Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 39)
Baban Manar Alƙasim
Shafin na BBC da yake kan
facebook ya ci gaba da cewa: (A mazaunin farjin mace akwai abin da ake kira
dan-tsaka (clitoris), wanda yake a bakin farjinta, maganar wanda ya gano shi
kansa dan-tsakan a tsakanin masana kimiyya, an ce wata abar muhawara ce ita ma,
domin sai a karni na 16 ne ma aka fara bayyana abin, a matsayin wani wuri ko
abu na musamman, wanda kowace mace take da shi, wanda kuma taba shi, ke sa mata
jin dadi. A littafin Realdo Columbo, mai suna De re anatomica, wanda aka
wallafa a 1559, ya bayyana dan-tsaka a matsayin ''cibiyar jin dadin mace'' amma
kuma a sauran ƙarnin da suka biyo baya, sai masana kimiyyar jikin dan adam, ba su
ba maganar jin dadin mace muhimmanci ba, kuma a kan haka, kusan aka manta ma da
maganar dan-tsaka.
A ƙarni na 20 ne maganarsa ta ƙara tasowa, amma duk da haka
masana kimiyya da dama, ba su ba shi muhimmanci ba, duk da cewa Sigmund Freud
ya yarda cewa mata za su iya samun inzali, amma ya yi amanna cewa inzalin da
mace baliga za ta yi sakamakon shiga ko taba cikin farjinta, ya fi wanda za ta
yi idan jin dadin ya taso daga dan-tsakanta ne, a rubutun da ya yi, ya ce idan
mace ta kasa ko kuma ba ta samun yin inzali daga jin dadin da ta samu na amfani
da cikin farjinta, hakan ya shafi matsalar rashin balaga ce ta jima'i. Idan
haka gaskiya ne, to sai a ce, akwai mata masu yawan gaske da ba su fahimci
yadda jin dadin jikinsu yake ba na jima'i, kusan kashi 30 zuwa 40 na mata sun
ce ba su taba yin inzali ba ta hanyar jima'i (tabarya a cikin turmi) kawai, ko
da yake da yawa kuma sun ce suna samun biyan bukata (inzali) ta hanyar yi musu
wasa da dan-tsakansu (clitoris), maganar cewa inzali ta sanadin saduwa da mace
ta farjinta shi ne inzalin da ya fi muhimmanci, ko ya fi duk wani inzali, abin
ya bata ran masu rashin kishin mata da yawa. Sabo da hakan kamar yana nuna cewa
matan da ba sa samun irin wannan inzali, kamar ba sa kokarin samun hakan ne
sosai, to dangane da hakan za a iya cewa, ke nan, samun irin wannan nau'in
biyan bukata (inzali) na jima'i dama ce ga kowace mata ko kuma sai wasu da suka
dace ne kawai?
Shin abu ne ma da zai iya
yuwuwa a ce mace ta yi inzali idan ba ta da dan-tsaka? Barry Komisaruk ya yi
sa'ar kama matakan farko na amsa waɗannan tambayoyi, a lokacin da yake nazarin yadda beraye suke
jima'i, wata rana, a lokacin da yake tura wani dan tsinken karfe a farjin macen
bera, sai ya ga ta yi wani abu da ya ba shi mamaki. ''Ina taba kofar yankin
da ke tsakanin farjinta da hanyar mahaifarta (cervix) sai kawai ta tsaya kyam
(macen beran),'' Ya ce: Ba wannan ba kadai, a lokacin irin wannan jin dadi
ga alama ba ta jin duk wani ciwo ko radadi, bayan wannan ne sai kuma mai
binciken ya koma kan mata, da wannan gwaji nasa, kuma ya gano daidai irin abin
ya gani a kan macen bera, wato jin dadi a cikin farji yana hana mace jin ciwo.
Amma ta yaya hakan ke faruwa? Domin gano hakan, Komisaruk ya gudanar da bincike
tare da Beverly Whipple, inda suka yi nazari a kan matan da ke fama da raunin
laka iri daban-daban, a binciken, sun gano cewa, su waɗannan mata, duk da cewa hanyar
jijiyoyin da ta tashi daga yankin farjinsu zuwa ƙwaƙwalwarsu ta toshe, ko ta
yanke,(saboda raunin da suka ji), matan suna ji idan an taba farjinsu ko can
cikin farjin (cervix).
Wasu daga cikin matan, har
sukan fitar da mani (inzali) sakamakon tattaba musu wurin, duk kuwa da cewa
hanyar da ke aikawa da sako daga matancin nasu (farji) zuwa ƙwaƙwalwa ta yanke, ''Matan da ke
fama da rauni a lakarsu, wadanda ba sa jin kamar dan-tsakansu na jikinsu, duk
da haka suna yin inzali idan aka tattaba musu farjinsu domin jin dadi''. Kamar
yadda Komisaruk ya ce ''Wannan ga alama ita ce babbar shedar da ke tabbatar da
cewa mace na yin inzali sakamakon jin dadi a cikin farjinta'' dalilin shi ne,
daga jijiyoyin da ke kusa da lakarta, sakon jin dadi (na tattaba farjin) yake
tafiya zuwa ƙwaƙwalwa'' Mata suna bayyana inzalin da suke yi (na sanadin) idan an
tattaba dan-tsakansu a matsayin karamin jin dadi kuma na waje, shi kuwa inzalin
da suke yi a sanadin samun jin dadi a cikin farjinsu, sukan bayyana shi a
matsayin, jin dadi na ciki kuma wanda yake shafar dukkanin jikinsu. Wannan
watakila sabo da jijiyoyin da suke kai sako ƙwaƙwalwa daga dan-tsaka, daban
suke da jijiyoyin da suke kai sako ƙwaƙwalwa daga ainahin cikin
farjinsu ne,'' kamar yadda Komisaruk ya yi bayani, kuma game da yadda (abin
mamaki) jin dadi a cikin farji yake hana mace jin zafin ciwo, watakila
jijiyoyin da suka hadu da laka (spinal cord) su ne suke hana aikawa da wannan
sako, na jin ciwo zuwa ƙwaƙwalwa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.