Ticker

6/recent/ticker-posts

Amon Gangumma Domin Zaman Lafiya a Arewacin Nijeriya (Drums For Peace By Northern Nigerian Oral Singers)

This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.

Alh. Ibrahim Muhammad

(Danmadamin Birnin Magaji)

Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin Magaji (Dan Alin Birnin Magaji), Zamfara, Nigeria

08149388452

birninbagaji4040@gmail.com

Tsakure

A wannan takarda, an tattauna matsayin makaɗi ko mawaƙi a cikin alummar Hausawa. Sa’annan an yi ƙoƙarin waiwayen wasu daga cikin alƙaluman da tarihi ya naɗe a fagen faɗakarwa kan amfanin zaman lafiya. Tattaunawa kan misalan waƙoƙin da aka kalato, domin nuna tasirin waƙar baka wajen tabbatar da zaman lafiya shi ne ƙashin bayan wannan takarda. An kammala da bayyana ra’ayin mai wannan takarda.

 

1.0     Shimfida

Idan aka waiwayi tarihin yaƙe-yaƙen da suka wakana tsakanin al’ummun ƙasar Hausa, za a iya kallonsu ta fuskoki da dama, amma ma fi karɓuwa shi ne, domin a kara faɗin ƙasa, a samu bayi da abinci, wata daula ta mamaye wata daular. Da wannan za a ga ko a wancan zamanin da ake irin waɗannan yaƙe-yaƙe ana jikkata al’ummar da ba su da ƙarfi, wasu kuma a ƙangi na bauta suke mutuwa; hasali ma, jelar bauta kan bi zuri’arsu tsawon lokaci. Babu shakka da wuya ka samu dan Arewacin Nijeriya yana alfahari ko bugun gaba da cewa shi ko iyayensa bayi ne, sai ta kama dole ne za a faɗa, kuma ya yi shiru domin ƙyamar bautar. Da wannan shimfidar za a kalli yadda ƙoƙarin gina wani sashe na alumma ke cutar da wani sashe na alumma. Kuma da haka manyan dauloli na ƙasar Hausa ko ma a ce na Afirka suka ginu. Wannan tsokaci ba zai manta da yanayin da Nijeriya ta shiga ba, a lokacin yaƙin basasa a tsakanin shekarun 1967-1970 wanda ya jefa al’ummar yankuna da dama cikin tagayyara na rashin abinci da salwantar rayuka da rashin kwanciyar hankali. Duk wannan watayar ana son a lalabo fahimtar waƙar baka na ƙasar Hausa kan wannan yanayi da al’umma kan shiga na jirkidiri, da tagayyara a lokuta na tashin hankali. Kafin a waiwayi misalan tashin tashinar da suka gabata kan wannan yanayi, yana da amfani a san ma’anar tashin hankali, da kuma zaman lafiya.

 

2.0     Ma’anar Zaman Lafiya

Zaman lafiya shi ne rashin wanzuwar tashin hankali, ko yaƙi, ko rashin jituwar da kan iya haifar da tarzoma a cikin al’umma. Zaman lafiya kan tsaya matsayin aminci da salama. Idan mai rubutu ya farga da kalmomin da aka zuba domin bayyana ma’anar zaman lafiya, za a fahimci duk abin da ba zaman lafiya ba, to shi ne tashin hankali. Inda kuma babu tashin hankali, to hankalin yana kwance, zukata na jin daɗin tafiyar da alamurransu na kowane fanni na rayuwa. Ƙarin fahimta a nan, shi zaman lafiya, ana iya fassara shi da sha’awar mutum, ko mutane, inda za a ga cewar idan buƙatun mutum ko na jamaa sun samu yadda suke so, to su kam sun samu zaman lafiya. (Misali Ma’aurata)

 

2.1 Ma’anar Rashin Zaman Lafiya

 

Tashin hankali shi ne rashin zaman lafiya. Ko rashin samun biyan buƙatun rayuwa saɓani, rikici da tashin hankali. Idan fari (rashin abinci) a dalilin rashin ruwan sama, ko ƙafewar teku ko gulabe ya faru, to sai jama’a su shiga tashin hankali saboda rashin abinci. Rashin abinci kan haifar da rashi na rayuwa. A lokacin cutar murar mashako 2019 (COVID-19) al’ummar da wannan cutar ta shafa, sun tagayyara saboda tashin hankali.

Al’umma kan kasance ko dai cikin kwanciyar hankali (zaman jin daɗi), ko kuma cikin rashin zaman lafiya, wato tashin hankali.

3.0 Bitar Wasu Daga Tashin Tashina na Arewacin Nijeriya

 

A ƙaƙashin wannan taken an bibiyi tarihin tashin tashinar da suka taɓa faruwa a Arewacin Nijeriya, da kuma tasirin da wannan tashin tashinar ta haifar ga al’umma wanda wannan al’amari ba zai rasa nasaba da halin da Arewacin Nijeriya yake ciki ba a yanzu. Alal misali;

 

1.       Rashin jituwa tsakanin ƙabilar Tibi da ke Jihar Binuwai da takwarorinsu 'yan ƙabilar Jukun da ke Jihar Taraba, sanadiyyar ƙasar noma da muhalli da kuma tsoron mamaya ya kawo ɓarkewar tashin hankalin da ya tilasta wa waɗannan ƙabilu guda biyu ɗaukar makamai domin gwabzawa a tsakaninsu a cikin shekarar 1959. Faɗan ya sake afkuwa a cikin 1980 da 1990 da 2001.An yi hasarar rayuka da dukiya mai tarin yawa. Joshua, (2016).

2.       Sanadiyar matsalar ƙabilanci da bambancin addini da tattalin arziki da sha'anin siyasar mulki , Laftanal Kanal Odumegwu Ojokwu ya jagoranci yankin Gabas na Nijeriya wajen yaƙin basasa da Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya. Yaƙin da aka soma ranar 6 ga watan Yuli na shekarar 1967, sai da aka kwashe shekara biyu da wata shida da sati ɗaya da kwana biyu ana fafatawa, kafin a kawo ƙarshensa a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1970. Janar Yakubu Gowon ne ya jagoranci yaƙin daga gefen Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya. Shi ake kira da yaƙin Biafra ko yaƙin basasa na Nijeriya da ya laƙume rayuwar fiye da mutum miliyan ɗaya.

3.       Wani misalin kuma shi ne, wani tashin hankali da ya faru a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, ranar 17 ga watan Afrilu na shekarar 1978, wanda aka yi wa laƙabi da 'Ali Must Go'. Ƙungiyar ɗaliban Jami'ar a ƙarƙashin jagorancin Mista Segun Okeowo ne ta fito domin nuna rashin amincewarta da ƙarin kuɗin makaranta da aka yi a lokacin. Kanal Ahmadu Ali ne Ministan ilmi na Nijeriya a lokacin, shi ne dalilin da ya sa ake kiran wannan rikici da 'Ali Must Go '. Ɗalibai 8 ne suka rasa rayukansu da wasu Jama'ar gari.

4.       An samu rikici a garin Kafanchan a Jihar Kaduna a shekarar 1987, wanda ya faru ne sanadiyar rashin fahimta tsakanin jama'ar da ke zaune a yankin (Hausawa da sauran ƙabilun da ke cikin masarautar Jema'a, mai hedikwata a garin Kafanchan, Jihar Kaduna). An yi hasarar rayukan mutane 19 da Otal 169 da Coci 152 da Masallatai 5.

5.       Rikicin addini na Muhammadu Marwa da aka fi sani da suna 'Maitatsine' a Kano ya faru tsakanin 18 zuwa 29 ga watan Disamba na shekarar 1980. A wannan rikici Muhammadu Marwa Maitatsine ne ya soma yaƙar gwamnati, domin abin da ya kira 'rashin amincewa da ita'. An yi hasarar rayuka kimanin 4, 500 bisa ga ƙididdigar gawar da aka samu a wurin ajiye gawa na asibitoci a lokacin.

6.       Haka kuma, an samu tashin hankali a garin Funtua da kewaye a farko-farkon shekarar 1994, tsakanin al'ummar gari da wasu baƙin mutane da ake kyautata zaton gyauron mutanen Maitatsine ne . An yi hasarar rayuka masu yawa.

7.       Wannan bibiyar tarihin wasu daga cikin tashin tashinar da suka faru a Arewacin Nijeriya sun faru ne sakamakon wasu dalilai na rashin fahimta a tsakanin jama’a, ko kuma wasu jama’a masu halayya ta rashin son zaman lafiya su zama kashin bayan haddasa rashin fahimtar da zai kawo tashin tashina. Ana iya kuma amfani da ɓangaranci na ƙabilanci, ko wata matsala da ta faru al’umma suka koka amma ba a samu sauƙin al’amari ba, wanda matsuwa kan sa su yi fito-na-fito da junansu ko shugabanninsu, ko kuma da hukuma.

 

4.0 Samfurin Waƙoƙin Zaman Lafiya na Makaɗa da Mawaƙan Ƙasar Hausa

 

A ƙarƙashin wannan taken, an tsakuro samfurin waƙoƙin da makaɗa da mawaƙa musamman waɗanda suka fito daga yankin Arewacin Nijeriya, suna kira ga jama’a kan amfanin zaman lafiya. Misali

Mawaƙi: Alh. Musa Ɗanƙwairo Maradun

 

JAGORA: Zama lahiya shi ad da daɗi,

Allah yai muna tsari,

 

‘Y/AMSHI: Zama lahiya shi ad da daɗi,

Allah yai muna tsari,

 

JAGORA: Babu ƙasa mai daɗin ƙasammu,

Gamu da gero gamu da dawa,

Gamu da maiwa gamu da wake,

Ga shinkahwa ga masara,

 

‘Y/AMSHI: Akwai hikima ta abinci,

Ƙasammu ko wane kasso, shi ka kai ta ci,

Zama lahiya shi ad da daɗi,

Allah yai muna tsari,

(Waƙar Zaman Lafiya ta Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun)

 

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo yana ganin Allah ya wadata ‘yan Nijeriya da abinci iri-iri, wannan wadata ta abinci ai ba abinda ya fi hakan samun kwanciyar hankali, kamar mutum duk abin da yake so ya ci, zai noma ya kawo a sarrafa a ci.

