Ticker

6/recent/ticker-posts

Mawaka A Idon Hausawa: Korafi A Cikin Wakar Ranar Mawaka Ta Fati Da Kasim

Citation: Sani, A-U.; Hamma, A.; Aliyu, I. & Aliyu, K. A. (2022). Mawaƙa A Idon Hausawa: Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa Ta Fati Da Kasim. Sch Int J Linguist Lit, 5(7): 209-216. DOI: www.doi.org/:10.36348/sijll.2022.v05i07.002.

Mawaƙa A Idon Hausawa: Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa Ta Fati Da Kasim

Abu-Ubaida SANI1
Aliyu Hamma2
Ibrahim Aliyu3
Kachalla Aliyu Abubakar4

1Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Nigeria
2, 3, & 4 Department of Hausa Studies, College of Education, Waka-Biu, Borno State, Nigeria

Tsakure

Hausawa na ɗaya daga cikin al’ummu da Allah ya azurta da ɗimbin mawaƙa. Tun inda aka fito, Bahaushe na amfani da waƙa a kusan dukkan ɓangarori ko al’amuran rayuwarsa. Wannan ya haɗa da sana’o’i (noma da saƙa da dukanci da farauta da sarkanci da ƙira da makamantansu), da kuma zamantakewa da bukukuwa da gyaran muhalli da ma sauran sha’anonin da rayuwar Bahaushe ke ƙunshe da su. Sai dai kamar yadda akan ce; “Idan kiɗa ya canza, rawa ma sai ta canza,” haka ma siga da salon waƙoƙin Hausa na canzawa tare da canjin zamani. A yau zamani ya kai, an samu mawaƙa da dama da ke amfani da kayan kiɗa na zamani yayin rera waƙoƙinsu. Sai dai wani abu shi ne, mawaƙan ƙasar Hausa na fuskantar tsangwama. Sau da dama matsayinsu ga idon jama’a ba ya wuce maroƙa ko limamen shashanci. Wannan ne ya sanya mawaƙa da dama ke rera waƙoƙi da ke nuna ƙorafinsu ga hakan. Wannan takarda ta nazarci ɗaya da cikin waɗannan waƙoƙi mai suna Waƙar Ranar Mawaƙa wanda Fati da Kasim suka rera. Sakamakon nazarin na nuna cewa; mawaƙa na fuskantar tsangwama a ƙasar Hausa. Sannan al’umma ba ta tallafa wa waɗannan mawaƙa ta fuskar shawarwari da sauran abubuwa da suka dace. Daga ƙarshe an ba da shawarwari da suka haɗa da, a riƙa jawo mawaƙa jiki tare da ƙarfafa musu guiwa da nusar da su kan samar da waƙoƙi masu amfani ga al’umma ta fuskar ilimi da zamantakewa.

 

Fitilun Kalmomi: Waƙa; Mawaƙa; Ƙorafi; Tsangwama

 

1.0   Gabatarwa

Kamar dai yadda waƙa ta kasance hanyar isar da saƙwanni da kuma bayyana muradin zuci, mawaƙa kan yi amfani da waƙa domin ƙorafi game da wani abu da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafen da mawaƙa suka fi yi, shi ne tsegumi da kallon banza da aka faye yi musu; wani lokaci har da musgunawa daga hukuma. Sukan nuna rashin jin daɗin hakan cikin hikima da fasaha a waƙoƙi daban-daan da suke rerawa.

ɗaya ɓangaren kuma, a shekarun baya-bayan nan ne (wajajen 2013) mawaƙan Hausa suka ƙirƙiri wata ƙungiya mai suna Ranar Mawaƙan Hausa Foundation (RMHF), ƙarƙashin jagorancin Aminu Ladan Abubakar (ALAn Waƙa). Ƙarƙashin wannan ƙungiya, akan gudanar da taron mawaƙƙarshen kowace shekara. Akan ɗauki kwanaki ana gudanar da taron. Wato dai, har sai an shiga sabuwar shekara. Taron na samun halartar mawaƙa daban-daban, da masana waƙa (malamai) har ma da shuwagabanni da sarakunan gargajiya. A bisa wannan ne, Fati da Kasim suka shirya waƙar da ke nuna koke ko ƙorafi game da mawaƙa a idon Bahaushe a yau. Sun yi amfani da wannan taron mawaƙa da ake gudanarwa, inda suka kira shi Ranar Ɗaya Ga Watan Ɗaya. Za ta yiwu sun yi hakan ne kasancewar, wannan taro na samun halartar mafi yawan fitattun mawaƙa daga kowane ɓangare na ƙasar Hausa.

2.0   Waƙa A Ƙasar Hausa

Waƙa ba sabuwar aba ba ce da ake da buƙatar dogon bayani game da ma’anarta. Masana da manazarta da dama sun bayyana ma’anar waƙa a rubuce-rubuce da suka gabatar a matakan ilimi daban-daban. Masana da marubuta da suka yi tsokaci kan ma’anar waƙa sun haɗa da: Gusau, (1993) da Ƙaura, (1994) da Yahya, (1996) da Bunza, (1988) da Habibu, (2001) da Zurmi, (2006) da Maikwari, (2020) da makamantansu.

Waƙa wani furuci ne (lafazi ko saƙo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaitattun kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi. (Ɗangambo, a cikin Habibu, 2001).

Shi kuma Alƙali Haliru Wurno a waƙe ne ya bayyana nasa ra’ayi kan ma’anar waƙa kamar yadda Abdullahi, (2017) ya rawaito cewa:

Waƙɗumi ne hira ko labari,

Zargi yabo zagi da kiznin sharri,

Koko kwaɗai ga mutum ya ba ka ka amsa.

 

Labar ɗumi na wanda kay yi ga tsari,

Wani dunƙulalle kay yi jeri-jeri,

A cikin nashaɗi ko ganin ka ƙosa.

 

Waƙe bayani na kaɗanna da tari,

Wani bi ka sa gishiri ka yo mishi ƙari,

Haɗari na waƙe mai faɗin damassa.

 

Waƙa da waƙe Hausa sun ɗauke su,

Sunansu waƙa ko’ina an san su,

Ka biɗo bayani babu sai dai kansa.

 

Waƙa fasaha ne da yac cuɗe ka,

Kuma ba karatuna ba in an ba ka,

Ilimi dubu sai ka biɗo wani nasa.

 

A cikin ɗumi waƙe kamar rana ne,

Kuko ya zam hadarin ruwan bazara ne,

Shi taho da sanyinai na ma’aunin nesa.

(Alkali Haliru Wurno ma’anar waƙa)

Sai dai waƙa a ƙasar Hausa ba nau’i ɗaya ba ce kawai. Ɗangambo, (2007) ya ƙarfafa cewa: “Ya kamata mu tuna cewa akwai waƙoƙi iri biyu: rubutacciyar waƙa da waƙar baka, wato waƙar makaɗa.” Gusau, (2003) cewa ya yi: “Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amo kari da kiɗa da amshi.”

Abu ne mai wuya a iya ƙayyade asalin lokacin da Bahaushe ya fara waƙa. Wannan kuwa na faruwa ne dalilin kasancewar a farkon rayuwar Bahaushe ba shi da ilimin karatu da rubutu. Ya samu wannan ilimi ne bayan cuɗanyarsa da al’ummar Larabawa da kuma karɓar addinin Musulunci da ya yi. Bayan ya koyi karatu da rubutu ta hanyar amfani da baƙaƙen Larabci domin rubuta Hausa (ajami), sai kuma ya fara rubuta waƙoƙi. Wannan na nuna cewa, tun kafin zuwan Musulunci da kuma hanyar rubutu Bahaushe na rera waƙoƙi da baka. Game da zuwan Musulunci ƙasar Hausa kuwa, an samu bambancin ra’ayi tsakanin masana da marubuta. Habibu, (2001) ya nuna cewa waɗansu na ganin cewa addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun ƙarni na goma sha biyu. Wasu ma sun ce tun ƙarni na bakwai. Birnin-Tudu, (2002) ya bayyana cewa tabbacin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun zamanin sarkin Kano Ali Yaji. Wato shekarar 1349 zuwa 1385.

Wani babban lamari ya ɓullo duniyar waƙa yayin da Bahaushe ya samu ilimi da damar fara amfani da kayan kiɗa na zamani domin rera waƙoƙinsa. Amfani da fiyano da sutudiyo ya canji kalangu da ganga da dundufa da makamantansu na dangin kayan kiɗan gargajiya da Bahaushe ya saba amfani da su. Wannan sabon lamari ya samar da muhawara tsakanin masana waƙoƙin Hausa. Wasu dai suna da ra’ayin cewa, duk waƙar da aka sa mata kiɗa, to ta tashi daga rubutacciya. Saboda haka za a kira ta ne waƙar baka kai tsaye. Wasu kuma suna kallon cewa, sabon salo da waƙoƙin suka zo da shi, sun fi ƙarfin a kira su waƙar baka kawai. Idan aka yi haka, haƙiƙa ba a yi wa waƙar baka ta asali adalci ba. Domin ita ba sai an rubuta ba ake rerawa. Ma’ana ana rattabo ta ne kawai kai tsaye.

Wani bambanci da ke tsakanin waƙoƙin da ake samarwa a sutudiyo da na baka shi ne, a waƙoƙin baka ba a samun amsa-amo da daidaiton baituka kamar yadda yake samu a waƙoƙin zamani na sutudiyo. A wannan ɓangare (ƙafiya da daidaiton baituka) waƙoƙin zamanin sun fi kama da rubutattun waƙoƙi. A taƙaice dai, waƙoƙin sai suka kasance tamkar jemage; ba su ga tsuntsu ba su ga dabba. Wato dai siffofinsu ba su tsaya ga waƙoƙin baka ko rubutattu ba kaɗai. Za ta iya yuwawa, wannan ne dalilin da ya sa kafar intanet na Hausa mai suna amsoshi (www.amsoshi.com) ya kira irin waɗannan waƙoƙi da Waƙoƙin Zamani. Domin kuwa, duk inda aka zaga aka zago, dole ne a yarda waƙoƙin sun samu ne a zamanance. Sannan zamani yana tasiri ga waƙoƙin da su kansu mawaƙan.

3.0   Amfanin Waƙa

Haƙiƙa waƙoƙi suna taka muhimmiyar rawa wurin faɗakarwa tare da wa’azantarwa ga al’umma bayan ɗumbin nishaɗantarwa da akan samu daga gare suA fahimtar Zurmi, (2006), ba za a taɓa mantawa da gudummuwar rubutattun waƙoƙi ba a lokacin jihadin jaddada addinin Musulunci ƙarƙashin jagoranci Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. A zamanin yau kuwa, ɓangarorin rayuwa da dama sukan rasa armashi idan babu waƙa. Bello, (2017) ya zayyano wasu daga cikin fannonin rayuwa da waƙa ke taka rawar gani gare su. Sun haɗa da: siyasa, da ilimi da tarihi da makamantansu. A taƙaice, amfanin waƙa sun haɗa da:

i.                    Waƙa babbar hanya ce ta jawo ra’ayin al’umma a lokutan siyasa domin zaɓen wani ɗan takara. Mawaƙa na da babban gurbi wurin tallata ‘yan takara ta hanyar kurara su da fito da ayyukansu na alkairi fili tare da kushe abokan takararsu.

ii.                  Waƙa babbar hanya ce ta tallata haja ga ‘yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban. Masu shaguna da kamfanoni da ma sauran nau’ukan kasuwanci iri-iri kan nemi mawaƙa su tallata hajarsu.

iii.                Waƙa hanya ce ta ilimantarewa da faɗakarwa. Jama’a sukan samu ilmummuka daban-daban tare da wayewar kai daga waƙoƙin da suke saurara. Wannan ya haɗa da bayanai game da cututtuka, da yanayin siyasar ƙasa, da tarihi da makamantansu.

iv.                Waƙa hanya ce ta samun abin masarufi da dogaro da kai ga mawaƙa da dama.

v.                  Waƙa na samar da nishaɗi da annashuwa.

vi.                Kafa ce ta adana tarihi da al’adu. Akwai waƙoƙi da suke ɗauke da tarihin muhimman mutane cikin al’umma ko wasu muhimman lamura da suka faru. Ire-iren waɗannan waƙoƙi za su kasance tamkar taska na adana waɗanan muhimman tarihai har zuwa lokaci mai tsawo nan gaba.

vii.              Waƙa na tallafa wa waɗansu ɓangarorin adabin Bahaushe na baka da rubutattu. Misali, tazuniya a gargajiyance da finafinai a zamanance duk sukan yi armashi ta dalilin waƙoƙi da ake sanyawa ciki.

viii.            Waƙa hanya ce ta tallatawa tare da yaɗa harshe zuwa ga wasu al’ummu da duniya baki ɗaya.

ix.                Waƙa ta kasance babbar hanya da al’umma za su iya bayyana kukansu ga gwamnati ko wata majiya a matsayin ƙungiya ko ɗaiɗaikun jama’a.

4.0   Mawaƙa A Idon Al’umma

Duk da ɗunbin amfanin waƙa, mawaƙa na fuskantar matsin lamba tare da tsangwama ta fuskoki daban-daban. A mafi yawan lokuta akan ɗauki mawaƙa a matsayin watsattsun mutane waɗanda ba sa riƙo da addini. Wani lokaci akan ɗauke su a matsayin mabarata kawai sannan marasa mutuncin kai ko wata ƙima ta a-zo-a-gani. Wannan nazari ya yi hasashen wasu dalilai da za su iya kasancewa sanadiyar wannan kallon hadarin kaji da ake yi wa mawaƙa. Dalilan sun haɗa da:

i.                    Kasancewar wasu ɓata gari a cikin mawaƙa da ke ayyukan da suka ci karo da al’ada da kuma addinin Hausawa. Wannan ya haɗa da shigar da ta saɓa wa al’ada yayin gudanar da waƙoƙi da tarukan mawaƙa, da kuma waƙoƙin batsa da makamantansu.

ii.                  Mawaƙa da suka mayar da waƙa hanyar maula: Wannan ma zai iya kasancewar dalilin faɗuwar daraja da ƙimar mawaƙa a idon al’umma. Hakan na faruwa ne kasancewar addini da al’adar Bahaushe bai aminta da lalaci da mutuwar zuciya ba.

iii.                Siffa da salon Turawa: Waƙoƙin sutudiyo dai sun samu ne a zamanance, bayan cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu musamman Turawa. Ƙyamar da Bahaushe ke yi wa al’adun Turawa zai iya kasancewa dalilin da ya sa ya ƙyamaci waƙoƙin zamani. Wato dai an ci biri har an sha romonsa.

iv.                Shagala: Addinin Bahaushe bai yarda da shagala ba. Wannan zai iya zama dalilin tsangwama ga mawaƙa. Musamman yayin da aka ɗauki waƙa a matsayin hanyar shagala ga al’umma.

Haƙiƙire-iren waɗannan dalilai na da nasaba ga irin kallon da ake yi wa mawaƙa a ƙasar Hausa a yau. Irin wannan tsangwama ta sanya mawaƙa da dama sun yi raddi ko martani a cikin waƙoƙinsu. A cikin ire-iren waɗannan waƙoƙi na raddi sukan nuna baƙin ciki da takaicin salon kallon banza da tsangwama da ake musu. A wasu lokutan har sukan yi baƙar addu’a ga mutanen da ke neman ɓatanci gare su. A waƙar Ala da abokan ɗaninsa ta Hasbunallahu, za a iya kallon inda mawaƙan suka nemi tsari daga masu yin ɓatanci ga san’arsu ta waƙa kamar haka:

Ya mai tsare halitta mun zo ka taimake mu,

Ka ba mu kariya kar wani ɗa ya addabe mu,

Allahu kai katanga ta tsari ga magautanmu,

Masu bibiyar ɓatanci ga sana’unmu,

 

Mun zamma sai ka ce jemagu da iyalanmu,

Mun zamma mujiya a cikin jinsin yarenmu,

Suna ta cin amanar bayinka cikin hammu,

Sun shigga innuwar al’adu addininmu,

Allahu don isarka da mu kai kaƙ ƙage mu,

Ka ba mu kariya don ƙaunar Abu Batulu.

 

Haƙiƙa a baitukan da ke sama, mawaƙan sun nana cewa, masu neman ɓatanci ga sana’arsu ta waƙa suna jingina abin ne ga al’ada da kuma addini. Wato dai suna nuna cewa, waƙa ta ci karo da addini da kuma al’adar Bahaushe. A cikin wannan waƙar kuma, sun yi baƙar addu’a ga ire-iren waɗannan mutane (masu neman ɓatanci ga waƙa da mawaƙa), inda suke cewa:

Muna da maƙƙiya wanda ka yarda mun ka gan su,

Akwai na ɓoye wanda kawai Rabbi kai ka san su,

Rugurguje shirinsu ka mai da shi bissa kansu,

Da sun kira ka Allah don miƙa buƙatunsu,

Ka juyar da buƙatunsu ya Zuljalalu.

 

Cutar Gloria har cholera gami da tension,

Cutar hawan jini har Typhoid in addition,

Cuta ta kuturta da makanta a conclusion,

Cuta ta ƙanjamau mai hana ɗan Adam emotion,

Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

 

Cuta ta Asthma da Koshorko ka sa gare su,

Cutar Pneumonia da ƙarzuwa cikin jikinsu,

Ciwo na karkare da kurkunu ka sa gare su,

Cutar Malaria Fever sa ka kassara su.

Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

 

Cuta ta Anthrax Allah sa a jikkunansu,

Cuta ta Glaucoma a sa a maganansu,

Cuta ta Trachoma maƙala wa ijjiyarsu,

Ka mai da su kurame ka ɗoɗe maganansu,

Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

 

5.0   Game Da Waƙar Ranar Mawaƙa

Waƙar Ranar Mawaƙa waƙa ce da aka yi ta bisa salon ɗani. Salon ɗani dai yanayi ne da wani mawaƙi ke yin ɗani (wato tayawa ko tsokaci ko tsoma baki) a cikin waƙar wani mawaƙi daban. Wannan takarda ba ta mayar da hankali kan wani abu daban ba, face wadda waƙar ta zo da ita. Kenan dai, komai dangane da waƙar ko mawaƙan zai fito ne daga bakin su mawaƙan. Takardar ta fahimci cewa, mawaƙa biyu ne suka yi waƙar. Asalin mai waƙar sunanta Fati kamar yadda aka ambata a cikin ɗiyan farko a baiti na bakwai (7) na waƙar. Misali:

Fati waƙa fa kwalba ce …

Sai kuma wanda ya yi ɗani a waƙar da ke da suna Kamis, kamar yadda ya zo a ɗan fari da ke baiti na huɗu cikin waƙar. Misali:

Amma Kamis fa duk da haka …

Waƙar tana da baituka goma sha shida (16). Dukkansu sun kasance masu ƙwar huɗu in ban da baiti na sha shida da ya kasance mai ɗiya goma sha huɗu (14). Baitukan na da ƙananan amsa amo mai canzawa daga baiti zuwa baiti. Sannan waƙar tana da babban amsa amo na: ‘ma’ wanda ke zuwa ƙarshen kowane baiti.

A farkon waƙar an kawo shimfiɗa cikin salon siffantawa game da ranar mawaƙa, kamar haka:

Ranar ɗaya ga watan ɗaya,

Ga mu bai ɗaya,

A wuri ɗaya,

Shigarmu ɗaya,

Manufarmu ɗaya,

ƙasarmu ɗaya Najeriya.

Sannan waƙar tana ɗauke da amshi mai ɗiya biyu. Shi ma wannan amshi yana bayani ne game da ranar mawaƙa. Wato ranar ɗaya ga watan ɗaya. Amshin ya kasance kamar haka:

Ranar ɗaya ga watan ɗaya ita ce ranar mawaƙa,

Ranar baje kolin fikira da nishaɗantar da al’umma.

An buɗe waƙar da addu’a tare da salati ga manzo a baiti na ɗaya da kuma na biyu:

Ya Rabbi Ubangijin kowa,

Daga mai rai har zuwa gawa,

Rabbana ka tsare mu gantsarwa,

Mui waƙar babu ɓamɓarma,

 

Rabbana tsira amincinka,

Ka daɗa wa Makiyu zaɓinka,

Ka cika shi kakaf da yardarka,

Don ya tsamo ‘yan cikin ɓurma.

Baya ga haka, mawaƙan sun yi amfani da salailai daban-daban domin isar da saƙon waƙar. Waɗannan salailai sun haɗa da salon kamance da na abuntawa da sauransu. Sarɓi, (2007) ya bayyana ma’anar salo da cewa: “A fagen nazarin waƙa salo hanya ce da marubuta waƙoƙi ke bi wajen isar da saƙonsu ga jama’a.

6.0   Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa

Turken waƙar ranar mawaƙa ita ce ƙorafi. Turke da jigo kalmomi ne masu ma’ana ɗaya wanda ake amfani da su wurare daban-daban. Wato kamar dai yadda ake amfani da jigo a rubutattun waƙoƙi, haka ake amfani da turke a waƙoƙin baka. Abdullahi, (2017) ya rawaito ma’anar turke daga Ɗangambo (2007): “Jigo shi ne saƙo, manufa, ko abin da waƙa ta ƙunsa wato abin da take magana a kai.” Wannan ya yi daidai da ma’anar da Yahya (1997) ya bayar cewa: “Jigo na nufin saƙo ko manufa ko bayani ko ruhin da waƙa ta kunsa wanda kuma shi ne abin da waƙa ke son isarwa ga mai sauran ko karatu ko nazarinta.” ‘Yar’aduwa (2010: 149) ya ce: “Jigo kalma ce da masana adabin Hausa suka amince su riƙa yin amfani da ita wajen ambaton saƙon da zube ko wasan kwaikwayo ko waƙe suke ɗauke da shi.”

Kamar yadda aka bayyana a sama, jigo da turke na nufin manufar waƙa. Gusau, (1993: 28) ya bayyana ma’anar turke da cewa: “Turke shi ne abin da waƙa take magana a kansa wanda ya ratsa ta tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta.” Baituka da dama cikin waƙar Ranar Mawaƙa na ɗauke da ƙorafi game da irin kallon hadarin kaji da al’umma ke yi wa mawaƙa. Bayan baituka biyu na buɗewa, mawaƙiyar ta nuna matsayinsu da amfanin ranar mawaƙa inda take cewa:

Yau ce ranar mawaƙa,

Rana ta ruwan hazaƙa,

Bishiyar fikira muke tsinka,

Muke shayar da al’umma.

 

Ta yi amfani da salon abuntawar abuntawa, inda ta ta kwatanta baitukan hazaƙa da ake yi da ruwa a ɗiya na biyu. Ta yi haka dan ta nuna ɗimbin waƙoƙin fikira da hazaƙa da ake gabatarwa a ranar mawaƙa. A ɗiya na uku kuma sai ta yi amfani da salon abuntawa inda ta kwatanta waƙoƙin fikira da fasaha da mawaƙa ke gabatarwa da tsinkar bishiyar fikira. Daga nan kuma sai mawaƙiyar ta kawo ƙorafi a baiti na huɗu, inda take cewa:

Amma Kamis fa duk da haka,

Ana zagin mu ba shakka,

Har a sa mu sahu na ‘yan shirka,

A cire mu sahu na Islama.

A nan mawaƙiyar na ƙorafin cewa, duk da irin gudunmuwa da suke bayarwa wurin yaɗawa da tallata al’adun Bahaushe, al’umma suna tsangwama gare su. Har ma ana siffanta su da masu yin shirka. A baiti na biyar ma, mawaƙiyar ta yi ƙorafi na cewa:

Sai a ce kar ka auri mai waƙa,

Mace ko namijinsu su duka,

Maroƙa ne baƙar harka,

Ba a bambance mu gun ƙyama.

A nan tana ƙorafi da yadda al’umma ta ɗauki mawaƙa maza da mata a matsayin abin ƙyama, sannan maroƙa masu baƙar harka. Ta yi amfani da salon kamancen daidaito wurin nuna ƙyamar da ake yi wa mawaƙa maza da mata. Kamar dai yadda take cewa ba a bambance mu gun ƙyama (bambance mawaƙa maza da mata). Daga nan sai mai ɗani ya karɓa, inda shi ma ke ƙorafi a baiti na shida da cewa:

Fati wai don muna waƙar,

Aka sa mu cikin sahun shirkar,

Iko daga Rabbana Ƙadir,

Waƙa ta zam abin ƙyama.

A nan ya nuna takaicin yadda aka sanya mawaƙa a sahun shirka kawai a dalilin suna waƙa. Ya yi amfani da da salon kambama a wannan gaɓa. Domin kuwa laifin da ake tsangwamar waƙa da shi bai kai matsayin shirka ba. Amma a nan sai ya kambama abin ta hanyar kwatanta tsangwamar da tuhuma game da shirka. A ɗiya na uku da na huɗu kuma, sai ya bayyana cewa, waƙa iko ne kuma Ubangiji, amma jama’a sun kasa ganewa, a maimakon haka, sai suke tsangwamar masu wannan baiwa ta waƙa. A baituka na gaba kuwa, mawaƙan sun yi amfani da salon kamantawa wurin bayyana matsayin waƙa. A baituka na takwas sun kamanta waƙa da kwalabe da aka jera, sannan aka sanya musu abubuwa daban-daban:

Idan ga kwalabe an jera,

Na giya da turare da madara,

Zuma da ruwa fa har minira,

A dukansu a kwalba al’umma.

