Ticker

6/recent/ticker-posts

Addini Da Yaƙar Ta’addanci Don Tabbatar Da Tsaro: Tsokaci Kan Gudummuwar Malaman Ƙasar Zamfara A Ƙarni Na 21

This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.

Adamu Rabi’u Bakura
Email: arbakura62@gmail.com
Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria

Tsakure

Fahimtar abubuwan da suka shuɗe ta kowace fuskar fannonin rayuwar ɗan Adam abu ne mai matuƙar amfani ga ita kanta rayuwar. Wannan ne ya sa masana tarihi ke iƙirarin cewa duk wanda bai san abin da ya wanzu (faru) kafin haifuwarsa ba, zai kasance tamkar jinjiri har abada, domin zai zamanto da ilimin abin da ya sani ko ya gani, ba tare da fahimtar musabbabin wanzuwar abin ba. Shi tarihi yakan ɗauki fuskoki mabambanta, kamar na ƙasa ko al’umma ko addini ko managartan shugabanni ko adabi da sauran dangogin lamarin ilimin rayuwar zaman duniya. A waɗannan fannoni tarihi yana amfani wajen ilmantar da al’umma nau’in cikin da jiya ta ƙunsa, domin ba da damar sanin abin da yau za ta haifa da kuma irin daraja ko ƙaskanci abin da aka haifa ɗin zai samu a cikin rayuwa. Ganin cewa a farfajiyar ƙasar Hausa an yi wa tarihi riƙon sakainar kashi, alhali kuwa ta hanyarsa ne za a iya tsinkayo abubuwan da suka faru a baya don ƙoƙarin daidaita muhimman abubuwan da ake fuskanta, ta yadda za a ci moriyar managarciyar rayuwa mai ma’ana. Wannan ne ya sa wannan maƙala ta ƙuduri aniyar komawa cikin tarihi don zaƙulo irin rawar da malamai magabata suka taka wajen samar da tabbatuwar tsaro da bunƙasar garuruwan farfajiyar ƙasar Hausa, da musabbabin ƙulluwar dangantakar malamai da sarakuna da sanadiyyar bayyanar tashin hankali a far fajiyar daular Zamfara. Takardar za ta bayar da haske game tushen taɓarɓarewar zaman lafiya a Najeriya ta Arewa da yadda lamarin ya haɓaka har zuwa yau. Ƙarshe za a kawom faɗin-tashin da malaman addinin Musulunci ke yi don ganin an samu zaman lumana a wannan nahiya ta Zamfara da kuma ƙasa baki ɗaya.

1.0 Gabatarwa

Babu wani abu da zai inganta a farfajiyar wannan duniya tamu, dole sai tare da muhimman abubuwa guda uku. Irin waɗannan abubuwa kuwa sun haɗa da, ilimi, hanyar samun isassshen abinci da kuma hanyar tsaron zaman duniyarmu. Saboda kowane abu da ke cikin wannan duniya, in har ya kasance babu tsaro yana da abin da zai iya tarwatsa shi ya ɗaiɗaita shi.

Don haka, ashe ke nan, ya zama wajibi kuma haƙƙinmu mu tashi tsaye mu yi namijin ƙoƙari da ƙwazo fiya da na magabatanmu, domin zamani ya juya. Dole ne mu bi hanyar zamani mu tsare kanmu ga kowane irin al’amarin da ba zai kawo alheri da zaman ƙasashenmu cikin kwanciyar hankali da lumana ba. Kuma mu sani cewa a waɗannan rukunnan yankuna na ƙasar Hausa, an yi mazaje masu dabarun tsare ƙasashensu, da kishin ƙasarsu tare da biyayya ga shugabanni domin samun cikakken tsaron da zai wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Da ba don su ba, da yanzu ƙilan mun kasance a yankin nahiyar ƙasashen Amurka ko Saliyo a sakamakon harin kamen bayi da ya raba uba da ‘ya’yansa ko mata da mijinta. Irin wannan ɗanyen aikin da ya auku a wannan nahiyar, ya ƙasura ne a sakamakon irin alfanun da ƙasashen Turai suka dinga samu a wancan zamanin.

2.0 Wanzuwar Tsaro A Tsakanin Al’umma

Tsaro ya samo tushe ne tun lokacin da ‘yan Adam suka fara kafa mazaunai na dindindin a matsayin tunga da garuruwa har suka samar da shugabanni da za su yi musu jagaranci ta hanyar bayar da umurni da hani tare da hukunta wanda ya fanɗare. Ana cikin haka sai aka wayi gari wasu jinsin mutane na neman mamaye wasu, su handame musu mazauni tare da mayar da su ƙarƙashin ikonsu. Daga lokacin ne maganar tsaro ta soma kere. Daga nan sai aka fara zagaye muhallai da ƙayoyi domin kariya daga farmakin ba zata ta wajen abokan hamayya. Yayin da aka samu bunƙasar tungaye suka koma garuruwa sai aka fara gina ganuwa domin samar da cikakken tsaron rayuwa da dukiya da kariyar mutunci tare da ɗorewar zuriya. Tun daga lokaci sai samar da tsaro ya zama wajibi domin shi ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma da ke doron duniya. Kuma duk shugaba na gari mai kyakkyawan tunani, sai ya fara mayar da hankalinsa wajen lamarin inganta tsaro. Saboda sai da tsaro ne ake samun cigaba mai ma’ana.

Tsaro yanayi ne da ke cikin shirin ko-ta-kwana, tare da samar da cikakkar kariyar al’ummar ƙasa, ba tare da jiran gawon shanu ba har sai bala’i ya far musu, sannan a yi fargar jaji. Yakan kuma kasance yanayin da hankullan al’umma ke kwance, suna cigaba da tafiyar da lamurran harkokinsu na rayuwar yau da kullun cikin kyakkyawan yanayin zamantakewa tare da rashi fargabar aukuwar wani aibu ba.

3.0 Bayyanar Malamai A Farfajiyar Ƙasar Hausa Da Tasirin Addu’a

Bayan wafatin Manzon Allah S.A.W., sai sahabbansa suka yi azamar sadar da addinin Musulunci ga al’ummomi na kusa da na nesa. Bayan wucewar su, sai malamai suka ɗauki wannan nauyin, saboda su ne magada Annabawa, tamkar yadda Annabi S.A.W. ya bayyana. Sai dai Annabawa ba dukiya suka bari ba, sun bar ilimi ne, tun daga lokacin ne malamai suka duƙufa wajen shiryar da al’umma ga lamarin duniya da lahira.

3.1 Kafuwar Daular Sharifai A Ƙasar Zamfara

 Wani muhimmin abu da ya ƙara haɓaka sha’anin malanta da samuwar malamai ya ci gaba da haɓaka sannu a hankali shi ne, samuwar Daular Sharifai a ‘Yandoto wadda ta zama matattara ta gaggan malamai masu ƙoƙari yaɗa ilimin addinin Musulunci, lamarin da ya haifar da yawaitar gogaggun malamai na kowane fannin a wannan nahiya ta jihar Zamfara. Ita wannan daular, Yahaya ɗan Nafsal- Zakiyya ɗan Aliyu Zainul Abidina ɗan Sayyidina Husaini ɗan Sayyidina Aliyu Ibn Abi Talibi daga wajen Nana Faɗima shi ya kafa ta. Sharif Yahaya ya kafa daular ne a ƙarni na takwas Miladiyya. Kuma yana ɗaya daga cikin malaman Imam Malik, wannan ya taimaka wajen ƙaƙa-gidan da Mazhabar Malikiyya ta yi a ƙasashen Hausa, kamar yadda Ibrahim (2009: 16) ya nuna. Daular ta gudana har zuwa zamanin Shehu Usman Ɗanfodiyo.

3.2 Zuwan Malamai A Ƙasar Hausa da Tasirin Addu’a

Tawagar malamai Wangarawa daga Mali ta mutane arba’in sun sami zuwa Kano a zamanin mulkin Sarkin Kano Yaji 1349-1384. Manyan ayarin su haɗa da Abdur-Rahman Zaite da Mandawari da Shehu da Limamin Jujin ‘Yan Loba da kuma Limamin Maɗatai. Sun gabatar masa da maganar addinin Musulunci, sun ko yi sa’a sarkin ya karɓe su hannu biyu, ya kuma amince ya karɓi Musuluncin. Aka naɗa Mandawari Limamin gari, Zaiti kuwa aka naɗa shi Alƙali, Gurdumus Limamin Sarki, yayin da Lawan ya zama Ladanin Sarki, kamar yadda Ibrahim (2009:38) ya nuna. Sarki Yaji ya yi wa al’ummarsa umurni da yin sallah, aka kuma gina masallaci, kowace ƙabila ta yarda tana salla, sai ƙabilar Gazargawa kaɗai suka ƙi yarda da yin salla. Sai suka rinƙa zuwa masallacin suna shafa najasa.

Yayin da lamarinsu ya tsananta, sai aka sa Ɗanbayi da rundunarsa suna gadin masallacin tun daga magariba har zuwa safe; amma mutanen ba su daina sa wa masallacin najasa ba. Malamai suka yanke shawara, suka ga babu maganin abin sai addu’a, suka taru a masallacin suka yi addu’a, Allah kuwa ya karɓi addu’arsu. Shugaban mutanen ya makance, sauran duk wanda ya taɓa zuwa wurin ya sa najasa sai ya makance shi da matarsa (Dokaji, 1978:15) da (Waya,2000:6). Haka a zamanin Sarkin Kano Kukuna, sai sha’anin sarautarsa ya fara rawa, sai ya nemi Limamin ‘Yandoya aka yi masa wani dafa’i aka binne a Zauren Kuka da Zauren Turaki da Turakar Kano domin duk wanda ya sarauci Kano kada a cire shi, komai tsawon lokaci (Dokaji, 1978:26).

A zamanin Sarkin Kano Alwali, ɗansa da ake kira Ɗanmama da ke riƙe da sarautar Ciroman Kano, ya yi hawa tare da baradensa, ya tafi Gwale wajen gonakin Malam Abdullahi Suka, sai dawakansa suka kakkarya amfanin gonar malamin. Da malamin ya ga abin da Ciroman ya yi masa, sai ya yi addu’a a kan kada Allah ya ba yaron nan gadon sarautar ubansa. Shi ke nan tun daga wancan lokacin duk wanda aka yi wa sarautar Ciroman Kano, ba a taɓa ganin wanda ya sami sarautar Sarkin Kano ba, sai Sarkin Kano Abdullahi Bayero ɗan Abbas abin ya warware, kamar yadda Dokaji (1978:28) ya nuna. Tun daga wannan lokacin ne Kanawa ke riƙe da malamai, kuma ba sa wasa da addu’a a cikin kowane lamari.

Fahimtar irin tasirin da malaman addinin Musulunci ke da shi a fannonin lamurran duniya da ma na gobe ƙiyama, ya sa sarakuna da jinin sarauta kusantar malamai domin samun damar biyan buƙatunsu na ƙoƙarin samun shiga gidan sarauta ko kuma samun galabar murƙushe abokan adawarsu ko maƙwabtansu ta yadda za su dawo ƙarƙashin ikonsu. Sakamakon irin wannan mu’amala ce aka sami gwarzaye a farfajiyar ƙasar Hausa, kamar irin su Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo da sauransu.

Dalilan Taɓarɓarewar Tsaro A Jahar Zamfara

Bayyanar mulkin siyasa ya taimaka matuƙa wajen lalacewar tarbiyyar matasa a wannan jahar, musamman ta fuskar shaye-shayen abubuwan da ke sa maye. Duk da kasancewar an jaddada gudanar da shara’ar Musulunci, amma wannan bai hana maƙaraban shayar da matasa abubuwan da ke sa maye ba. Alhali kuwa sun san yin haka haramun ne. Ana yin haka ɗin ne domin cimma wata manufa ta siyasa. Da nau’in irin wannan matasan ne ake amfani wajen gallaza wa abokan adawar siyasa na cikin gida ko na wata lemar siyasa ta daban. Irin waɗannan ‘yanbangar siyasar ne akan tura su kasha wasu ‘yan siyasar da ake jin za su iya kawo cikasa ga wasu ko wani.

A bayyane yake ƙarara, an sha ganin irin waɗannan matasan suna aikata ayyukan ta’addanci a tsakanin jama’a ba tare da hukuma ta ɗauki mataki ba. An sha kisan bayin Allah a sakamakon bambancin siyasa, a rasa wanda ya aikata. Hasali ma irin waɗannan ‘yan bangar siyasar suna samun kuɗaɗen da suka wuce misali a shekarun da suka shuɗe. kuma da su aka yi yaƙin neman zaɓe,wanda suke cike da burin za su dara idan aka yi nasara. Sai lamarin ya zo musu ba yadda suka zata ba. Duban irin sauyin da ya faru gare su, shi yasa al’umma ke hasashen cewa irinsu ne suka tare a dawa suna gudanar da ta’addaci tare da abokansu da ke zaune a cikin birane da ƙauyuka suna aika musu da rahotannin mutane akai-akai don neman kuɗin fansa.

Wannan lamarin ya zama ruwan dare zagaye duniya. Allah ne kawai zai tsarkake ‘yan siyasar wannan jahar daga zargin mutane, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ba irin waɗannan mutane wasu muƙaman siyasa. Wani lamarin da ya ƙara sa su zama abin zargi bai wuce yadda aka rinƙa saka Alƙur’ani Mai tsalki cikin shadda ba, hasali ma zaɓe na ƙaratowa, lamarin sai ƙara ta’azzara yake. Idan kuwa abubuwa irin waɗannan na faruwa a jahar da ake da’awa da ta shari’a, ai dole ne al’umma su girbi abubuwan da suka shuka.

Gudummuwar Malaman Ƙasar Zamfara

Tun lokacin ɓarkewar yaƙin basasa na biyu da ya auku, malamai suke tsaye ga yin addu’o’in samun zaman lafiyar wannan yanki da kuma ƙasa baki ɗaya, a duk lokuttan da aka kammala sallolin farilla guda biyar da ake aiwatarwa kowace rana. Ba nan kaɗai ake aiwatar da irin waɗannan addu’o’in ba, har da wuraren taron ɗaurin aure ko zanen suna ko naɗin sarauta ko wata walima. Irin waɗannan addu’o’i da malamai suke aiwatarwa ba ƙaramar garkuwa ba ne wajen yaƙar ta’addanci a tsakanin al’umma.

Masarautun Ƙasar Zamfara

Yayin da lamarin rashin tsaro ya yi ƙamari wasu masarautu sun yi ƙoƙarin kiran tarurrukan malamai da limamai domin tattaunawa game da matakan da ya kamata a ɗauka don maganin matsalar ɓarayi da ta kunno kai da kuma satar shanu. Misali a Masarautar Bakura, Sarkin Ɓurmin Bakura ENGR. Bello Sani, ya kira irin wannan taron malamai da limaman da ke farfajiyar masarautarsa, inda ya nemi shawara game da hanyar da ta dace a bi domin maganin bala’in da ke tunkarar al’ummar masarautar da jaha da kuma ƙasa baki ɗaya. Malaman suka tsayu a kan cewa, yayin da bala’i ya kunno kai irin wannan, ba wata hanyar da ta dace sai a fuskanci lamari addu’a.

Masanan sun shawarci sarkin da ya bayar da umurnin yin amfani da masallatan juma’a a riƙa yin addu’o’i a ranakun Alhamis da Juma’a bayan sallar asuba a sauke Alƙur’ani a duk sati. Yayin da shi kansa Sarkin Ɓurmin Bakura ya bayar da gudummuwar Ƙur’anai guda sittin a raba a manyan masallatan juma’a da ke garuruwan uwayen ƙasa da zawiyyoyin da ke faɗin masarautar (Sulaiman,2020).

Kwamitin Da’awa na Ƙaramar Hukumar Mulki ta Bakura, sun zagaya saƙo da lungu da ke yankin domin wa’azin wayar da kan al’umma dangane da muhimmanci tsaro a yankunansu da kuma illar zubar da jinin al’umma da salwantar da dukiyarsu ba bisa haƙƙin shari’ar Musulunci ba. Masanan sun faɗakar da al’ummomin cewa, wajibi ne kowane musulmi ya kasance wakilin jami’an tsaro a cikin yankinsu, ta hanyar sanya ido a kan irin nau’o’in mutanen da za su yi hulɗa da su. Yayin da suka ga baƙuwar fuska wadda ba a san matsayinta a cikin al’ummarsu ba, sai a hanzarta kai rahoto wajen jami’an tsaron yankin don binciken matsayinsu a yankin.

Masu wa’azi a masallatan juma’a da ke faɗin masarautar kuwa, suna faɗakar da masallata game da irin gudummawar da ya kamata su bayar wajen kawar da ta’addaci tare da samar da tsaro da hanyoyin kare kansu. Malaman sun samar da wasu addu’o’i ga al’ummar masarauta waɗanda za su dinga karantawa domin neman kariya ga ƙasashensu da jaha da kuma ƙasa baki ɗaya. Misalan addu’o’in su ne kamar haka:

بسم الله الر حمن الرحيم   

يس والقرءان الاحكيم .(1000) تبت يدآ أبى لهب .(1000) إنك لمن المرسلين.(1000)ماأغنى عنه ماله وماكسب .(1000), على صراط مستقيم.(1000), سيصلى نارا ذات لهب.(1000),تنزيل العزيز الرحيم.(1000), وامرأته  حمالةالحطب.(1000),لتنذرقومامآأنذر ءاباؤهم فهم غافلون.(1000), فى جيدها حبل من مسد.(1000)

بسم الله الرحمن الرحيم 

لقد جآءكم رسول من انفسكم عزيز عليه ماعنتم حريص عليكم بالمومنين رءوف رحيم. فإن تولوا فقل حسبي الله لا إله الاهوعليه توكلت وهو رب العرش العظيم.(41)

بسم الله الر حمن الرحيم 

اللهم اقطع أجل أمل معتدين وشتت اللهم شملهم وأمرهم,وفرق جمعهم, واقلب تدبيرهم, وبدل أحوالهم , ونكس أعلا مهم, وأكل سلا حهم , وقرب آجا لهم, ونقص أعمارهم, وزلزل أقدامهم, وغير أفكارهم, وخيب آمالهم, وخرب بنيانهم, واقلع آثارهم حتى لا تبقى لهم باقية ولا يجدوا لهم واقية, واشغلهم بأبدانهم وأنفسهم, وأبدهم بصواعق انتقامك, وابطش بهم بطشا شديدا,وخذهم أخذاعزيزا,إنك على كل شىءقدير, ولاحول ولاقوة إلابالله العلى العظيم. اللهم لا نمنعهم ولا نرفعهم إلابك, اللهم إنا نجعلك فى نحورهم, ونعوذبك من شرورهم,يامالك يوم الدين إياك نعبد, وإياك نستعين عليهم, فدمرهم تدميرا. وتبرهم تتبيرا فاجعلهم هباء منثورا, آمين 

اللهم من أرادنا والإسلام والمسلمين بسوء اوشرٍ فاضربه بسيف انتقامك القاتل, وارمه رمية تصيب منه المقاتل, وأذقه وبال امره عاجلاًغيرَ آجلٍ, اللهم اقمع بأسهُ, وَاعقدْلسانه, وألجمْ فاهُ, واحْبِس يديْهِ, وَحُلْ بينناو بينهُ كيف شئتَ و أنَّى شئتَ, بِقُوَّتك ياقوىُّ يا متينُ, اللهم اجعله عبرة للحاضرِ والبَاد, فإنك أنت المَليكُ المقتدر القا هرُ فوق العبادِ. 

