This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.
Halima Mansur Kurawa
Department of
Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara State
Tsakure
Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta shafi kowa da kowa. Gwamnatoci da hukumomi
da ɗaiɗaikun, Mutane, kuma a cewar kowanne yana
bayar da gudummawa wajen daƙile wannan matsalar. Daga ɓangaren makaɗan baka tuni ba tun yau
ba, a cikin waƙoƙinsu suke nusar da jama’a wasu
abubuwan da idan da an yi riƙo da su da ba a samu kai a halin da ake ciki yanzu ba. Abubuwan ne wannan
takarda, ta duba don ganin irin gudummawar da suka bayar ko jama’a ta yi
tsinkaye ta koma kan ɗabi’unta da al’adunta na zamantakewa kyawawa. Makaɗan da aka kafa hujja
daga waƙoƙinsu na yankin ƙasar Zamfara ne. Bahaushe kuwa yace; “Mai ɗaki shi yasan inda yake yi masa yoyo”.’
Fitilun Kalmomi: Gudummawa,
Makaɗan Baka, Tsaro,
Zamfara
1.0 Gabatarwa
Adabi kamar yadda
Yahaya (1973) ya ce, “wata babbar hanya ce da ɗan’Adam yake yin amfani da ita don ya sadar da abubuwan da suka shafi
rayuwarsa da ta ‘yan’uwansa (iyalinsa ko dangi ko ƙasarsa) ga su ‘yan’uwan
ko wasu daban. Abubuwan da yakan so ya sadar ɗin nan kuwa sukan shafi wani abu ne da ya daɗaɗa masa zuciya ko wanda ya sosa masa rai...” Gusau, (2011: 1-2). Adabin Hausa ya rabu zuwa manyan
gidaje guda biyu, su ne adabin baka da rubutaccen adabi.
Waƙoƙin baka na Hausa, suna ƙarƙashin adabin baka. Ana
aiwatar da su don isar da wata manufa da ta ƙunshi, ilmantarwa da nishaɗantarwa da wayar da
kai yadda za a inganta tsaro don samar da zaman lafiya. Wannan takarda, ta yi nazari ne a kan gudummawar da
makaɗan
baka suka bayar wajen
samar da tsaro a Jihar Zamfara.
Daga kaɗe-kaɗen da ake da su a ƙasar Hausa har akwai kiɗan yaƙi. makaɗan yaƙi su ne waɗanda suke waƙoƙinsu lokacin yaƙe-yaƙe. (Gusau, 1996: viii). Tarihi ya
nuna lokacin da ake yaƙi a ƙasar Hausa, makaɗi yakan shiga rundunar yaƙi yana kirari da
zuga gwaraza, da sanya tsoro da razani ga abokan gabarsu, kodayake akan samu
wasu su ɗauki makami, kamar yadda Ata Mai Kurya ya yi, har
ake yi masa kirari, “ Ga kurya ga mashi”, amma galibi ba sa yaƙi, don haka ba a
kashe makaɗi a filin daga in ba makami ya ɗauka ba, kamar yadda ba a kashe mace. Gusau (1996: v) ya ambaci
sunayen waɗansu makaɗan yaƙi da suka haɗa da: Wari Mai Zarin Gobir da Ata Mai Kurya da Umaru Na Maiyaƙi da Kara Molo da
kuma Idi Kura Gazau.
1.1 Kadadar Bincike
Wannan nazari a kan makaɗan baka ne na Jihar
zamfara, don ganin gudummawar
da suka bayar a cikin waƙoƙinsu wajen samar da tsaro.
1.2 Dabarun Bincike
Wajen tattaro misalan waƙoƙin, an yi amfani da
bugaggun littattafai da maƙalu da kuma sauraren waƙoƙin da aka naɗa a faifan CD.
1.3 Ra’in Bincike
Makaɗan baka, ba mahunkuta
ba ne, ba kuma jami’an tsaro ba ne, amma duk da haka suna bayar da wata
muhimmiyar gudunmawa cikin samar da tsaro, suna yin haka ne kuwa ta amfani da
irin baiwar da Allah ya yi musu, ta fasahar waƙa. Lura da haka aka ɗora wannan aiki a kan
karin maganar Bahaushe da yake cewa: “Sandar da take hannunka da ita ka ke duka”. Haka kuma wannan nazari
ya dace da ra’in ‘Mazhabar Gudunmuwar Adabi ga Al’umma, wato ‘psychosanalyical Theory’.