Mawaƙi: Mammalon Shata

 

JAGORA: ‘Yan Nijeriya,

mu shirya zaman Nijeriya, mu ji daɗi,

 

JAGORA: Inji Gwamnonin ƙasa,

mu shirya zaman Nijeriya, ya yi daidai,

 

JAGORA: Kowa Allah ya ba,

A bishi a zauna lafiya, A yi komai,

 

JAGORA:   Talakkawa nai kira,

Ku bar cika ‘yan zantuttukan mu na banza,

(Waƙar Zaman Lafiya ta Mammalon Shata)

 

Mammalon Shata ya yi kira ga talakawa da su bar duk wasu kalamai da za su kawo tashin tashina a cikin al’umma. Shugaba zaɓin Allah ne, duk wanda ya zama shugaba, sai a goya masa baya. Wannan shi ne zaman lafiya.

Mawaƙi: Dr. Mamman Shata Katsina

 

JAGORA: Ay zama lafiya,

‘Yan Nijeriya.

 

‘Y/AMSHI: Ay zama lafiya,

‘Yan Nijeriya.

 

JAGORA: ‘Yayan Yarabawa

Hatta Ibo,

Hausawa ku da Barebari,

Hillani hay ya zuwa Tibi,

Ay zaman lafiya,

Shi ne yaf fi kyau.

 

JAGORA: Manya da yara ƙanana duka,

Mata da maza kun ji, Mun gargaɗi,

Ay zaman lafiya, Shi ne ya fi kyau,

 

JAGORA: A bar yin tunani,

Ana waiga baya,

Komi ya zo anka ce ya wuce,

Dangi ku bar son kuna tuntuna shi,

Zaman lafiya shi ne ya fi kyau.

 

Waƙoƙi uku (3) da aka zuba a sama ta Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, da Mammalon Shata, da kuma Alhaji Mamman Shata Katsina duk an samar da su ne bisa kiran da Shugaban Ƙasar tarayyar Nijeriya ya yi na cewa, su ma makaɗa da mawaƙa su tashi su ba da tasu gudummawa wajen ganin Nijeriya ta samu zaman lafiya. An yi waɗannan waƙoƙi a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1975 a lokacin da aka gama yaƙin basasar Nijeriya, wanda haɗin alummar Nijeriya shi ne abu na farko da gwamnati ta sa a gaba.

 

Mawaƙi: Alhaji Shehu Ajilo Ɗanguzuri

 

JAGORA: Allah wahidun,

ka taimaki ‘yan Nijeriya,

Ƙasarmu ta zauna lafiya,

Baki ɗaya.

 

JAGORA: Babangida ya yo ɗamara,

Sani Abacha ya yo ɗamara,

Domin haɗa kan Nijeriya, baki ɗaya.

 

JAGORA: Wanne bambanci a kai,

Har Yarabawa, har izuwa Ibo,

Ku zo mu taru muzauna lafiya baki ɗaya.

 

JAGORA: Babu zama gun mai kiɗa,

don sojoji sun ɗammara, hatta kwastan sun ɗammara,

Ga ‘yansanda na ɗammara,

Imagireshin sun yo ɗammara,

Har Nebi sun yo ɗammara.

Domin haɗa kan Nijeriya,

Baki ɗaya.

 

Mawaƙi: Dr. Adamu Ɗanmaraya Jos

 

JAGORA: Barebari Fulani,

Manyan abokan fa wasa,

Wasanku ba zage-zage,

Wasanku ba doke-doke,

Sai dai ƙoƙarin zumunta.

 

Barebari Fulani,

A cikinku wa ah hwa babba,

 Idan da babba,

Wallahi yau ga ni ga ku,

Sai ku faɗi a yanzu,

Mawaƙi: Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai

 

JAGORA: ‘Yan Nijeriya

‘Yan uwa mu yi ƙoƙari,

Mu zan haɗa kammu,

Mu kama hanyar gaskiya.

 

JAGORA: Kifi da kada,

Da kwaɗo da tsari dorina,

Halittassu daban-daban,

Amman in mun tuna

 

‘Y/AMSHI: Dug gidansu,

Yana ruwa, ‘yan Nijeriya,

‘Yan uwa muyi ƙoƙari,

Mu zan haɗa kammu,

Mun kama hanyag gaskiya,

 

JAGORA: Ina Yarabawa,

Ina Nuhwawa,

Ina Jama’ar Ibo,

Had da ku jama’at Tibi,

 

‘Y/AMSHI: Dum mu taru,

Mu je gaba dai,

Mu komayanuwa,

‘yan Nijeriya,

‘Yan uwa mu yi ƙoƙari,

Mu zan haɗa kammu,

Mu kama hanyag gaskiya.

