Ticker

6/recent/ticker-posts

Kalubalen Tsaro a Masarautar Gummi: Sigoginsa da Dabarun Tunkararsa

This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.

Ƙalubalen Tsaro a Masarautar Gummi: Sigoginsa da Dabarun Tunkararsa

Abdullahi Sarkin Gulbi (Ph.D.)
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria
gulbi.abdullahi.udusok.edu.ng

Sa'adu Musa
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria 

Tsakure

Matsalar tsaro a yau ta zama tamkar wutar daji da ta buwayi a kashe musamman a Arewacin Nijeriya da sauran sassan ƙasar nan. Jihar Zamfara ta zamo ɗaya daga cikin jihohin da suke fuskantar irin waɗannan matsaloli na tsaro. Galibi yankunan da wannan matsala ta yawaita kuwa sun haɗa da Zurmi,Shinkafi, Tsafe, Maru, Maradun, Talata Mafara, Bakura, Anka, Bukkuyum da kuma Gummi. Wannan muƙala an gina ta ne da nufin nazartar irin ƙalubalen tsaro a masarautar Gummi ta jihar Zamfara da zimmar fito da irin yankunan da suke fama da taɓarɓarewar tsaron da kuma irin ɓarnar da ake yi wa jamaar da nufin samar da wasu dabaru ko hanyoyin da za su taimaka wajen rage matsalar tsaron ko magance ta kwata-kwata. A ƙoƙarin tabbatar da binciken an lura da nauoin taaddancin da ake yi wa mutanen yankin kama da satar shanu da garkuwa da mutane da uwa uba kashin gilla na babu gaira babu sabar. An yi amfani da hanyar hirarraki da waɗanda abin ya shafa domin tace bayanan da aka samu a wajen su.

1.0 Gabartawa

Maƙasudi wannan muƙala shi ne domin a nazarci irin matsalar tsaron da take addabar mutanen ƙasar Gummi da kuma hanyoyin magance ta. Don haka, za a yi waiwaye game da taƙaitaccen tarihin Gummi da kewayenta da sigogin matsalar tsaron da kuma dalilan taɓarɓarewar tsaron tare da hanyoyin magance matsalar.

1. 1 Ma’anar Tsaro

Kalmar tsaro kalma ce da ke nufin kare wani abu,[1] kalmar tana kuma iya ɗaukar ma’anoni kamar kiyayewa, ko kula, ko kariya, ko fako.

A wannan muƙalar kuwa an jingina tsaro’da nufin dabaru ko hanyoyi ko tsare-tsare, ko tanade-tanaden domin kiyaye ko tabbatar da kariya ga rayuka da dukiyoyin alumma. A wata fahimtar kuwa, tsaro na nufin kariya daga duk wata tsangwama da barazana ga walwalar alumma tare da bai wa alumma damar gudanar da hulɗa da zamantakewa cikin lumana.

1.2 Rabe-Raben Tsaro

Idan kuwa aka yi duba dangane da rabe-raben matakan tsaron kuwa, za a ga cewa akwai tsaron gargajiya da kuma na zamani. Haka kuma akwai tsaron cikin gida (internal Security) da kuma tsaron waje (external security) Tsaron cikin gida (internal security) na nufin kariya ko rashin ababen da ka iya yin zagon ƙasa ga fahimtar juna tsakanin mabanbantan alummomi da ɗorewar kyakkyawar zamantakewar yan-ƙasa. Haka kuma, yana nufin matakan da ƙasa ke ɗauka wajen kare muhimman hukumomi daga maƙiya da yan kanzaginsu da ke cikin ƙasar domin ta tabbatar da buƙatunta na kiyaye ɗiyaucinta, aladunta, tattalin arzikinta da samar da ababen more rayuwa domin biyan buƙatun yan-ƙasa (DSS 2012).

Tsaron Gargajiya: Wannan tsari ne tsaro da ya shafi dabarun samar da kariya a gargajiyance wanda alumma suka tashi a cikinsa tun kafin haɗuwar su da dabarun tsaro na zamani. Irin wannan ya kasu zuwa gida biyu muhimmai kamar haka;

1.       Tsaro na jiki: Wannan tsaro ne da ya shafi dabarun kariyar kai daga cuta, misali akwai magungunan tsari irin su; Baduhu da layar zana da sagau da shashatau da kuma magungunan tauri da makamantansu waɗanda ake tanada domin samun kariya daga cuta ko ɓacin rana.

2.       Tsaro na gari: Wannan nauin tsaro ana yin sa ne domin samar da kariya ga gida da dukiya da gari ko yanki. Daga cikin matakan wannan tsari na tsaro sun haɗa da; kafin gida ko gona ko mata da katanga ko darni ko ɗaurin gari ko haƙo ko ganuwa ko ƙofa ko kura waje da sauransu. Akan yi amfani da waɗannan nauoin tsaro ne a gargajiyance domin a samar da tsaro ga gida ko gari ko kuma yanki ko wata dukiya.

3.       Tsaron Zamani: Wannan tsaro ne da ya shafi amfani da dabarun tunkarar tsaro irin na zamani wanda ya haɗa da jamian tsaro masu kaki da farin kaya da naurori da makamai irin na kimiyyar zamani domin a kawar da barazanar rashin tsaro.

 2.0 Kafuwar Garin Gummi

Garin Gummi ya kafu da kuma bunƙasa ne a ƙarƙashin jagorancin Zamfarawa da suke da asali daga wani ƙauye da ake kira Tunfafi ko Tunfafiya[2]. Wato Zuriar Ali Bazamfare) Wani masanin[3] tarihi cewa ya yi Su waɗannan Zamfarawa da suka taso daga Tunfafi ta ƙasar Talata Mafara, sun yi hijira ne zuwa yamma a ƙarƙashin jagorancin Ali Bazamfare zuwa wani gari da ake kira Fakai a ƙasar Zuru, daga nan ne kuma suka dawo wani gari da ake kira Danko duk a ƙasar Zuru ɗin , a wannan gari Ali Bazamfarae ya haifi ɗa da ake kira Kure, bayan yaron ya girma sai ya ba shi sarautar garin, ya koma wani gari da ake kira Zauma, a wannan gari ma ya haifi yaya guda biyu, ɗaya ana kiran sa Ɗanƙofa ɗayan kuwa ana kiran sa Muhammadu Waru.

A shekarar 1782 ne sai Muhammadu Waru ya ɗebo wasu daga cikin jamaar mahaifinsa (Ali Bazamfare) da ke zaune a can Birnin Zauma suka dawo wani ƙauye da ke kusa da garin Gummi mai suna Kagarar Fulani suka zauna. Kasancewar Muhammadu Waru jarumi a fagen yaƙi da taimakon jamaar da suke kusa da shi, ya ba shi damar samun karɓuwa a idon jamaa, har mazauna Gummi suka ga ya dace da ya zo ya shugabance su a matsayin Sarkin Gummi na farko a tarihin Sarakunan Masarautar Gummi.

Tarihi ya tabbatar da cewa, lokacin da Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da jamaarsa suke je Zamfara, musamman a ƙasar Gummi, ya tarar da cewa Sarki Muhammadu Waru ya gama haɗa kan dukkanin ƙauyuka da ke maƙwabtaka da shi a ƙarƙashin kulawarsa. Ya taimaka wa Shehu wajen jaddada addinin Musulunci a ƙasar Kabi, wanda a sakamakon hakan ne Shehu Ɗanfodiyo ya ba shi Tutar Girmamawa. Jin daɗin irin yadda Shehu ya karrama shi, Muhammadu Waru ya ga ba a bin da zai yi ya rama abin da aka yi masa, sai ya yanke shawarar sanya a gina wa Shehu Ɗanfodiyo Masallaci a garin Sifawa. An gina wannan masallaci ne a shiyar Yar Katanga wadda a halin yanzu ake kira shiyar Yamma. Wannan Masallaci har yanzu yana nan ana amfani da shi, duk da yake an mayar da shi ginar zamani[4]

2.1 Jerin Sarakunan Masarautar Gummi

 

Suna

Lokaci

Adadin Shekaru

1

Muhammadu Waru

1782-1807

25

2

Sarki Ɗankunyau

1807-1819

12

3

Sarki Bawan Yari

1819-1847

28

4

Sarki Salihu

1847-1847

Wata 6

5

Umar Ɗan Aisha

1847-1864

17

6

Ibrahim Ɗangwado

1864-1867

3

7

Abdullahi Laje

1867-1892

25

8

Sarki Aliyu Na ɗaya (I)

1892-1904

12

9

Sarki Ɗan bau

1904-1910

6

10

Muhammadu Andi

1910-1933

23

11

Muhammadu Maidabo

1933-1976

43

12

Muhammadu Ɗanguntu

1976-1983

7

13

Alhaji Aliyu Isah Andi

1983-2011

28

14

Alhaji Aliyu Adamu

2011-2013

Shekara (1) da W.7

15

Alhaji Justice Lawal Hassan

2013-Yau

Sarki mai Ci yanzu

An sami wannan bayani ne a ofishin sakataren Emiyan Gummi 12/10/2019.

3.0 Dabarun Tsaro a Masarautar Gummi

Wannan fasali zai yi bitar irin sarautun da ke janye da a akalar tsaro ne a gargajiyance a faɗin masarautar tun gabanin lamarin tsaro na zamani ya yi cikakken tasiri a kan su. Daga cikin irin sarautun da suke da alhakin tsaron kuwa sun haɗa da;

i.                     Sarautun Bayi na Sarki.

ii.                   Sarautun Bayi masu kula da fada.

iii.                 Sarautun kula da tsaro na gari.

iv.                 Sarautun fitattun Sanaoin gargajiya.

3.1 Sarautun Bayi na Sarki.

A ƙarƙashin wannan, za a bayani ne dangane da wasu sarautu da suka shahara ga aikata hidima da samar da tsaro a ciki da wajen fadar Sarki. Waɗannan sarautun kuwa, sarautu ne da ake yi a cikin zuriar bayin sarki tun a jiya da kuma yau. Akan yi sarautun ne a bisa gado. Daga cikinsu akwai;

i.        Shamaki: Shi ake fara gani kafin sarki ya fito daga cikin gidansa kuma shi ke yi ma mutanen iso ga sarki. Wannan sarautar tana da muhimmancin gaske domin bincikar abin da yake tafe da mutum kafin ya ga sarki. Irin wannan matakin kuwa, yakan taimaka wajen magance matsalar kai wa sarki marmaki a fada.

ii.      Sallama: Aikinsa shi ne raba kyautar sarki, musamman ga makaɗan fada. A wasu lokuta kuma yakan isar da gaisuwar talakawa zuwa ga sarki, tare da yi masu iso wajen sarki. Wannan ya nuna cewa a tsarin sarauta a ƙasar Hausa sarki mutum ne mai darajar gaske, wanda ake taka- tsantsan da barin jamaa na saduwa da shi kai tsaye. Domin ka da wani abin shairi ya same shi.

iii.    Shimfiɗa: Wannan sarautar akan kira ta da suna Baraya a wasu masarautun ƙasar Hausa, shimfiɗa ne yake da hakin kula da shimfidar sarki da abin da duk ya shafi shimfiɗun masarauta da tufafi da abinci. Wannan mutum ke kula da abincin da sarki zai ci musamman idan sarki ya fita rangadin yankinsa. Ana yin haka ne domin ka da sarki ya sha guba a cikin abinci.

iv.     Barga: Shi ne mutumin da ke kula da abincin dawaki da kilisarsu da tafiyarsu da kuma zaɓensu da ƙaruwar ko raguwarsu. Haƙƙinsa ne ya zaɓI dawakan da za a tafi da su wajen yaƙi.

v.       Zagi: Shi ne wanda ke yi wa sarki ja gaba duk inda za ya tafi, yana riƙe da kayan doki ya kuma dafa wa sarki sirdi a lokacin da yake hawa da sauka da kuma riƙe buta idan shantali baya kusa. A wasu masarautu irin wannan sarauta ana kiran tad a suna Ma ja sirdi.

vi.     Uwar Soro: mahaifiyar sarki ko yarsa ko gwaggonsa, ko uwar gidansa wadda ta wanke shi wadda ke iya gaya masa duk abin da ake jin nauyin gaya masa, aikin ta shi ne kula da huldar cikin gida a tsakanin sarki da yayansa da danginsa musamman mata. Sannan takan ci abincin da aka yi ma sarki domin ta tabbatar da daɗinsa, da lafiyar abincin.

vii.  Jekadiya: Mace ce wadda ke isar da saƙon sarki zuwa ga iyalinsa ko saƙon yayansa da ƙannensa zuwa ga sarki. Galibi akan naɗa babbar yayar sarki ko gwaggonsa a wannan sarauta. Aikinta ya so ya yi kama da na Uwar soro.

3.2 Sarautun Bayi Masu Kula da Fada.

Wannan kaso na masu hidimar tsaro su ne waɗanda alhakin tsaro a fada ya rataya a kan su. Fada waje ne da ake shirya doka da tsare ta, hakan ya sa ake da wani tsari na musamman domin samar cikckken tsaro a fada, kuma hakan ya sa ko a zaman fada aka yi tsari na musamman domin yin kafa-kafa da samun matsalar tsaro a fadar sarakunan ƙasar Hausa. Daga cikin waɗanda ke janye da akalar tsaro a fada sun haɗa da;

Sarkin Dogarai

Sarkin Fada

Tsara

3.2.1 Sarkin Dogarai

Shi ne shugaban dogarai a fada. Shi yake da alhakin yanke hukunci ga duk wani dogari da ya aikata wani laifi a fada ko cikin gari, kafin a sanar da sarki. Sarkin dogarai mutum ne da ya ƙware a shaanin tafiyar da mulkin gargajiya. Yana ɗaya daga cikin makusantan sarki, hakan ya sa da wuya sarki ya zartar da wani abu a fada ba tare da saninsa ba. Yana bayar da gudunmawa ga tsaro a fada da kuma faɗin masarauta.

3.2.2 Sarkin Fada

Shi kuwa sarkin fada shi ne shugaban fadawa baki ɗaya. Shi ke kula da yadda lamarin fadanci ke gudana a fada, yakan bayar da shawara ga sarki idan bukata ta taso. Akan yi shawara da shi masarauta dangane da lamarin tsaron gari ko yanki.

3.2.3 Tsara

Wannan shi yake kula da yanayin zama a fada. Shi ne ked a alhakin kula da inda baƙi za su zauna a cikin fada musamman ga wanda bai sa yadda tsarin zaman fadar yake ba. Ga al’adar masarautar ana zama ne gwargwadon darajar ‘yan majalisar sarkin. Yana daga cikin aikinsa hana duk wata baƙuwar ijiyar dab a ya aminta da ita ba ga ganin sarki.

3.3 Sarautun Kula da Tsaro na Gari

A nan, takardar ta zaƙulo wasu daga cikin masu hidimar bayar da tsaro ne a cikin gari. Gudunmawarsu a tsarin sarauta a ƙasar Hausa shi ne, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin alumma. Ire-iren waɗannan sarautun kuwa sun haɗa da;

  1. Ƙamshin gari
  2. Barade
  3. Makama
  4. Maza Waje
  5. Yari
  6. Sarkin Baƙi
  7. Baushi
  8. Ƙofa

Ƙamshin Gari

Kamar yadda sunan ya nuna, wannan mutum ne daga cikin fadawan sarki wanda yake da alhakin shaƙo abubuwan da ke gudana a cikin gari da kewaye domin ya kawo wa sarki rahoto na abin nan take. Daga cikin abubuwan da yakan samo labarin abkuwarsu sun haɗa da; sata da kwartanci da faɗace-faɗace da duk wani laifi da ake zargin mutum da aikatawa. Idan Ƙamshin ya kawo wa sarki labarin faruwar wani abu a masarauta, lallai sarki ba ya wasa da ɗaukar matakin hukunta duk mai laifi. Hakan ya sad a zarar aka ga Ƙamshin gari a unguwa ko ƙauye, to, lallai za a ga cewa mutane sun sha jinin jikinsu domin ka da a ce ga abin da suka yi. Aikinsa ya yi kama da maaikatan farin kaya (SS) na yanzu.

Sarkin Yaƙi (Magayaƙi)

Shi ne shugaban rundunar yaƙi, idan yaƙi ya tashi shi yake tanadin abubuwan da ake buƙata, shi ne kuma yake aikawa sarakuna da sanarwar yaƙi.

Barade

Shi ne ke shugabantar mayaƙan sama wato waɗanda suke akan dawaki a wajen yaƙi, sarautar ta kasu kashi biyu, akwai Baraden yayan sarki akwai kuma Baraden sarauta watau Baraden sarki.

Maza Waje

Babban aikinsa ga samar da tsaro shi ne yake bayar da sanarwa idan aka sami labarin wasu za su kawo hari a yankin. Saboda haka, da an ji sanarwarsa to, sai batun azama a fita fagen daga. Watse da irin wannan tsari a zamantakewarmu ta yau ya haifar da samun yawaitar ‘yan ta’adda a cikin al’umma.

Sarkin ƙofa ( Ƙofa)

Shi ke tsaron ƙofar gidan sarki, ya rufe ta, kuma ya hana wanda ba a yarda da shiga gidan sarki ko fada ba. Ga aladar Hausawa, Ƙofa shi ne shugaban masu kula da ƙofofin gari domin samar da cikakken tsaro. A nan ma idan an lura aladar tsaro ta amfani da ƙofofin gari ya zama abin tarihi.

Sarkin Baƙi

A zamanin da, babu garin da ba a samun sarkin baƙi a faɗin ƙasar Hausa. Sarkin baƙi mutum ne da akan naɗa tare da aza masa nauyin kula da shiga da ficen baƙi a faɗin gari. Shi ne yake saukar da baƙin da aka yi a gari. A yau wannan aladar tsaro ta yi rauni ƙwarai.

Yari

Wannan sarauta ce ta kula da ladabtar da masu laifi. Al’ummar Hausawa suna da wannan tsari tun kafin haɗuwar su da Turawa. Galibi idan aka kama wani mai laifi akan bai wa Yari ajiyar sa ne na tsawon wasu kwanaki. Bayan zuwanTurawan Mulkin mallaka ma aikin Yari bai sauya ba, domin sarakuna kan kai masu laifi a gidan Yarin gari ne kafin a tura su zuwa kotu ko ga ‘yansanda. Har yanzu a wasu ƙauyukan ƙasar Gummi akan kai dabbobi da aka kama a gonaki idan Fulani sun yi ɓarna a gidan Yari domin hukunta su.

4.0 Waiwaye a Kan Matsalar Tsaro a Ƙasar Gummi a Yau

Taɓarɓarewar tsaro a yankin Gummi daga bayan nan ya samu, tun lokacin da aka fara satar shanu da garkuwa da mutane a nufin amsar kuɗin fansa, Gummi ba ta zama ɗaya daga cikin garuruwa ko yankunan da suka sami wannan matsala ba. Sai dai duk da haka, akwai rashin jituwa na Manoma da Fulani da ake samu nan da can. Matsalar rashin tsaro ta samu ne bayan har an yi zaman sasantawa da yan taaddan jihar Zamfara. Sai kawai suka mayar da hari a wasu sassa na ƙasar Gummi, musamman a garuruwa da ƙauyukan da suke da daji mai ruƙuƙi, wato a yammaci da kudancin Gummi ke nan kamar Barikin Daji da maƙwabtan ƙauyukan da suke kusa da garin.

4.1 Garuruwa da Ƙauyukan da Suke Fuskantar Matsalar Tsaro a Ƙasar Gummi

A nan muƙalar za ta zayyano garuruwan da suke fuskantar matsalolin rashin tsaro a yankunan ƙasar Gummi. Daga cikin fitattun garuruwa da ƙauyukan da suke fama da waɗannan yan bindiga sun haɗa da;

1. Barikin Daji

2. Bardoki

3. Gayari

4. Ƙaraye

5. Gwalli

6. Babban Rafi

7. Gyalange

8. Gaftu

9. Lanke

10. Unguwan Noma

11. Illelar Auwal

12. Ɗanawo

13. Gidan Illo

14. Tudun Baushe

15. Sago

16. Kabawa

17. Kagali

18. Masallaci

19. Maikada

20. Birnin Tudu

21. Falale[5]

4.2 Sigogin Matsalar Tsaro a Ƙasar Gummi

Yanayin taɓarɓarewar tsaro a ƙasar Gummi kamar sauran sassan Arewacin Nijeriya da jihar Zamfara yana tafiya ne bisa siga ɗaya. Galibi masu addabar mutane sukan aiwatar da waɗannan nauukan taaddanci a cikin garuruwa da ƙauyuka ko kuma a kan hanya. Waɗannan sigogin rashin tsaron kuwa sun haɗa da;

i. Garkuwa da Mutane

ii. Satar Shanu da ɓarnata kayan gona (Abinci)

iii. Kisan Gilla da ƙare dangi

iv. Fyaɗe ga mata da yanmata

4.2.1 Garkuwa da Mutane

Wannan babbar matsala ce da ta saka dubban mutanen yankin shiga cikin zulumi da ko ta kwana a cikin garuruwa da ƙauyukan yankin. Dukkan garuruwan da aka lisafo a sama suna fuskantar wannan barazana daga yan bindiga.

4.2.2 Satar Shanu

Matsalar tsaro a ƙasar Gummi da satar shanu ta soma, har abin ya gagari magancewa. Ana samun irin wannan matsalar ne a yankunan da suke zaune cikin daji sosai da Fulani. Wani mugun abu da yake faruwa a wasu lokuta da mutanen ƙauyukan ne ɓarayin ke haɗa kai a yayin aiwatar da satar.

4.2.3 Kisan Gilla

Wannan nauin taaddanci yakan faru a dukkan wuraren da wannan muƙala ta rattaba. A wasu lokuta yan bindigan kan aike da saƙon kai hari a gari kuma su je, su yi ɓarna yadda suke so, su wuce. Akwai dalilai da dama da suke haifar da irin wannan taaddanci a yankin Gummi, galibi ɓarayin sukan kai irin wannan hari ne inda suka sami turjiya daga mutanen ƙauye ta fuskar ƙalubalantar su ko fito-na-fito da su har su yi wa ɓarayin ɓarna, ko kuwa a garuruwan da suke da matasa masu aikin sa-kai.

5.0 Dalilan Taɓarɓarewar Tsaro a Ƙasar Gummi

Dalilai da yawa sun taimaka wajen taɓarɓarewar tsaro a Gummi da kewaye. Daga cikinsu kuwa akwai;

i. Rashin Ilmin addini da na zamani ga jamaar yankin.

ii. Rashin nagartattun sanaoin dogaro da kai.

iii. Rashin isassun jamian tsaro a cikin garuruwa da ƙauyukan yankin.

iv. Rashin wayar da kai ga jamaar yankin game da amfanin zama lafiya.

v. Yawaitar yan rashin kishin ƙasa da suke haɗa kai da yan taadda wajen aiwatar da miyagun ayyukansu.

vi. Sakacin hukuma da jamian tsaro wajen daƙile hare-haren yan taadda a yankin.

vii. Ayyukan yan sa kai na kashin gilla ga Fulanin yankin.

viii. Sakacin shugabannin Fulani da Manoman yankin wajen magance matsalar ɓarnar kayan gona.

ix. Rashin hanyoyin sufuri a cikin dazukka da garuruwan da suke a nesa da manyan garuruwa.

x. Sakacin Iyaye da shugabanni wajen tarbiyyar matasan yankin.

xi. Rashin Jamian tsaro masu kula da kan iyakokin Gummi da makwabtanta.

6.0 Dabarun Magance Matsalar Tsaro a Ƙasar Gummi

Magance matsalar tsaro da ake fuskanta a Gummi da jihar Zamfara baki ɗaya abu ne mai sauƙi idan an yi amfani da waɗannan matakai kamar haka;

a.       Samar da kyakkaywar makoma ga matasan yankin wajen ilmantar da su da kuma samar masu da sanaoin dogaro ga kai. Yin haka zai hana su haɗa kai da baƙin haure wajen addabar yanuwansu ta hanyar garkuwa da su ko satar dukiyoyinsu.

b.       Inganta tarbiyyar matasan yankin daga matakin gida da unguwa da sauran jamaa.

c.        Tsayar da mulkin adalci daga sarakuna da shugabannin siyasa. Hakan kuwa ba zai samu ba sai sarakuna sun kawar da kwaɗayin samun kuɗi cikin sauƙi daga talakawansu. Samuwar hakan ne ya sa ake zargin wasu sarakuna da hakimai da hannu wajen rura wutar rashin tsaro a Zamfara.

d.       Tsare dokokin Allah SWA da martaba su.

e.       Martaba dabarun tsaron ƙasa irin na gargajiya da muka gada kaka da kakanni.