A wannan baiti ya yi amfani da salon duguwar siffantawa; inda ya siffanta nau’ukan waƙa (ta fuskar jigo) da kwalabe. Kwalaben kuwa sun haɗa da na giya da na turare da na madara da na zuma na da ruwan minira (lemon kwalba). A baiti na tara (9), sun bayyana falsafar da ke cikin wannan siffantawa kamar haka:

Kwalba mai giya haramun ce,

Amma mai ruwa halali ce,

Mai zuma kuma magani dace,

Ga zaƙi ga waraka kuma ma.

Wannan baiti na tara (9) na nuni da cewa, waƙa ba abar ƙyama ba ce har sai idan jigonta ya kasance abin ƙyama. Mawaƙan sun nuna cewa, jigo da salon waƙar da aka yi, shi zai nuna matakin da ya kamata a ajiye ta. Sannan cikin hikima suka nuna cewa, tun da ya kasance a mawaƙa akwai masu waƙoƙi na gari da ke amfanarwa (misali, faɗakarwa da ilimantarwa), a ɗaya ɓangaren kuma akwai waƙoƙin shashanci; ya kamata ne jama’a su riƙe waƙoƙin ƙwarai masu nagarta, su fita batun waƙoƙin shashanci – kamar dai yadda idan aka jera kwalabai, za a bar na giya a ɗauki na ruwa da zuma da makamantansu.

A baituka biyu da suka biyo baya (baiti na 11, da na 12), mawaƙan sun sake fito da maganar da ke sama fili, suna nuni da cewa; waƙa na iya kai mutum wuta ko aljanna. Wuta ko aljanna ga mawaƙi kuwa ya danganta da yanayin waƙarsa. Suka ce:

Waƙa na kai mutum fa wuta,

Idan a cikinta yai wauta,

Tana kuma kai shi aljannata,

Idan a cikinta yai salama.

 

Ko me ka faɗi cikin waƙa,

Da shi za ai hukuncinka,

In alkairi ka sassaƙa,

In sharri ne da shi shi ma.

Wato dai mawaƙan na ƙara jaddada cewa, bai kamata a riƙa yi musu kuɗin goro ba ta hanyar yi musu kallon banza baki ɗaya. Domin kuwa, ko da an samu masu waƙoƙin wauta, cikin mawaƙan akwai masu waƙoƙin salama da za ta iya kai mutum aljanna. A baiti na goma sha biyu (12), sun faɗƙarara cewa, duk abin da mai waƙa ke faɗi cikin waƙarsa, da shi ne za a masa hukunci.

A baiti na goma sha uku (13) kuwa, sun nuna cewa, waƙa fa ba aikin jahilci ba ce. Aiki ne na ilimi wanda ko ciki masu ilimi ma, sai ɗaiɗaikun mutane ke iya waƙa. Suka ce:

Waƙa aiki na ilmi ne,

Jahili bai yin ta kun gane,

Ko mai ilimi sai yai aune,

Ya cika ta da tsantsar hikima.

Wannan magana tasu ta yi daidai da ra’ayin masana waƙa da dama. Masana waƙa suna da ra’ayin cewa, waƙa baiwa ce da Ubangiji ke sanya wa ɗan Adam. A taƙaice dai ba kowa ke da baiwar waƙa ba. Wanda ba shi da baiwar waƙa kuwa, ko da an yi yunƙurin koya masa, ba zai iya koya ba.

A baitukan gaba kuwa (baiti na 14 da na 15), mawaƙan sun kawo wasu muhimman amfanin waƙa guda biyu. Suka ce:

Waƙa na kau da yin yaƙi,

Tana sa wa cikin sauƙi,

Samun ‘yanci fa ba yaƙi,

Tana ɗaga yarenku sama.

 

Duk yaren da babu mai waƙa,

Akwai wahala ya ɗaukaka,

ƙasa yaren da ke waƙa,

Sai ya fi na sauran hawa sama.

A nan sun ja hankalin jama’a zuwa ga rawar da waƙa ke takawa wurin samar da zaman lafiya. Za a iya yarda da maganarsu yayin da aka yi dubi da ɗinbin waƙoƙin da mawaƙa daban-daban suka rera domin jan hankali da faɗakarwa zuwa ga zaman lafiya da haɗin kai da guje wa tashin hankali. Ɗaya daga cikin ire-iren waɗannan waƙoƙi ita ce waƙar Abubakar Ladan Zariya mai suna; ‘Waƙar Haɗin Kan Afirka.’

A gaba kuwa sai suka nuna cewa, waƙa wata babbar garaɓasa ce a cikin yare, da ke taimakawa wajen bunƙasa yaren. Sun nuna cewa, yaren da ba su da mawaƙa, ko ba a waƙa cikinsa, ba zai kai sauran yaruka da suke da mawaƙɗaukaka ba. Za a iya hasashen gaskiyar wannan zance kasancewar waƙa hanya ce ta adana harshe da yaɗa shi tare da kundace al’adunsa da dai sauran muhimman abubuwa da suka shafe shi. Waƙa hanya ce da ke sa a riƙa jin amon masu wannan harshe cikin al’ummun kusa da na nesa.