 

JAGORA: Kun gani Nijeriya,

Mai yawan faɗin ƙasa,

Al-adummu daban-daban,

Addinnanmu daban-daban,

Allah mai ƙaddarowa,

A kowane al-amar,

 

‘Y/AMSHI: Shi yaƙƙaddaro,

Munka zamni wuri ɗaya,

Kuma ƙasanmu tana ɗaya, ‘yan Nijeriya,

‘Yan uwa mu yi ƙoƙari,

Mu zan haɗa kammu,

Mun kama hanyag gaskiya.

 

JAGORA: Kam mu yadda da ‘yan baranda,

Da ‘yan zambar ciki,

Masu son su haɗa mu ɓanna,

Su koma tsallake.

 

‘Y/AMSHI: Idan ta rikkice,

Su buƙata ta biya, ‘yan Nijeriya,

‘Yan uwa muyi ƙoƙari,

Mu zan haɗa kanmu,

Mu kama hanyag gaskiya.

 

Mawaƙi Shehu Ajilo da Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos da Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai sun bi sahun su Alhaji Musa Ɗanƙwairo wajen kiran alumma, da a fahimci babu ƙasar da za ta ci gaba, al’ummarta su samu bunƙasa, sai in akwai zaman lafiya da ƙaunar juna.

5.0 Tattaunawa

 

Kusan kowace al’umma tana da tarihi. Ko da al’ummar nan ba su iya tuna asalin tarihin kafuwarsu, to suna iya yin kintaci-faɗi ko labarin kunne-ya-girmi-Kaka. Ta kowace fuska za a bi ko ta nazarin harshe ko ta nazarin al’adun mutane, ko ta yanayin muhallin da jama’a suke zama, ko siyasar jama’a, idan dai za a bi diddigin tarihin duk wata al’umma da ke da al’adu a matsayin hanyar tafiyar da rayuwarsu, to lallai sai a lalubi ƙumshiyar adabinsu na baka, wanda waƙoƙin baka suna daga ciki. Waƙoƙin baka, da maganganun hikima da azanci na kowace al’umma, su ne rumbun tarihin wannan al’umma. Idan za a bi diddigin tarihin yadda al’ummar Hausawa suka rayu tsawon zamunna, to lallai sai an haɗa da adabinsu na baka, musamman waƙoƙin baka. Misali Yaƙe-yaƙen da suka wanzu kafin kafuwar manyan daulolin ƙasar Hausa, za a tarar mawaƙan baka sun taka mhimmiyar rawa wajen zuwa filin daga na yaƙi su gwarzanta mayaka. Haka manyan sarakuna musamman waɗanda suka mulki daulolin ƙasar Hausa (Kabi da Zamfara) duk suna da fitattun mawaƙa.

Fitattun mawaƙan zuriarsu sun rike waƙar baka har zuwa wannan zamani. A wannan shimfiɗa an ga cewa tun wajen kafuwar al’umma mawaƙi yana da nasa gurbin da babu mai iya mayewa sai dai shi kansa ko waninsa mawaƙi (mai gadonsa ko mai haye). Bayan kafuwar alummar Hausawa, mawaƙi ya samu matsayin malami16 mai wayar da kan jama’a idan kowane al’amari za a wanzar, sai mawaƙi ya tallatar da wannan alamari ga jamaa. Kowane fanni na rayuwar al’umma za a tarar mawaƙi kan shiga wannan gonar ya waƙe wannan al’amari, ya karɓu ga jama’a. Da wannan aka samu rukunnan mawaƙan baka da rubutattu masu yin waƙoƙi da jigogi mabambanta17

Mawaƙa tsofaffin hannu, da na zamani sun yi iyakan ƙoƙarinsu (a lokutta daban-daban) wajen kiran jama’ar Nijeriya baki ɗaya kan su zauna lafiya. A ƙunshiyar waƙoƙin kamar yadda aka gani a sama, matanin wasu daga cikin waƙoƙi ne masu ɗauke da addu’o’i da kiraye-kiraye ga jama’a ta sigogi da salailai masu ban sha’awa, da jigon zaman lafiya tsakanin ƙabilun Nijeriya masu bambancin al’adu da addinai. Waƙoƙin sun yi tasiri ƙwarai a wancan zamani, yanzu kuma sun zama abin sauraro da misalai. Fashin baƙin hakan yana biye a ƙarƙashin naɗewa.

Tasirin da waɗannan waƙoƙi suka yi an gan shi a cikin waƙar Alhaji Musa Ɗanƙwairo (Waƙar ‘Yan Arewa Godiya dai mukai, Allah ya maimaita mana ga Jihar Arewa mai halin girma) inda ya nuna cewa

Gwamnatin Arewa ta Marigayi Sardaunan Sakkwato, Sir. Ahmadu Bello ta kawo ayyukan ci gaba a wasu yankuna na Arewacin Nijeriya. Misali a Sakkwato an yi Kamfanin Siminti, akwai Kamfanin gyaran motoci na Abdallah a Gusau, a garin Kano an kafa Kamfanoni na yin kwanon rufin gidaje da kwanonin cin abinci kuma a Kanon ake yin alewar lemu. Wannan ya nuna cewa mawaƙa suna gabatar da buƙatocin jama’arsu ga sarakuna da masu mulki. Mawaƙan kuma su ke tunatar da sarakuna da masu mulki na zamani a kan su cika alƙawuran da suka ɗauka na yi ma jama’a aiki. Idan aka samar da waɗannan ayyukan to sai mawaƙan su koma su sanar a waƙe irin hidimar da sarakuna da masu mulkin suka yi kamar yadda waƙar ta nuna.

6.0 Naɗewa

Naɗe tabarmar wannan tattaunawa za ta ɗauki wani salo ba na bitar abin da aka bayyana a cikin wannan maƙala ba, sai dai bayyana ra’ayin mai nazari a cikin ƙunshiyar wannan maƙala. Mawaƙa na da, da na yanzu sun taka rawar gani kuma suna kan takawa wajen ilmantar da al’umma. Ana iya cewa kowane al’amari ba ya samun karɓuwa sai da mawaƙa. Amma kuma wani abin ban haushi na daga ɓangaren al’ummar Hausawa ta yanzu, duk wani abin da mawaƙi zai faɗi, ko da kuwa na faɗakarwa kan shiga haɗari ne, sai ka ga an yi biris da lafuzansa na hikima an kuma afka ga haɗarin. Misali, duk kiran da su Ɗanƙwairo da Ɗanba’u suka yi, cikin lafuzzan hikima da zayyanawa, amma bai hana al’ummar Hausawa da na Fulani suka afka cikin halin da suke ciki yanzu ba. Idan nusarwar da Ɗanmaraya Jos ya yi wa Barebari da Fulani cewar manyan abokan wasa ne tsawon daɗewa, ga auratayya ta shiga tsakaninsu har an mayar da su ƙabila ɗaya a matsayin Hausa-Fulani, shin me ya kawo muguwar tsana a yanzu har suka fara yi wa juna duka da zage-zage?

Kasancewata ma’aikacin nemowa da watsa labarai, ya saka na tsinci wasu bayanai a kan wannan sana’a tawa na ikirarin da Hausa-Fulani ke yi na cewar sun sha Arkanai (kaskanci da wulakanci da Zalunci) a hanun wasu ƙabilu na Arewacin Nijeriya, kamar Hausawa da Birom da Tibi da Kanuri tsawon lokacin da har aka ƙure haƙurinsu. Da tura ta kai bango, sai suka fara kai ƙarar cin zarafin da ake yi masu ga magabata a hukumomi, duk da haka sai shari’a ta yi musu yankan ciki da yankan baya, da haka nan suka sake ɗaukar matakin a mutu duk. Wato yanzu za su ɗauki fansa.

Kafin in kakkaɓe tarbarmar da na naɗo, ina son in bayyana irin koken da Hausa-Fulani suke yi:

i.            Gwamnatoci ba su kula da lamurran jin daɗin talakawa ta fuskar biyan buƙatun rayuwa

ii.        Jami’an tsaro kan tare iyalan Hausawa a hanyarsu ta zuwa kasuwa, ko wurin buki ko dai wata hanya su wulaƙanta su, kuma su ƙwace wasu daga cikin dukiyoyinsu

iii.    An karɓe burtalolin da Hausa-Fulani suke kiwon dabbobinsu; an mayar da waɗannan burtalolin gidaje da gonaki ko wajen wasu hidimomin rayuwa18

iv.     Akwai ‘yan leken asiri masu ɗauko sirrin talakawa ko wasu al’ummu zuwa ga shugabannin da suke da mugun nufi kan talakawa

Waɗannan koke-koke suna daga cikin abin da ya sa Nijeriya ta Arewa take cikin halin da take ciki a yanzu, wanda wannan yanayi ya fi ƙarfin muryar mawaƙi wajen faɗakarwa. Babu wani amo da zai tashi sama, na waƙa da zai sa shugabanni su yi wa waɗannan alumma adalci. Dalilin cewa hakan shi ne, babu waƙoƙin da za a maimaita ko a samar, da suka fi waɗanda mawaƙanmu na baka da rubutattu suka samar, amma aka kasance a halin da ake a yanzu. Masu mulki ba su sauraren kiran mawaƙi, haka nan talakawa da matasa sun mayar da mawaƙi abin samar da kiɗa da waƙa domin nishaɗantarwa. Abin ya zama tamkar a sha ruwa a koma wasa.

 

Manazarta

Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Government Printing Press, Katsina.

Birnin Magaji, I.M (2018). “Duniyar Makaɗan Fada Jiya da Yau. A Cikin Taguwa Multi- Disciplinary Journal of Humanities Katsina: Umaru Musa ‘Yar’aduwa University, Katsina.

Birnin-Magaji, I. M. (2020). Ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗan Baka, 1900-2000”, Maƙalar da Aka Gabatar a Taron ƙara wa Juna Ilmi kan Daular Zamfara, Wanda Tsangayar Fasaha ta Jami’ar Usumanu Danfodiyo ta Shirya a ranakun 27-29 ga Fabrairu.

