Ranar Hausa ta Duniya (International Hausa Day)

    Ranar Hausa (Ko kuma #RanarHausa) da turanci Hausa Day, Rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta.an fara bikin farko a shafukan sada zumunta musamman ta shafin twitter da niyyar hada L1 da L2 na masu magana da harshen Hausa. An zaɓi ranar 26 ga watan Augusta domin tuna ranar da aka ƙirƙiro haruffan "ƙ" da "ɗ" da "ɓ" wanda babu su a haruffan Turanci.

    A Yayin bikin na cika shekara 5, mutane fiye da 400,000 suka gudanar da bikin ta yanar gizo da wasu kasashen da Hausawa suke zaune a sassa daban daban na duniya irinsu Faransa, Amurka, Kamaru, Ghana, Nijar, da Najeriya, kuma a irin wanan rana hausawa na duniya na cika shafukan zumunta da da zantuttuka masu nuna Alfahari da yarensu, wasu wajajen sukan shirya bukukuwa a wanan rana.

    Asali

    Ranar Hausa dai ta samo asali ne a shekarar 2015 bayan É—an jarida Abdulbaqi Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta suka ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da harshen Hausa za su haÉ—u su tattauna ci gaba da kalubalen da harshen ke fuskanta a karni na 21. Kuma ana bikin Ranar Hausar ne a 26 ga watan Agustan kowace shekara a Duniya.

    Muhimmanci

    An ƙirƙiri wannan rana ce domin duba da mahinmancin ta ko kuma mahinmancin da zata bada. Makasudin wannan rana dai itace. Domin ciyar da yaren hausa gaba, al'ummar su, al'adunsu da kuma samun hadin kan hausawa a duniya baki daya.

    A kowace shekara idan ranar ta zagayo ma'abota shafukan sada zumunta ke yin amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara.

    Nasarorin da Aka Samu

    Wadanda suka ƙirƙiro wannan ranar sun ce sun yi haka ne domin tuna wa da al'ummar Hausa game da muhimmancin harshen da yadda za a ciyar da shi gaba.

    Sannan kuma ranar ta kasance a matsayin wata rana da ake ƙalubalantar al'ummar Hausawa domin fiddo da sabbin bincike da nazarce-nazarce domin habbaka harshen na Hausa.

    Babbar nasarar da za a ce Ranar Hausa ta Duniya ta haifar ita ce haÉ—a kan al'ummar Hausawan duniya a duk inda suke. A shekarar da ta gabata, an gudanar da bikin Ranar Hausa a kashe 17, cikinsu har da Faransa da Saudiyya.

    Hausawa na haduwa a wannan rana domin sada zumunci da kuma tattaunawa a kan yadda za su taimaka wa juna.

    A wannan shekarar "ana sa rai za a gudanar da bikin a ƙasashe sama da 30.

    Girman Harshen Hausa

    Masana harshe da dama na yi wa harshen Hausa kallon wani harshe mai yaduwa a fadin duniya, inda yanzu haka nazarce-nazarce ke nuna cewa Hausa ce harshe na 11 a fadin duniya wajen masu amfani da harshen kuma na daya a Afirka ta yamma.

    Sai dai akwai jayayya tsakanin manazarta kan girman Hausa a nahiyar Afirka, inda wasu ke ganin harshen Swahili da ake yi a kasashe da dama na yankin Afirka maso gabas ya dara na Hausa wanda ake yi a yankin Afirka ta yamma da Afirka ta tsakiya da ma kusurwar Afirka.

    Sai dai nazarce-nazarce sun nuna harshen Hausa yana gaba da na Swahili ta fannin yawan masu yin yaren inda ita shi kuma Swahili ke gaba wajen yawan kasashen da ake yin yaren.

    Tuni dai manyan kafafe irinsu Facebook da Google suke amfani da harshen Hausa inda tuni manhajar amfani ta Android da IOS suka shigar da shi cikin harsunan da yake amfani da su.

    Ko a Shekarar 2020 sai da hukumar Lafiya ta Duniya ta sanya Hausa a cikin harsuna guda uku da ta zaba domin yaki da annobar korona a Afirka.

    Ana fatan harshen Hausa zai samu karbuwa nan ba da jimawa ba cikin harsunan amfani na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar hada kan ƙasashen Afirka ta AU da ma Kungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS.

    Iyaka dai har yanzu ana bukatar bincike sosai da nazari a kan harshen Hausa ta hanyar sabbin kirkire-kirkire na zamani domin daga martabar harshen.

    Ranar Hausa ta Duniya

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.