1.4 Tambayoyin
Bincike
Daga ƙarshen wannan bincike ana son a fito da
amsoshin wasu tambayoyi kamar haka:
1.Waɗanne irin matakan
tsaro Bahaushe ya ke da su a al’ada?
2.Ta yaya makaɗan baka suke bayar da
gudunmawa wajen samar da Tsaro?
2.0 Ma’ana da Asalin
Waƙar Baka
Gusau
(1993) ya bayar da ma’anar
waƙar baka da cewa:
...wani
zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da
daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi.
Akwai masu ra’ayin
cewa kirarin da ake yiwa sarakuna da kuma wanda ake yi wa maza, a filin yaƙi, ko na farauta, tare da waɗanda ake yi a wurin
bautar iskoki, su ne suka haifar da waƙar baka a ƙasar Hausa. Ga misali, Abba da
Zulyadaini (2000: 6) sun nuna a wajen yaƙi a kan samu masu yi wa maza kirari domin
su nuna jarunta da bajinta a filin daga, ko kuma bayan an koma gida masu irin
wannan kirari kan bi kan waɗannan
Jarumai suna yi musu kirari. A wani lokaci ma su jaruman ne kan yi wa kansu
alwashi, idan sun yi wata bajinta a filin daga kamar yadda Idi na Manga Kura Gazau yake yi
wa kansa kirari a lokacin da ya yi wata bajinta yana cewa:
Na Manga
Kura Gazau,
Kau da kara aikina.
Gafara
Bello ubana,
Ban san kai na ba.
Tsinin
mashi Idi bai san manya ba,
Shi
bai san yaro ba.
An
ban manyan shanu ba don yaƙi ba,
In batun yaƙi na, Namanga sai ya
zaɓa.
Kowab bi ta horon uwa,
Ba yai yaƙi ba.
Su
wane an bi ta horon Uwa,
Ana ɗaka zamne”.
Makaɗi kan yabi wanda ko
waɗanda
yake yi wa waƙa ya kuma kushe magautansu. Kushe
abokin gogayyar na ƙara fito da ƙarfin tsaro da wanda ya fifita ya ke da
shi.
3.0 Gudunmawar Makaɗan Bakan Zamfara
cikin samar da Tsaro
Jihar Zamfara
Kamar yadda Gusau
(2012: 109) ya bayyana, an tabbatar da Jihar Zamfara ne ranar 1 ga watan Oktoba,
1996, da ayyana garin Gusau ya zama babban birnin Jihar. Jihar ta Zamfara tana
da ƙananan hukumomi goma sha huɗu (14) da suka ƙunshi ƙaramar hukumar Anka da Bakura da Birnin Magaji
da Bunguɗu da Bukkuyum da Gummi
da Gusau da Ƙauran Namoda da Maradun da Maru da
Shinkafi da Talatar Marafa da Tsafe da kuma Zurmi. Jihar daga Gabas, ta yi iyaka da Jihar Katsina, daga
Yamma ta yi iyaka da
Jihohin Kebbi da Niger. Daga Kudu kuma ta yi iyaka
da Jihar Kaduna, sannan ta yi iyaka da sabuwar Jihar Sakkwato daga Arewa.
Waƙoƙin makaɗan bakan Zamfara cike suke da misalai na
yadda al’ummar Hausawa suka yi da watsi da al’adunsu masu kyau da yadda talauci
da rashin aikin yi ya yi katutu a tsakaninsu musamman matasa. Waɗannan dalilan sun isa
su kawo rashin tsaro a Jihar Zamfara da ƙasa gaba ɗaya, kuma makaɗan sun yi faɗakarwa a kan hakan. Misali: Sani Sabulu yana cewa:
Jagora: ‘Yan’uwa Salamu alaikum,
Na yi Sallama na ƙara,
Sallama mutuncin baƙo,
Don ɗan gida shi ɗau kai da muƙami.
Jagora: Yaƙi noman Sarki, Yara tafiya noman falke,
Kowa ya san kowa yara ku riƙa min ‘ya’yana,
Na yi Sallama na ƙara,
Sallama mutuncin baƙo,
In ya yi sallama ya wuce gori ko wata rana.
(Mainasara, 2016: 238)
Matakin farko na
samar da tsaro shi ne idan maigida ya yi baƙo ya sanar da mai unguwa, don kar a sauki
mugun iri. Ba a saukar baƙo sai an san ji daga ina yake? Gurin wa ya zo? Mene ne ya kawo shi? Tsawon wane lokaci zai
zauna.?
A wani wuri kuma sai
yace:
Jagora: Mu riƙa shuka alheri,
Jama’a mu riƙa shuka alheri,
Mu riƙa shuka alheri,
Jama’a mu riƙa shuka alheri,
Sharri ga mai shi haɗari ne,
Ɗan’uwan kare ne,
Kullum in ka ganai da
mai shi yaka yawo. Mainasara, A. ( 2016:
238)
A nan kuma sai ya ce:
Jagora: Kui mana sawun yadda zan ji daɗin fira,
: Duniya sai an yi
hanƙuri,
: Duniya in babu hanƙuri,
: Al’amarin wani ba ya gyaruwa sam-sam-sam.
Gindin Waƙa: Allah Mai Dama Mai Hagu Gatana.
Mainasara, A.(2016: 164)
Aikata alheri ga kowa da yin haƙuri a cikin al’amura na rayuwa, su suke sa al’amura su gyaru, rasa waɗannan yana kawo tashe- tashen hankula da taɓarɓarewar tsaro.Ɗanƙwairo yana cewa:
Jagora: Arziki shi ad da daɗi,
: Talauci bai da daɗi
: Yana kawo turobul,
Y/Amshi: A ɗora hwaɗa da mata
: Kak ka sake a ram
ma,
: Sa’idu shirin ka ya yi.
Jagora: Wannan ya cuta ma,
‘Y/Amshi: Kai nai,
Jagora: Ka ga ƙato ba ya noma,
:
Ba aikin gwamnati.
:
Bai aikin Local Government
: Kuma bai sana’a,
:
Yana yawo da gangan
:
Irinsu ka ɗibga
sata,
:
Suna,
‘Y/Amshi:
’Yan sace-sace,
Jagora: : Irinsu ka ɗibga ɓanna,
:
Suna ‘yan sace-sace
:
Suna ta,
‘Y/Amshi : Kashin mutane,
Jagora: Suna ta kashin,
‘Y/Amshi : Mutane,
:
Ɓanna ta ku kai,
‘Y/Amshi : Ba fa gyara ne ku kai ba,
G/Waƙa: Ayi aiki na gaskiya,
:
Kam mu ɓatad
da kanmu
(Gusau, 2019: 435)
Wadata daɗi ne da ita. Wadatar abinci da sutura da muhalli ga jari
ga kuɗin ɓatarwa. Kishiyar wadata shi ne kai tsaye makaɗin ya faɗi zaman kare a karofi da mutane suke yi, wato babu noma, babu
wata sana’a, babu ilmin zamanin da za a yi aiki irin na gwamnati, su ne suke haddasa
talauci. Dubi yadda makaɗin yace turobul (trouble), ɓarna kowace iri ta shiga ƙarƙashin wannan kalma,
sace-sacen jama’a don neman kuɗin fansa da fitintinu da tayar-da-zaune- tsaye da kisan jama’a.
Idan al’umma ta samu kanta a haka, to tsaro ya lalace ke nan, babu shi.
A wani wuri kuma makaɗan kan yi tunasarwa da jan hankali ga nauyin da yake akan
hukuma da duk wanda jagorancin jama’a ya ke hannunsa, yadda za a tunkari matsalar
rashin tsaro. Ɗanƙwairo yana cewa:
Jagora: Ko daɗai gyara ba ya,
‘Y/Amshi: ɓanna.
Jagora: Ko daɗai mai gyara ba ya ɓanna,
‘Y/Amshi: Ko daɗai mai gyara ba ya ɓanna,
Jagora: Ku manyan Sarakuna ,
: Ham manyan da ƙanana,
: To ku ko dagattai,
: Alhakin jama’a na gare ku,
: Ku ne iyaye,
: In talakkawanku ya yi ɓanna,
: Ko ko sun kai faɗa,
: Ƙara ku zo garinsu,
: Ku je ku tara su wuri ɗai,
: Ku sasanta su,
: Kada ku gama su gaba,
: Kada ku gama su
‘Y/Amshi:
Gaba.
Jagora: In kuma sunka ƙiya,
: Ƙara ku je ku koma,
: Ku je ku sasanta su,
: Kada ku gama su gaba,
: In dai kuma sunka ƙiya
: Ƙara ku je ku koma,
: Ku je ku sasanta su,
‘Y/Amshi: Kada ku gama su ɓanna,
: In kuma har sunka ƙiya,
: Na san halin talakka,
: Halin jaki gare shi,
: Ku rarrabkai da gora,
: Yas san,
‘Y/Amshi: Mulki yana nan
: Ku rarrabkai,
‘Y/Amshi: Da gora ya san mulki yana nan.