اللهم كن لبِلادِ الإسلامِ والمسلمين حافظًا من مكرِ كُلِّ ماكرٍ, وفُجُورِ كلِّ فا جرٍ, وغدرِ كلِّ غادرٍ, وحسدٍ كلّ حاسدٍوحا قدٍ, و ظلمِ كلِّ ظا لمٍ, وفسادِ كلِّ فاسدٍ, وشما تة كل شا متٍ وعداوةِ كلِّ عدوِّ, ومن كلِّ سوءٍ و شرٍّ, ومن كلِّ بلاءٍ و مرضٍ وضرٍّ, و نجنا والمسلمين اجمعين من جميع المهالك والمضارِّ والمعاصى والحرام والضلال, يا شديدَالمحال, يا من إليه المرجعُ والمآلُ. اللهم عليك بكلِّ من يؤْذِى المسلمين.

اللهم احفظ بلادنا من شر الكوارِثِ والزلازِلِ والسُّيُولِ والبراكتن و جميع البلايا, وثبِّتْ الأرض من تحت اقدام المسلمين, وزَلْزِلِ الأرض من تحت أقدام أعداء المسلمين. اللهم زلزل الأرض من تحت اقدام الكافِرِين بقوَّتك يا قوِيُّ يا متين, يا خير السائلين,يا حرْزَ الضعفاءِ والمساكينَ.  

Ganin irin muhimmiyar rawar da malaman ke takawa ne, kwamitin tsaro na Ƙaramar Hukumar Mulki ta Bakura ya sanya malamai cikin kwamitin a matsayin masu bayar da shawara ga babban kwamitin tsaro wanda Masarautar Bakura da Ƙaramar Hukuma suka kafa.

Faɗakar Da Al’umma Ta Sigar Waƙoƙi

Malamai da almajirai sun yi ƙoƙarin bayar da tasu gudummawa wajen kawar da wannan masifar da ta addabi al’umma ta hanyar rubuta waƙoƙi cikin sigar rubutun ajami da na boko domin faɗakar da al’umma game da amfanin zaman lafiya da aibin shiga cikin lamarin ta’addanci, musamman matasa waɗanda ‘yan siyasa ake yi wa iza mai kantu ruwa, domin biyan muradunsu na siyasa. Sai dai a nan za a kawo misalai ne daga waƙar Malan Is’haƙa Wadatau Ubaidullah, wadda ke ɗauke da muhimman abubuwan wa’aztarwa, mai take: “Faɗakarwa Ga ‘Yan Uwa Danginmu” da ake hasashen ta ƙunshi wasu daga cikin muhimman abubuwan da wannan takarda ke magana a kansu.

Misali, a cikin waƙar, malamin ya soma da jan hakalin al’umma, musammam matasa don guje wa yaudarar ‘yan siyasar nan da ke amfani da tsattsauran ra’ayin addini ko bambanci ƙabila ko ɓangaranci (yanki) ko bambancin harshen al’umma, wajen tayar da zaune-tsaye domin cimma manufarsu ta siyasa. Ga abin da yake cewa:

Lura ku farka ku zan cikin hayacin kanku,

Wansu mutane salon su zan riƙa juya ku,

Don cimma nufinsu gunku sai sun raba kanku,

Ta addini ko jiha ko harshenku,

Ka san haka ɗan ƙasarmu don kar a zuga ka.

A wani baitin malamin ya yi tsokaci ne game da irin nau’in iza-wawa-rima da masu kwaɗayin mulkin wannan zamani ke yi wa matasa wajen tura su su aikata ayukkan assha don su sami biyan buƙatun kansu, daga bisani su yi watsi da su. Yana jan hankalin jama’a don su kula da makirce-makircen ‘yan siyasa wajen tunzura yaransu ta yadda za su tayar da husuma, domin su sami damar ci da gumin al’umma ba don taimakonsu ba. Hasali ma ya shawarci matasa da kada su sake su koma karnukan farautar waɗanda ke tura su zuwa ga bangar siyasa. Ya ƙara da cewa, duk wanda aka kashe shi ya yi hasara, ƙarawa da ƙarau in wani amfani ya zo, iyayen gidansa zai riska, ba ruwansu da wanda aka kashe ko aka naƙasa. A waɗannan baitocin ga a abin da yake cewa:

Shi mai cutarka shi ka zuwa ya zuga ka,

Yana sababin faɗa anan za ya gaya ka,

Mi za ka jira ga wanda yak kashe yankinka,

Ko ya ka sake har aka danne ƙabilarka,

Tada jidali haƙiƙa ne zan kare ka.

 

Kullun su tuƙa su warware bai ƙare ba,

Ya za su kawar da hankalinku su yo zamba,

Sui maka kicihi ga ‘yan uwanka kuna gaba,

Suna daɗa dariyarku wai ba ku gane ba,

Su iska kai kaba suna riƙa juya ka.

 

Kar ku zamo karnukan farauta ku biye su,

Ku za su iza shiga cikin haɗari bas su,

Komai ka kashe su za su sa birgamensu,

Kai kuma ko an kashe ka su sun yi nakansu,

Da ma nufarsu kansu kai kuma a iza ka.

Malamin ya nuna munin tada fitina da sakamakonta tare da kawo muhimmanci zaman lafiya da haɗin kan al’ummar ƙasa. Ya kuma jawo hankullan irin mutanen nan da ke ƙoƙarin raba kan al’ummar ƙasa tare da nuna aibin rashin mutunta al’dun juna da ƙin karɓar ra’ayoyin al’umma da rashin son ci gaban juna da nuna ƙyama ga wani jinsin al’umma. Hasali ma ya kawo irin munin da abin zai haifar a tsakanin al’umma. Ga abin da yake cewa:

Ka san duk wanda kat taɓa wa mutuncinsa,

Ya hanƙura sai ka bi shi kar riƙa zagin shi,

Ya ƙyale kab bi har kana riƙa taka shi,

Ya bar ka ka zare hannuwanka ka tsone shi,

Ai ko bai so ba dole zai kwaɓe hannunka.

 

Bari neman tada hargitsi gun jama’arka,

Ƙyale bala’i ka daina fatan ya ishe ka,

Allah ya tsare idan ya zo ba ya barin ka,

Haƙiƙa jikinka ba ya tsere jadalinka,

Tsuntsun da ya ce ruwa ya zo shi zai doka.

 

Mi yaf fi zama da lafiya don Rahmani,

Ka zauna babu fargaba alheri ne,

 Kyautace yanayin mu’amala shi nasara ne,

Haɗin kan ‘yan ƙasarka tushen ni’ima ne,

Nemi zama lafiya ƙasarka da yankinka.

 

Kar ka rabe kan mutan ƙasa don gurinka,

Yare harshenka ne abokin hulɗarka,

Shi ne sirrinka nan tsakanin jama’arka,

Kar ka zata wanda ba ya jinai bai son ka,

Yanayin hulɗa ka sanya ƙauna ko ƙinka.

 

Ƙabilanci ta’assubi mai saka ƙyashi,

Ya ci rayukkan mutan ƙasa wani sharrinshi,

Wanda ake wa ya ciutu har shi mai yin shi,

Da za ka yi tambaya wurin wanda ka yin shi,

Wa ce riba yac ci gunsa ba za ya gaya ka.

Ya kuma tunatar da al’umma cewa, sun fito daga tsatso ɗaya ne, wato su zuriyar Annabi Adamu ne Hauwa’u kuma Allah cikin hikimominsa ya halicce mu mabambantan harsuna ƙabila nau’i-nau’i da kamannu daban-daban da falsafar tunanin zaman duniya da addini su ma sun saɓa da na juna. Ya kuma yi kira ga Musulmi da Kiristoci da su kula da yanayin tsarin zamantakewar wannan ƙasa da ta kasance ta haɗin kai (tarayya) ce, don haka kar wani ya aibanta wani. Kowa ya tsaya matsayinsa kada wanda ya raina wani ko ya tsokani wani da fitina a sakamakon bambancin addini ko na jinsin al’umma, domin lalurar zaman ƙasa da ta haɗa al’umma. Ga abin da yake cewa a waɗannan baitocin:

Yare yanayinsa ‘yan uwan juna ne shi,

Adamu shi ne uba ga duk wani mai yin shi,

Allah yay yi shi yay yi yare harshenshi,

Mu ya yi mu ƙaba’ila Tabaraka da nufinshi,

Domin hikimarsa Jalla mun daɗa gode ka.

 

Dubo kwanan ƙasarka ɗai gun jama’a su,

Duba yawan ‘yan ƙasarka duba halussansu,

Duba kamannunsu kana ga al’adarsu,

Dubi tunaninsu kana ga addininsu,

Musulmi da kirista waɗansu na don kaka.

 

To mu muslim da ku kirista nika zance,

Ai kowane nasa yar riƙe don ya amince,

Kai kar ka taɓani ban taɓa ka mu tan tance,

Yanayin tsarin zaman ƙasar tarayya ce,

Kar ka yi ciuta gare ni kar in ciuta ka.

 

Komai kaka ji a ranka kan addininka,

Ai ba ka fitar da ni ƙasar don gurinka,

Ni ba ni fitar da kai ƙasarka ta gadonka,

Kai ba ka hana ni in yi, ni ba ni hana ka,

Komai ya zamo haka ka san ya wuce yin ka.

 

Tunda lalurar zama ƙasa ɗaya ta haɗa mu,

To, sai mu tsaya mu tattaro hankullammu,

Ya za mu zama da kammu ba mai ciuta mu,

Kai tsare huruminka in tsare nau haƙƙimmu,

Kar ɗaya yai tsokana ga ɗai ko raina ka.

Ba nan kawai ya tsaya ba a wajen ƙoƙarin ganin an kawar da ta’addanci an samu zaman lumana a tsakanin al’umma, malamin ya nemi iyaye da maga’isan yara da su sanya idanunsu akan nau’in mutanen da ‘ya’yansu ke mu’amala da su, a makaranta ne ko a gida, musamman mutanen da ba su da kimtsi ko kan gado, don gudun kada a ɓata tarbiyyar ‘ya’yansu, wanda hakan na iya zama masifa ga iyayen da kuma al’umma baki ɗaya. Ga abin da yake cewa a waɗannan baitocin:

Lura da yaronka gun abokan hulɗar shi,

Makaranta ko gida ga mai son ya matse shi,

Mugu zai ɓata naka komai kirkin shi,

Mahaƙar kanwa ruwanshi dole ya ɓata shi,

Ka ga zaman tare zai raba ka da kirkinka.

 

Kuma kar ka sake a gan shi tare da shashasha,

Don ba ya gudun a gan shi yai aikin assha,

Komi aka sha a dinga yin maye zai sha,

Ya ka ga tafiyarku shi ya sha kai ba ka sha,

Babban haɗari ka zan biyar mai ciuta ka.

Su ma matasan bai bar su a baya ba, domin ya fito fili ƙarara yana kira gare su da su guji zama ‘yan bangar siyasar waɗanda ke sa su shan ƙwaya da daga tare da ba su muggan makamai domin gudanar da ta’addancin kashe ko raunana abokan adawa (hamayya). Ga abin da ya ce:

Kamar wasu ‘yan ƙasa da ke son mulkinku,

Babban haɗarinsu gunku ɓata ɗabi’ar’ku,

Ƙwaya suka ba ku har da daga su zuga ku,

Ku sha ku buge su baku adda su iza ku,

Ku je ku kashe waɗansu ko kai a kashe ka.

Ya kuma faɗakar da al’umma cewa, duk abin da mutun ya shuka shi zai girba. Wato idan ka cutar da wani yau gobe kai ma sai ka sami wanda zai yi maka kamar yadda ka aikata ga wani. Ga abin da yake cewa a wannan baiti:

Ɓarnar da ka je ka yo ka san ita za a yi ma,

Yau in wani ya yi jibi wancan za ai ma

Ya kai kuma za ka yo ya zan kai ba ai ma,

Komi kaka jin kana iya wa, wani nai ma,

Ai maka rauni anaƙ ƙasa ko a kashe ka.

Ya tunatar da al’umma nau’in ni’imar da Allah ya yi musu, ta ƙoshin lafiya, da yadda aka yi watsi da ni’imar aka auka cikin halaka ta hanyar fanɗarewa da ƙin bin dokokin Allah da na hukuma. Ya kuma bayyana haɗarin da ke tattare da hakan. Ya tunatar da matasa cewa, da zarar an naƙasa su, waɗanda ke amfana daga ta’addancin nasu, za su guje musu domin ba sa sake wani amfani gare su. Ga abin da ya ce:

Allah ya yo ka lafiya ya raya ka,

Kai sai kaz zaɓi yin ta’adda ka sa kanka,

Ko ba ka san aƙibar ba kay yaudari kanka,

Wai kai ɗan wane, wane ne gagara doka,

In aka naƙasa ka, ka gama sai su ije ka.

Haka, ya nemi matasan da su yi amfani da idon basira, su lura da yanayin da suke ciki da wanda ‘ya’yan waɗanda suke ta’addanci don su, suka kasance. Yaya suke yi musu tarbiyya? Suna ayyukan da su suke aikatawa na ta’addanci ko yaya? Su duba nau’o’in makarantun da suke kai ‘ya’yansu a nan cikin gida da ƙasashen waje, yayin da su aka yi wa nasu ilimin riƙon sakainar kashi.

Haka ma za a sami ‘ya’yan Sanatoci da na ‘Yan Majalisar Wakilai da na Majalisun Dokoki da na Shugabannin Ƙananan Hukumomi sun yi karatunsu ko suna yi a makarantu da jami’o’in ƙasashen waje ko masu zaman kansu. Sun yi haka ne don ‘ya’yansu su sami damar yi wa ‘ya’yan waɗanda iyayensu ke yi wa mulkin danniya da sunan dimokaraɗiyya, su ma su yi musu, idan su sami ingantaccen ilimi. Saboda suna da masaniyar samun ingantaccen ilimi shi ne gishiƙin ɗorewar ci gaban kowace al’umma, rashin sa kan jefa ta cikin bauta ta ƙasƙanci. Wannan ne manufar ‘yan siyasa, shi yasa suke karkatar da kuɗaɗen al’umma wajen taskace su a ƙasashen waje da sunan biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansu. Hasali ma rahoton CBN ya nuna ana kashe 1.6 tiriliyan a duk shekara wajen biyan kuɗin makarantar ɗalibai da ke karatu a ƙasashen waje. Ga abin da ya ce:

Kai je ka aje dabarka zo saka kunnenka,

Saurari uban gidanka zancenshi a kanka,

Horo yaka yi ga ɗansa kar ya bi hanyarka,

Aiki na ta’adda bai da kyau bari sa kanka,

Dubo ayukansu shin waɗanne ka burge ka.

 

Sai su bi hanya su kai suna daɗa komowa,

Sai ɗaga murya suke suna daɗa ƙarawa,

Sun cire kunya idonsu wa suka shaya wa,

Mutunci ag gare ka sa iya ketawa,

Zaginka gare su bai wuya ko dukan ka.

 

Wai su sun kai ga ƙul ta huskar wayewa,

Zatonsu ka zan tsagera shi ne wayewa,

Ko ƙin ladabi ga babba ko kuma rainawa,

Ko yin ‘yan shaye-shaye wanda ka ciutarwa,

Bas su ka koma Sakandare ka yi ilminka.

 

Sun ce ma ɗiyan ku bar biyar masu takobi,

Babu makoma gare su, yau babu ta gobe,

Ku je ku yi ilmi don ku zan manyan gobe,

Duk makarantar da kaf fi so yau ko gobe,

Nan a gida ko ƙasar waje zan tura ka.

 

 Daure ku yi ilmi tunda shi ne nasarar ku,

Don ku bi sawummu kui ta taunar mulkinku,

Masu biya gummu sai ɗiyansu su zan binku,

Sun zama bayinku ba su da ilminku,

Har abada sai a bi ku ba mai mulkinka.

Wani wurin kuwa, malamin faɗakar da al’umma ne ya yi domin su falka daga shantakewar da suka yi, su yi nazarin yadda lamurran ‘yan siyasar ƙasar nan ke gudana, ta yadda suke ƙoƙarin jefa ‘ya’yan talakawa a cikin mummunan tafarkin ta’addanci, yayin da ba su barin ‘ya’yansu su kusanci ‘yan ta’addan. Ya kuma nemi ‘yan siyasar da su yi ƙoƙarin gina ayukkan alheri a tsakanin al’umma baki ɗaya. Hasali ma ya nuna rashin dacewar su zama jagororin al’umma, domin ana buƙatar shugaba ya kasance mai hani ga aikata munanan ayukka tare da yin horo ga aikata ayukkan da za su wanzar da alheri a tsakanin al’umma. Ga abin da yake cewa a waɗannan baitocin:

Biri kuwa yai kama da siga ta mutane,

Wane ɗa ne nasu kag ga ya zo yai zaune,

Ya riƙe adda jiran bala’i da mutane,

Shi ya zama ɗan daba ubansa yana zaune,

Ko kusa bai faruwa uban ba ya barinka.

 

Komi kaka so ga ɗanka gun ɗan wani so shi,

Komi kaka ƙi garai a gun wani ma ƙi shi,

Amfanin hankali ga mai shi aikin shi,

Ka hana ɓanna ga ɗanka, ɗan wani ka iza shi,

To mi ah hankalinka mi ak kirkinka.

Kusan bakin al’ummar ƙasa ya zama ɗaya ta haujin yadda ake zargin ‘yan siyasar ƙasarnan da cewa su ne ummul haba’isan waɗannan nau’o’in ta’addancin da ke gudana a ƙasar nan. Hasalima, binciken kwamitin malamai da aka ɗora wa alhakin sulhu a tsakanin manoma da makiyaya da Gwamnatin Zamfara ta naɗa da yadda aka yi watsi da rahoton, da rushe kwamitin tare da sanya waɗanda ake tuhuma ( zargi ) da hannu dumu-dumu wajen aikata ta’addanci, a sabon kwamitin da gwamnatin ta sake ƙaddamarwa, duk abubuwa ne da suka ƙara haifar da shakku a zukatan al’ummar wannan jahar. Wani lamari mai ɗaure kai kuwa shi yadda aka riƙa samun ‘yan siyasa da hannu dumu-dumu a cikin lamarin, har ta kai ana ba ‘yan ta’adda muƙamai daban-daban a cikin gwamnati. Shi ma Malamin ya bi sahun al’umma a inda yake cewa:

‘Yan bangar siyasan nan fa ku kuka gina su,

Sai kui nazari ku gane mi yah haifa su?

Abu biyu na ɗayan haƙin uwaye na kula su,

In an ƙi kula su, sai su nemo hanyarsu,

Komai muninta don su rayu suna ɗauka.

 

Na biyu ku manya-manya wanda ka tura su,

Kui maslaha gun su a’a sai sun kashe kansu,

Kun danne haƙƙuƙuwansu kun hana su ishe su,

Sai ga buƙatarku ɗai ku samma su ku iza su,

Sui ta bala’i wurin su kare buƙatarka.

Yayin da aka nazarci waɗannan baitoci biyu da suka gabata, aka kuma koma a kan rahoton Sabi’u Ɗanmudi, wakilin wata jarida ta kafar sadarwa mai suna “Jaridarmikiya.com”, a kanun labarin da ya yi wa take: Tonon Silili: Yadda muka shigo da ‘yanta’addan Fulani daga Mali, Saliyo, Senegal da sauransu. Domin su taimaka mana a zaɓen 2015. Wakilin jaridar ya nuna cewa:

Abubakar Kawu Baraje, tsohon jigo a jam’iyyar APC mai mulki a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ya gano asalin rashin tsaro da ake fama da shi a ƙasar nan tun bayan kwararowar Fulani daga ƙasashen makwabta kamar: Saliyo da Mali da Senegal da Nijar da Chadi da aka kawo cikin ƙasar domin zaɓe a 2015.

Ya bayyana haka ne a garin Ilorin a wani ɓangare na gudanar da bukukuwan cikarsa shekaru 70 a duniya. Baraje, ya bayyana cewa, Fulanin da ke haddasa fitina a ƙasar nan ba ‘yan asalin Nijeriya ba ne. A cewarsa, an kawo Fulanin da ke haddasa matsalolin tsaro, a ƙasar ne domin su taimaka wajen samun nasara a zaɓen 2015. Bayan an yi zaɓe Fulani sun ƙi fita. Ni da sauran masu tunani na rubuta kuma na gargaɗi waɗanda muka fara APC da cewa hakan zai faru, amma babu wanda ya saurare mu” ( Jaridar Mikiya 3/8/2022). (Jaridarmikiya.com).

A wasu baitukan nasa, faɗakar da al’umma ne ya yi, ta hanyar bayyana musu cewa, ba wani mahaliki da zai iya wadata (yalwata) su da abubuwan buƙatunsu in ba Allah ba. Hasali ma duk wani abin duniya da mutun zai samar bai kai kwatankwacin rayuwa ba. Ya ƙara lurar da matasan cewa, duk wani ƙoƙarin faranta musu rai da aka yi, ba za su kai farin cikin ‘ya’yan ‘yan siyasar ba. ya kawo misalan nau’o’in makarantun da suka tura ‘ya’yansu. Ya sake karkato da hankullan al’umma don su gane cewa, wasu harkokin da ‘yan siyasar ke da’awar gudanarwa don al’umma, yaudara ce kawai da ha’inci da cutar ƙasa, mafi yawan amfanin yana zurara ne a aljihunsu. A ɗaya haujin kuwa, tunatar da masu riƙe da madafun iko ne ya yi, inda ya nuna cewa, duk matsayin da mutun ya sami kansa a kai, an ba shi ne a matsayin reno, ta yadda zai kiyaye abin kamar nasa, ba tare da salwantar wani sashe ko aibu ya sami abun ba. Ya yi nuni da cewa, duk wanda ya aiwatar da wata yaudara a cikin abin nan da Allah ya ba shi kulawa, haƙiƙa Allah zai kama shi, kamun da ba zai kuɓuta ba, kamar yadda suka zo a waɗannan baitocin:

 Yara ku farka abun da ab baku gane ba,

Ba mai maku arziƙi idan ba Allah ba,

Komai suka ce su baku bai yi kamar rai ba,

Ba ku ji daɗi irin na ‘ya’yansu ba duba,

Ko makarantun da sun ka je wa ka saka ka.

 

Allah ya yo ku ‘yan ƙasa ɗaya a mutane,

Duk wasu albarkatunta haƙƙin jama’a ne,

Keɓe shi ga wansu su kaɗai zalunci ne,

Duk wani matsayi da anka ba ka amana ne,

In kuma ka ci ta Rabbana ba ya barinka.

A waɗansu baitocin kuwa, ya jawo hankullan matasan ne game da gurinsa na ganin sun kasance mutane nagari da za su amfani kansu da al’umma baki ɗaya. Idan suna son neman wani matsayin siyasa ne, sai su shiga a dama da su. Amma kada su yarda su zama kangararrun da za a yi amfani da su wajen cimma wata manufa ta siyasa da ke iya wanzar da tashin hankali a tsakanin al’umma. Ya yi kira ne gare su don su kyautata halayensu na kirki tare da kauce wa duk wani abu da zai sa su wanzar da tashin hankali da hargitsi, ta yadda al’umma za ta more wa alherin wanzuwar rayuwarsu ta duniya. Haka ya buƙace su da aiki da umurnin da iyaye nagari ke yi wa ‘ya’yansu a kan aikata kyawawan ayyuka tare da guje wa ayukan assha, a inda yake cewa a waɗannan baitocin:

Na yi kira gunku ku matasa jama’ata,

Ba ni ƙiyayya da ku nufina ku kwatanta,

Kui ta siyasarku in kuna da buƙatarta,

Amma rigar dabar siyasa ku aje ta,

Domin tsare lafiya mu amfana da ranka.

 

Ko babu uba gare ka to kashe kunnenka,

In ka ji wani ɗa, ubansa na sa masa doka,

Je ka kayi kaza ka bar kaza tara hannunka,

Kama ka riƙe, ya zan wasiyya ne gunka,

To, inga ta yadda mai uba zai tsere ka.

A wani baitin kuwa, addu’ar neman samun shiriyar Ubangiji ya yi wa matasan, domin su amfani kansu da kuma al’ummar ƙasa baki ɗaya, a inda yake cewa:

Na roƙi Rashidu rabbu mai yanda yake so,

Mai iya sauyin dare da rana tafiyar su,

Don sunayenka masu tsarki dukkansu,

Yarammu da sun ka kauce hanya ka shira su,

Sa su ga hanyar da ta fi domin rahamarka.

 

Shirya su su zan cikin mutane shiryayyi,

Ya zan sun shiryu babu sauran wani maye,

In ka shirya su bai wa kowa aikin yi,

Yai amfani ga kansa dangi da iyaye,

Har ma jama’ar ƙasa su more bawanka.

Ya kuma cigaba da tunatar da al’umma irin sakamakon da mutun zai samu a ranar sakamako (lahira) na dukkan nau’o’in ayyukan da ya aiwatar a zamansa na duniya. Waɗanda suka yi ayyuka nagari za su kasance a ƙarƙashin inuwar Al’arshi, wadda ba wata inuwa a ranar sai ta Al’arshin. Saboda haka, a ƙaurace wa duk wasu shaye-shayen abubuwan da ke sa hankalin mutun ya gushe har ya kai ga aikata abubuwan da Allah ya hana. Ga abin da yake cewa:

Komi ka aikata ka iske jaza’insa,

To in aikinka ya yi kyau Jalla ya ansa,

Sannan kuma lahira ya saka a inuwarsa,

Ranar kuma babu innuwa sai inuwarsa,

To kada kurɓi ya ɓata sha tsare aikinka.

Ya kuma jawo hankalin al’umma da su haɗa hankalinsu waje ɗaya don bin diddigin abubuwan da suka aikata na ƙwarai da akasansu a zamansu na duniya, su auna su da kansu, su duba wace riba ce suka ci, wadda za ta sa su samu rahamar Ubangiji a sakamakon taimaka wa al’umma da tarbiyyar dangi da sauran jama’a. Ga abin da yake cewa:

Ka soma hisabi a kanka kan ya taho kanka,

Shiga gulbin tuntune a kogin ayukanka,

Duka alhairin da kay yi taro shi da kanka,

Tattara manya da ‘yan ƙanana na sharrinka,

Haɗa su ka auna su hankalinka sakelinka.

 

Auna tsawon rayuwarka auna ayukkanka,

Mi ya rage ma na rayuwa ga ƙiyasinka,

Mi kay yi naƙwarai a duniya don lahirarka,

Mi kai wa jama’a na taimako da halalinka,

Mi kas shiuka na tarbiya gun zuriyarka.

Ya nemi al’umma da su yi ƙoƙari tanadin haɗuwarsu da Allah, kafin ajalinsu (mutwarsu), domin tana iya aukuwa a kowane lokaci ba tare da sanin mutun ba. Idan lokacinta ya zo ba a daɗa wa mutun ko daƙiƙa ba, sai tafiya ba wani jinkiri da za a yi ma mutun na shiri. Babu abokin zama a kabari sai aikin da mutun ya aikata a rayuwarsa ta duniya, idan ya aikata alheri shi ne zai zauna tare da shi, in akasinsa ne kuma shi ne abokin zamansa. Ya kuma tunatar da jama’a cewa, duk abin da mutn ya mallaka a duniya, nan zai bar su. Abin da ya rage ga mutun shi ne bayanin yadda ya tara su. Su kuwa magada yayin da uban ya karɓi kiran mahaliccinsa, sai su yi ta tsalle game da garaɓasar da za su kwasa in an raba dukiyar. Ga abin da ya ce a waɗannan baitocin:

Kai zama da shirinka don gamonka da mahalicci,

Manzon mutuwa idan ya zo ba wani zance,

Sai tafiya wadda dole ne za ta kasance,

Ko dare ko rana safiya ko da marece,

Ran ban kwana da duniya da iyalinka.

