Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 24)
Baban Manar Alƙasim
Sanin wasu 'yan bambance-bambance
yakan taimaka wajen yi wa abokin rayuwa hanzari, mace da namiji har abada ba
daya suke ba, sunansu dai mutane a jumlance, amma in ka kira namiji da
"mace" ransa zai baci, haka da za ka ce wa mace da "namiji"
za ta ji zafi, kenan ko a suna mun tabbatar ba daya muke ba, bare mu fara duba
sassan halitta da rayuwa, duk in muka ce namiji ya fi mace, zai yi wahala ka ce
muna nufin ya fi ta matsayi ne a wurin Allah, don tun halittar namijin farko ba
a bar shi shi kadai tare da ita ba, shari'a ta tabbatar a wurare da dama kan
cewa dalilin halittarta bayan bautar Allah sai natsar da mijinta, da tattara
masa jin dadinsa, gami da hada shi a matsayin cikakken namiji.
Ita kuwa matar duk wata hidima
tata ƙarama ce ko babba tana wuyarsa ne, kenan ba ita ce kadai baiwarsa
ba, dukansu bayin juna ne, ko mu ce shi ne ma bawan, don ba abincinta da abin
shanta da suturarta gami da matsuguni kadai take buƙata a wurinsa ba, hatta ba da
kariya na ita kanta da mutuncinta duk yana kansa, wajibinsa ne ya kula da lahiyarta
kamar yadda yake kula da tasa, kenan sai ma mun tambayi kayukammu, shin ma waye
bawan ita ce ko shi? Namiji kam Allah ya yi shi da girman jiki da ƙarfin zuciya, wannan ya sa za a
same shi wani lokaci da zafi gami da ƙarancin tausayi, ita kuwa mace
halittarta ta bambanta da ta namiji a jiki da sura, komai na ta mai laushi ne
yadda zai iya karbar wancan halittar ta namiji, wasu abubuwan ba sakaci ba ne
ko rashin kulawa, Allah bai yi su ne ba da surar da ya yi mu, ya bar su haka ne
yadda za mu iya amfana da su, da a ce komai na su irin namu ne, to rayuwar za
ta kasance tamkar namiji ne ya auri namiji, ba na gardamar cewa akwai mata
tamkar maza, akwai kuma wasu mazan wadan da gwara matan da su, waɗannan ba za mu yi ƙiyasi da su ba.
Yanayin rayuwa kamar yadda muke
kallo, jiki gaba dayansa ta É“angaren zartar da abubuwa shi yake
daidaita kai-komo na dan adam, abin nufi a dabi'ance mai rauni yakan jingina ne
a jikin mai ƙarfi don ya sami kariya, ya kuma sami rufin asiri, wannan ba a
tsakanin mu mutane ba hatta dabbobi da tsintsaye in muka lura abubuwan da
namiji yake yi don macen da take tare da shi, akwai jin cewa shi ne mai ƙarfi, kuma shi ne mai ba da tsaro
da kariya kuma shi ne mai kula da yara da kuma abinci, ita kuma macen da irin
gudummuwar da take badawa don ganin wannan gamayyar ta ba da ma'anar da ake buƙata wajen gina kyakkyawar
zamantakewa. Irin waÉ—annan bambance-bambancen ne
suke sanya namiji ya yi ƙoƙarin warware matsalolinsa ko da
da masifa ne, abin haushi kuma ba kowani lokaci za ka iske yana da gaskiya ba,
ita kuwa mace takan warware matsalolinta ne cikin hikima da natsuwa gami da
'yan dabarbaru, wasu lokutan ma takan hada da 'yan koke-koke don cin ma
burinta, kuma tabbas buƙatarta takan biya a wasu
lokuta, to amma duk da cewa namiji ƙaƙƙarfa ne kuma jarimi mai ƙarfin zuciya, sai dai mace ta
fi shi juriya wajen shanye abin da yake damunta, takan iya jure bacin rai da
wahala duk a lokaci guda. In ma ana tunanin cewa ita tana buƙatar soyayya ne, da tausasawa,
takan gamu da bacin rai ba ƙarami ba a wurin namiji, har ta
tabbatar da cewa ba ya ƙaunarta, amma ta jure
wahalhalun nemo wa kanta komai, ta sha wahalar ciki da haihuwa da ƙarancin barci sabo da kukan
jira-jirai, amma kullum ka gan ta a tsaye kamar ba ita ba, namijin da mace take
gallaza masa cikin sauƙi ake gane shi, ko rana daya ta
tabo shi ana iya gane shi a waje, mace kuwa takan yi kukan zuci bakinta yana
dariya, don haka koda a ce namiji ya fi mace a aikin jiki, ba shakka ita kuma
ta fi shi a juriya.
Ya kamata kowani namiji kafin
ya fara neman mace ya san cewa takan canja nan da nan a kan ƙaramin abu, wani lokacin ma ba
dalili, sau da yawa namiji yakan hasala, masamman in ya tuna cewa bai yi mata
komai ba, to wannan ya fi faruwa ne a dalilin wasu ƙwayoyin halitta da macen take
da su, in mace tana al'ada dan abu ƙarami yana iya harzuƙata, haka lokacin da take da
juna biyu, ko idan girma ya fara kama ta wato shekara 40 - 45, wasu a lokacin ƙwayoyinsu suke dakatawa, sai ka
ga jinin haila ya fara gardama, a irin wannan yanayi ba dole ba ne saurayi ya
gane, amma maigida yakan sani, don haka ya san irin ma'amallan da zai yi da ita.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.