Bisa ga bayanin masana irin su Muhammad (1978 da 1979 da 1980) da ‘Dangambo(2007) da Sa’id(1981 ) da Yahya(1997) da Gusau(2014) wak’a ta kasu kashi biyu ne wato ta Baka da Rubutatta kuma kowace da irin nata

 ___________________________________
DAKTA BELLO BALA USMAN
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
080 27459617
___________________________________

 GABATARWA


Bisa ga bayanin masana irin su Muhammad (1978 da 1979 da 1980) da ‘Dangambo(2007) da Sa’id(1981 ) da Yahya(1997) da Gusau(2014) wak’a ta kasu kashi biyu ne wato ta Baka da Rubutatta kuma kowace da irin nata sigogin da suka bambanta ta da ‘yar uwar tagwaicinta. Akwai sigogi  na tarayya da suka wajaba a same su a kowace wak’ar Hausa ta baka da wadda ake rubutawa. Sigogin sun had’a da jigo da tsari da kari da reri da za’ben kalmomi da hikima; wad’anda sai an same su kafin wak’a ta amsa sunanta na wak’a ga Bahaushe Yahya(2010).

  • Lallai ne ya kasance wak’a tana d’auke da wani sak’o da ake son isarwa ga jama’a. Misali ko sak’o na siyasa ko na soyayya ko gargad’i ko zambo da sauransu.

  • Haka ma tilas sai an zuba tunanin nan cikin irin siffar wak’a wanda ya bambanta da misalin zube ko wani sak’on da ba na wak’ar ne ba.

  • Sannan sai an za’bo kalmomin da za a yi amfani da su, an tace su domin su hau irin tsarin da yake na wak’ar ne.

  • Haka ma dole kalaman nan da aka had’a ya kasance ana iya rera su bisa ga wani sautin murya irin na wak’a ba wai a fad’e su kawai kamar yadda ake magana ko zance na yau da kullum ba.

  • Sai an samu kari ko baharin da za a gina wak’ar a kan sa.

  • A k’arshe lallai ne tsarin da za a yi na maganar nan ya kasance ya k’unshi wata hikima ta rayuwa ko kuma hikimar harshe wadda da an ji ta an san cewa an yi wa kalaman wani tsari mai burgewa.


Nazarce-nazarcen da magabata suka yi ya tabbatar mana cewa tun can inda aka fito wak’ok’in Hausa na baka da ka ake yin su, su kuwa rubutattu da alkalami da takarda ake rubuta su. Wato su rubutattu na masu ilimi ne wad’anda ke da wata k’warewa ta rubutu da karatu akasin masu yin ta baka wad’anda su ba sai suna da wani ilimi na karatu da rubutu ba. Masu wak’ar baka suna sarrafa wata baiwa ce da Allah ya ba su ta iya shirya magana mai dad’i da hikima. Su kuwa masu rubuta wak’a bayan baiwar da Allah ya yi musu na iya tsara wak’a, suna kuma da ilimin rubutu da karatu.

Tun can inda aka fito lokacin da Bahaushe ya fara tsara tunaninsa na wak’a a rubuce, aka zo k’arni na goma sha bakwai inda muke da dahir na samfurin irin wak’ok’in da suka fi ko wad’anne tsufa a k’asar Hausa, har aka zo ga k’arni na goma sha takwas da na sha tara lokacin da aka samu tarin wak’ok’in da malaman jihadi suka rubuta, har aka zo k’arni na ashirin inda aka kai ga samun rubutattun wak’ok’i na boko a bisa ga wannan fasali muke. Wato wak’ar da ake rubutawa ta bambanta da ta baka.https://www.amsoshi.com/contact-us/

RUWA-BIYU


Allah cikin ikonsa ya yi halittu jinsi-jinsi kuma iri-iri misali akwai mutane bak’ak’en fata da farare. A tsarin yad’uwa bak’i kan haifi bak’i ne, haka shi ma farar fata ‘ya’yan da kan fito daga tsatsonsa farare ne. To amma idan fari da bak’i suka had’u, sukan samar da ‘ya’yan da ba fari ba kuma ba bak’i ba. Irin wad’annan ne ake kira ruwa-biyu ko barbarar yanyawa. Ko a dabbobi ma idan aka had’a misali rago da akuya suka yi barbara ko aka had’a ruwan halittarsu, abin da za a haifa zai zama baina-baina ne; shi ba dangin awaki ba kuma ba na tumaki sak ba. Haka ma a duniyar kimiyyar k’ere-k’ere yanzu an kai ga k’irar ababen hawan da suna iya aiki da fetur a matsayin makamashi, kuma ana iya amfani da makamashin lantarki ko hasken rana don sarrafa su. Wad’annan irin ababen sufuri su ne ake ce ma hybrid a Ingilishi, kalmar da kuma ake kiran abubuwan da aka ambata tun farko.

Irin wannan cigaba ne ya samu wak’ok’in Hausa a k’arni na ashirin da d’aya; domin a yanzu ana samun wak’ok’in da suka had’a sigogin wak’ar baka da na rubutatta. Idan aka nazarce su sai a iske suna da sigogi wasu daga cikin sigogi tara da Sa’id(1978) ya yi bayanin an san rubutattar wak’a ke zuwa da su kamar amsa-amo (k’afiya) da mabud’i, sannan kuma a ga suna da wasu sigogin da aka san na wak’ar baka ne kamar kar’bi da rashin daidaiton d’angwaye. Aikin Chamo(2010) ma ya yi nuni da cewa an samu sauyi a zubin wak’ok’in k’arni na ashirin da d’aya. To irin wannan sauyi ne nake ganin ya d’auki siffa ta had’akar sigogi a wak’a d’aya wanda a nan na kira ruwa-biyu.

IRE-IREN SIGOGIN WAK’OK’I RUWA-BIYU


Wak’ok’in nan na k’arni na ashirin da d’aya suna da sigogi daga dukan ‘bangare biyu na wak’a. Duk da yake har yanzu ana samun wak’ok’i rubutattun da na baka kamar yadda aka san su tun can da amma mafi yawancin wad’anda ke tashe yanzu suna zuwa da wannan sabon zubi na ruwa-biyu. Wato a irin wad’annan wak’ok’in sai mai nazari ya ga yana da matsala wajen yanke shawara. Idan aka ce rubutatta ce to yaya aka samu sigogin ta baka kamar kid’a da amshi da kar’bi a cikinta. Kuma idan aka ce ta baka ce to yaya za a yi da sigogin rubutattar wak’a da suka fito fili ‘baro-’baro kamar mabud’i da amsa-amo da k’ayyadadden zubin ga’bo’bin layuka da na baiti, duk da yake wannan zubin ga’bo’bi yakan wuce k’a’idojin rubutattar wak’a? Sai dai ana iya lura da cewa ana iya samun mawak’i/mawak’iya d’aya da za a iya kasa wak’ok’insa/ta gida biyu. Kashi d’aya na wak’ok’in baka kacokam, kashi d’aya kuma na wak’ok’i ruwa-biyu.[1]

Daga cikin sigogin da ake samu a cikin wak’ok’in nan da ke nuna cewa su ruwa-biyu na akwai:


KI’DA


Amfani da kayan kid’an gargajiya ko na zamani ya zama wata siga da ta karad’e wak’ok’in da ake yi a zamanin nan. Yanzu kusan a ce dukkanin wak’ok’in suna d’auke da wani nau’i na kid’a, wato kid’an ma shi ne za a fara ji kafin ma a soma wak’ar. Kamar dai yadda yake a wak’ok’in baka inda sai mawak’i shi kad’ai ko tare da makid’ansa sun tsayar da irin kid’an da za su yi wa wak’ar sannan a fara ambaton kalaman wak’ar.To haka yake a yanzu amon kid’an za a fara ji kafin a ji wak’ar d’auke da sak’on da aka yi niyyar isarwa.

AMSHI


Siga ta biyu da ake amfani da ita a wak’ok’in ita ce ta amshi. Yahya(1997) ya bayyana da cewa “Amshi d’ango ne ko d’angogi da ake maimaitawa a-kai-a-kai cikin wak’a, ko da yake akan sami rubutacciyar wak’a mai amshi, amma wak’ar baka ce ta fi shahara da wannan tsari.” Shi kuwa Gusau(2008) ya nuna cewa “akan ra’ba ma wak’ok’in kid’an fiyano wani amshi irin na wak’ok’in baka kai tsaye.” Ba wak’ok’in fiyano kad’ai ke da amshi a wannan zamani ba hatta wak’ok’in ruwa- biyu na madahu da na siyasa da na wa’azi duk suna d’auke da wani nau’i na amshi. Yanzu ma yana da wuya a samu wak’ar da ba ta da amshi. Misali a wak’arsa ta Baubawan Burmi Aminu Ladan Abubakar (Alan Wak’a) ya yi amfani da amshi kamar haka:

Baubawan burmi,

Kasassa’barmu ce kan za’ben jagora,

Iye-iye.

Shi kuwa Yakubu Muhammad a wak’arsa ta Zumunci an yi amfani da amshin:

Shi zumunci yana k’ara kusanci k’warai,

Ai zumunci yana harhad’a kan ‘yan uwa


KAR’BI


Wak’ok’in sun yi tarayya da wak’ok’in baka wajen amfani da kar’bi; wani irin nau’i na amshi inda masu amshi ke yi wa jagora cikon wata magana da ya fara bayan kalamansu na amshi da suke maimaitawa King(1981). Misali Nazir ya samu kar’bi a wak’arsa ta Sardaunan Ganye:

Jagora: In na ce Bismillahi

Kar’bi: Shi Rabbana in ka kira shi

Ba zai bar ka ba sai ya dafa

Jagora: Ku taya ni da rok’onsa

Kar’bi: Allah ka d’aukaka wak’ar tamu, sannan ka d’aukaka mai wak’a

Ka d’aukaka mai wak’a sannan ka kyautata k’arshensaA wak’arsa ta Sama Cibiyar Nisa Ado Gwanja an yi amfani da kar’bi a wasu wurare misali kafin ya k’arasa wak’ar ya samu kar’bi kamar haka a wak’ar.

Jagora: Yara iye dutse, dutse ba rabon gara ba

Mai amshi: Yara iye dutse, dutse ba rabon gara ba.

Jagora: Mata ku ringa takawa

Mai amshi: Dushe ba rabon gara ba

Jagora: Ku yo rausaya, ku ringa juyawa

Mai amshi: Dutse ba rabon gara ba

Jagora: Idan kun yo farin ciki ku  nunawa

Mai amshi: Dutse ba rabon gara ba.


KAR’BE’BENIYA


Kamar yadda ake samu a wak’ok’in baka su ma wak’ok’in zamani suna cike da wani irin nau’i na amshi wanda ake kira kar’be’beniya King(1981). A kar’be’beniya tamkar hira ce za ta wanzu tsakanin jagora da masu amshi. Ko kuma jagora ya yi tambaya su amsa masa. An samu misalin irin wannan a wak’ar Ajnabi ta Nagudu:

Jagora: Yau gari ya yi wayewa, bak’o a gidanmu ya sauka

Kar’be’bniya : Eh

Jagora:  Shi nake ba ki labari, abokin da bai da tamka

Kar’be’beniya:  Eh

Kar’be’beniya :  Amini koko habibi mai tarin albarka

Kar’be’beniya : Eh

Jagora: Yarinta har ma girma, da ni da shi a ce sambarka

: Mun ga d’aukaka, so ya ha’b’baka

Kar’be’beniya :  A zaman juna, hak’uri ga tawakkali

Amshi: Ajnabi bak’o, zuciya na kai sak’o

So da shak’uwa, bai misaltuwa

Soyayya, sak’o ne mai asaliA nan za a lura cewa  baiti aka raba tsakanin jagora da mai amshin. Irin wannan salon kar’be’beniya ce Kabiru Yahaya Classic yake amfani da shi tsakaninsa da wadda take yi masa amshi.

Ga misalin baitocin wak’ar da Classic ya yi wa Garkuwan Kwatarkwashi Alhaji Mani Aliyu:

Jagora: Bungud’u mun san Allah mun san Annabinmu,

Mun yi karatun ilimi kuma bai gagarar mu,

Gwargwadon hali mun san mai gudunmu,

Kamar wane mun jigata da shi ya butulce.

Kar’be’beniya : Karanka’bau gona ban san mi za ka yo ba,

Hakin banza ba sa wa kuma ba hana ba,

Bungud’u kowa bai ce ma Allab bari ba,

Ba ka kwana Bungud’u sai dai kauce-kauce,

Jagora: Had da ni yai min k’aryar banza ta rago,

Da za ni haihu ya ce shi zai ba da rago,

Yai yi mini k’arya ya rufe kainai da bargo,

Kai wa maza k’arya balle ni ta mace.

Kar’be’beniya : Dama inda yak’ k’ware wajjen d’auke-d’auke,

Wanda yaw wahala gunka ka bar shi tanke,

K’urungun Bungud’u an saba da bugun fatake,

Ga shi Gwamnanai ya hana ‘yan sace-sace.Wani fitaccen salon kar’be’beniya shi ne wanda Aminu Ala da El Mu’az da Yahaya suka yi amfani da ita a wak’ar Haka Allah Yas So.

AMSA-AMO


Daidaita ga’bo’bin kalmomi a baiti a farko ko tsakiya ko k’arshe, wata fitacciyar siga ce a rubutattun wak’ok’i. Wak’ok’in nan na k’arni na ashirin da d’aya sun d’auki wannan tsari inda suke k’ok’arin daidaita irin ga’bo’bin da ke a k’arshen baitocin wak’ok’insu, wani lokaci har su yi amfani da sigar inda ba ta dace ba.

A wak’arsa ta K’urunk’us Dauda Kahutu Rarara ya yi amfani da amsa-amon ciki da waje, kodayake bai cika amfani da irin wannan tsari a fitattun wak’ok’insa ba. Ga misalin:

Jagora: Biyan bashi dole ne ga dukkan mai hankali,

Halin kirki ya fi kyau, ga jagora adali,

Na tuba gurin Ilahu, na ce masa madali,

Ashe ba Malam ba ne, a boko ya sanar da su.

Amshi

Jagora: Sai wani Honorabul kwatsam, yaz zam malami,

Ashe wai zai takara ta Gwamna, ku ji tsegumi,

Sannan ni ban sani ba, sun sa ni cikin d’umi,

A yau ta kai ta ‘bare da shi, oho na ce da su.Ado Gwanja  ya bi irin wannan tsarin amsa-amon ciki da waje a wak’arsa ta Indosa:

Mai saurarona, bana sauti ya sauya,

Fad’a wa mai fafe gora, yau ce ranar tafiya,

Ado Gwanja ne, ga wani baiti na shirya,

Mai dukan sauti, buga ganga mu yi taken a sha ruwa-ruwa.

Ado Gwanja ne, na Aminun Dawayya,

A sauya salon tako, tun da kid’ana ya sauya,

Lokaci in har zai zo maka ba ya bari sai ka shirya.

Mai saurarona, don jin dad’in gangar, bi ni mu je fagen rawa.

Ayye, Wasu nij ji suna magana, wai mata muka wa wak’a,

Kuma in na kad’o sautin, har da mazan sai sun taka,

Kai ya zama dole iri, za ya fito ranar shuka,

Sai doki ya kai doki, a kwalliyatai za ka jiyo k’arar k’ararrawahttps://www.amsoshi.com/contact-us/


ZUBIN LAYUKAN BAITI


K’ayyade layukan baiti fitacciyar siga ce a rubutattun wak’ok’i. ‘Dangambo(2007) An saba da zubin gwauruwa (mai layi d’aya) da ‘yar tagwai (mai layi biyu) da k’war uku (mai layi uku) da k’war hud’u ( mai layi hud’u) da k’war biyar (mai layi biyar) da tarbi’i (mai layi biyu ga asali wani ya k’ara mata biyu ta koma hud’u) da tashd’iri mai kama da tarbi’i, amma ita raba baitin asali biyu ake yi, kowane d’angon asali ya sami k’arin d’ango. Ta haka sai wak’ar ta ri’banya baitoci; idan wak’ar asali an san ta da baiti goma sai ta koma mai baiti ashirin saboda tashd’iri da aka yi mata da kuma tahamisi (mai layi biyu ga asali, wani ya k’ara mata uku ta koma biyar). A bisa ga wannan tsarin ake sai da aka zo wannan zamanin inda aka sake fasalin layukan baiti kamar yadda Chamo (2010) ke cewa: “Zubin wak’ok’in k’arni na 21 ya sha bamban da na wak’ok’in k’arni na 19, da na 20 ta fuskar yawan layuka a baitoci” Misali ana samun wak’a mai layi shida-shida a baiti ko ma fiye. Dubi yadda Fati Nijar ta yi a wak’ar Ka Yi Mun Gani:

Jagora:  Rabbi tutil mulki, kai kad’ai ne mai bayarwa,

Dukkan lamarina, ni da kai nake yin farawa,

Sallama ga Ma’aiki, Mak’urar kyau gatan kowa,

Alihi sahabai, mai nagarta nai gaidawa,

Duk wanda ya bi su, shi ne za yai dacewa,

Mu kama salati da hailala, a Jigawa ba za mu fad’i ba.