 

Tafiya wadda babu waiwaya ba komowa,

Kwancin ƙabari a kai ka zangon somawa,

Makara a saka ka an ɗaga za a ficewa,

Shi ke nan ka yi sallama babu tsayawa,

Ka tafi ka bar su kai kaɗai sai aikinka.

 

Duk wasu ‘yan tarkacen da kar riƙa ratawa,

Kay yi ta haɗama a kansu ba ka hutawa,

Yau ga su a tare, sai magada ka rabawa,

Kai sai da na sani jidalin Tarawa,

Hisabin yada kab biɗe su ɗai ya ishi ranka.

 

Wansu mgadan suna tumami don ba ka,

Giwa ta kwanta dama yau ɗebi da kanka,

Sui ta bushasha abunsu kai sun manta ka,

Ko sisi ba su sa ku tare a ƙabrinka,

Duk yada suka sonka ba su zarce lufafinka.

Ya ƙara jan hankalin al’umma da su bi lamarin duniya a hankali, saboda kasancewarta rayuwa ce mai ƙarewa, duk abin da aka aikata, sakamakonsa za a tarar. Haka duk matsayin da mutun ya sami kansa, an yi waɗanda suka fi shi, sun shuɗe ba su. Ya sake jaddada wa al’umma cewa, duk aikin da mtun ya aikata, sakamakonsa ne zai riska. Saboda haka kada mutun ya aikata mugun abu, kada kuma ya kusance shi, kada ya taimaka wajen aikata shi. Idan mutun, Allah ya jarrabe shi da wani matsayi a tsakanin al’umma, ya yi amfani da shi wajen hana kowane irin aibi gwargwadon ikonsa. Idan malami ne, ya fito fili ya gargaɗi al’ummar da ke aibin. Su kuma sauran jama’a sai su guje wa masu ayyukan assha ɗin, gujewar da za ta taimaka wajen gyara halayyarsu. Ga abin da ya ce:

Taka sannu wagga rayuwa mai ƙarewa,

Ka ci ribar rayuwarka kafin ƙarewa,

In ka mutu ka yi ka gama babu daɗawa,

Ba komowa a duniya don gyara wa,

Komai ka riga ka aikata shi ka ishe ka.

 

Komi kaka ji a duniya sanyaya ranka,

Don wani ya fi ka ya yi kafin zuwanka,

In ka yi khairi ka iske khairi ka jiran ka,

In ka yi sharri ka iske sharri ka jiran ka,

Za ka yi girbin abubuwan da ka shisshiuka.

 

Kar ka yi sharri kashedi kar ko ka matsa shi,

Kar kuma ka yi taimako a gun wani don yin shi,

In ka samu ka sanya hannu ka ije shi,

In ba dama faɗa da baki ka hana shi,

In ka kasa aboka to ƙishi a ranka.

Ya yi kira ga duk wanda ya yi imaniu da ranar Sakamako kuma ya tabbatar da akwai hisabi (binciken ayyuka), ya san zai mutu a rufe shi a kabari, ba ɗan rakiya sai abin da mutun ya aikata ne zai tarar. Kuma a ranar tashin ƙiyama babu wani daga cikin dangi, kamar uwa, ko uba, ko mata, ko miji ko ‘ya’ya ko abokai da za su taimaki mutun, kowa tasa ta ishe shi. Hasali ma dukiya ba za ta amfani mutun da komai ba a wannan ranar, sai jinƙan Ubangiji, shi ma ga wanda ya bi tafarkin samunsa, kamar yadda ya nuna a baitocin waƙar a inda yake cewa:

Inda ka san da lahira lalle za ka,

Ka san tafiyar ga babu mai iya kare ka,

Ka san kuma za a yo hisabin ayukanka,

Ka san kuma ran da kam mace an ka rufe ka,

Kai sai ayukan da kay yi su za su ishe ka.

 

Kaito mutum ɗan Adam akwai kaya kanka,

Wannan ranar da babu ɗai mai kare ka,

Babu uwa ba uba kaza ba danginka,

Ba ‘ya’ya babu dukiya mai kare ka,

Wannan ranar Tabara sai dai rahamarka.

Ya kuma ƙara jawo hankalin al’umma ta hanyar fayyace musu cewa, lahira gida biyu ce, wato ko gidan wuta ko gidan aljanna, waɗanda daga nan duniya ake neman su. Wanda ya ji tsoron haɗuwa da Ubangijinsa a duniya ya bi umurnin Allah sau da ƙafa, sai a saka shi a Aljanna. Shi kuwa wanda ya bi son ransa, ya zaɓi ƙawace-ƙawacen duniya ya zarce hadda, ya yi girman kai ga bin umurnin Allah, makomarsa wuta. Saboda haka tun a duniya mutun ke zaɓen nau’in gidan da yake so, sai Allah ya saka shi, kamar yadda malamin ke cewa:

In ka tafi Lahira gida biyu suke nan,

Nemansu a duniya ake ga ayyukkannan,

Tsoron Allah barin hawa Aljanna ke nan,

Zaɓen duniya da yin ɗaga sai wuta ke nan,

Zaɓi na zaɓi ka aikata Jalla ya saka.

Haka kuma, ya bayyana wa al’umma cewa, Allah bai tauye wa kowa haƙƙinsa ko ya yi ha’inci don a ƙwari (cuci) wani, haka ba zai lamunce wa duk wani mai cutar al’umma ba. Duk abin da mutn ya aikata a rayuwarsa ta duniya da makamancinsa za a mayar masa a ranar hisabi. Ya kuma shawarci mutane da su horar da rayuwarsu da kyawawan ɗabi’u bisa tafarkin addini Musulunci, ta haka sai su samu kimtsi daga Allah, bisa ga bin daitacciyar hanya tagari, kamar yadda ya nuna a baiti mai zuwa inda yake cewa:

Allah ya tabbatar ba zai zalunci ba,

Sannan ba za ya ƙyale mai zalunci ba,

Aya hamsi da huɗu cikin yasin duba,

Ba a yi muku sai abun da kuka yi maza tuba,

Kai tarbiyyar halinka Allah ya shira ka.

Idan aka dubi wannan baitin za a ga cewa, malamin ya ƙarfafa hujjarsa da zancen Allah a inda yake cewa:

To, a yau, ba za a zalunci wata rai da kome ba. Kuma ba za a saka muku ba face da abin da kuka kasance kuna aikatawa (Sura ta 36 aya ta 54, Alƙur’ani Mai tsarki).

Malamin ya kamala waƙar ne da yi wa ƙasar Nijeriya addu’ar samun kyautatuwar al’amurranta tare da kare ta daga dukkan fitintinun da ke tunkarar ta. Ya cika da yin salati ga Fiyayyen halitta Annabi S.A.W., a inda yake cewa:

Taimaki Najeriya Tabaraka ka shira ta,

Amin ya Rabba Wahidun kuma Ka tsare ta,

Tammat nai hamdala a nan zan dakanta,

Salli ala Ɗaha Rabbana Sarkin kyauta,

Ƙara daɗin jinƙayinka gun sa Habibinka

Kwamitin Malamai Na Jaha

Ganin yadda lamarin tsaro ya taɓarɓare a wannan jaha har abin ya kai lahaula wa la ƙuwati, al’ummomi daga kowane lungu sai koke suke, musamman a Masarautar Ɗansadau, inda aka sami asarar ruyukan al’umma. Wannan lamarin ya haifar da canjin yawu a tsakanin tsohon ɗan majalisar tarayya Sanata Sa’idu Muhammad Ɗansadau da tsohon gwamnan Alh. Abdul’Aziz Yari Abubakar. A sakamakon haka ɗin ne aka gayyato wani mai asirin kama ɓarayi da ake kira Ali Ƙwara domin ya bayar da tasa gudummuwa. Ya zo ya kuma yi aikinsa na wani ɗan lokaci. Ya yi kuma nasarar kama maɓarnatan da jami’in ‘yansada da ke kula da makamai na rundunar ‘yansanda ta jahar Zamfara, amma tun daga lokacin da kafafen ‘yaɗa labarai suka bayyana lamarin ba wanda ya ƙara jin komai.

Ayyukan Kwamitin Malamai

Gwammanati ta kafa kwamiti, wanda aka kira kwamitin sasantawa tsakanin rikicin manoma da makiyaya a ƙarƙashin shugabanci marigayi Malam Abubakar Tureta. Kwamitin ya yi duk abin da ya kamata ya aiwatar. Kasancewar kwamitin na malamai ne, ya samu karɓuwa da amincewa a tsakanin al’ummomin da lamarin ya shafa. Kwamitin ya samu ganawa da waɗanda aka zalunta da ma azzaluman. Saboda irin yadda al’umma ke mutunta malamai da harka malanta, har ‘yan ta’addan sun bayyana wa kwamitin, kanwa uwar haɗin rikice-rikicen da yadda suke ruruta wutar fitinar da alfanun da suke riska sakamakon ta’addanci. Malaman sun rubuta cikakken rahotonsu mai ɗauke da bayanan waɗanda ake tuhuma, sun kuma danƙa rahoton domin ɗaukar mataki na gaba. Sai dai maimakon a binciki waɗanda ake tuhumar, sai gwamnatin ta rushe kwamitin, ta sake kafa wani kwamitin aka kuma sanya mutanen da ake tuhuma cikin kwamitin. Wannan shi ya haifar da watsewar kwamitin (Kanoma,2019). Malamin ya ƙara da cewa:

Lokacin da aka yi wannan kwamiti, kasancewar an ce ya zama na malamai ne, to irin haɗin kan da al’umma suka bayar, abin za ka sha mamaki! Da jami’an tsaro da masu ɓarnar. A lokacin da anka haɗa rahoton farko aka miƙa ma Gwamna. To matsalar da anka samu, da anka haɗa rahoton nan na farko har anka  miƙa ma Gwamna, ya je ya aje bai ma karanta ba.

Malamin ya ci gaba da cewa, suna jiran gwamna ya kira su, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Har Malam Abubakar Tureta ya hasala, ya ce masa haka mutumin nan zai muna. Malamin ya ƙara da cewa:

Mun gano asalin abubuwan, masu yi, da hanyar da za a bi a magance, ga hanyar da kuma su za a haɗa su Fulani da manoma duk a haɗe su, ga ɓarayi, a ci nasara a kai. Masu ɗaukar fansa, da masu koke-koken ga koken da su Fulani su ka yi. Kuma ga lokacin da an kai ƙarshen matsalar!

Bayan sun bayar da rahoton farko duk da kasancewar suna sane da irin halin ko oho da aka yi game da ƙoƙarin da suke yi na yaƙar ta’addanci cikin ruwan sanyi ta hanyar lalama, sai suka ci gaba da aiki ba kama hannun yaro. Sun sami damar haɗa rahoto na biyu. An yi ƙoƙarin a zauna ba a sami zaman ba, sai ran da Gwamnatin Tarayya ta naɗo wani kwamiti da ta turo, sai aka ce yaya za a yi, daga ƙarshe sai aka gabatar da rahoton da kwamitin malamai suka rubuta. Yayin da kwamitin Gwamnatin Tarayya ya karɓi rahoton ya duba, sai suka ce da gwamnati ta yi aiki da rahoton ai da tuni an kawar da matsalar (Kanoma,2019).

 Malamin ya tabbatar da cewa, suna cikin tafiyar da aikinsu sai wasu suka yi wani kwamiti na daban, amma suka buƙaci malamin da ya ba su kwafen rahotonsu, haka su ma ‘yansanda sun karɓi kwafen rahoton. Sai lamarin ya kusan zama kamar ana wasa da hankalin al’umma ne. Dalili kuwa shi ne, duk wurin da malamai suka tafi, sai bayan sun bar garin sai wani kwamiti na daban ya ziyarci muhallin, akwai garin da kwamitin na biyu ya tafi mutane ishirin kawai suka halarci zamansu.

Ke nan wannan lamari yana buƙatar ayar tambaya. Tambayar kuwa ita ce: Me ya sa duk gari ko ƙauyen da malamai suka kai wa irin wannan ziraya al’umma na yi musu lale-marhaba, yayin da kwati na biyu in je bai ganin kowa sai waɗanda zuwansu wurin ya zama dole? Amsar tambayar a bayyane take, domin al’ummomin ba su da tabbas tare da shakku da ke cikin zukatansu game da kwamitin (Kanoma,2019).

Kamar yadda wannan maƙala ta kalato, a daidai lokacin da malamai za su sake mika wani rahoton, sai mutanen nan da suka kasance abin tuhuma ga malamai saboda hannun da suke da shi cikin ta’addanci, aka sanya su cikin kwamitin. Kuma gwamna da kansa ya ce ya jaddada kwamitin tare da su a matsayin ‘yan kwamitin. Saka su kwamitin shi ya kawo ƙarshen aikin kwamitin, kamar yadda (Kanoma, 2019) ya bayyana.

Da gwamnati ta yi amfani da shawarwarin da ke ƙunshe cikin rahoton, da lamarin bai ta’azzara haka ba. A ƙoƙarin malaman na yaƙar ta’addanci da ya dabaibaye Jahar Zamfara, sun gabatar da maƙalu a tarukan faɗakar da al’umma da dama a cikin gida da kuma wajen jaha. Daga cikin irin waɗannan muƙalun da malaman suka gabatar sun haɗa da muƙalu masu take:

1.       Nauyin da Allah Ya Ɗora ma Shugabanni a Kan Harkokin Tsaro.

2.       Muhimmancin Zaman Lafiya da Ci Gaban Addini a Duniya.

3.       Illolin Ƙabilanci da Tasirin Ƙabilanci Wajen Haddasa Fitina.

4.       Gudummuwar da Kowa Zai Bayar Wajen Samar da Tsaro da Yaƙar Fitinoni.

5.       Illolin Garkuwa Da Mutane.

6.       Nauyin da ke Kan Jami’an Tsaro Wajen Tabbatar Da Tsaro.

Shawarar Malamai Ga Gwamnatin Jahar Zamfara

A ƙoƙarin malaman Jahar Zamfara na yaƙar ta’addancin da jahar ke fama da shi sun shawarci gwamnatin jaha da aiwatar da wasu gyare-gyare a matakai da sassa daban-daban kamar haka:

(a)    Makarantu

Kasancewar makarantu wurare ne na koyarwa tare da horar da ɗalibai ayyukan da za su yi wa al’umma amfani, saboda haka ya kamata a cusa wa ɗaliban halaye na musamman da suka haɗa da:

a.       Tsoron Allah, da kishin ƙasa, da girmama iyaye, da na gaba, da hukuma, da gaskiya, da riƙon amana.

b.       Haka kuma, tawali’u da aiki tuƙuru da sadaukar da kai da tsabta da son juna duk abubuwa ne da suka wajaba a horar da ɗalibai su a duk faɗin makaratun jaha, ta hanyar tilasta darussan addinin Musulunci domin shi ke horar da zukatan ɗan Adam.

(b) Shugabannin Makarantu

Shugabannin makarantu da malamai, su ne aka ɗorawa alhakin koyarwa tare da gyara halayen ɗalibansu. Wajibi ne su kasance abin koyi ga ɗaliban. Su kuma zama masu kulawa da halin da ɗalibansu ke ciki tare da nuna damuwa game da ci gaban ɗaliban. Hakan ba zai samu ba sai an horar da malamai masu tarbiyya da dattako waɗanda za su tafiyar da wannan gagarumin aiki tare da ba su haƙƙoƙinsa da kuma kyautata musu kamar yadda ya kamata.

(C) Bayar da Kyakkyawar Kulawa ga Al’umma

Wajibi ne gwamnati ta dubi buƙatar bayar da kulawa ta musamman wajen sake halayyar zamantakewar al’umma da ke zaune a ɓangaren birane da karkara domin dawo da ɗa’a tare da magance rashin aikin yi da rashin bin doka da taɓarɓarewar ɗabi’u da aikata munanan laifuka.  Wajibi ne a bayar da kulawa ta musamman domin samar da tsaro mai ɗorewa da zai wanzar da zaman lafiya ta waɗannan hanyoyi:

a.       Sake dawo da ɗa’a da daidaitawa a tsakanin al’umma, ta ba kowa haƙƙinsa.

b.       Hana miyagun halaye.

c.        Samar da cikakken tsaro a kowane lungu da saƙo da ke faɗin wannan jaha.

d.       Ciyar da matasa gaba da samar musu ayyukan yi, tare da farfaɗo da cibiyoyin horar da matasa sana’o’in hannu a lungu da saƙo na wannan jahar.

e.       Inganta makarantu da asibitoci, ta hanyar samar musu da wadatattun kayan aiki da kwararrun ma’aikata tare da ba ma’aikatan haƙƙoƙinsu kamar yadda doka ta tanada.

f.        A taimaka wa ƙungiyoyin tsaro da ke gudanar da sintiri a garuruwa da kauyukan da ke faɗin wannan hajar.

g.       A yi amfani da ƙwararrun malaman addinin Musulunci masu tsoron Allah da tawali’u wajen ilmantar da al’umma, muhimmancin neman ilimi da kawar da jahilci da wajabcin ɗaukar nauyin iyali da muhimmancin kula da ci gaban jama’a. Su kuma faɗakar da jama’a muhimmancin kula da lafiya da tattalin arziki da haƙuri a lamarin rayuwa. Su kuma faɗakar da mata haƙƙoƙinsu da nau’in gudummuwar da za su bayar wajen tabbatar da tsaro a tsakanin al’umma. Su faɗakar da al’umma game da muhimmancin tarbiyyar ‘ya’yansu tare da ciyar da su daga abinci na halal.

h.       A samar da hanyoyin ayyukan da suka dace da mata.

i.         A wayar da kan mata game da haƙƙoƙinsu.

 (d) Abubuwan Da Gwamnati ya Kamata ta Kawar

Akwai abubuwa da dama, amman a nan ya kamata a duba a cikin sha’anin kasuwanci kamar:

a.       Alguussu (maguɗi ko amaja).

b.       Ƙarin farashin kaya ba tare da wani dalili ba, musamman a lokacin azumi.

c.        Rashin amana a tsakanin abokan ciniki.

d.       Ɓoye kayan masarufi.

e.       Rashin taimakon juna a tsakanin ‘yan kasuwa da kuma al’umma.

A aikin gwamnati kuwa akwai abubuwa da ke buƙatar kulawa ta hanzari kamar:

a.       Rashin kyakkyawan shugabanci nagari.

b.       Rashin bin ƙa’idar aiki, wato dokokin aiki da ƙa’idojin kashe kuɗaɗen hukuma.

c.        Karɓar hanci da bayar da rashawa.

d.       Magance hauhawar talauci a tsakanin ma’aikatan gwamnati, ta hanyar biyansu haƙƙoƙinsu bisa ga la’akari da yadda yanayin rayuwar al’umma ke tafiya ta yau da kullum.