G/Waƙa: A yi aiki da gaskiya,
: Kam mu ɓatad da kanmu.
(Gusau,
2019: 436-437)
A musulunci akwai hanyoyi guda uku da ake bi wajen gyara ɓarna, su ne: hannu da baki da zuciya. Shugabanni su ne suke da damar bin
hanya ta farko don gyara ɓarna a tsakanin talakawansu, kamar yadda makaɗin ya nuna. Barin Jaki ana dukan taiki da gangan shi ya ƙara ta’azzara
rashin tsaron da ake fama da shi a jihar Zamfara. Sannan ya ƙara jaddadawa
shugabanni nauyin da yake a kansu na horo da kyakkyawan aiki da hani ga aikata
mummuna. Ya ce:
Jagora: Riƙe talakkawanka da kyawo,
: Kai musu hairi,
: Ka sa su hanyoyin Musulunci,
: In sun hamɓare ka tanƙwaso su,
‘Y/Amshi: In ko sun ƙiya a ba su kashi.
: Wani lokaci, talakka,
: Bai san talaka
bai san talakka ne ba.
G/Waƙa: Babban Jigo na Yari,
: Uban Shamaki tura haushi
(GusauS.M.2019: 245)
Haka kuma makaɗan sun yi abin da Bahaushe yake cewa hannunka ba ya ruɓewa ka yanke kayar, domin
a wurare da dama sun yi nasiha ga masu haddasa tashin hankali da samar da
rashin tsaro da irin abin da yake jiran wanda bai tuba ba. Misali:
Umaru Maisa’a Tubali,
Isa yana cewa
Jagora: A yi dai tahiya ga hili
nan,
‘Y/Amshi: Nan ya ji daɗi,
: Can ya yi kuka,
: Kaya cike ba mai amsar mai.
Gindin Waƙa: Kai munka sani Iro Sadauki,
: Gwarzon Ajiya mai Badarawa.
(Gusau, S.M.2009: 174)
Bahaushe na cewa “ abin da mutum ya shuka shi zai girba”,
makaɗin na nuna duk abin da mutum ya aikata na rashin daidai, yana ganin ba komai ba
ne, to yana nan an rubuta masa, zai tarar da shi a lahira, inda zai yi nadama
don ganin munin abin da ya aikata.
Wannan wa’azi ne babba, ga ‘yan ta’adda da masu garkuwa
da mutane don samun kuɗin fansa, da suke jin daɗi na dukiyar da suke karɓa, amma a lahira za ta zame musu baƙin ciki don tarin zunubi
mai nauyi wanda ba su da mai taimaka musu ɗaukarsa. Wannan
magana ta dace da faɗin Allah mai girma da ɗaukaka da yake cewa: “Wanda duk ya aikata wani kyakkyawan aiki , daidai da ƙwayar komayya zai
gan shi. Haka kuma wanda ya aikata wani mummunan aiki kwatankwacin ƙwayar komayya zai
gan shi.” (Sura ta 99: Aya ta 7-8)
Salihu Jankiɗi kuma ya ce:
Jagora: Kowad dama hura da haki ciki,
‘Y/Amshi: Ga garin toka ya sanya,
: Ga garin taba ya sanya,
: A tsare shi ya sha shi yay yo ta.
Gindin Waƙa: Na Shimfiɗa sarki yai nasara,
: Allah daɗa girman dattijo.
(Gusau, S.M. 2002: 155)
Makaɗin na yin kira in an tashi yin hukunci, ‘kowa ya ɗebo da zafi bakinsa.’ Kada a riƙa hukunta talaka ana barin masu hannu da shuni, ko masu uwa a gindin murhu.
Daga abubuwan da suke faruwa na rashin tsaron nan, ana ganin yadda ake kasa hukunta
wasu dake da hannu a ciki, saboda wani matsayi ko wata dangataka tasu.
Sani
Sabulu kuma ya ce:
Jagora: Wanda yay yi ma sheri,
: Shi yaka liƙewa.
Sanƙira: Ana ko magana!
Mainasara, A. (2016: 160)
Idan abubuwa suka kai inda suka kai, wanda aka zalunta ya
rasa mai karɓa masa haƙƙi, sai ka ji ya yi
‘Allah Ya isa’. A wannan ɗan waƙa makaɗan na haƙurƙurtar da waɗanda aka zalunta, a hana su ɗaukar fansa, su kuma sa a ransu cewa wanda duk ya aikatamusu
wani abu na ta’addanci to a ƙarshe mummunan
aikinsa a kansa kaɗai zai koma. Haka kuma wannan ɗan waƙa yana iya zama
gargaɗi ga masu cutar da jama’a su ji tsoro tun da abin da ya
je shi yake komowa.
Maidaji
Sabon Birni kuma yace:
Jagora: In zama yai daɗi mutane ka ɓata shi,
:
Tun da ban cuci mutum ba, to kar ya cuta min,
:
In kuma ya cuce ni Allah shi rama min.
A nan makaɗa Maidaji Sabon Birni yana nuna wa jama’a su za su yi
tattalin zaman lafiya, hakan kuwa ba zai samu ba sai kowa ya kiyaye haƙƙin ɗan’uwansa, abin da baka son a yi maka to kar ka yi wa wani, kamar yadda
Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi, ya ce:
Imanin ɗayanku ba zai cika
ba, har sai ya so wa ɗan’uwansa abin da
yake so ga kansa.
Idan kuma aka cutar da kai to sai ka miƙa kukanka ga Allah,
kamar yadda makaɗin ya nuna:
Jagora: In kuma ya cuce ni Allah shi rama
min.
4.0 Sakamakon
Bincike
Al’adar
Bahaushe ta ilimantar da shi ayyukan da idan ya aikata su yana iya karya masa
al’amarinsa. Daga cikinsu akwai ƙiyayya da gaba da jahilci. Kamar yadda
ya san haƙuri da yin gaskiya da aikata alheri
suna daga maatakan da zai ɗauka su samar da tsaro, cikinsu akwai
waɗanda yake iya ɗauka a kan kansa da waɗanda ya ɗora wa shugabanni nauyin samar masa da su.
A
sakamakon binciken an samu cewa waƙoƙin makaɗan bakan Zamfara suna nusarwa da
tunatarwa da al’umma na abubuwa da za su naɗa da waɗanda za su kauce wa wajen samar da tsaro.
5.0 Kammalawa
Wannan takarda ta yi ƙoƙarin bayanin gudummawar
da makaɗan baka na ƙasar Zamfara suke
bayarwa na samar da tsaro ga al’umma, kamar yadda ya zama wajibi a kan kowa ya
bayar da irin tasa. Bahaushe ya ce “Sandar da take hannunka da ita kake duka”. Mun ga yadda makaɗan suka nuna aikin da talakawa za su yi
da wanda shugabanni za su yi don samar da tsaro, ta yadda tsaro zai tabbata, al’umma
ta yi walwala, arziƙi ya kewaya, idan ka ji daɗin waƙar da suka yi, ka ba
su rabonsu. Ina amfanin baɗi ba rai?
Aikin samar da tsaro ba aiki ne na mutum ɗaya ba, kowa sai ya bayar da gudunmuwa gwargwadon abin da yake da shi kamar
yadda makaɗa suka yi. Hukuma kuma ta sani doka kaɗai ba ta samar da
tsaro, ita ce ma mataki na ƙarshe da za a ɗauka. A maimakon haka
a nuna wa mutane sanin mutuncin ɗan’Adam da ba wa kowa haƙƙinsa.
Manazarta
1. Abba, M. &
Zulyadaini, B. 2000. Nazari kan Waƙar Baka ta Hausa. Gaskiya Coorporation Limited.
2. Gusau, S.M 2019 Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Huɗu. Kano: Century Research and Publishing
Limited.
3.
Gusau, B.M da Gusau, S.M 2012 Gusau ta Malam SamboKano: Century Research and Publishing Limited.
4. Gusau, S. M. 2011. Adabin Hausa a Sauƙaƙe. Kano: Century Research and Publishing
Limited.
5. Gusau, S.M. 2009 Diwanin
Waƙoƙin
Baka (Littafi na Ɗaya). Kano: Century Research and
Publishing Company.
6. Gusau, S.M. 2002 Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi.Kaduna: Baraka Publishers Limited.
7.
Gusau, S.M. 1996.
Makaɗa da Mawaƙan Hausa (Littafi
na Ɗaya). Kaduna: Fisbas
Media Services
8. Gusau, S.M. 2015. Mazhabobin Ra’i da Tarke A Adabi da Al’adu
Na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.
9. Mainasara, A. 2016. “Nazarin Adon Harshe a Waƙoƙin Sani Sabulu Kanoma
(1957-2000)” Kundin Digiri na Biyu.
Kano: BUK
10. Yahya, I.Y 1973. “Tarihin Adabin Hausa: Ma’anar Adabi”.
Maƙala wadda ya Gabatar a Kano. Jami’ar
Bayero, Kano.
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.017
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.