Amshi:

Jagora: Jama’a ta Jigawa, mata da maza duka kowa,

Ni Fati Nijar, sallama nai k’arawa,

Ga ni d’auke da sak’o, wanda na san zai burgewa,

……… Zannan adali yau nai d’aukowa

Jigo kuma ango, mai kishi gun talakawa,

Sule Lamid’o d’an halaliya, namijin gaske, gamji jagaba.

Amshi.

Jagora: Addu’a talakawa, mun yi Allah yai amsawa,

Matsaloli sun kau, mun ga haske yau a Jigawa,

Samun managarci, zuciya tasa tsaf kyakkyawa,

Gwamna Sule ya zo, alkhairi yai kawowa,

Ba ma kokwanto, mun gani kuma mun shaidawa,

Zuciya hankali ta yi kewaya, a Jigawa yau babu fargaba.

A wak’ar Dauda Kahutu Rarara “Masu Gudu Su Gudu” ya yi amfani da tsarin mabambantan layukan baiti domin an samu baiti guda d’auke da layuka fiye da goma, wani baitin ya k’unshi layi goma, wani tara a cikin wannan wak’a. Dubi wannan baiti:

Assalamu alaika salam jama’a na k’asa barkanmu haka,

Ga Rararan wak’a na Kahutu gida kun shaida haka,

Jami’a gonar wak’a in ka mana adalci mu maka,

Ana maganar canji APC sai ta kar’bi duka,

In kai maganar turmi kowa ya san aikinshi daka,

Shi injin Tahuna an fi yi masa lissafi da nik’a,

Ita PDP tim’bir muka ce za ai kuma an yi haka,

Mun hallaka PDP a saman da k’asan mu ne da d’aka,

A kasa, a tsare, a raka in ji Baba Janar shi ne waraka,

Yau ga canji ya zo, APC kullum na ha’baka,

Yau dai mu ne da tuwo, mu ne da miya, mu ne da duka,

Janaral na talakawa ko Turawa sun shaida haka,

Buhari muke magana in ji Rarara Allah ya rik’a,

Talakawa sun ce addu’ar da sukai ta kar’bu duka,

Janaral ya kar’bi sama, Allah taya ka rik’o addu’ar talakawa.Haka aka lura da irin wannan tsari a wak’ok’in Kamilu Gashuwa kamar “Gafara Koko” da ma sauran masu wak’ok’in zamanin nan.


SHARAR FAGE


Wani sabon zubi da aka lura da shi a wak’ok’in k’arni na ashirin da d’aya shi ne na sharar fage, inda mai wak’a zai bud’e wak’arsa da wani abu kafin ya koma ga zubinsa na rubutacciya mai k’war hud’u. Dubi yadda Dauda Kahutu Rarara ya share fage a farkon wak’ar “K’urunk’us” da cewarsa:

Amshi:  K’urunk’us, Kwankwaso ya firgita su,

Allah ya kawar da su,

K’urunk’us, a za’be an ka da su,

A kotun an ka da su,

Kwankwaso ya tarwatsa su,

Allah ya kawar da su.

Jagora:  Tawassul ga Allah da yai wawa yai gwani,

Yai Dauda Kahutu Rarara tun tuni,

Yai Abdullahi Gwarzo bawan Allah da ni,

Yai Rabi’u Kwankwasonmu shi ne yai ‘Dangwani,

Yai Sadiyya Lawal cikin Fagge mu yi zamani,

Yai Titi ‘Dandamargu gemunsa daban da su.

Amshi:

Jagora: Salati marar addadi gun khairul anbiya,

Manzona ‘Dan Amina haskenka ya zagaya,

Har ahali har Sahabu su duka zan bayyana,

Har Sharifai suna ciki ban manta da su.

Amshi:

Jagora: Biyan bashi dole ne ga dukkan mai hankali,

Halin kirki ya fi kyau da jagora adali,

Na tuba gurin Ilahu na ce masa madali,

Ashe ba Malam ba ne a boko ya sanar da su.

Amshi:

Sai wani Honorabul kwatsam yaz zam malami,

Ashe wai zai takara ta gwamna ku ji tsegumi,

Sannan ni ban sani ba sun sa ni cikin d’umi,

A yau ta kai ta ‘bare da shi koko na ce da su.

Amshi:

Jagora: Batun shari’a an gama ina wani mai tsegumi,

Da na ji gunaguni da sa jama’a zullumi,

Sun tattara dukkanin bayanansu na tsegumi,

Da d’ai d’ai aka ya da su.


MABU’DI 
Wani abin lura a wak’ok’in k’arni na ashirin da d’aya shi ne sun rik’e al’adar nan ta rubutacciyar wak’a ta sanya mabud’i a wak’ok’insu. Misali Alan Wak’a ya bud’e wak’ar “Baubawan Burmi” da cewarsa:

Jagora: Allah malikal mulki,

Tutal mulki man tasha’u a kan mulki.

‘Yan amshi: Iye-iye

Jagora: Allah mun yi zaman dirshan

Tamkar fittila a lokon alkuki.Mafi yawan wak’ok’insa sukan fara da mabud’I, wato ambaton sunan Allah, wani lokaci har da yin salati.

Dubi yadda Nura Oruma ya yi wa wak’arsa ta Umar Mai Akwai S/Tudu Turakin Jabo mabud’i bayan ya ba mai yi masa amshi  amshin wak’ar kamar dai yadda aka san mawak’an baka na yi  a farkon wak’ok’insu :

Jagora: Mai Akwai S/Tudu

‘yar Amshi: ‘Yan Jabo kun yi dace da Turaki

Jagora: Ga zama lafiya

‘Yar Amshi: Bajinin Atiku ne Gagara-gasa

Gidan Sarkin ‘Burmi Jabo yau an yi nad’insa

Jagora: Rabbana Allah Wahidun Gwani na yi kiranka

‘Yar Amshi: Saraki mai martaba

Jagora: Kai ne kad’ai guda ba ka da tamka

‘Yar Amshi: Mai Akwai S/Tudu

Jagora: Kai kay yi mai kud’i kay yi talakka

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora: Ga abin da kan nufa wa ka hana ka?

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Jalla ka taimaka du’a’inmu ka amsai

Amshi:

Jagora: In Ilahi ya yarda duniya wa ka hanawa?

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Da ya furta KUN mutum zai ta d’agawa

‘Yar amshi: Mai Akwai S/Tudu

Jagora: Mai kushe da hassada ba ya iyawa

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora: Idan yai wa  d’an Adam tarin baiwa

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Bishiyarsa nan da nan za ta yi rassai

Amshi:

Jagora: Rabbana mik’a salati inda d’an d’a ga Amina

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Manzon da ke hanawa a yi ‘barna

‘Yar Amshi: Mai akwai S/Tudu

Jagora: Mahamudu duniya shi fittila na

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora: Alaye da Sahibai sun shiga raina

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Da Sheikh Ussumanu ma ba ni cire mai

Amshi:

Jagora: Babu tababa sallama ado ce ga musulmi

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Jagora: Duw wanda yai yi zai so ya ji amin

‘Yar Amshi: Mai Akwai S/Tudu

Jagora: Jama’ar gari ku taso ku rik’a min

‘Yar Amshi: Ku sha zama lafiya

Jagora:  K’asar  Jabo, fada nis so a gwada min

‘Yar Amshi: Turaki mai martaba

Gidan Sarkin ‘Burmi Jabo, in gane kalarsa


AMFANI DA SANK’IRA


Yin amfani da Sank’ira siga ce sananniya da aka san wak’ok’in baka da ita kamar yadda binciken Tsoho (2010) ya tabbatar. Sai ga shi  an samu shaiduddukan da ke tabbatar da ita a wak’ok’in nan na k’arni na ashirin. Suna amfani da sank’ira kamar yadda aka san ana yi a wak’ar baka. Misali Marigayi Umar Abdul’Aziz Baba Fadar Bege da aka sani da rubuta wak’ok’in ruwa-biyu na madahu ya yi amfani da sank’ira daga farkon wak’arsa Dad’in Duniya zuwa k’arshe:

Jagora: Jalla Mafi girma, gyara Jalla mafi girma

Sank’ira: Kai! Fadar Bege

Jagora: Jalla mafi girma

Sank’ira: Allah ke nan, mafi girma

Jagora: Allah mai kowaaaaaaaaaa, mai kome

Sank’ira: La’ila ha illallahu, Ka ji Lillahi Wahidun K’ahharu

Jagora: Jalla mafi girma

Sank’ira: Mak’agin Muhammadur Rasulullahi

Jagora: Sarkin daraja, Allah kai tsira ga Ma’aikina

Sank’ira: Allah da ya k’agi mutum da aljan, yai mala’ika da Annabi

Jagora: Yara duniya dad’i

Sank’ira: Allah da yai dabba yai tsuntsu. Annabi Muhammadu

Jagora: Duk dad’in duniya, mun san bai yi zama da Ma’aiki ba

Sank’ira: Sarkin Muhammadur Rasulullahi, ke nan, A’a!

Jagora: Yara duniya dad’i, duk dad’in duniya, kun san bai yi zama da Ma’aiki ba

Sank’ira: Annabi Muhammadu, kai duk dad’in zama bai yi zama da muhammadur Rasulullahi ba

Jagora: Allah Rabbi nike sawa, mai mulki da abin mulka

Sank’ira: Mai mulki da abin mulka, Muhammadur Rasulullahi

Sank’ira: Kai! Duk dad’in duniya, bai yi dad’in zama da Muhammadur Rasulullahi ba

Jagora: Allah Rabbi ka dafa man, kullum kai nika wa kuka

Sank’ira: Annabi Muhammadu, Allah kai muke rok’o

Jagora: Zuljalali abin bauta, amsa min da abin rok’a

Baituka ne zan wa Annabi, ban tsaro su da wasa ba

Sank’ira: Eh! Baituka za mu yi wa Muhammadur Rasulullahi

Jagora: Allah mai kowaaaaaaaaaaaa mai kome, Jalla mafi girma

Sank’ira: Eh mana! Sha kira da baiwa

Jagora: Sarkin daraja, Allah kai tsira ga Ma’aikina

Sank’ira: Allah kai tsira ga Annabin da babu irinsa

Jagora: Yara duniya dad’i, duk dad’in duniya kun san bai yi zama da Ma’aiki ba

Sank’ira: Annabin da ba shi da farko ba shi da k’arshe

Annabin da shi kad’ai ne a gaba, babu wani a bayansa.Irin wannan salon amfani da sank’ira ne Ali Jita ya yi a wata wak’arsa da yake lissafo abokan sana’arsa d’aya bayan d’aya Baba Ari yana k’arin bayani a kan duk wanda aka kira cikin mawak’an nan.

KARI


A wajen za’ben kari ko bahari ma za a lura da cewa wak’ok’in nan sun raba k’afa domin akwai wad’anda aka gina su kan Karin Aruli da kuma wad’anda aka tsara su bisa ga Karin wak’ok’in baka. Fitaccen misali shi ne wak’ar Dad’in Duniya ta Madahu da Fadar Bege ya d’ora a kan Karin wak’ar Sani Sabulu mai wannan sunan. Haka ma wak’arsa ta Babba ‘Dan Babba aron karin wak’ar Sa’adu Bori na Nijar ya yi ya tsara tasa.

Jagora:  Manzon Allah Babba d’an Babba

‘Yan amshi: Manzon Allah Babba d’an Babba

Jagora: Kai nike kira Sarki

K’ara ban dubun tsarki

Nai shirin shiga aiki

Zan yabon Ma’aiki

Babba d’an Babba.

‘Yan amshi: Manzon Allah Babba d’an Babba

Jagora: K’ara yo salatinka,

Gun cikon Ma’aika,

Mai idon ganinka,

Shi kad’ai ya gan ka,

Babba d’an Babba.

‘Yan amshi: Manzon Allah Babba d’an Babba

Jagora: Alihi in sanya su,

Ham maza da matansu,

Na dad’e da k’aunar su

Dole ne in gaishe su,

Su kad’ai nake duba.