Sakamakon Bincike

Binciken ya gano wasu abubuwa da dama da suka zama musabbabin wanzuwar sukurkucewar rashin tsaro a Nijeriya ta Arewa, musamman a Zamfara wanda ya samo tushe tun daga lokacin shigowar mulkin jamhuriya ta farko wadda ta haifar da abubuwa kamar haka:

a.       Zubar da martabar sarakunan ƙasar Hausa, waɗanda su ne iyayen al’umma, kuma jagororin Addinin Musulunci da dukkan al’ummomin da ke zaune a masarautunsu.

b.       Sa musu tarnaƙi tare da hana su gudanar da ayyukansu na kare rayuwa da dukiyoyin al’ummomin da ke zaune a masarautunsu. Wannan ya faru ne a sakamakon ƙwace haƙƙin mallakar ƙasa da kula da raba filaya da dazuzzuka daga gare su aka mayar ga ‘yan siyasa tun a 1960.

c.        Ɗauke haƙƙin kula da doka da kiyaye bin doka daga hannun sarakuna aka mayar ga ‘yan siyasa. Saboda haka sarki bai da ikon hana ɗanta’adda zama a cikin hurumin masarautarsa.

d.       Bayar da fifikon gaske ga ilimin zamani fiye da ilimin addini, wanda ke tarbiyyar ruhin al’umma.

e.       Watsi da nagartattun hanyoyin zaɓen shugabanni da Addinin Musulunci ya sharɗanta.

f.        Fifita gidan duniya da ƙawace-ƙawacenta a kan gidan gaskiya.

g.       Bayan waɗannan abubuwa, an gano cewa, ‘yan siyasa ne na wannan ƙarnin suke da alhakin kawo ‘yan ta’adda daga wasu ƙasashe don cimma burinsu na kafa gwamnati a shekarar zaɓen 2015, kamar yadda suka riƙa tuna wa junansu asirai da yadda suke mu’amulla da ‘yan ta’addar ta fuskoki da dama.

Shawarwari

Wannan takarda na ganin cewa, akwai shawarwarin da za su iya taimakawa wajen shawo kan matsalolin da aka tattauna a sama. Su ne:

a.       Akwai buƙatar a mayarwa sarakuna ayyukansu na farko, tun kafin bayyanar siyasa. Saboda sun fi kowa sanin lungu da saƙo na hurumin ƙasarsu. Hasali ma su suka kusanta da al’ummarsu, kuma su ke zaune tare da su.

b.       Duk wani jami’in gwamnati da aka tura a yakin masarauta, ya kasance yana ƙarƙashin kulawar shugaban, wato basaraken masarautar.

c.        A ba sarakuna damar bayar da izini a cikin hurumin masarautunsu tare da ikon korar duk wanda zai zama sanadin tada zaune tsaye a huruminsu ko da kuwa ɗan asalin masarautar.

d.       A bar wa masu zaɓen sarki na kowace masarauta dammar gudanar da ayyukansu kamar yadda yake a da, daga nan sai a gabatar da wanda aka zaɓa ɗin ga Sarkin Musulmi, kamar yadda yake.

e.       A kafa majalisar sarakuna ta jahohin arewa, a ɗora mata alhakin ladabtar da sarkin da ya yi laifi.

f.        A sake bibiyar kundin tsarin mulkin ƙasar nan don hana ‘yan siyasa cire sarki.

g.       Sarakuna su tsame kansu daga lamurran siyasa, su kasance a tsayinsu na iyayen al’umma.

Kammalawa

Bisa ga abubuwan da suka gabata, an fahimci cewa tun daga lokacin da addinin Musulunci ya shigo ƙasar nan malamai ke kai da kawo wajen ƙoƙarinsu na faman yaƙi da abin da ke wanzar da ta’addaci wato jahilci da shi kansa ta’addancin ɗin. Sakamakon haka ɗin ne a kwana a tashi har aka samu kafuwar Daular Usmaniyya. Daular ta samar da kyakkyawan tsarin shugabanci, wanda ya wanzar da kafuwar ɗakunan shara’a a duk faɗin daular. Irin waɗannan ɗakuna sun taka muhimmiyar rawa wajen yaƙar ta’addanci.

Haka an ga irin yadda malaman jahar Zamfara suka bayar da muhimmiyar gudummuwarsu ta haujin wa’azi da gudanar da addu’o’i don ganin an kai ƙarshen wannan lamari. Akwai buƙatar kowa da kowa ya tsaya ya binciki irin miyagun ayyukan da yake aikatawa, ya tuba ya dawo ma turba ta gari. Ko za mu sami saukin wannan lamari. Wajibi ne ga masu riƙe da madafun mulki da su sanya tsoron Allah a cikin dukkan lamurran gudanar da ayyukan jahar nan. Su fa tuna akwai ranar da za su tsayu gaban mahaliccinsu su yi bayani dala-dala game da yadda suka tafiyar da wannan jahar. Adalcinsu ne zai kuɓutar da su. Daga ƙarshe ya zama wajibi a ba al’ummar Nijeriya ta Arewa cikakken ‘yancin da shari’ar Musulunci ta ba su, musamman Musulmi. A kuma yi tanadin da zai ba masu zaɓen sarki cikakken ‘yancin bin ƙa’idar da shari’a ta ɗora musu na zaɓen shgabanni kamar yadda addinin Musulunci ya sharɗanta. Yin haka zai taimaka a samu shugabanni masu tsoron Allah. Wanda hakan zai taimaka wajen daidaituwar alamura.

Manazarta

Abraham,R.C.(1972) Dictionary of the Hausa Language, London: University Press LTD
Abubakar, A.T.(2015)
Ƙamusun Harshen Hausa, Zariya: Northern Nigerian Publishin Company Limited.

Arnett, E.J., (1920) Gazetteer of Zaria Province In Nigeria: Northern Nigeria, London: Waterlow and Sons Limited.

Arnett,E.J. (1920) Gazetteer of Sokoto Province In Nigeria: Northern Nigeria, London: Waterlow and Sons Limited.

Bargery, G.P. (1993) A Hausa- English Dictionary And English-Hausa Vocabulary, Second Edition, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Boyd, J & Maishanu, H.M. (1991) Sultan Saddiq Abubakar III : Sarkin Musulmi, Ibadan: Spectrum Book limited.

Dokaji, A.A. (1978) Kano Ta Dabo Ci Gari, Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

Ɗalhatu, U. (2002) Malam Jafaru Ɗan Isiyaku: The Great Emir of Zazzau, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Ɗanmudi, S. (2022) “Tonon Silili: Yadda Muka Shigo Da ‘Yanta’addan Fulani” Jaridar Mikiya 3/8/2022, Jaridarmikiya.cm

Garba, C.Y. (1990) Ƙamusu Na Harshen Hausa, Ibadan: Evans Brothers Nigeria Publishers LTD

Ibrahim, U.F. (2001) Prince of The Times: Ado Bayero And The Transformation of Emiral Authority in Kano, Eritrea: African World Press.

Ibrahim,S.M (2009) “Rikirkiɗar Haruffan Larabci Cikin Ajami” a cikin Mujallar Tarihin Ajamin

Hausa Kafin Jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo, Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

Kano, J.B. (2006) Ƙamusun Hausa, Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Labarai, M.W. (1967) Gyaran Tsarin Harkokin Shari’a A Nijeriya Ta Arewa, Kaduna: Obadaki Press.

Nigeria, F. R. (1981) Report of Tribunal of Inquiry On Kano Disturbances (MAITATSINE) Kaduna: N.N.N. Commercial Services.

Nijeriya, J. T. (1976) Matakai Na Gyara Tsarin Mulkin Ƙananan Hukumomi, Kaduna: Government Printer.

Nijeriya, J. T. (1982) Tsarin Mulki Na Shekarar 1979 Na Jamhuriyyar Tarayyar Nijeriya, Kaduna: NNNLtd., Commercial Printing Department.s

NNAK / 973-1669- Historical And Ethnological Notes (1929-1931).

NNAK/ C.36- Emir’s Oder 1933-1934.

NNAK/ 223-C.4037– Judicial Council and Alkali’s Court: Appeals And Jurisdiction 1932-1942.

NNAK/c14/1946- Power of Arrest of Emir 1946.

Sufi, A.H. (1990) Mu san Kanmu, Kano: Mainasara Press.

Talata Mafara , M. I. (2004) Gudummuwar Malamai Ga ‘Yaɗa Addinin Musulunci A Ƙasar Hausa, Maƙalar da aka gabatar wajen taron ƙara wa juna sani wanda Majalisar Sarkin Musulmi ta shirya domin cika shekara ɗari biyu da kafuwar Daular Usmaniyya. Wanda aka gudanar a Cibiyar Nazarin Alƙur’ani ta Attahiru Ɗalhatu Bafarawa, Sakkwato 23-25 watan Yuli,2004.

Tsiga, I.A. (1985) Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo, Kano: Shonuga Commercial Press.

Ubaidullah, I.W. (2021) “Faɗakarwa Ga ‘Yan Uwa Danginmu”, An gabatar da ita ne a Gasar Rubutattun Waƙoƙin Hausa da Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ta shirya a kan tsaro a Arewacin Nijeriya.

Urguhart, A.W. (1987) “Planned Urban Landscape of Northern Nigeria”, Ahmadu Bello University Zaria.

Waya, Z.I. (2000) Kano Da Masarautarta Jiya Da Yau, Zariya: Gaskiya Corporation.

Yahaya, A.D. (1980) Native Authority System In Northern Nigera 1950 – 1970: A Study of Political Relation With Particular Reference To The Zaria Native Autkority, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.015 

Post a Comment

0 Comments