Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 41)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 41)

Baban Manar Alƙasim

Yau dai za mu ƙarƙare bayanin BBC da suka yi a shafinsu na facebook 23/10/2015, sai mu dora da nazarin wasu malaman muslunci a kai, amma da farko ga tambayar da suka yi:- . Ko girman dan-tsaka yana da tasiri? Wannan ya haifar da wani tunanin kuma, Pauls tana tunanin ko girma, da kuma wurin da dan-tsakan mata masu lafiya yake, yana da tasiri kan yadda suke yin inzali cikin sauki a lokacin jima'i (ta cikin farjinsu)? Sabo da haka ne sai likitar da wasu abokan aikinta suka samo wasu mata goma da suka ce ba kasafai suke samun yin inzali ba, ko kuma ma ba sa yi a lokacin jima'i, da kuma wasu matan 20 da suka ce su kuma suna yin inzali kusan ko da yaushe.

Likitocin sun yi amfani da na'ura wajen daukar hoto da bayanin yadda dan-tsakan matan yake a lokacin jima'i, daga nan sai suka gano cewa, idan dan-tsakan ba shi da girma kuma yana da nisa daga farjin mace, da wuya wannan mata ta yi inzali ta hanyar shigar zakari ko wani abu cikin farjinta, idan aka duba waɗannan nazarce-nazarce za a ga cewa akwai hanyoyi da yawa da mace za ta iya samun inzali.

Ko dai ta hanyar jin dadi a cikin farjinta (shigar azzakari ko wani abu) ko tattaba dan-tsakanta ko kuma yi mata duka biyun a lokaci daya, ƙarin nazarin da Komisaruk ya yi ya nuna cewa sakonnin jin dadi daga sassan matancin mace daban-daban hadi da kan nononta, duka suna haduwa a wuri daya, na gaba dayan ƙwaƙwalwarta, ko da yake, ya dan bambanta a sassan ƙwaƙwalwar. Komisaruk ya ce, ''akwai abin da yake haddasa kowane irin inzali kuma kowanne da irin dadin da ke jawo shi'' watakila wannan shi ya sa hada jin dadin dan-tsaka da cikin farji da kuma hanyar mahaifa a lokaci daya, yake sa mata jin tsananin dadin inzali ko fitar da mani, wanda ke cike da sarƙaƙiya ko wuyar fahimta, kamar yadda matan suke bayyanawa, cewa abu ne da ba za ka iya ba da misalinsa ba''. Su kuwa matan da ba kasafai suke samun yin inzali ba lokacin jima'i na cikin farjinsu ko kuma duk wani nau'i ma na jima'i, sakon Pauls gare su mai sauki ne, kuma shi ne 'a jarraba wasu hanyoyin'.

Likitar ta ce ''Sai mata su zo wurina a matsayin marassa lafiya, su ce, ba sa yin inzali, saboda haka lalle suna ganin suna da wata matsala, ba wata matsala a jikinsu, kusan kowa yana da dan bambanci da wani, wasu matan suna bukatar samun jin dadi sosai na tsawon lokaci a dan-tsakansu a lokacin jima'i, wasu kuwa sai an dan dage kadan, sabo da haka sai mazansu watakila sun yi amfani da hannu ko wani abu.

Abin dai shi ne, mata su sani cewa, idan ba su yi inzali ba lokacin saduwa da su ta farji kai tsaye, wannan ba wata matsala ba ce'' Dakta Emmanuele A Jannini yana da karin sako ga mata: ''Ba jima'i kadai za ki mora ba, ki mori dadin sanin kanki, da fahimtar wacece ke a yau, domin kila ki zama daban gobe'' kuma ka da ki rena tarin hanyoyi daban-daban na samun inzali wadan da ake da su'' ka da ki dauki jikin mace kamar na'urar da a ko da yaushe za ta yi abu kamar yadda ta saba" in ji shi. Yanzu bari mu fara da bayanin da Yusuf Abul Ghait ya yi a littafinsa na (A'ashab Sihriyya wa Sifat Tibbiyya lil Mu'ashara Zaujiyya) ya ce " Gazawa irin ta namiji tana nufin rashin miƙewar gaba ne, ko da ya miƙe sai ya kwanta kafin wani dan lokaci" To amma da yake ya yi bayani mai amfani za mu dauko bayanansa da kuma wasu magunguna da namiji zai yi amfani da su sabo da tsaro, jan ido ko 'yan sulalla ba su ne kadai mazantaka ba, wani lokacin iya riƙe gida tana nufin jarumta ne a shimfida, irin wannan karatun ba ko ina ake yi ba sai a kiyaye. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments