Ticker

6/recent/ticker-posts

Jakin Madugu: Darasi Ga Kowa

Da La'asar sakaliya, Madugu ya dawo daga birni bayan ya sayar da iccen da ya labta wa jakansa. Ya kwance musu shimfiɗa, ya ba su ƙurari suka sha, sai ya yi musu dabaibayi ya kora su bayan gida domin su ɗan taɓa kiwo, shi kuma ya shige kudandaninsa ya mimmiƙe.

Yana nan kwance yana ƙidayar tanka, sai ya ji gigib a bayan gida. Ya zabura da sauri ya zagaya don ya ga abin da ke faruwa, sai ya ga ashe gohonsa ne garɗin ciyawa ya ja, ya faɗa rijiya. Ya ruga ya kira maƙwabta domin su taimaka masa.

Da suka taru, suka yi cirko-cirko suna tunanin yadda za su fiddo jaki. Suka yi tunanin duniyar nan suka rasa dabara. Sai Madugu ya ce, "kai, da wahalar banza bari kawai a cike rijiyar da shara. Don jaki guda dai na sayi wani idan Allah ya kai mu amaryar wata."

Sai ya tafi wata tsangaya ta almajirai ya ɗebo su, ya nuna musu rijiya ya ce su cike masa ita da shara. Yara suka fara kwaso shara daga bola suna antayawa cikin rijiya.

Allah da ikonsa sai ya ba jakin nan wata dabara, duk sa'adda aka zuba masa shara sai ya girgije jikinsa sharar ta zube ƙasa ya take. Ana watsa masa shara yana kakkaɓewa yana takewa. Ana haka, ana haka, shara ta fara tasowa sama tare da jaki. Can gab da Magariba, yara sun kusa cike rijiya, sai aka ga jaki ya yiwo tsul ya fito waje. Aka yi ta mamaki.

To, jaki ma ke nan ya samu dabarar kakkaɓe shara daga jikinsa, ya mayar da ita tsanin cin nasara, to ina ga kai ɗan Adam? Kul ka bari matsalolin duniya suka lulluɓe ka, suka hana ka ci gaba. Maishe su shara ka kakkaɓe su ka take ka yi gaba, tamkar dai yadda jakin Madugu ya yi.

Jakin Madugu

Daga

Bukar Mada
08/08/2022

Post a Comment

0 Comments