Pi: Jerin Abubuwan Da Ake Buƙata Kafin Samun Damar Yin "Mainnet Migration" (Komawa Kafar Dindindin)

    A harshe mai sauƙi Mainnet (Kafar Dindindin) na nufin asalin kafar intanet da za a mayar da Pi ɗin da aka yi Mining (haƙa), wanda a can ne za a riƙa hada-hadar Pi ɗin. Misali, a can ne mutum zai iya tura Pi ga waɗansu ko kuma a tura masa. Kafin mutum ya samu damar komawa Kafar Dindindin, akwai abubuwan da suka wajaba a kansa da ya aikata waɗanda su ne za su ba da damar a masa KYC (Tantancewa). Ku biyo ni tiryan-tiryan. Abin ba wuya.

    Mataki na 1: Buɗe manhajar Pi ɗinka sannan ka danna ƙananan layuka uku na menu da ke kusurwar sama ta hannun hagu. Duba hoton ƙasa domin kallon yadda abin yake:

    Menu bar

    Mataki na 2:
     Nanna wurin da aka rubuta Mainnet. Ga hoton yadda yake a ƙasa:

    Mainnet



    Shi ke nan ka kammala! A nan za ka ga dukkannin abubuwan da ake buƙata domin yin KYC tare da samun damar komawa Kafar Dindindin.

    Duk matakin da ka wuce/kammala, to za ka ga an ja masa maki cikin koren launi. Waɗanda ba ka yi ba kuwa, wato waɗanda ake buƙata ka yi kafin komawa Kafar Dindindin, to za ka ga an yi musu alama da akwati mai jan launi. Duba misali a dogon hoton da ke ƙasa.

    Checklist

    A nan za a ga cewa, mafi yawansu an yi musu alamar akwati mai jan launi. Hakan na nuna cewa, mai akawun ɗin bai kammala su ba.

    Ka tabbatar da cewa ka kammala dukkannin waɗannan matakai domin samun damar yin KYC da kuma komawa zuwa Kafar Dindindin.

    A haƙi Pi lafiya!

    Click HERE to read this post in English.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.