Birnin Magaji, I. M (2020). “Makaɗa Ibrahim Narambaɗa A Fadojin Ƙasar Hausa Takardar da aka gabatar a taron Ƙasa da Ƙasa Kan Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali, A Jami’ar Bayero Kano Ranar 15-17 ga Watan Satumba ,2019.

Birnin Magaji, I. M. (2020). “Sauye-Sauye na Ci Gaba ga Manyan Masarautun Jihar Zamfara1900-2000 (The Transformation of Emirates in Zamfara State). (1900- 2000).” Maƙalar da Aka Shirya Domin Bugawa a Mujallar da ake Shiryawa Shekera-Shekara a Tsangayar Fasaha da Ilmin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usumanu Danfodiyo, Sakkwato.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano, Ahmadu Bello University Press, Zaria.

Chafe, K. (2016). “Jihar Zamfara: Tarihinta da Ƙalubalenta da Ribatarta a Tarayyar Nijeriya” Maƙalar da aka Gabatar a Taron da Gwamnatin Zamfara ta Shirya na Cikar Jihar Zamfara Shekarau Ashirin da Kafawa wanda aka Gudanar a watan Oktoba 2016, a Gusau, Jihar Zamfara.

Danjuma, M.S. (1982). “Gudummuwar Waƙoƙi ga Rayuwar Bahaushe” Takardar da ya Gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.

Gusau, S. (1984). “Nazarin Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Baka na Hausa Cyclostyled Edition, Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Gusau, S.M. (1988). Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye-yanayensu. Kundin Digiri na Uku, Jami’ar Bayero, Kano

Gusau, S. (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa, Bench Mark Publishers, Kano.

Gusau, S. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya, Bayero University, Kano Inaugural Lecture no 14.

Gusau, S. M. (2019). Diwanin Waƙoƙin Baka Juzui na Huɗu Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun (1909-1991)., Century Research and Publishers, Kano

Infakul Maisuri: Taƙaitaccen Tarihin Ƙasashen Tukururu na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, Fassarar Sidi Sayudi da Jean Boyd, (1974). Longman, (2003). Active Study Dictionary, Edinburg Gate.

Sani, A. R. (2019). “Nazarin Salo a Cikin Wasu Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo Maradun, Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Tambuwal, I. (2002). “The Facinating Emirates of Zamfara State, Matani kan Tarihin Masarautun Zamfara” da ke Jiran Dab’i. A Publication of Zamfara State Council of Chiefs.

 

 

Ratayen

Samfurin Waƙoƙin Zaman Lafiya Daga Makaɗa da Mawaƙan Ƙasar Hausa

 

Mawaƙi: Alh. Musa Ɗanƙwairo Maradun

 

JAGORA: Zama lahiya shi ad da daɗi,

Allah yai muna tsari.

 

‘Y/AMSHI: Zama lahiya shi ad da daɗi

Allah yai muna tsari.

 

JAGORA: Ku tashi mu bak kwana,

Yan Arewa ban da, Sake mui ta yin shiri.

 

‘Y/AMSHI: Zama lahiya shi ad da daɗi,

Allah yai muna tsari.

 

JAGORA: Ba mai kashe wuta,

In ban da ruwa.

 

‘Y/AMSHI: Kowa ya ɗamri aniya,

Zama lahiya shi ad da daɗi ,

Allah Yai muna tsari.

 

JAGORA: Ilmi da hankali,

Da sanin Allah ga yan Arewa tun hwarko.

 

‘Y/AMSHI: An sammu da haka

zama lahiya shi ad da daɗi Allah yai muna tsari.

 

JAGORA: Babu ƙasa mai daɗin ƙasammu

gamu da gero,

Gamu da dawa gamu da maiwa gamu da wake  ga shinkahwa ga masara.


‘Y/AMSHI: Akwai hikima ta abinci

ƙasammu ko wane kasso shi ka kai ta ci

zama lahiya shi ad da daɗi Allah yai muna tsari

 

JAGORA: Nijeriya abinmu na gado ne

zama tare ba bambanci tun asalinta

 

‘Y/AMSHI: Zama lahiya shi ad da daɗi

Allah yai muna tsari

 

JAGORA: Rijiyoyi da famfo da fitila

 

‘Y/AMSHI: Duka gwamnati ta shira muna

Zaman lahiya shi ad da daɗi Allah yai muna tsari

 

JAGORA: Gadojin motoci da Silma da hotal

 

‘Y/AMSHI: Gwamnati ta shira muna

Zama lahiya shi ad da daɗi

 

Mawaƙi: Mammalon Shata

 

JAGORA: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi

 

JAGORA: Inji Gwamnonin ƙasa

Mu shirya zaman Nijeriya ya yi daidai.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya mu shirya zaman Nijeriya mu bi juna.

 

JAGORA: Har wakilai na kira mu shirya zaman Nijeriya mu bi juna.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

JAGORA: Kowa Allah ya ba,

A bi shi a zauna lafiya a yi komai.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

mu shirya zaman Nijeriya mu jidaɗi

 

JAGORA: Kuma kowane ɓangare,

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu jidaɗi

 

JAGORA: Manyan Maluma

Mu shirya zaman Nijeriya mu bi juna.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

JAGORA: Talakkawa nai kira

Ku bar cika yan zantuttukan mu na banza.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

JAGORA: Yarbawa nai kira

Ku tashi mu zauna Lafiya ya fi daidai.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

JAGORA: Jama’ar Ibo nai kira

Ku taru mu zauna Lafiya mu bi juna.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

JAGORA: Kuma Gambari nai kira

Ku taru mu zauna Lafiya mu ji daidai.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

JAGORA: Yau na Barno ina kira

Ku shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Mu shirya zaman Nijeriya mu ji daɗi.

 

Mawaƙi: Dr. Mamman Shata Katsina

 

JAGORA: Ay zama lafiya

‘Yan Nijeriya.

 

‘Y/AMSHI: Ay zama lafiya

‘Yan Nijeriya.

 

JAGORA: Don Zama lafiya

Shi ne yaffi kyau.

 

‘Y/AMSHI: Ay zama lafiya

‘Yan Nijeriya.

 

JAGORA: Yayan Yarabawa

Hatta Ibo

Hausawa ku da Barebari Hillani hay ya zuwa Tibi

Ay zaman lafiya

Shi ne yaf fi kyau.

 

‘Y/AMSHI: Ay zama lafiya

‘Yan Nijeriya.

 

JAGORA: Manya da yara ƙanana duka

Mata da maza kun ji mun gargadi

Ay zaman lafiya shi ne ya fi kyau

 

‘Y/AMSHI: Ay zaman lafiya

‘Yan Nijeriya

 

JAGORA: A bar yin tunani

Ana waiga baya

Komi ya zo anka ce ya wuce,

Dangi ku bar son kuna tuntuna,

Shi zaman lafiya shi ne ya fi kyau.

 

‘Y/AMSHI: Ay zaman lafiya

‘Yan Nijeriya

 

Mawaƙi: Alh. Shehu Ajilo Ɗanguzuri

 

JAGORA: Allah wahidun,

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

 Ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Rokon Allah nikai

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Don ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: kun yi kiɗan Nijeriya

Ga waƙar nijeriya

inji Ajilo Shehu ƙanen Lawai

Don ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Malamai na addu’a

Har Kiristoci na addu’a don ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Babangida ya yo damara

Sani Abacha ya yo ɗamara domin haɗa kan Nijeriya baki ɗaya.

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya.

 

JAGORA: Wanne bambaci a kai

Har Yarabawa har izuwa Ibo

Ku zo mu taru mu zauna lafiya baki ɗaya.

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Wanne bambaci a kai

Ina Yarbawa har Ibo

Ku zo mu taru mu zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Babu zama gun mai kiɗa

Don sojoji sun ɗammara

Hatta kwastan sun Ɗammara

Ga yansanda na ɗammara

Imagirashin sun yo ɗammara

 Har nebi sun yo ɗammara

Domin haɗa kan Nijeriya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya


JAGORA: Rokon Allah nikai Waƙar ga du’a’i zan haɗa

Allah ka taimaki ‘yan Nijeriya don ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Kai nima hanyar kiɗa

Dole in godewa haliku

Tun da ya ba ni fasahar tambura

Har ma na yi wa Nijeriya addu’armu mu

Ta zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Rokon Allah nikai

Dare ko rana zan daɗa

Allah ka taimaki ‘yan Nijeriya

Don ƙasarmu mu zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Yara komai akai

in nai addu’a hanyar kiɗa zuljalalu ka taimaki

 ‘Yan Nijeriya don ƙasarmu ta zauna lafiya

baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: A daina bambanci duka yara

Idan Yarabawa sun zaka

Inyamurai ma in sun hallara

To Hausawa gara mu hallara

Mu je mu tattauna mu yi shawara

Don ƙasarmu ta zauna lafiya lafiya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Inda duf fitina take

Ya Allah ka tsare Nijeriya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: In da duf fiitina take

Zuljalalu tsare Nijeriya

don ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

‘Y/AMSHI: Allah Wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Kai Ado in ji tambura

Isah Liman inji tambura

Kai Basiru Bashar kui man kiɗa

Addu’ar da na wa Nijeriya

Don ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

JAGORA: Gadar gayan shi ke kira

Da ya kira ni in yi kiɗa

Ya ce Ajilo Shehu ƙanen Lawai

Idan kana busa waƙar zamani

Mi za ka ce ma ‘yan Nijeriya baki ɗaya?

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya.

 

JAGORA: Ni kuwa Shehu na ce masa

To Muhammadu in maganar kiɗa kai ni Alhaji ba shakka ba ne

Da ka ce ni kaɗan ka ji addu’a

Addu’ar da na wa Nijeriya

Na haɗa ta da roƙon haliku baki ɗaya.

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

ka taimaki ‘yan Nijeriya

ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya.

 

JAGORA: In Yarabawa na kira

Ku Yarbawa kui mana

Addu’a don ƙasarmu ta Zauna lafiya baki ɗaya.

 

‘Y/AMSHI: Allah wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya.

 

JAGORA: Ƙabilar Ibo na kira

Sai na ce Ibo kui muna

Addu’a don ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya.

 

‘Y/AMSHI: Allah Wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya.

 

JAGORA: Yan yara komi a kai

Ku ba ni kiɗan Nijeriya

Don ƙasarmu ta zauna lafiya baki ɗaya.

 

‘Y/AMSHI: Allah Wahidun

Ka taimaki ‘yan Nijeriya

Ƙasammu ta zauna lafiya baki ɗaya

 

Mawaƙi: Dr. Adamu Dan Maraya Jos

 

JAGORA: Barebari Fulani

Manyan abokan fa wasa.

 

Wasan ku ba zagezage

Wasan ku ba doke doke

Sai dai ko ƙarin zumunta.

 

Kun kashe gobara nono Fulfulde sun ba ni kyauta

Kanuri Allah iya nan.

 

Kashe gobara doki Kanuri kun gadi kyauta

Fulfulde kun gadi kyauta.

 

Barebari Fulani a cikinku wa ah hwa babba

 idan da babba wallahi yau gani ga ku sai ku faɗi a yanzu.

 

Kanuri sun ba ni kyauta

Fulfulde sun ba ni kyauta

Manyan abokan fa wasa.

 

Na sauka Barno

Kanuri malan sun ba ni doki

Sun ba ni Makka da kuɗin kashewa.

 

Na sauka Yola Fulfulde Malan sun ba ni shanu

Sun ba ni Makka da kuɗin ɓatarwa

Dukan ku kun ba ni kyauta.

Barebari Fulani

A cikinku wa ah hwa babba

 Idan da babba nan a cikin fa taro

Wallahi yau gani ga ku.

                                       

Mawaƙi: Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

 

JAGORA: ‘Yan Nijeriya

yan uwa mu yi ƙoƙari

 Mu zan haɗa kammu

M#un kama hanyar gaskiya.

 

‘Y/AMSHI: ‘Yan Nijeriya

Yan uwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

Mun kama hanyar gaskiya

 

JAGORA: Gyara mai sama

Allah kai ke da mu

 

‘Y/AMSHI: Ka taimaki Nijeriya

Kandami babban ƙasa

‘Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

Mun kama hanyar gaskiya.

 

JAGORA: Gyara mai sama

Allah kai ke da mu

 

‘Y/AMSHI: Ka taimaki Nijeriya

kandami babban ƙasa

‘Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

Mun kama hanyar gaskiya.

 

 

JAGORA: Kifi da kada

Da kwaɗo da tsari dorina halittas su daban-daban

Amman in mun tuna

 

‘Y/AMSHI: Dug gidansu

Yana ruwa

‘Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

Mun kama hanyag gaskiya.

 

 

JAGORA: Kifi da kada

Da kwaɗo da tsari dorina Halittas su daban-daban

Amman in mun tuna

 

‘Y/AMSHI: Dug gidansu yana ruwa

‘Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

Mun kama hanyag gaskiya.

 

JAGORA: Ina Yarabawa

Ina Nuhwawa Ina Jama’ar Ibo

Had da ku jama’at Tibi

 

‘Y/AMSHI: Dum mu taru

Mu je gaba dai

Mu koma yan uwa

‘Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

mun kama hanyag gaskiya.

 

JAGORA: Ina Yarabawa

Ina Nuhwawa Ina Jama’ar Ibo

Had da ku jama’at Tibi

 

‘Y/AMSHI: Dum mu taru

Mu je gaba dai

Mu koma yan uwa

 Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

mun kama hanyag gaskiya.

 

JAGORA: Kun gani Nijeriya

Mai yawan faɗin ƙasa

Aladummu daban-daban

Addinanmu daban-daban

 Allah mai ƙaddarowa

A kowane al-amar

 

‘Y/AMSHI: Shi yaƙ ƙaddaro

Munka zauni wuri ɗaya kuma ƙasanmu tana ɗaya

 Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

mun kama hanyag gaskiya.

 

JAGORA: Kam mu yadda da yan baranda

da yan zambar ciki

masu son su haɗa mu banna su koma tsallake.

 

‘Y/AMSHI: Idan ta rikkice

Su buƙata ta biya

Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

Mun kama hanyag gaskiya.

 

JAGORA: Albarkak ƙasa

ba kamar Nijeriya akwai zinari da fetur cikin Nijeriya

 

‘Y/AMSHI: Akwai koko

Gyaɗa, auduga na nan ciki

 

 JAGORA: Masana’antu da dama

Cikin Nijeriya akwai kamfunna

Da dama cikin Nijeriya

 

‘Y/AMSHI: Saboda hakan ga

Mu ba mu jin ƙyashin wani

Yan Nijeriya

Yanuwa mu yi ƙoƙari mu zan haɗa kammu

Mun kama hanyag gaskiya.

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.023 

Post a Comment

0 Comments