Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 38)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 38)

Baban Manar Alƙasim

To kafin mu shiga wannan bayani, zan so mu ji bayanan masana game da wannan harka, a ƙarshe sai mu tuntubi malaman muslunci masamman wadan da suka jima da rasuwa don gano yadda haƙiƙanin abin yake, da irin riƙon sakainar kashi da muka yi da zamantakewarmu da iyalinmu, haƙiƙa saduwa a muslunci babbar abu ce wace Allah SW yake ba da lada a kan yin ta, kenan rashin gudanar da ita yadda ya dace yana iya kai mutum ga saba wa Mahaliccinsa, yanzu dai bari mu fara da nazarin bayanin BBC a shafinsu na Facebook wanda suka sake a 23/10/2015, daga ciki suke cewa:- . (JD Salinger ya taba rubuta wata kasida da ke cewa ''jikin mace kamar molo yake sai kwararren mawaƙi ne zai iya kada shi yadda ya kamata'' ka taba shi ko ka shafa shi, yadda ya dace, sai ka kai mace wani zango, a cikin wasu 'yan daƙiƙoƙi za ta rasa inda take a duniyar nan, amma idan ba ka san yadda za ka yi mata abin da ya dace ba, abin da zai iya biyo baya, sai ciwo da damuwa ko kuma lami kawai. Wannan ya sha bamban matuƙa da yadda namiji yake, domin shi gogan, in dai har mazakutarsa za ta tashi, wasan da za a yi ma ta na 'yan mintina zai sa ya yi inzali (ya fitar da mani), me ya sa inzali yake da matukar dadi? Me ya sa mata suke yin inzali fiye da sau daya a lokaci daya?

Kuma ko da gaske ne ma akwai wannan wurin da ake cewa mace ta fi jin dadi idan an taba ma ta shi? Waɗannan na [daya] daga [cikin] tambayoyin da suka dade suna ba wa masana kimiyya wahala wajen sanin amsarsu ''Mun yi nasarar zuwa duniyar wata amma ba mu fahimci yadda jikinmu yake ba sosai,'' in ji Emmanuele Jannini na jami'ar birnin Rum, Tor Vergata, wanda ya dauki kusan tsawon shekarunsa yana aiki (koyarwa da bincike) domin kokarin ganowa. A shekarun nan masana ilimin jima'i na sosai sun yi ta bincike da nazari da dama a kai, kuma a karshe dai sun fara ganin haske na fahimtar yadda wasu abubuwan suke.. Watakila babban ƙoƙarin da za a ce masana kimiyya sun yi shi ne, na shawo kan mata, su kawar da kunya da wasu al'adunsu, su yi wasa da jikinsu domin jin dadi da biyan bukatar jima'i da kansu, ko kuma ma su sadu da namiji.. Daya daga cikin jagororin wannan bincike shi ne Barry Komisaruk, na jami'ar Rutgers da ke New Jersey, wanda yake son ya tabbatar ko bambancin ƙwaƙwalwa zai iya sa a fahimci dalilin bambancin jin dadin jima'i tsakanin mace da namiji, ta tabbata cewa, duk da bambancin yadda suke ji a lokacin jima'in, kusan aiki iri daya ƙwaƙwalwar namiji da ta mace suke yi a lokacin inzali, kamanceceniyar namiji da mace a yayin inzali ta fi bambancinsu yawa, nesa ba kusa ba, '' inji Komisaruk. ''Abin da muke gani shi ne, ƙwaƙwalwar ce gaba dayanta take kama aiki gadan-gadan'' wannan kila shi zai iya bayyana abin da ya sa inzali ke mamaye jikin mutum gaba daya, abu ne kamar a ce, idan daji gaba daya ya kama wuta, da wuya ka ce ga daga inda wutar ta tashi, ''A yayin inzali, idan komai ya kama aiki a lokaci daya, wannan zai kawar da bambancin aikin wani ɓangare da wani ɓangare'' kamar yadda Komisaruk ya yi bayani. Ƙila wannan ne ma ya sa ba ka iya tunanin komai a wannan lokacin, akwai wuraren da ke da alhakin kula da jin dadi a ƙwaƙwalwar mutum, inda a duk lokacin da wani sako ya je wannan wuri, mutum yake jin matuƙar dadi, wannan ne ma ya sa bera zai iya zabar samun wannan jin dadi a maimakon abinci, wanda har ma zai iya haƙuri da abincin yunwa ta kama shi har ya mutu, in dai zai sami wannan jin dadi. .. Ba mamaki ashe mutum ya kan so idan ya yi inzali ya kara yi, akwai wasu muhimman bambance-bambance da ake gani, wadan da za su iya bayyana abin da ya sa yanayin mace da namiji yake bambanta a lokacin, Komisaruk da Kachina Allen sun gano wata sheda ta farko-farko da ke nuna cewa wasu bangarori na ƙwaƙwalwar namiji ba sa jin duk wani wasa da ake yi wa mazakuta ko marenansa, jim kadan bayan ya fitar da maniyyi.

Sabanin haka, ita mace irin waɗannan bangarori na ƙwaƙwalwarta suna jin irin wannan wasa idan an yi mata a wurin farjinta, bayan ta samu biyan bukatar farko, yadda jin dadi yake; Idan wannan hoton aikin ƙwaƙwalwa ya haifar da cece-kuce, to wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta da kokarin fahimtar yadda inzali ya kasu daban-daban, shi azzakari yana da jijiya ko hanya daya ce kawai, ta kai wa ƙwaƙwalwa sako, shi kuwa farjin mace yana da irin wadan nan jijiyoyi ko hanyoyi uku ko hudu). A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments