Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana'a Sa'a: Shawara Ga Masu Niyyar Kai Yara Wajen Koyon Sana'a

Akwai abubuwan da suka kamata masu niyyar kai yaransu wajen koyon sana'a su yi la'akari da su:

1. Kar ka bari yaro ya san daɗin kuɗi ba tare da ya san wahalar samun su ba.

2. Ka yi ƙoƙari ka kai shi wajen sana'a da zarar ya kammala aji uku na sakandare yadda zai iya kammala koyon sana'ar a lokacin da zai kammala sakandare.

3. Ka tabbatar inda ka kai shi koyon sana'a ba kyauta ake koyarwa ba. Ka biya a koya masa. Idan ma kyauta ne to ka riƙa yiwa mai gidansa ihisani lokaci zuwa lokaci. Duk inda ake biyan kuɗin koyo da gaske ake yi.

4. Ka tabbatar wanda zai koyawa ɗan ka ko ƙaninka sana'a mai tarbiyya ne. Ko shakka babu wasu ɗabi'un sa za suyi naso a kan yaron. Misali gaskiya, amana, jajircewa d.s.s.

5. Kar ka bari sai yaro ya girma sosai sannan ka ce ya je ya koyi sana'a. A wannan lokacin gani zai yi takura ce kuma idan ya fara balaga zai iya jin kunya don kar budurwarsa ta gansa yana koyo. 

6. Kar ka kai yaro koyon sana'ar da ba ta cigaba ko tafiya da zamani. Ka riƙa kasa kunne ka na sanin sana'o'i na zamani don kar ka yi wa yaro kuskure. Wani lokacin ana iya bawa yaro zaɓi na irin sana'ar da ya ke so. In babu matsala sai a kai shi.

Shawara kyauta

Gyaran wayoyi

Post a Comment

0 Comments