Mawaƙan sun rufe waƙar da wani dogon baiti mai ɗiya goma sha huɗu (14). A cikin wannan baiti suna nuna rukunnen al’umma da ke da daraja cikin duniya da suka yi waƙa. Sun haɗa da shuwagabannin ƙasa, kamar yadda suka kawo a wasu ɗiya na baitin:

Shugabannin ƙasa suna waƙa,

Muhammad Wardi yai waƙa,

Jibson Gwarma yana waƙa…

Sun kuma nuna cewa, manyan malamai ma kuma sahabbai suna waƙa. Cikin waɗannan sahabbai mawaƙa, har da wanda ya yi dace da aljanna a dalilin waƙa. Inda daga ƙarshen baitin, suka yi addu’ar Allah ya haɗa su da irin wannan dace (ta aljanna). Sun bayyana hakan cikin wasu ɗiya na baitin kamar haka:

Manyan malamai suna waƙa,

Sahabbai ma suna waƙa,

Abubakari mai waƙa,

Umar shi ma yana waƙa,

Usuman shi ma yana waƙa,

Imamu Ali yana waƙa,

Annabi ya sa a mai waƙa,

Da mai waƙar yai waƙa,

Allah ya ji daɗin haka,

Yai mai kyauta da aljanna,

Allahu ka sa da mu mu ma.

 

7.0   Sakamakon Nazari

ƙarshen wannan nazari, an fahimci manyan abubuwa guda uku, kamar haka:

Mawaƙa a ƙasar Hausa na fuskantar tsangwama da matsin lamba. Sau da dama akan musu kuɗin goro kan cewa dukkansu ɓatattu ne da suka yi tarayya cikin shashanci. Ya kamata al’umma da ma gwamnati ta fahimci cewa, mawaƙa ba su taru sun zama ɗaya ba. Ko da an samu masu waƙoƙin shashanci, akwai waɗansu mawaƙan masu ɗimbin yawa da ke waƙoƙi masu ɗauke da ilimantarwa da faɗakarwa kan ɓangarorin rayuwa daban-daban.

Ba a tallafa wa masu basirar waƙa ta fuskar ƙarfafa sumu guiwa ko ba su agaji na shawarwari da kayan aiki da makamantansu. A maimakon haka, sai ma akan yi ƙoƙarin mayar da su saniyar ware. Domin samun cigaba mai amfani, ya kamata gwamnati da sauran al’umma su riƙa jawo mawaƙa kusa tare da ba su shawarwari da buƙatar su (mawaƙan) rera waƙoƙi kan wasu lamura masu buƙatar a ja hankalin jama’a gare su (kamar sabbin cututtuka ko wata sara mara kyau da dai sauransu). Za a ci gajiyar hakan, kasancewar mawaƙan na da baiwar tura saƙwanni zuwa ga ɗumbin al’umma cikin ƙanƙani lokaci.

Waƙa na da tasiri matuƙa tare da ɗimbin amfani wurin isar da saƙwanni da suka shafi faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa da dai makamantansu. Kasancewar waƙa mai ɗimbin amfani, wanda ko bayan nishaɗantarwa da faɗakarwa da ilimantarwa, akan yi nazarinta a makaranti da ke matakan ilimi mabanbanta; ya kamata a samu haɗin kai da aiki tare tsakanin gwamnati da makaranti da ma sauran al’umma baki ɗaya game da lamarin waƙa, duk don cin gajiyar alfanunta tare da ƙoƙarin kawar da shagala da ke ciki.

8.0   Kammalawa

Haƙiƙa waƙa hanjin jimina ce, akwai na ci akwai na zubarwa. Tasirin waƙa ga al’umma na da dogon tarihi. Al’ummu da dama na ba wa mawaƙa daraja da ƙima ta musamman. Ko a cikin Hausawa, ba a ko’ina ba ne, sannan ba koyaushe ba ne ake nuna tsangwama ga mawaƙa. Duk da haka, mawaƙa a ƙasar Hausa na fuskantar tsangwama da takunkumin al’ada. Wannan kuwa na  da nasaba da halaye da ɗabi’u da salailai da suka samu a zamanance, waɗanda suka ci karo da al’ada da addinin Bahaushe na Musulunci. Ƙungiyoyin mawaƙa da hukumomi na da rawar da za su iya takawa wajen ganin mawaƙa ba su wuce gona da iri ba.

Manazarta

Abdullahi, S. M. (2017). “Kuɗi A Idan Mawaƙan Hausa Na Baka Da Rubutattu, Waƙar Kuɗi Ta Alhaji Audu Wazirin Ɗanduna Da Ta Alhaji Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja” Kundin digiri na farko da aka gabatar a Sashen Harunan Nijeriya, Jami’ar Usamnu Ɗanfodiyo Sakkwato

Bello, S. A. (2017). “Tasirin Waƙa A Cikin Al’ummar Hausawa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙƙin Aminu Ladan Abubakar.” Takardar da aka gabatar a taron masoya Aminu Ladan Alan Waƙa, a makarnatar Ado Gwaram, Kano

Birnin-Tudu, S. Y. (2002). “Jigo da Salon Rubutattun Waƙoƙin Fura’u na Ƙarni na Ashirin.” Kundin babban digiri na uku (Ph. D.) wanda aka gabatar a Sashen Harrunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (1988). “Nason Kirari Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na 20.” Maƙalar da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Ɗangambo, A. (1980). “Hausa Wa’azi Verse Fron CA 1800 to CA 1970: A Critical Study of Form, Content, Language and Style. A Ph. D. thesis submitted to the University of SOAS, London.

Dangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Fede Waƙa. Zaria: Amana publishers LTD.

Gusau, S. M. (2003). Jagora Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark.

Habibu, L. (2001). “Bunƙasar Rubutattun Waƙoƙin Hausa a Ƙarni na Ashirin (20).” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Ƙaura, H. I. (1994). “Ƙawancen Salo a Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin Wa’azi da Madahu da Kuma Siyasa.” Kundin kammala digiri na biyu (M.A.) wanda a aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Maikwari, H. U. (2020). “Wasu Al’adun Hausawa Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a matakin jarabawa ta cikin gida a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jamiar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Usaman, B.B. (2018). Ruwa-Biyu: Sabon Zubin Waƙoƙin Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya. An tsakuro daga: https://www.amsoshi.com/2018/03/ruwa-biyu-sabon-zubin-wakokin-karni-na.html.

Yahya, A. B. (1987). “The Verse Category of Madahu With Special Reference To Theme, Style and the Background of Islamic Soures and Beliefs.” A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Yahya, A. B. (1996). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Service.

‘Yar’aduwa, T. M. (2010). Jagoran Nazain Rubutaccen Adabin Hausa. Ibadan: HEBN publishers PLC.

Zurmi, A. D. (2006). “Tsoratarwa a Cikin Waƙoƙin Wa’azi na Nana Asma’u.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

 

Ratayen Waƙar Ranar Mawaƙa Ta Fati Da Kasim


Ranar ɗaya ga watan ɗaya,

Ga mu bai ɗaya,

A wuri ɗaya,

Shigarmu ɗaya,

Manufarmu ɗaya,

ƙasarmu ɗaya Najeriya,

 

Amshi

Ranar ɗaya ga watan ɗaya ita ce ranar mawaƙa,

Ranar baje kolin fikira da nishaɗantar da al’umma.

 

1. Ya Rabbi Ubangijin kowa,

Daga mai rai har zuwa gawa,

Rabbana ka tsare mu gantsarwa,

Mui waƙar babu ɓamɓarma,

 

2. Rabbana tsira amincinka,

Ka daɗa wa makiyu zaɓinka,

Ka cika shi kakaf da yardarka,

Don ya tsamo ‘yan cikin ɓurma.

 

3. Yau ce ranar mawaƙa,

Rana ta ruwan hazaƙa,

Bishiyar fikira muke tsinka,

Muke shayar da al’umma.

 

4. Amma Kamis fa duk da haka,

Ana zagin mu ba shakka,

Har a sa mu sahu na ‘yan shirka,

A cire mu sahu na Islama.

 

5. Sai a ce kar ka auri mai waƙa,

Mace ko namijinsu su duka,

Maroƙa ne baƙar harka,

Ba a bambance mu gun ƙyama.

 

6. Fati wai don muna waƙar,

Aka sa mu cikin sahun shirkar,

Iko daga Rabbana Ƙadir,

Waƙa ta zam abin ƙyama.

 

7. Fati waƙa fa kwalba ce,

Ita mai ɗaukar kalamai ce,

In ta ɗau mara kyau ta lalace,

Kuma mai yi za ya sha fama.

 

8. Idan ga kwalabe an jera,

Na giya da turare da madara,

Zuma da ruwa fa har minira,

A dukansu a kwalba al’umma.

 

9. Kwalba mai giya haramun ce,

Amma mai ruwa halali ce,

Mai zuma kuma magani dace,

Ga zaƙi ga waraka kuma ma.

 

10. Wannan ne hukuncin waƙa,

In ka ɗau zance ka sassaƙa,

In mai kyau ne ya cece ka,

In yai muni akwai rigima.

 

11. Waƙa na kai mutum fa wuta,

Idan a cikinta yai wauta,

Tana kuma kai shi aljannata,

Idan a cikinta yai salama.

 

12. Ko me ka faɗi cikin waƙa,

Da shi za ai hukuncinka,

In alkairi ka sassaƙa,

In sharri ne da shi shi ma.

 

13. Waƙa aiki na ilmi ne,

Jahili bai yin ta kun gane,

Ko mai ilimi sai yai aune,

Ya cika ta da tsantsar hikima.

 

14. Waƙa na kau da yin yaƙi,

Tana sa wa cikin sauƙi,

Samun ‘yanci fa ba yaƙi,

Tana ɗaga yarenku sama.

 

15. Duk yaren da babu mai waƙa,

Akwai wahala ya ɗaukaka,

ƙasa yaren da ke waƙa,

Sai ya fi na sauran hawa sama.

 

16. Shugabannin ƙasa suna waƙa,

Muhammad Wardi yai waƙa,

Jibson Gwarma yana waƙa,

Manyan malamai suna waƙa,

Sahabbai ma suna waƙa,

Abubakari mai waƙa,

Umar shi ma yana waƙa,

Usuman shi ma yana waƙa,

Imamu Ali yana waƙa,

Annabi ya sa a mai waƙa,

Da mai waƙar yai waƙa,

Allah ya ji dadin haka,

Yai mai kyauta da aljanna,

Allahu ka sa da mu mu ma.

Waƙa a ƙasar Hausa

Post a Comment

0 Comments