‘Yan amshi: Manzon Allah Babba d’an Babba


TSARMIN ‘DAN WAK’A


A cikin wak’ok’in nan na k’arni na ashirin ana samun inda ana cikin zubin baitocin rubutattar wak’a sai a tsarma wani d’an wak’ar baka. An ga irin wannan misali a wasu wak’ok’in Siyasa. Misali a wak’ar Aminu Isiyaku Rinji ‘Bagwai mai suna “PDP Tsumma Da Jini” wadda ya rubuta cikin zubin k’war hud’u a kowane baiti. Sai ga shi a baitin k’arshe na wak’ar ya sako d’an wak’ar baka ya rufe da shi haka:

In ba mu lafiya ba assibitin zuwanmu don kwantarwa,

Duka assibiti ba magunna da likkitan dubawa,

Mu ne muke zuwa mu tsumayi zuwa na mutuwar d’aukewa,

In ka ga shugaba a garinku siyasa fa ta dawowa,

Da sun ci k’urri’a shi ke nan mu da su fa sai gilmawa,

In ba su lafiya sai can a k’asar waje ake dubawa,

Batu na ilimi mu dagur-dagur muke ‘yan uwa,

Don babu ilimi ba yalwatas su malaman koyarwa,

‘Ya’yanmu ne suke hoririya a cikin ajin koyarwa,

Su ko suna fitar da d’iyansu k’as ashen waje koyowa,

Haka ci gaban yake? Ko ci baya tambaya amsawa,

Tambaya amsawa,

Tambaya amsawa,

Ina da mai shirin amsawa?

Ko da mai amsawa?Wani misali ya samu a wak’ar ALA ta Baubawan Burmi inda daga tsakiya ne ya kawo wani d’an wak’a wanda ya sa’ba wa tsarin da yake a kansa na rubutattar wak’a tun farko. Ga yadda ya zuba d’an tare mai amshinsa:

‘Yar Amshi: Ala mai fad’akarwa,

Da’in kukan kokawa,

Allah ne ke sakawa,

Sannan shi ke cirewa,

In ya so zai canzawa,

Ba mai ikon hanawa.

Jagora: Dole in koka da tsiwa,

Dubi k’asar nan Arewa,

Ba ilimu talakawa,

Ba mu da aikin ta’bawa

Mun zama jujin zubawa,

Tarkacen tarkatawa.An ga irin wannan tsarmin d’an wak’ar baka a cikin rubutatta a wak’ar Haruna Aliyu Ningi ta Shegiyar Uwa inda yana bisa ga tsarin k’war hud’u sai a tsakiya ya kawo wannan d’an:

Jagora: Tumburun buk’un

‘Yan amshi: Baba a sha maganin k’aba,

Jagora: Ina ake jik’on?

‘Yan amshi: Sai Nassarawa can garin Wamba,

Jagora: Da me ake zuwa?

‘Yan Amshi: Baba ka je da k’atuwar kwalba,

In ka nannaga, sai ka nufaci k’atuwar salga.
GAZA


Ita gaza wata ‘yar tsawa ce da mawak’an baka ke yi don su mayar da hankulan ‘yan amshi da makad’ansu ga aikin da ake yi na wak’ar, musamman idan suka ga wani abu na neman janye mataimakan daga wak’a.

To hatta irin gazar nan ta shigo cikin zubin wak’ok’in zamanin nan, inda za a rik’a jin suna ambaton kalmomi irin su ‘haba!’ ko ‘sama!’ ko ‘hayya kai!’

KAMMALAWA


Wannan mak’alar ta yi bibiyar cewa lamarin nazarin wak’ok’in Hausa ya tabbatar da samuwar wak’a iri biyu ne; ta baka da rubutatta kuma kowace da irin sigoginta in ban da irin sigogin da kowacensu sai ta same su kafin ta amshi sunanta na wak’a.Amma sai ga shi a k’arni na ashirin da d’aya an samu wak’ok’in da ke da ruwa-biyu. Wato sun had’a sigogin ta baka da na rubutatta yadda za su iya fad’awa kowane kashi. Ire-iren sigogin da ke had’aka a wak’ok’in sun had’a da kid’a da amshi da kar’bi da kar’be’beniya da amsa-amo da zubin layukan baiti da sharar fage da mabud’i da amfani da sank’ira da kari da tsarmin d’an wak’a da gaza. To samun wad’annan a tare a wak’ok’in ne ya sanya aka yanken hukuncin cewa ruwa-biyu ne. Saboda suna da sigogin duka biyun yadda yana da wuya su tsaya a kashi d’aya kamar yadda aka saba gani inda aka fito.


MANAZARTA