 

 

7.0 Sakamakon Bincike

Wannan muƙala kamar yadda aka gani ta yi nazarin rashin tsaron da yake addabar yankin Gummi a yau da kuma tantance wuraren da matsalar tsaron ta yawaita da fayyace dalilan rashin tsaron da hanyoyin magance shi. Dangane da haka, muƙalar ta taskace sigogin rashin tsaro guda uku da ake da su a ƙasar Gummi da gano garuruwa da ƙauyuka guda ashirin da ɗaya (21) da suka fi fuskantar matsalar. An fayyace dalilai guda goma (10) da suka haddasa samuwar rashin tsaro a ƙasar Gummi tare da tsakuro dabaru ko hanyoyin magance matsalar tsaro guda biyar (5) a yankin.

8.0 Naɗewa

Wannan muƙala kamar yadda aka gani wani yunkuri ne na lalubo dabarun magance taɓarɓarewar tsaro a ƙasar Gummi. An nazarci abin ta fuskar maanar tsaro da rabe-rabensa da kuma sigoginsa da wuraren da suke fuskantar barazanar tsaro a ƙasar Gummi. A ƙarshe an fito da dalilai da kuma hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro a Gummi da ma Zamfara gabaɗaya.

Manazarta

Abbas, H (2014), Gargajiya da Tsaro: Mafita Ga Rashin Tsaro A Ƙasa. Journal of Hausa Studies. F.C.O.E (TECH), Gusau, Zamfara State.

Achi, B. (1985), The Development and Functions of City Walls in the Savanna Belt of the Nigerian Area. M. A Dissertation, ABU Zaria.

Adamu, M. (1979), The Hausa Factor In West African History. ABU Press, Zaria.

Adamu, M. T. (1997), Asalin Hausawa Da Harshensu. Ɗan Sarkin Kura Publishers, Kano.

Alhassan, H. da wasu (1982) Zaman Hausawa, Zaria: Longman.

Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe Alada, Legas :Tiwal Nigeria Ltd.

CNHN (2006) Ƙamusun Hausa, Kano: Jamiar Bayero.

Department of State Services (2012). Manual. Abuja: National Headquarters State Services.

Dokaji, A. A. (1978), Kano Ta Dabo Ci Gari. NNPC, Zariya.

El-Amin, A. (2007), Hassan sarkin Dogarai. Printed in Kano.

Garba, A.S. (2020) Insecurity in Bukkuyum L.G.A From the Lenses of Ungoverned Spaces. Paper presented at the National conference on Zamfara Kingdom. Organized by FAIS UDUS.

Sarkin Gulbi, A. (2013), Tsafe-Tsafen Dimokuraɗiyya. Maƙalar da aka gabatar a    taron ƙara wa juna sani na ƙasa na farko da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jamiar Bayero          Kano ta shirya daga ranar 14-16 ga Janairu, 2013.

Sarkin Gulbi, A. (2014), Magani A Maaunin Karin Magana. Kundin Digiri na Uku. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jamiar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Yahaya, Y. I. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC, Zaria.[1] CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Shafi na 452.

[2] Wani kauye ne a yankin karamar Hukumar Talata Mafara

[3] Hira da Mai martaba Sarkin Gummi Alhaji Aliyu Abara Gummi Emir na biyu, A gidansa ranar Assabar 12-2-2000 da misali karfe 10:00 na safe. Mun yi wannan tattaunawa ne kafin ya zama Sarki.

[4] Wannan bayani an same sa ne ga Ubandoman Sifawa Hakimin cikin gari, ɗan kimanin shekara sittin a gidansa, ranar Jumaa 28-08-2014, da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

[5] Akwai sassacin faruwar irin wannan taaddanci a cikin garin Gummi da wasu kauyukka da dama da suke cikin karkara inda babu rukukin daji a zagaye da su.

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.013

Post a Comment

0 Comments