Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 25)
Baban Manar Alƙasim
Ita kuwa mace takan cin ma
burinta ne wajen samun kasancewa uwa kuma abar ƙauna, in har ta fara tunanin
cewa ba a ƙaunar ta, sai cutar yawan tunani ta fara neman kama ta, ko kuwa ta
shiga neman daddadar magana a duk inda take ganin za ta samu, in ba ta samu a
wurin mijinta ba, kuma babu hanyarta a wurin mahaifa da ƙawaye, to za ta iya nema a wasu
wuraren, tun ma ba wannan zamanin da hanyoyin sadarwa suka yawaita ba, soyayya
ta ɓangaren renon zuciya za ta iya samuwa
da kalmomi masu tsada, ko 'yan kyaututtuka ko wasanni. Ba shakka namiji bai
cika bude baki ya ce wa mace "Ina son ki" ba, to bare ya ce
"Wallahi ina bala'in ƙaunarki" wannan sai dai in
tana budurwa ko bazawarar da ake zawarcinta, galibin masu fadin ma za ka taras
da Larabci ko Turanci suke fadi, don da Hausa tana da dan nauyi, mu ba mu girma
mun iske uwayemmu suna fadi a gabammu ba, sai dai akwai kula ta masamman wace
namiji yake ba wa mace, wannan kam alamar soyayya ce ba ko shakka, ya kamata
mace ta riƙa fahimtar haka, in wasu suna kwashe rabin dare suna hira da
matansu, ke kuma na ki ba ya iyawa, wannan ba ya nufin na ki mijin ba ya ƙaunarki, haka in wani yana fita
yawo da ta sa iyalin, ko yana zaman gida suna wasa da dararraku, in na ki ya
gaza ba ya nufin cewa ba ki auri mai son ki ba, soyayya sam ba a magana da
wasanni kadai take ba, ta kutsa bangarorin rayuwa da dama.
Su a kansu mata sun dan
bambanta ta wajen tantance abin da suke buƙata a wurin mazajensu, wata
jari kawai take so a ba ta, wata buƙatarta kawai ta ga ta zauna da
maigidanta tana hira, wata wasanni kawai take buƙata, wata ma shimfidarce ba ta
isar ta, wato maigidan ba ya gamsarwa, wata so take a riƙa taya ta ayyukan gida masamman
girki da gugar kaya, ko da a ce akwai mai aikin gida ba ta buƙata in dai ba maigidan zai yi
da kansa ba, wata buƙatarta a riƙa taya ta renon yara, wata abin
da ta ce so take a dauke ta a gaban mota su fita yawo, akwai wadda ta ce buƙatarta kawai maigidan ya riƙa dauke mata kudin man shafawa
da na kalanzir da dai sauransu, wata buƙatarta ta ga cewa ita ce mai
mulkin gidan, kowace mace da abin da take so, haka kowani namiji da abin da ba
zai taba iya yin sa ba, kenan rashin matsa wa maigida a kan sai ya yi wani abu
ya fi zama soyayya sama da a ce an matsa masa sai ya yi abin da ba ya so.
A nan ba ina ƙoƙarin cewa mace ta tsaya aiki a
cikin gida ne kawai ba, ko namiji shi kadai ne aka san shi da aiki a waje,
akwai mata da dama da suke aiki a kamfanoni da wasu ma'aikatan gwamnati da masu
zaman kansu, kuma ayyukan da suke yi ko kusa wani namijin ba ma zai iya
kwatankwacinsa ba, amma duk shaharar da mace za ta yi da ayyukanta na waje, in
dai tana da matsala a gidanta to da sauranta, domin ba za ta taba samun
kwanciyar hankalin da take buƙata ba, haka namijin da yake
narke a gida, in dai bai tsayar da waje daidai ba to ba zai taba samun abin da
yake so ba. Ta ɓangaren tunani ma, akwai irin wannan
bambance-bambancen tsakanin mace da namiji, domin shi namiji sau tari in wata
matsala ta fado masa yakan tsaya ne ya yi tunanin mafarinta, da kuma yadda za a
warware ta, yakan duba ƙusurwoyi daban-daban kafin ya
yanke hukunci, yakan manta da abin da yake damunsa wasu lokutan, don dai kawai
ya ci nasara a kan abin da yake so, ita kuwa mace ba ruwanta da nawa a cikin
lamari, duk matsalar da ta taso mata tana da maganinta na nan take, in aka
kyautata ma ta ta faranta, in kuma aka munana ma ta a ji ba dadi, duk kuma abin
da ya biyo baya sai a yi tunanin yadda za a yi maganinsa, wani lokaci a yi kuka
wani sa'in a yi ta ban haƙuri tare da nuna gazawa, ba
wani nauyin da za ta ji wajen ta nuna maka cewa tunaninta fa ba daya ne da na
ka ba. Wasu lokutan za ka ga namiji ya dawo aiki a jigace, in malamin makaranta
ne ko ma'aikacin ofis da ya shigo gida zai fara binciken wasu takardu, don dai
aikinsa ya fita daidai, takardar da ya gama da ita sai ya yaga ta ya jefar don
kar ta rikita masa lissafi, a irin wannan halin ita mace tana ganin bata mata
daki yake yi bayan ta gyara, ta ajiye komai a ma'ajiyarsa, sai ta riƙa ganin ya fito ma ta da
littafai masu ƙura ya kakkaba ma ta, ko ya zaƙulo su alhali ya san ba zai mai
da su inda ya ciro ba, ba hankali ne ba ta da shi ba, amma hanyar tunanin ce
kowa da ta sa.
Namiji yana da tabbacin cewa ƙauna daban saduwar shimfida daban, don wani lokacin kowa yakan sakankance cewa wane ba ya son wance, amma sai ka ga suna ta haihuwa, akwai wasu mazan da ba a raba su da mace, yau ka gan su da wannan, gobe da wancan, buƙatarsu kawai suke biya ba za su taba aurensu ba, kenan biyan buƙatunsu kawai suke yi da su, kamar dai auren holewa, wanda za su hole da mace in sun biya buƙatarsu su tsallake ta su nemo wata, ba su buƙatar zama da ita samsam bare ta zama uwar 'ya'yansu, wannan sha'awace zalla ba soyayya ba. Ita mace in ba karuwa ce ko mai auren holewa ba takan dauki saduwa ne a matsayin soyayya, wanda take ƙauna tana iya ba shi komai na ta, shi ya sa ba wahala ka ga an yaudare ta, uwaye suna yawan sanya wa diyoyinsu idanu, don mugaye suna iya amfani da sunan soyayya su ribace su, mace ko da babbace a baki ne kawai za ta ce maka ta san bambancin saduwa da soyayya, amma a zahiri wanda ta ƙi jininsa ba wai ta amsa sallamarsa ba ko ganinsa ba ta ƙauna, to bare ya sa rai da taban jikinta, wanda take so kuwa kullum za ka gan ta da shi, wasu abubuwan tabbas za ta gaya maka haram ne amma ba za ta iya tsallakewa ba. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.