da habaici. A cikin zambo ana siffanta mutum da dai duk wani abu da ya shafe
shi, yadda zai taimaka a gane da shi ake Ɗangambo, (2008: 73).
Mawallafin ya yi amfani da zambo a cikin waƙar, inda yake yi wa abokin hamayyar
jam’iyyar APP zambo, inda ya yi masa zambo a cikin baiti na 65. Misali:
65 Har gobe kadab-karan yana ƙasa dandanƙuwa,
Ga nauyi in ka lura ta sa yai naɓuwa,
Biredin da kuke shirin saye sam ba shi da totuwa,
Na ga mutanen da huluna marasa ƙoƙuwa,
Sai tafiyar tai tsawo su sa a yi masa toliya.
A wannan baitin mawallafin ya zambace abokin hamayyar jam’iyyarsu ta ANPP,
inda yake nuna rashin tasirinsa da koma bayansa na rashin cigabansa a wajen
al’umma. Yana kuma nuna jam’iyarsu fanko ce kawai ba ta da wani amfani da za ta
kawo wa al’uma, sannan kuma yana nunawa ‘yan hamayya jam’iyar da suka ɗauko ba za ta yi musu amfani ba mayaudara ne kawai ba za
su kawo wani cigaba ba.
Haka kuma mawallafin ya yi amfani da dabarar sanya tatsuniya a cikin waƙar inda ya kwatanta ɗan takarar jam’iyyar APP da Gizo, da kuma halayen Gizon
da ya kwatanta ɗan takarar na wayo wato, ya yi
amfani da wayon da Gizo yake da shi na ƙarya ya sanya ya haskaka ya kuma kwatanta Ƙoƙi da abokiyar hamayya. An san
cewa kullum Gizo shi yake yi wa Ƙoƙi
wayo a cikin tatsuniya, domin haka shi ne kan gaba. Ga misalin;
40 Ga Gizo ga Ƙoƙi yau akwai ni da tatsuniya,
Mai son ya ji sai ya ban tukuicin wazobiya,
Magana ce ga ta nan a fili tatacciya,
Bana kuma Gizo ya fito da ƙaryarsa na kwalliya,
Ya haskake ko’ina a yankin Najeriya.
A taƙaice, a wannan baitin mawallafin ya yi amfani da dabarar sanya tatsuniya a
cikin waƙa.
5.0 Kammalawa
An fahimci
Aminu Ibrahim Ɗandago marubuci ne da yake da ƙwarewa
da basira wajen iya sarrafa harshe da azanci a waƙoƙinsa. Nazarin kuma ya gano amfani da sarrafa
harshe a cikin waƙa musamman ta siyasa,
hanya ce ta: jawo hankalin mai sauraro ko karatu da riƙe
tunanin mai sauraro ko karatu da nuna
gwanintar harshe da sa waƙa armashi da yi
wa waƙa kwalliya. Bugu
da ƙari kuma nazarin ya gano irin ɗimbin
hikimomin da mawallafin ya yi amfani da su a cikin waƙar na
sarrafa harshe ta hanyar yin amfani da kalmomi da jimloli domin su bayar da saƙon
ga jama’a. A ƙarshe
wannan nazari zai ba da gagarumar gudunmawa a fagen ilimi musamman ga ɗaliban
ilimi da manazarta wajen ƙara
fahimtar sarrafa harshe a cikin rubutacciyar waƙa musamman
ta siyasa da kuma yadda za a nazarce su da yi musu sharhi.
Manazarta
1. Abubakar,
U.S (2017) “Nazari da Sharhin Rubutattun Waƙoƙin
Siyasa” na Musa Yunusa Saye. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
2. Adamu, A.
I. (2012) “Salo da Sarrafa Harshe a cikin Wasu Waƙoƙin
Jam’iyyun ANPP da PDP a Jihohin Kano da Jigawa”. Kundin Digiri na Biyu. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
3. Adɓance Learners’ Dictionary 1995) Oɗford Uniɓersity
Press
4. C.N.H.N.
(2006) Ƙamusun Hausa na
Jami’ar Bayero Kano. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity
Press.
5. Ɗangambo,
A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe
Waƙa (Sabon tsari) Kaduna: Amana
Publishers Limited.
6.
Dangambo, A. (2008), Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga
Rayuwar Hausawa (Sabon tsari) Kaduna: Amana Publishers Ltd.
7. Sa’id, B.
(2002) “Rubutattun Waƙoƙin
Hausa na Ƙarni na Ashirin a Jihohin Sakkwato da Kebbi
da Zamfara”. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar
Bayero.
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.022
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.