Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 26)

    Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.

    Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 26)

    Baban Manar Alƙasim

    Akwai wasu haƙƙoƙi da suka zama tilas ga duk namiji ya san su, matuƙar yana son ya fara neman aure, don a ƙarshe dai zai zama maigida ne, haka ita ma macen a ƙarshe za ta zama uwargida ne, matuƙar kowa cikinsu yana da wannan burin a cikin zuciyarsa to dole ya san haƙƙoƙinsa da na abokin rayuwarsa, da ma na yaran gida, don ya san yadda zai inganta zamansa da su, aure kamar sauran abubuwa ne na ɓangaren rayuwa, ko dai a yi shi daidai kamar yadda aka tsara shi, ko kuma ya baci, sau tari yakan hada: Maigida, uwargida, uwaye da yara ƙanana.

    1) Kamar shi namiji ya zama tilas a kansa, ya girmama matsayin iyalinsa, ya ba ta duk wani 'yancin da take jin ta cancance shi, ya sa ta ta riƙa jin cewa ita ce shi gaba daya, kuma in har ba shi a gidan ba ya nufin ba mai gidan matuƙar dai tana nan, kasancewarsa maigida bai nuna cewa duk wani ƙarfi da iko da isa wajen yanke hukunci sun zama na sa, ita ba ta da ta cewa (barawo a hannun mata), ko a ce duk wani abin da za ta kawo matuƙar ya saba na sa to ya zama shirme, a'a, shi dai shugaba ne, ita kuma mataimakiyarsa ce, galibi an fi ganin tasirinta ne in ba shi, amma shugaba da mataimaki tushe ne na komai. Iyalin gaba dayansa daga mátà ko mátá zuwa 'ya'yansu duk na maigidan ne a matsayinsa na jagora, shi ne mai kula da rayuwarsu da kuma jin dadinsu, wato dai duk wani abin da suke buƙata shi ne mai badawa, in yana kyautata musu gwargwadon hali kamar yadda shari'a ta ce, bai da buƙatar sai ya yi mazurai, ko ya fadi cewa shi ne babba kafin a yi masa biyayya, ƙauna da daukar nauyi suna iya ba shi duk abin da yake buƙata na sarauta da shugabanci a gidansa. b) Nuna ƙaunar namiji ga iyalinsa wajibi ne, ga tambaya: Shin mutum zai iya fushi da kansa kuma ya rayu cikin jin dadi?

    Idan mutum ya dauki iyalinsa tamkar ɓangaren jikinsa zai yi wahala a ce yana fushi da su, idan matsayin mace shi ne ta nuna ƙauna ta ƙarshe ga maigidanta, to shi ma fa akwai buƙatar ya dauki nauyin iyalin gaba daya ya dora a kansa, a Ƙur'ani Allah SW Ya bayyana cewa Ya fifita maza a kan mata don a sami jagora, kuma don nauyin da yake kan mazan na ciyarwa, ba shakka nuna kulawa da daukar nauyi ko ba furuci an san ginshiƙi ne mai ƙarfi na soyayya. c) Na san wasu mazan sukan so mace don kudinta ko na ubanta, ba laifi ba ne talaka ya auri mai kudi, ko 'yar maikudi, amma kar ya kasance kwadayin kudin ne ya ingiza shi nemanta, mutumin da zai auri wace ta fi shi, kuma yana da kwadayin abin hannunta to a ƙarshe dai shi ne zai dawo ƙasa, ita kuma ta koma sama, don daukar nauyin da zai yi shi ke kawo shugabanci, masamman a rayuwarmu ta yau, in kana da abin da za ka bayar kai ne abin girmamawa, wato yaro da gari abokin tafiyar manya. d) Ko da yake mace ita ce uwargida, komai yana hannunta ne, wannan bai nufin ba ta buƙatar taimakon maigidan a wasu abubuwan da suka shafi aikin cikin gida, mun san ba za mu nemi ya wanke bayi duk safiya ba, ko sharan gida da tsaftace daki, to amma in zai samo ma ta mai taimako ba laifi, in kuma babu hali ko sanya idonsa kawai a wajen tarbiyyar 'ya'yansa abu ne mai mahimmanci, kar dai a ce ya sakar ma ta komai don ganin shi ma yana da wasu abubuwan yi a waje.

    e) In ya kasance gida lafiya to maigidan zai sami kwanciyar hankali, ma'ana in uwargida ba ta jin dadin zaman da take yi da yaranta, kullum cikin tashin hankali, haƙiƙa ba za ta iya kula da gida ko da maigidan kamar yadda ya dace ba, ashe sanya idonsa a kan 'ya'yansa mata tun suna ƙanana abu ne da ya zama wajibi, ballantana ma ana cewa "Ido wa ka raina? Ya ce wanda nake gani kullum" sau da yawa maigida kallo kawai in ya yi wa yaransa yana iya gyara wasu abubuwan, ba ma sai ya yi magana ba, kenan bincikensa game da yadda tarbiyyar yaransa take tafiya abu ne da yake wajibi. Yara masamman mata sukan fi shaƙuwa da mahaifinsu ne idan sun fara tagazawa, sabo da shi bai da lokacin da zai matsa wajen sanya musu idanu; ina suka je? Me ya sa suka makara? Da wa suka tsaya? Me ake yi a can?

    Me ya sa na neme ki ban gan ki ba? Da dai 'yan tambayoyin da uwaye mata suke yi wa diyoyinsu don tabbatar da tarbiyyarsu bisa hanya miƙaƙƙiya, a irin wannan gujewa da 'yammata suke yi wa mahaifansu mata akwai buƙatar kusantowar mahaifi gare su don rage wa ita uwar ta su nauyin tarbiyya, in ta sami dama-dama za ta iya miƙewa da hidimar mahaifin kamar yadda ya dace. f) Yakan wajaba kuma a kan maigida ya riƙa rarrabe lamurran gida da matsalolin waje, ba shakka wasu magidantan suna fama da ayyuka masu wahala kafin su sami abin da za su rufa wa kansu asiri da iyalinsu da shi, wani lokaci ma har gwara masu aikin ƙarfi, kamar uwayenmu na karkara, ko masu leburanci, birkiloli da masu faskare, a kan masu cajin ƙwaƙwalwa, irin su malaman makaranta, ma'aikatan banki da sauran ofisoshi, waɗannan kulum cikin cajin ƙwaƙwalwa suke, da zarar sun iso gida don hutawa, dan abu kadan za a yi musu nan da nan ka ji sun hau sama, tun ma ba masu rataya kayan sarki ba, yana da kyau a ajiye matsalolin waje a wurin aiki, a cika gida kuma a samar da soyayya da ƙauna, masamman ga ƙananan yara wadan da har yanzu ba su san Annabi ya faku ba. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

    Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 26)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.