Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Saki Matarsa Saki Uku Ararrabe, Shin Yana Da Damar Mayar Da Ita?

𝐓𝐀𝐌𝐁A𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Da fatan Malam yana cikin koshi lafiya

Ina da tambaya kamar haka: Abokina ne ya Saki matar sa shika ɗaya Sai aka daidaita ta dawo suka cigaba da Zama

Bayan wani lokaci mai tsayi sai wata matsala ta sake faruwa har ya sake ta Saki biyu a lokaci ɗaya, Bayan ta gama Idda sai yake shirin mayar da ita akan yaji fatawar wani Malami cewar wannan Saki biyu a lokaci ɗaya yana matsayin shika ɗaya. Malam mene ne gaskiya akan wannan fatawar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Gaskiya nidai ban san wani Saɓanin malamai game da wanda ya yi irin wannan sakin ba. Abin da na sani, kuma na karanta kuma na ji daga bakin Malamai shi ne duk wanda ya saki matarsa saki uku daban daban, sakin nan uku sun tabbata a kansa, babu wani saɓani.

Da ache saki ukun ya yisu ne a cikin lafazi guda, to shi ne wasu Maluman suke da saɓani a kansa, suna cewa ana ɗaukarsa amatsayin saki ɗaya. Amma shi ɗinma mafiya rinjayen Maluman Ahlus Sunnah wal jama'ah sun tafi tabbatuwarsa.

Tun daga kan mafiya rinjayen Sahabban Manzon Allah ﷺ har zuwa kan Maluman tabi'ai da kuma Shugabannin Mazhabobin nan guda huɗu duk sun tafi akan cewa saki uku cikin kalma guda saki ne na bidi'ah amma kuma ana tabbatar dashi akan saki uku ɗin.

Kamar yadda kuma duk wanda ya saki matarsa saki uku daban daban, ararrabe ɗaya bayan ɗaya, ko kuma ɗaya daban, biyu daban shima duk ana tanbatar dashi amatsayin saki ukun ne, babu saɓani.

Don haka babu damar komawa har sai bayan ta yi wani auren kuma sabon mijin ya yi cikakkiyar saduwar aure da ita.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments