Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 40)
Baban Manar Alƙasim
Majiyar ta BBC dake shafin
facebook ta ci gaba da cewa: (Matattara (G spot ): Wannan wuri shi ne
matattarar jin dadi wanda masana ke wa laƙabi da G spot da harshen
Ingilishi, da dadewa wannan wuri mai farin jini, shi ne aka sanya a gaba, a
farkon shekarun 1980 ne aka ƙirƙiro masa wannan lakabi (G spot)
sabo da ƙwararren likitan matan nan na Jamus, Ernst Grafenberg. A shekarar
1950 ne likitan ya bayyana wani sashe na gaban farjin mace wanda yake da daidai
da wurin da mafitsara take a daya É“angaren bangon, a wasu bincike-binciken
da aka yi bayan nasa na farko, an gano tarin jijiyoyin jini da wasu jijiyoyin
da kuma baki bakin jijiyoyin da mani ke bi, wadan da dukkaninsu sun tattaru a
daidai wannan wuri.
A kan haka ne ake ganin tattaba
wannan wuri, ta hanyar jin dadi musamman a wasu kadan daga cikin mata zai iya
sa su tsartar (fitarwa da karfi) da wani ruwa dan kadan daga mafitsararsu,
wanda kuma ba fitsari ba ne, daga gano wannan wuri kuma, sai labari ya fara
fita a game da wannan dan wuri mai ban mamaki da ta'ajibi, da ke gaban bangon
farjin mace. Sai ma'abota soyayya (maza da mata) suka rinƙa duƙufa domin gano wurin, kuma abin
takaici sau da dama ba sa iya gano shi. Wasu mata masu rajin kare 'yancin mata
(feminists) sai suka ce, yadda ake yayata muhimmancin wannan wuri (G spot),
wata dabara ce kawai ta maza, domin mayar da hankali kan yin jima'i ta hanyar
shigar da zakari cikin farjin mace, bayan da hankali ya karkata zuwa ga
muhimmancin dan-tsaka (clitoris) a_ jima'i, a lokacin bunkasar da aka samu ta
ilimin jima'i a shekarun 1960 da kuma da 70, shedar tabbatarwa ko kuma ƙaryata cewa akwai wannan wuri
(G spot) ba ta da inganci ko ƙarfi sosai kuma yawanci ana
zuzuta ta ne.
Wani nazari da ya musanta
tabbatar wannan wuri, ya dogara ne ga wani hoto na asibiti da aka dauka na wata
mace daya kawai, rikici kan ainahin sunayen daidai na bangarori ko sassan cikin
farjin mace da kuma maganar daga ina wannan halitta ta cikin farjin ta fara
kuma ina ta ƙare ya ƙara kawar da muhawara kan wurin (matattarar jin dadi). Amma duk da
haka an lura da cewa akwai bambanci na zahiri tsakanin matan da suke cewa suna
yin inzali idan suka samu jin dadi a cikin matancinsu (jima'i), da kuma wadan
da suka ce ba sa yin inzali ta wannan jin dadin, ashekarar 2008, Jannini ya
wallafa sakamakon wani bincike da ya kunshi mata tara da suke yin inzalin ta
hanyar jima'i turmi da tabarya (zakari cikin farji) da kuma wadansu 11, wadan
da su kuma, suka ce ba sa yin inzali ta wannan hanya kadai (wato sai an hada da
taba wasu wuraren). Kuma wani bincike da aka yi na asibiti ya gano cewa wadan
da suke yin inzalin, suna da kaurin fata a daidai wannan wuri da ake cewa
matattarar jin dadin (G spot), yayin da su kuma wadan da ba sa inzalin fatarsu
ta wurin ba ta da irin wannan kauri, daga nan ne sai Jannini ya yanke cewa
wannan bambanci watakila shi ne shedar tabbatar wannan wuri, da ake muhawara a
kan kasancewarsa da kuma rashinsa. Amma karin wasu bincike-binciken sun sa a ƙara tunani a kan lamarin, ''Kalmar
wuri na iya sa a ga kamar wani abu ne da za ka danna ko ka tura ka samu inzali
ko jin dadi,'' ya ce, tana nufin akwai wani abu na zahiri da ko dai yana wurin
ko kuma ba ya nan, ba wanda ya iya bayyana wannan abu karara a matsayin wuri''.
To tun da ba wani maballi ba
ne, menene kenan? A wurin masu bincike da dama, amsar mai sauƙi ce: kuma ita ce dan tsaka, ko
da yake a wurin mutane da yawa dan-tsaka wani abu ne kawai mai kamar siffar
kwayar fi (pea) a karkashin saman fatar bakin farji, binciken baya-bayan nan ya
nuna cewa abin ya wuce girman yadda aka dauke shi. Nazari ya nuna abin ya kai
tsawon kusan inci uku da rabi ko tsawon dan yatsan hannun yawancin mutane, abin
ya taho ne daga cikin saman farji har zuwa baki, inda a ƙarshe ya dan fito, yawancin
mutane suna ce masa dan-tsaka, kuma suna ganin shi ne É“angaren da ya fi sa mace jin dadi a
jikin wannan dan dogon abu, wanda kafafunsa kuma sun rabu ko sun bude a kofar
farjin.
Za kuma a iya bayyana shi da
cewa azzakari ne mai kai biyu, daman kuma dukkaninsu, wato azzakari da shi
dan-tsakan irin jijiyarsu daya, kuma sun samo asali ne daga farkon halittar
jiki daga wuri daya, yayin da na mace yake karewa a matsayin dan-tsaka, shi
kuwa na namiji sai ya zama azzakari da marena. Amma kuma suna da wani bambanci
mai muhimmanci, domin shi azzakari ba ya ci gaba da girma da zarar mutum ya
balaga kamar yadda kwayar halittar mazancinsa (testosterone) ke samuwa. Shi
kuwa dan-tsaka yana ci gaba da girma inji Jannini, “Ba wai dan karamin
azzakari ba ne kawai”. Farji ma yana samun sauyi sakamakon kasancewar kwayoyin
halittar matanci, wanda wannan zai iya taimakawa wajen fahimtar abin da ya sa
sha'awar mace ke sauyawa tsawon rayuwarta. Wannan sarkakiya za ta iya sa a gane
cewa abu ne mai wuyar gaske a tabbatar ko kuma a musanta cewa akwai wurin da
ake cewa matattarar jin dadin mace (G spot), ba abu ne mai sauki ba, ka sa mace
jin dadi daga gaban bangon farjinta kadai, yayin jima'in za ta iya kasancewa
kana gugar É“angaren cikin dan-tsakan da kuma
mafitsararta, ƙarin binciken da Jannini da Odile Buisson suka yi a Saint Germain
da ke Faransa ya tabbatar da hakan. To sai dai abin yana kara sarkakiya a wajen
wasu matan, domin shigar zakari cikin farjinsu zai iya a wannan lokacin ya rika
tattaba waje da cikin dan-tsakansu, kuma su ji dadi a sanadin hakan, misali a
2009, wata mata mai shekara 42 ta je asibitin Rachel Pauls, wata likitar mata a
Cincinnatin Ohio da ke Amurka, matar an haife ta ba tare da mafutsara ba, kuma
an yi mata tiyata domin gyara mata wasu daga cikin waÉ—annan matsaloli.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.